EELHAM🌹

48&49

by @rabearhwakili

Episode 48 & 49📲





***






بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai




    𝐵𝐴𝑌𝐴𝑁 𝑊𝐴𝑇𝐴 𝐵𝐼𝐴𝑌𝐴𝑅


Abubuwa da yawa sun faru ciki hadda dawowar mubeena wata ɗaya da suka wuce sanadin ciwon mahaifinta.
  Bappi sun dawo suma wata biyu  kenan amma sun baro AS a chan dan akwai wani aikin da ya tsaida shi, 
    Bikin su Ruqqy saura kwana biyu tunda su bappi suka dawo aka kara tsaida date gashi yanzu sauran kwanaki biyu ya rage musu su amarce.
   Watan eelham biyar kenan  da yan satika da mutuwar auren ta zuwa yanzu ta kammala iddar ta tun last 2 month, watan ta biyu da sati uku kenan da kammala idda, 
  AS kuwa ana saka ran dowowarshi zuwa gobe ko jibi ranan daurin auren kenan.

_______ gida ya cika makil da mutane ba masaka tsinke yan Abuja ma sun iso ciki harda su Ummi, mufeeda, Sarah, Raihana, yusrah, ga ko wacce da cikin ta ɗan ɗass dashi dan sun kusa shiga watan haihuwa, inda su eely suka rinƙa jan su da niman magana wanda tun suna tankawa har suka haƙura dan sun kashe musu baki,

"Elham kije ummi tana kiranki" cewar Ruqqy da fitowar ta daga ɗakin ummi kenan sai wani ya mutse fuska take.
  Daukan hijab ɗinta tayi ta fito daga ɗakin tana shiga na ummi da sallama dauke a bakinta, falon Ummi cike yake da mutane har wani bai jin maganar wani, cikin jam'i ta gaida su tana shigewa cikin ɗakin ummi, 
   "Ummi gani"
"Ansa ki maza ki shanye ki bani cup yanzu".
   Cikin ya mutsa fuska dan maganin ɗaci ke gareshi tace "Ummi idan nasha fa amai yake son ya sani"
   "Eh ki dai sha shi hakanan koda zaki a mayar dashi! Kiyi maza kar maganin ya bi iska,ga kuma saura nan"
   "Cikin shagwaɓe fuska tace ummi dan Allah a rage yawan su"
  "Anƙi a rage! zaki sha ko sai na gwab je ki?"
   "Zan sha Ummi"
Bata kuma tanka mata ba ido kawai ta kawo ta zuba mata,
  ganin haka ne sai ta kafa kai ta shanye tana sauke kofin daga bakin ta, mikawa Ummi cup ɗin tayi tana kakarin amai, 
   "Ashe Allah yasa ki amayo da maganin nan kiga yadda zanyi dake a gidan nan"
   Cikin ya mutsa fuska tace "ummi  ɗaci ga kuma ya tsaya min a maƙoshi"
  "Karba kora da wannan zai wuce"
"Dan Allah ummi kiyi hakuri"
    "Ni mi kakayi min daughter! magani ne kuma gasu nan sha ya zama dole daman kinyi shiru da bakin ki"
    Karɓan na hannun ummi tayi wannan karan ba wasa ta shaye inda ummi ta ƙara dama mata wata da tasha madara ai nan fa ta buɗe baki ta shanye tas, na karshen ta miƙa mata wanda ya kasance fruit ne akayi blanding sai aka zuba madara a ciki, miƙa mata tayi tace "ga wanga na karshe duk da nasan ba sai na tirsasaki ba". Cikin dariya ta karɓa hadda su godiya nan take ta shanye tas tana haɗa cups ɗin da tasha magungunan.
   "Ko kefa! anjima ki kuma dawo akwai na rana" 
"Ummi dan Allah a barshi haka harshe na kaman zasu tsinke dan ɗaci"
   "Wuce ki bani waje tunda ku baku san gata ake muku ba sai nan gaba zaku gane har ma kuzo kuna nima"
   Ba shiri dariya ga kwace mata wai gata fa wai kuma zasu dawo,
"Ooh dariya na baki koh! Muna nan dake zaki bugo kice Ummi wannan maganin dan Allah a samo min"
    "Magani fa a'a!maganin mi nene Ummi?".
   "Maganin sanyi ne"
"Mun gode Ummi"
Cikin dariya tace "ai godiya sai nan gaba daughter".
  Cikin rashin fahimta tace "insha Allah"
  "Ummi bara naje zamu shiga mall nida su jawaher" 
  "Toh kuyi maza ku dawo kunga yamma ta yi! Ko da kun bari ma ko zuwa gobe idan Allah ya kaimu,tunda ba yau zaku yi amfani dashi ba"
   Cewa tayi "duk yadda kikace Bara naje na sanar musu".
    Ta tashi zata wuce kenan sai ga meenal ta shigo tana cewa "EElham daman kina nan su jawaher suna ta nemanki! da suka gaji kuma suka wuce sunyi tunanin ko kin fasa zuwa ne".
    "Na fasa,sai gobe"
Kedai kika sani! Gwara ma dai da suka wuce! Ga kuma Anwar can yana neman ki"
   Bata tsaya sauraran ta ba jin tace Anwar yasa ta fita babu shiri tana nufan part ɗin goggo,
  Babu wasu mutane a nan ɗin cikin jam'i ta gaishesu tana shiga cikin dakinta,inda ta samu Anwar a zaune saman gado hannun shi riƙe da wayar da AS ya bar mishi.
   Suna ganinta Anam ta fara ɗaga hannu tana washe yan haƙoranta masu haske guda shida itama da murmushi ta ƙara sa wajenta,daukan ta tayi ta hau wulwula ta ita kuwa sai dariya take. Saida eelham ta gaji sannan ta zauna tana maida numfashi, kallon Anwar tayi tana cewa "boy babu magana?".
   "Ba ke ce kika wuce kika barmu ba"
   "I'm sorry ba gashi na dawo ba"
Gaɗa kai yayi yana zuwa wajen su nan ta rinƙa yi musu wasa ka gansu gwanin sha'awa....


___________________
                                         𝑪𝑯𝑰𝑵𝑨
 sosai ƙasar China ya karbi AS yayi fresh sosai harda haske ya ƙara, aiki yake cikin nutsuwa da kwarewa wanda da ka kalli fuskar shi zaka gane yana cikin farin ciki dan yadda fuskar shi yake a sake ba kamar kullum ba.
    Tun satin da ya wuce yaso ya koma Nigeria saboda labarin da ya samu na gama iddar eelham a bakin meenal da take gaya masa, wanda shi bai ma san ta fito ba. Amma yanzu zuwa gobe insha Allah i War haka yana Nigeria sannan kuma meenal tana da babban kyauta.
    Gajiya da aikin da yake yayi,matsar da laptop gefe yayi ya jawo wayar shi yana dialing dayar number shi.

Suna cikin wasan da take musu taji wayar Anwar tana ringing, jawo wayar tayi dan taga wake kiran amma ganin an sa PAPA MHIE yasa ta gane baban Anwar ke kira dan da haka yayi saving number, Saida ta kusa katsewa sannan tayi picking tana daurawa Anwar a Kunni, cikin yin ƙasa da murya tace "papa" tashi tayi ta nufi waldrop.
   "papa?"
 "Na'am boy ina little?" 
     "Gata nan tana wasa"
   Shima yaji ɗuriyar ta cewa yayi "ykk ya gida ya school"
"Lfy papa! banje school ba umm tayi min taking excuse a school"
  Cikin son ya ja firan yace "to mi yasa?" 
  "Wai su Anty suna aure tace bazanje ba sai an gama"
  "Ok ina umm ta ke" kallan side ɗin da take yayi sannan yace "tana aiki"
   Saida ya sauke nunfashi sannan yace "ba ta"
   Daga inda yake zaune yace "umm papa yace a baki" yi tayi kaman ba taji abinda Anwar ɗin yace ba ta cigaba da aikin ta, Anwar Sarkin naci shi zatan shi ko bata ji bane yasa ya ƙara cewa "umm take"
   Ai ba shiri da juyo  ta na  danƙara mishi hara da dauke kai lokaci ɗaya. 
   "Papa ta ƙi"
"Kayi kuka sai ta karɓa"
Da yake shima Anwar  A ne nan ya ƙara miƙa mata wayar cikin muryan kuka yace "umm take" jin muryan shi ne kamar na mai kuka yasa ta juyo ai kuwa kuka zai farayi mata. Cikin dakiya ta kauda kai, shi kuwa Anwar ganin haka ne sai ya buɗe baki ya hau kuka sosai kamar wanda aka zagi iyayen sa.
   Aje kayan hannun ta tayi tana zuwa garesa ɗago shi tayi tana cewa "is ok! where is the phone?".
   Miƙa mata yayi Saida yaga tasa wayar a Kunni sannan yayi shiru, yana yiwa Anam wasa 
   Duk abinda suke yana jin su sai faman zuba murmushi yake
  Elham kuwa Shahada tayi sannan tace "Assalamu alaikum"cikin ƙasa da murya, jin sanyayar muryarta yasa ya sauke ajiyar zuciya kafin da kyar ya amsa da cewa "Wa'alaikis Salam" sosai muryan shi ya dake ta amma sai ta dake tana cewa "ina wuni yaya" 
   Bai amsa ba sai tambayar da ya wurgo mata yana cewa "mi yasa Anwar ya baki waya kika ƙi karɓa?".
   Cikin sanyin murya tace "ina aiki ne"
   "Uhm! Aikin da kike ba ya a jiyuwa?" Kin kulashi tayi idan ma bata karɓa ba ina ruwan shi.
   Katse mata tunani yayi da cewa "ina jinki"
     "A'a" 
"Ina fatan kayan su boy ya zama ready?"
   "sai gobe zan karɓo"
"Ok! Mi kike son na dawo miki da shi? 
   Cikin turo baki kaman tana gaban shi tace "babu"
    "Bazaki faɗa ba?"
   Cikin ɗan shagwaɓa wanda bata san tayi ba tace "seriously babu"
  Ok! ina kan hanya gobe, ki je wajen ummi ki karɓo key na mota ki bama mai wankin mota ya wanke! Shima part ɗina ki shiga ki gyara min,wajajen 4 zan sauka ina bukatar ganin su Anwar a airport kar kuma ki haɗasu da driver kinji ni"
   "Toh yaya wa zai kawo su?"
"Baki da ƙafa?"
   Sai ka a ramin taka amma a fili cewa tayi "amma yaya........" Katse ta yayi da faɗin "ban son musu kiyi yadda nace" yana gama faɗin haka ya datse call ɗin. 
  Bin wayar tayi da kallo tana mamakin karfin halin shi, ji yadda yake commanding ɗinta kamar wani ubanta,aje wayar tayi tana ci gaba da yin aikin ta,Saida ta gama ta ɗauki Anam suka fito daga ɗakin.
   Duk da ba yanzu zatayi gyaran ba sai zuwa gobe haka ta nufi wajen ummi,cikin kunya tace "Ummi yaya yace na karbi key na mota da na part ɗinshi na gyara mishi".
   Cikin basarwa kaman bata san halin da take ciki ba tace "ki buɗe bed side drawer akwai key  a caki sai ki ɗauka".
  Cikin jin nauyin ta da ya dirar mata lokaci ɗaya ta miƙe tana shiga cikin dakin ba jimawa ta fito hannun ta dauke da key sallaman Ummi tayi sannan suka fice daga ɗakin, Saida ta koma part ɗin goggo ta aje key sannan ta koma cikin yan uwan ta Anwar na manne da ita wani da bai san ta ba zaice ko yaran ta ne ko dan kamannin da suke....

_____________
                                     𝑲𝑶𝑮𝑰 𝑺𝑻𝑨𝑻𝑬
Gida ne dan matsakaici da gani kasan mutanan gidan talakawa ne tukub, sai dai suna da rufun asiri ba kaman sauran gidajen dake a layin anguwan ba.
   Tsakar gidan malale yake da cement wanda yayi luwai da gani mutanen gidan suna da tsafta. ɗakuna uku ne jere wands suka kasance falle ɗadɗaya sai yar langa langan kitchen ɗinsu amma komi na cikin shi a tsaftace yake babu wani datti ta chan nisa ban ɗaki ne guda ɗaya da ta kasance ba mai girma ba

Wata farar mata ce ta fito daga ɗaki tana gyara daurin ɗan kwalin ta, kitchen ta shiga ta hasa wuta tana daura tulun ruwan maganin da mallam yake wanka dashi,
 tana a nan tsaye har ruwa ya tafasa sannan ta dauko bucket ta juye ruwan tana aje shi daga wajen kitchen.
  Dayar ɗakin ta shiga bakin ta ɗauke da sallama dattijo ne a kwance akan tabarman kaba, da ganin wannan dattijon zaka san yana jin jiki.
 "Mallam sannu" 
  "yauwa tabawa! Allah yayi miki albarka".
   "Amin ya Allah! Daman nace ga ruwan nan na juye"
    Da yake akwai shi da juriya haka ya yunƙura ya miƙe yana mai dafe da bango har ya fita daga ɗakin, ita kuwa matar nan ta ɗauki ruwan ta kai mishi zuwa ban daki.
   Dayar ɗakin ta shiga babu komi a dakin sai katifa da kuma bagco ɗin kayayyaki a ƙasa
   "Ke mubeena baza ki tashi barci nan hakanan ba yamma tayi".
   "Dan Allah mama ki ɗan bari na ƙara koda na 1 hour ne".
   "Na hour 2 ne zaki ƙara, maza tashi"
    Cikin zumbura baki ta tashi ta fito daga ɗakin sai surutai take ita fa shi yasa sai tafi ƙarfin wata biyar batazo ganin gida ba,hakan baya wani damun. Dan gani take idan tazo takura mata ake.
   Tana zaune a nan mallam ya fito daga toilet yana bin bango ganin sa ne yasa ta miƙe da nufin taimaka mishi amma sai ya dakatar da ita da faɗin "karki damu zan iya" matsa mishi tayi haka dai ya zauna akan tabarman da aka fito masa dashi waje yana sauke nunfashi. 
    Mubeena ce tace "Sannu mallam! Allah ya ƙara sauƙi" da Amin ya amsa yana duban ta cikin rashin jin ƙarfin jiki yace "yaushe zaki koma gidan ki ne? Kinga ni jiki na da sauƙi".
   "Baya ƙasa yana China sai in ya dawo ne zan koma shine ya barni".
  Cikin gamsuwa yace "to shikenan kafin ki wuce kiyi kiran shi ki faɗa masa zaki zaga yan uwa idan ya bari sai ki shi shigar musu".
Tab itakam mi zai kaita shiga gidanjen nasu ai cewa zatayi Ahmad bai bari ba idan tace haka tasan bazai ƙara magana akai ba a zahiri kuwa cewa tayi "insha Allah mallam zanyi mishi magana daman na daɗe ban shiga wajen su ba".
   "Allah ya bada iko"
  Da Amin ta amsa suna cigaba da fira.
Baban mubeena kenan mallam bilyaminu tare da mahaifiyar su zuwaira, mubeena tana da yayu guda biyu itace ta uku daga ita sai auta.
Mahaifin ta ya kasance dan kasuwa wanda AS shi ya bashi jari,da yake mutumin kirki ne dakyar ya amsa kudin shine yaje ya kama shago a kasuwa yana Saida su hatsi.
   Mubeena ta kasance tana bala'in tsoron mahaifin ta dan ya kasance mutum ne mai tsauri wajen kula da tarbiyan yaransa
   Yayun mubee duk mata ne kuma sunyi aure tuni mubeena da autan su ne akayi musu aure a rana ɗaya.

"Mallam ga maganin nan"
"Toh sannu tabawa Nagode"
Mama ce ta dubi Mubeena tana cewa "Mubeena tashi kije kiyi talge karkuma ki cika gari"
   Tashi tayi ta shige kitchen tana yi tana ƙunƙugumi hardai ta saki ta kama aiki bilhakki....


____________
                                𝑾𝑨𝑺𝑯𝑬 𝑮𝑨𝑹𝑰
 part ɗin AS ta shiga dan ta gyara,
   Ɗakin ba wani datti yayi ba dan ummi ta na saka meenal gyaran shi akai akai,
    kitchen  ta shiga ta kwaso abin shara.
  Gyara part ɗin tayi yayi tsaff sai walƙiya yake bayan ta gama sai ta kunna burner, da tularen wuta na itace nan da nan dakin ya rikice da kanshi sai ta kunna ac dan ɗakin ya dauki sanyi, bayan ta gama duk abinda zata yi ne ts kulle kofan da key, part ɗin goggo ta koma, shiga  kitchen tayi dan haka kawai taji tana son tayi mishi wani abun,
  Duba abinda babu tayi tana yin list ɗinsu ATM ɗinta ta dauko ta fito daga ɗaki tana nufan wajen driver tana cewa  "Mallam idi dan Allah ka  taimaka ko bakin kasuwa ne ka ɗan siyo min su".
  "A Hajiya ai ba komi"
Karba yayi yana wuce wa wajen mota, maida duban ta tayi ga mai yi musu wankin motan tace "mallam lado an kammala wanke motar?". 
   "Eh Hajiya yanzu nake gamawa ga ma makullin nan".
  "Sannu da aiki na gode" tana karɓan key ɗin tayi ciki dan ta cigaba da aikin ta.
   Jawaher ce ta shigo kitchen hannun ta dauke da ledar bayan ta kuma mufee ce da ɗan cikin ta da yayi mata ɗass.
   "Shi yasa naji gidan nan sai tashin kamshi yake ashe cheaf ce da kanta a kitchen yau" cewar mufeeda dan sunyi catering class lokacin da suke karatu a Sokoto.
   "Mai ciki! kece tafe ashe shi yasa na rinƙa jin kukan jarirai ashe kina hanya". Cewar EElham 
  "kin manta ba mai ciki ba mai tumbi! Ni dai wa ake shirya ma wannan better?".
    "Ban sani ba".
Jawaher kuwa da sai da ta gama buɗe buɗen ta sannan tace "EElham ga shi malam idi yace a kawo miki".
    Godiya tayi mata sannan ta buɗe ledar tana ciro kayan ciki, Saida ta gama fidda komi sannan tace "mallamai kunyi min tsaye a kai"
    "A'a ba sai kin yi mana kora da hali ba muma akwai abinda muke daman wajen goggo aka aiko mu"
Taɓe baki kawai tayi ba tare da ta ƙara ce musu komi ba,su kuma suka fita daman ba zama ya kawo su ba dan har sun fita suka haɗu da driver a ƙofa shine yace su miƙawa eelham shiyasa ma suka dawo.
   Cikin nutsuwa da kwarewa ta rinƙa aiki Anwar yana taya ta da surutu dan bai yadda yaje ko ina ba itama ta hana sa fita wai kar yaje azo kuma ana niman shi, 
   Ba ita ta kammala abincin da take ba sai karfe 2:30.
   jera cooler da ta zuba abinci tayi cikin baske mai girma ga ya haɗu anyi mishi kwalliya mai burgewa, daukan basket ɗin tayi ta fito ta shiga ɗakin ta dashi dan bata isa ta aje shi anan ɗin ba.
    Shirya su Anwar tayi bayan ta ƙara yi musu wanka inda  ta saka musu kayan kanti masu kyau da tsada, sosai sukai kyau aje Anam tayi ta shige toilet dan yin wanka,
  Ba jimawa ta fito,zama tayi a dressing mirror tana tsane ruwan jikin ta,lotion ta dauka mai sanyi kamshi ta shafa ma skin ɗinta tana kuma bi da humra masu kamshi, powder ta murza a face ɗin ta sama sama sai lip balm da ta shafa kaɗan shima, waldrop ta buɗe ta dauki kaya ta saka dan ganin Anwar hankalin shi baya kanta, hijab ta saka wanda ya hau daidai da kayan jikin ta, tulare ta kuma fesawa shima ba da yawa ba ta dauƙi key na mota da na part ɗin shi sannan ta dauki Anam,  dayar hannun kuma ta riƙe basket dashi, Anwar shima tashi yayi yabi bayanta suka wuce daga ɗakin lokacin har 3:40 tayi dakin goggo ta shiga ta sallame ta akan zata dauko mutum a airport, goggo kuwa daman tun dazu take hakalce da ita taga sai kaiwa take da komowa ga harda su yin sanwa
   "Da basket ɗin zakije airport?"
 Cikin basarwa tace "a'a zan aje ne! Ni na wuce".
   "Ke kika sani a dawo lafiya"
"Amin"
Fita sukai daga part ɗin zuwa na AS wanda sai da ta duba taga babu mai kallon ta sannan tayi sauri ta buɗe ƙofan ta shiga, aje Anam tayi bisa cushion sannan ta dauki basket ɗin ta nufi dining area tana jera cooler a kai sai da ta gama jerawa takai basket ɗin kicthen ta fito ta dauki Anam suka fice tana kulle ƙofa.
  parking lot suka nufa tana kiran mallam idi driver daman ta gaya mishi tun dazu zai kaita airport,da sauri ya iso yana karɓan key ɗin dake hannun ta,buɗe mata back sit yayi suka shiga ga harda Anwar dake ta jin dadin papan sa zai dawo.
    Koda suka isa airport sauran 5 minth ya rage su sauka, suna a ciki. Mota suka ji ƙaran saukar jirgi alamun dai sun sauka.
  ita fa bataga zata iya fita tarban shi ba dan haka tace wa Mallam idi yaya Ahmad suka zo dauka, gane mi take nufi ne sai ya fita yana ta raba ido sai can ya hango AS ƙarasawa wajen da yake yayi yana yi mishi sannu da hanya haɗi da karban briefcase da ke a hannun shi ba musu kuwa ya sakar mishi yana amsa gaisuwar da yayi mai, haka dai har suka ƙarasa wajen motar inda driver ya buɗe mishi,yana zira kai kuwa kamshin Tulare ya buge shi wanda har ta kaisa ga lumshe oily eyes ɗin sa bai ma sani ba, ta maza yayi ya shiga motar, yana zama kuwa Anwar ya faɗa jikin shi yana "papa over miss you" murya a dan shaƙe ƙaman mai mura yace "same boy"
   Duk da yasan akwai mutum a gefen shi amma sai ya basar ya saka hannu ka ɗauki Anam itama da tazo wajen shi, "Ummi na kinyi kiɓa fa mi kike ci haka" yayi maganar kamar yana magana da wata babba, satan Kallan EElham yayi ganin hankalinta gaba ɗaya yana kan wayar da take operating dauke kai yayi yana mamakin jin kanta, da kuma yadda ta ɗauke kai kaman bata san mutum ya shigo cikin motar ba, Saida ya bari driver ya tada motar sun fara tafiya sannan ya bama Anwar wayar shi dan hankalin shi ya dauku daga kansu daman tuni ya jefa sa front sit, kallan ta yayi a karo na babu adadi, hannu ya sa ya zare wayar daga hannun ta yana kallon abinda take, haɗe rai  yayi ganin chatting take da bestie,cikin ɗan fusata yace "baki iya gaisuwa bane? Ko izinin yin haka ne bai baki ba?" 
   Kanta daurewa yayi to ita kam wa zai bata izini,amma ganin bata kyauta ba yasa tace "ina wuni ya hanya" Kallan lips ɗin ta dake motsawa yayi kafin ya dauke kai, jin bai amsa ba yasa ta ɗago taga mi yasa bai amsa ɗinba, sai dai a maimakon idanun ta ya sauka a kanshi sai ya sauka akan dayar wayar sa dake a tsakanin su inda taga  PRETTY DARLING tana kira, lokaci ɗaya mood ɗinta ya canza amma da yake tasan hannun ta sai ta dauke kai, amma ji take kamar ta dauki wayar ta wancikalar da ita.
  AS kuwa da bai san halin da take ciki ba ya dauki wayar wanda duk shagwaɓa mubeena take masa shikuma yana biye ta ne dan ya ɗan samu sausaucin abinda yake ji a zuciya dan shima ji yake kaman zai kama da wuta. 
   Elham kam Kiris ya rage tayi boosting a wajen, daura kanta tayi kan kujera ta baya ta datse ido, amma a zahiri baza ka taɓa gane halin da take a ciki bah............✍