EELHAM🌹

50&51

by @rabearhwakili


Episode 50 & 51📲





***






بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai



___________
  Har suka iso gidan bai dai na wayar da suke ba, cikin kunan zuciya ta buɗe ƙofa zata fita amma sai ya riƙe mata hijab ta gefe, dakatawa tayi daga fitar ta kuma ƙi ta juyo ta kalle shi, 
   Yanke wayar yayi zuwa lokacin driver ya fita Anwar ma da ya hango yaron Anty Hanan tuni ya fita,
  "Nace ki fita ne? Ko na sallame ki?"
Sosai tayi ƙoƙarin danne muryata tana ƙara sawa kanta nutsuwa cikin dakiya tace "akwai abinda zanyi a ciki".
   Zuba mata ido yayi ganin lokaci guda duk ta birkice sai dai ya gaza gane mike damun ta, shima cikin cinkusashiyar murya yace "daga yau kar na ƙara ganin ki da wannan guy ɗin".
   Daman a wuya take dashi,kaman ba yanzu ya gama waya da matar shi ba! Ita ba ta ce komi ba sai shi ne zai Wani kafa mata doka to da akayi mene?.
   Cikin tsiwan ta tace "sai na kula shi! dan wanda yaso ka kaima ka so s........." Ɗalle mata lips ɗin da yayi shi ya katse ta cikin jin zafi ta dafe lips ɗin cikin taurin kai ta ƙara furta "waya dashi kuma yanzu na fa......" Kai hannun yayi zai ƙara kwaɓe mata lips tayi sauri ta saka hannun ta rufe baki tana hararan shi ta ƙasan ido.
   ɗan matsowa yayi kusa da ita amma dai jikin nasu bai haɗu ba cikin muryan gargaɗi yace "mu zuba ni da ke! Dan Allah karki fasa ɗaga wayar shi".
    "Ko yanzu ya kira sai na ɗauka"
    "Mi kikace?"
"Ni bance komi bah"
Kyaleta kawai yayi amma sarai yaji abinda tace, buɗe ƙofa yayi zai fita tace "wayata"
    "Zo ki ƙwata"
Ido kawai ta zuba mishi ganin ya juyo yana kallon ne sai ta dauke kai, tana ma fita daga motar gaba ɗaya, part ɗin goggo ta shige zuciyarta duk a dagule.
   Shima ɗin fita yayi yana bin bayan ta dan so yake ya karɓi key
    da sauƙin mutane a falon goggo wanda duk tsoffi ne, gaishe su yayi yana shiga ɗakin goggo wanda sai da ta bashi izini sannan ya shiga gaisheta yayi da sake fuska,wanda rabon da yayi haka tunda suka dawo daga Abuja, itama ɗin amsawa tayi tana shan ƙamshi wai ita tana ramawa,
  Dube dube yayi yaga babu eelham a ɗakin cikin yin ƙasa da murya yace "goggo ina take?"
  "Wa ke nan?"
Cewa yayi "umm ɗin su boy"
   "Yanzu ta fita kila tana ɗakin ta dan naga ta shigo sai baƙin rai take yiwa mutane".
   Tashi yayi bai ce mata komi ba ya fita cewa tayi "daman ai halin ku ɗaya".
    Bai saurare ta ba ya fita daga ɗakin yana shiga Wani corrido, ɗakin da yake tunanin nan ne nata anan ya tsaya yayi knocking,
  Elham da take kwance tana ji tayi shiru dan ta zata ko su meenal ne saboda su ta kulle ƙofan dan tana buƙatan kadaici, 
   Ganin ba budewa zatayi ba yasa yayi trying ɗayar number shi da yake wajen Anwar, cikin Sa'a kuwa wayar tana gefen ta tana kuma kallon call ɗin shi su na shigowa sai da ta mula dan kanta sannan yayi picking ba tare da tace komi ba.
   Cikin fusata yace "zoki bani key gani a ƙofa" 
    Bata jira ya ƙara cewa komi ba ta yanke call ɗin wanda hakan da tayi ya mugun ɓata mishi rai fiye da farko.
  Saida ta ga dama ta miƙe tana saka hijab sannan ta dauki key ta nufi ƙofa sai faman zumbura baki take.
   buɗe kofan tayi ganin shi a tsaye ne yasa tana daga ciki ta miƙa mishi batare da tace komi ba,
   Harde hannu yayi a ƙirji yana kallon ikon Allah sai da taji hannun ta ya gaji sannan cikin shagwaɓa tace "gashi"
   Kauda kai gefe yayi yana sakar dan guntun murmushi, ba tare da ya kuma dube ta ba murya a dake yace "muje" 
  Ba musu kuwa suka fito saidai shine a gaba, sai da ta bari sun zo daidai wajen Cushion dake gefen ta ta aje mishi key a nan haɗi da faɗin "yaya ga shi" tana faɗan haka ta koma dakin da sauri harda datsewa da key.
  Ɗauka yayi yana kudira sai yayi maganin ta 
  Sosai gyaran dakin da tayi yayi masa kyua ga kuma tularen da tasa sunyi masa kamshi kwarai.
Ruwa ya watsa ya gabatar da sallar la'asar da ta kubce musu bayan ya idar ne ya fito falo dan yunwa yake ji zai yi kiran Ummi kenan idanun shi suka sauka akan dining da yaga anjera wormers masu azabar kyau, tashi yayi yana karawa dining ɗin,buɗe wormers yayi ganin dai abinci ne mai rai da lafiya yasa ya zauna ya naɗa dan AS baya wasa da cikin sa,ga kuma yaji abincin yayi masa daɗi fiye da tinani,Saida ya kammala sannan ya baro nan ɗin ya zauna a falo,waya ya dauka ya yi kiran ummi
   Bayan ya gaisheta ne take tambayan shi ya sauka ne? 
   "A ummi tun 4 har naci abincin da kika aiko min"
   "Abinci kuma! A'a gadai shi nan ina neman wanda zai kawo maka"
   "Toh Ummi wa ya aje abinci a nan?".
  "Wa kasa ya gyara maka part?"
       "Umm ɗin boy"
"Yauwa toh inaga ita ta aje maka".
    Cikin gamsuwa ya amsa da toh yana cewa sai ya shigo gaisheta. Nan sukai sallama yana aje waya da jinjina kokarin da eelham tayi.....

______________
                        Tun 7:30 pm aka fara daukan mutane zuwa hall din da za'a gabatar da dinner zuwa 8 kuwa babu wanda yayi saura sai amare da kawayen su suka rage wanda sai yanzu suke isowa, Anty Hanan ce ta shigo tana cewa "har yanzu ba'a gama shirin bane ga kuma motan daukan ku ya zo".
   "Aunty mun gama"
"Toh ku taso muje" masa sukai suna miƙewa.
    Shirye suke cikin less mai tsada da ɗauka idanu wacce ta kasance purpule anyi musu ɗinkin doguwar riga fitted amma bata kama musu jiki ba sosai, sosai dinkin yayi kyau dan tailor yayi ɗinkin ne irin na zamanj wanda ko makiyin su sai ya sara. head ɗin kansu ta kasance silver sai gyalen da akayi musu pinning ɗinshi shima silver wanda yake ɗan sharan ƙasa, hakan sai ya ƙara fidda asalin kyau, ta kalmin ƙafasun su ma silver ne ɗan pos din dake hannun su ya kasance purpule.
   Ƙarasawa sukai wajen motar da angunan su ke ciki inda Ruqqy ta shiga na Umar meenal ma ta shiga na angon nata, sauran kawaye suma suka shishiga sauran motar.
   Haka suka tafi cikin convoy.

___________ 
                Ke dai sai a hankali tun ɗazu kin gagara ki gama shiri kizo ki wuce ko? Ai Ni nasan take taken ki so kike karkije, amma insha Allahu sai kin tafi wajen nan koda da son ranki ko akasin haka,yan uwan ki suna program kice baki zuwa,to idan baki je su waye zasu? Maza fito daga ɗakin nan kafin na shigo na same ki"
    Daga cikin ɗakin tace "goggo Ni nace bazanje bane?"
   "Baki ce ba amma take taken ki kenan".
Duk wannan draman da suke AS na jin su shi tunanin shima ko ta wuce, 
  Fitowa tayi daga dakin.
Tubarakallahu Masha Allah.
Shirye take cikin ash an black ya Allah sosai sosai sasai shirin yayi fitting ɗinta ya kuma ƙara fidda mata da kyawunta duk da ba wani kwalliya tayi ba powder da lipgloss sai dan kwallin da ta shafa ma Golden eyes ɗinta wanda hakan ya ƙara fidda girman su da shape.
   Sake AS yayi da baki da kyar ya iya tattaro yawun bakin shi yana dauke kanshi daga kanta cewa yayi "goggo bara naje" 
     "Da ka wuce mun da wannan mai taurin kan dan tana iya zuwa ta laɓe tace taje" 
   "To goggo sai mun dawo" adawo lafiya tayi musu ita kuwa eely da ke ta faman zumbura baki tace "kuɗin manni! Ko haka zani?" 
    Ban da kuɗin manni! Wato ga ki mai wayau, Ina wayenda na baki jiya nace ki riƙe?"  "Na kashe"
   Toh shikenan sai ki tashi ki tafi hakanan".  jin haka ne sai ta miƙe ta shiga ɗaki tana daukan kuɗi ta saka cikin jaka sannan ta fito.
   Ganin fitowar ta ne yasa ya miƙe yana ficewa ita sallaman goggo tayi tana bin bayan shi koda suka isa wajen mota dake shi zai yi driving sai ya buɗe mata gefen shi tana shiga ya rufe ya zaga gefen driver tada motar yayi suka fice daga gidan bayan mai gadi ya buɗe mishi gate,
    A hankali yake driving baka bin motsin kowa cikin su sai na karatun da yake tashi a ciki, haka dai har suka isa babban hall ɗin, parking yayi wajen da aka tanada dan aje motoci, sauke pin din motar yayi ganin shirin fita take, ba tare da wasa ba ya dauki tissue ya miƙa mata haɗi da cewa "goge powder ɗin nan da jan baki".
Yau ake yin ta cikin da marairaicewa tace "dan Allah yaya ka bari"
      Naƙi na bari! Zaki goge da Kanki ko sai na goge miki?".
   Mutum nan yana shigar mata hanci da yawa fah tunda ya dawo shikenan bata da sukuni duk ya bi ya saka wa duk motsin ta ido, amma zata na dai na sakar mishi fuska ne,hannu ta saka ta karɓa ta goge powder dake a fuskar ta daman ba wani da yawa tasa ba, lipgloss ɗin ma ta rage musu yawa sai ta bar kadan ta yadda bakin ta bazai bushe ba, "na gama"
  Ba tare da ya ƙara yi mata magana ba ya ciro bandir din yan dubu ya mika mata kin karɓa tayi tana cewa "ina dasu" 
 "Daman Nima nace baki da ne? Oyah karɓi"
    Badan taso ba ta saka hannu biyu ta karɓa tana yi mishi godiya,fita yayi itama ta buɗe kofa ta fita.
   A jere suke tafiya Saida suka zo wajen entrance din shigane ne sai ta tsaya nufin ta idan ya fara yin nisa sai tabi bayan shi, ai kuwa kaman ya san mi take nufi sai yace mata "muje Koh"
 "Ni dai ka fara tafiya" 
"Babu inda sani ƙafata kafar ki"
 Ganin dai da gaske yake sai ta fara shiga sannan shima ya shiga daidaita tafiyar nasu yayi duk da eely tafiya take sannu a hankali dan ya wuce amma shina sai ya rage saurin nasa suna takawa dai-dai nan fa mutane sukai musu chaaaaa da idanun barin ma da suka ga AS yasha ash shadda da hularsa baƙa takalman ƙafan shi su ma baƙaƙe ne, wanda kwalliyar eelham ma haka ta zama na ash an black, 
   Idon da yayiwa eelham yawa ne yasa tafiyar nata ƙarayin sanyi, cikin ikon Allah har suka isa wajen zama daga ta chan gefe in da babu mutane sosai.
   Kujera ya ja mata amma taƙi zama shi ɗin ma ƙin zama yayi sai idanun da ya zuba mata masu kaif.
  Turo baki tayi tana cewa "Ni ka dai na kallo na".
    Kin dauke idon sa yayi daga kanta yace "samu waje ki zauna"
    Tana kumbura ta zauna shima zaune ta kai yana kallon ta "DEJARHT". Batare da ta kalle shi ba tace "na'am"
   "Mi akayi miki kike ta faman fushi?".
  "Babu"
  Gaɗa kai kawai yayi badan ya yadda ba nan kowa ya fita harkan ɗan uwan sa,
 Suna a nan har wajen one hour bakin su bai kuma saɓa ba dan duk yan miskilan cin sun motsa.
   "Zan je gida"
Daman shima ya gaji da zama a wajen dan ita kawai yake zaune akan ƙaran kiɗan duk sun cika mishi Kunni.
    Tashi sukai suna nufan inda yayi parking, shiga sukai ya bama motar wuta suka bar hall ɗin. Suna kaiwa gida batace mishi komi ba ta fita zuwa part ɗin goggo dan daman bacci take ji,shi ɗin  ma nashi part din ya wuce

Yan dinner ba sune suka dawo ba sai sha biyu na dare lokacin eelham ta dade dayin bacci
_________________
                             𝑹𝑨𝑵𝑨 𝑩𝑨𝑻𝑨 𝑲𝑨𝑹𝒀𝑨
Rana bata karya saidai uwar ɗiya taji kunya.
  babba masallacin juma'a cike yake da manya manyan yan ƙasa waɗan da ake damawa da su, tun daga kan gamnoni,manya manyan yan siyasa, da masu muƙa mai, da manyan yan kasuwa waɗan suka shahara da masu kudi wanda suka tada kai  duk su suka cika  masallacin sanadin auren yaran  ALHAJI YUSUF wanda shima ake damawa da shi cikin manyan yan kasuwa.           
    Bayan idar da sallah jumma'a aka daura auren su meenal tare da angonta sannan aka daura na Ruqayyah da nata angon sai aure na karshe da aka daura inda sankira ya ke maimaitawa an daura auren 𝑨𝒉𝒎𝒂𝒅 𝒀𝒖𝒔𝒖𝒇  𝑨𝒉𝒎𝒂𝒅 𝑺𝒂𝒓𝒂𝒌𝒊  𝒅𝒂 𝒂𝒎𝒂𝒓𝒚𝒂𝒓𝒔𝒂 𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒉𝒕 𝑼𝒔𝒎𝒂𝒏 𝑨𝒉𝒎𝒂𝒅.
  Ji yayi kaman a mafarki yake jin wannan daurin auren,sosai ya tafi dogon tunani wanda ya fidda shi daga cikin hankalin shi har sai da Umar dake kusa dashi ya taɓo shi jin yana ta magana shiru,
   Cikin nutsuwar sa ya ɗago wanda fuskar shi bai baiyanar da komi ba dan duk abinka baka isa hango komi saman fuskar shi ba,,
Jan shi Umar yayi suka koma wajen da yake da sauƙin hayaniya,cewa yayi  "AS ya akayi haka?, daman harda kai a masu auren a yau shine koda wasa baka taɓa gaya min ba?".
   Cikin sauke ajiyar zuciya yace "Nima ban san komi ba sai yanzu"
     "Ikon Allah! Sai kayi biyayya da kuma fatan Allah yasa haka yafi alkhari".  Gaɗa kai yayi.
  suna a wajen ne sai ga bappi ya ƙaraso fuskar shi ƙawace da murmushi cewa yayi "kun san dai za'a neme ku kuka zo nan kuka tsaya?".
   Haƙuri suka bashi suka bi bayan shi inda duk inda suka gitta sai anyi musu Allah ya sanya alkhairi.

    Bayan sun dawo daga masallaci ne gida ya dauƙi guda in da abokan nan wasa suke ta jan AS da wasa amma shikuwa ya sha mur kaman ba dashi suke ba.

Zaune suke suna fira irin na ƙawayen amare, meenal ce ta shigo ɗakin cikin kwalliyarta, sosai tayi kyau ta ku ma fito a amaryarta, cewa tayi  "babies kun ji labarin da ake a waje kuwa?". 
   Sarkin son gulma Yusrah ce tace "ina muka je bare muji! Kedai shafa mana".
   "Aikuwa Nima baza kuji a baki na ba duk wacce take son ji ta fita ta jiyo da kunnin ta".
  "Amma kekam yar walaƙanci ce,kinsan bazaki faɗa ba mi na kwaɗaita mana toh?". Cewar Sarah da ke ta fama da farin ƙasa dan tana yawan samun taruwan yawu a baki.
    Kallon su tayi tace "ko wuta ke fita daga bakin ku baza kuji ba, duk mai son taji ta fita waje".
   "Ku ma dai kun iya naci tace baza ta faɗa ba amma kun dage sai kunji, kamar baku san wulaƙancin meenal ba" cewar jawaher da ta gama baza Kunni dan taji amma shine ta koma da raina musu hankali.
   "Bazan fa faɗa ba ahem"
Elham dai da take jin su batace musu komi ba dan bata jin daɗi jikinta,ganin zasu dame ta yasa ta miƙe ta fita daga sashen zuwa na grandma, koda ta shiga yan uwa suka hau kanta da guɗa wanda ya bata mamaki, amma sai tayi tunanin ko sun zata meenal ce, da wannan tunanin ta watsar ta shige ɗakin grandma, da sallama ɗauke a bakinta, goggo ce ta amsata da mamaki take kallon goggo, ita kuwa goggo cikin basarwa tace "daman yanzu muke shirin kiran ki! Zauna bari iyayen naki su ƙaraso".
  Ita fa an daure mata kai amma bata da karfin musu,zama tayi a  ƙasa gefen ƙafafun grandma tana daura kanta a kan cinyar ta,shigowar da su bappi sukai ne yasa ta gyara zama, gaishe su tayi,
Amsawa sukai da kulawa, duban wajen sukai ganin AS bai nan sai Abba ya fidda waya yayi kiran sa akan yazo ya same su a ɗakin grandma, babu jimawa sai gashi ya shigo, Saida bappi ya fara buɗe taro da addu'a sannan yace "mun buƙaci ganin ku ne kai da Ummina dan kuji hukuncin da muka yanke a kanku tun sati ɗaya da ta wuce, duk da mun san munyi muku shishigi barin ma ita ummi na wacce a yanzu ita ya kamata ta kawo mana wacce take so, sai bamu Bata wannan dama ba, ba kuma mu ne mi izinin ta ba, dan haka Ummi na kiyi haƙuri mun  yi miki ba daidai ba ,amma ko yanzu idan kin nuna baki so ki faɗi zuciyar ki!" Dan nufasawa yayi kadan kafin ya cigaba da cewa "satin da ya wuce Hajiya mama da goggo sun buƙaci da a haɗa auren ku dan ya kasance babban burin dan uwa na wato mahaifin Ummi na, ko da suka tumtuɓemu ni da Abban ku, a ranan mun buƙaci da a sanar da Ummina amma sai goggo ta hana a kan cewa muna da damar yanke duk wani hukunci, ita mai biyayya ce, ta kuma buƙaci da a boye muku har sai in an daura, Toh Alhamdulillah a yau aka daura muku aure keda ɗan uwan ki Ahmad......."
   Ai tun daga nan ta daina gane maganar da yake jikin ta ya rinƙa rawa sosai ga kuka nason ya kufce mata wanda take ta iya bakin ƙokarinta wajen ganin tayi controlling kanta amma hakan yacitura duƙar da kanta tayi sai ga wasu hawaye Masu zafi yana kwaranya daga fuskar ta.
    Bayan bappi ya gama bayanin shi shima Abba ya dauka haɗi da faɗin "Ahmad ga Ummi nan mun baka amanarta, bawai dan batada wanda take so yasa muka aura maka ita ba a'a! Munyi haka ne dan mu cika wa babanta burin shi, inda ace yana a raye da yafi kowa farin ciki da haka, dan haka ka kula mana da ita amana, kar ka manta a mana take a gare ka, ka kula da ita, Allah ya baka ikon yin adalci  a tsakanin su".
    Su goggo suka amsa da Amin shima ya amsa amma a kan labba.
Sosai su Abba suka saka ma eely albarka wanda bata ma san suna yi ba, tashi sukai suka wuce daga part ɗin.
   Shesheƙar kukan da take ji ne nan ta gane eely kuka take, jawota tayi jikinta tana lallashinta da bata baki amma ina kaman ƙara tunzura ta take,dan sosai ta ƙara volume ɗin kukan kaman ranta zai fita,nan fa suka haɗu suna ta bata baki dan sun gano ba auren take yiwa kuka ba iyayen ta ta tuna duba da yadda ta kamƙame grandma,ganin dai idan suka tsaya Elham sai ta saka su kuka sai goggo ta janye jiki tana cewa bari taje ta bar baƙi, tana fita ita grandma ta janye jikin ta dakyar tana cewa Ahmad kazo ka lallashi matar ka dan tafi ƙarfin mu, shi kuwa gani yake wannan kukan da take dan bata son shine shi yasa sai hakan ya sage masa gwiwa, ita kuma grandma tana gama faɗa tasa kai ta fice daga ɗakin tana yiwa ƴaƴan nata addu'a samun rahama.
  Kukan ta sosai yake taɓa mishi zuciya, yaso ne ya shareta tai tayi  amma ganin ba zai iya ba sai ya ƙarasa zuwa cushion ɗin da grandma ta barta, ta daura kai a hannu Cushion ɗin.
   Zama yayi daga gefen ta ya ɗanyi jimmm  kafin a hankali cikin sanyi murya yace "DEJARHT".
  Bata ma san yana yi ba dan gaba ɗaya hankalinta basa tare da ita, jin shiru bata amsa bane yasa ya dafa bayan ta a karo na farko da haka ta faru, taɓatan da taji anyi ne shi yasa ta ɗago da fuskar ta da suka ɗan kumbura saboda kukan da ta sha, ganin shine yasa tayi kokarin mayar da kanta,amma sai ya katse hakan da riƙe mata fuska, dole ta ɗago da kai tana kallon shi, shima kallan nata yake da oily eyes ɗinsa, gyara zama yayi yana facing ɗinta da kyau, dauke kai tayi wasu hawayen na ƙara gangarowa daga fuskar ta, kwacewabtake so tayi amma yaƙi ba ta daman hakan,
  Ganin tana son ta kwace sai ya saka ta a jikin shi yana shafa kanta alamar lallashi.
  Tun tana kuka mai sauti har ya koma shesheƙa daga baya kuma yaji tana sauke ajiyar zuciya, cikin sanyin murya yace "DEJARHT" jin shiru bata amsa bane yasa ya leƙa fuskarta gani yayi tana bacci,bai kuma cewa komi ba sai gyara mata kwanciya da yayi, Tun shima yana ido biyu har bacci yayi gaba dashi cikin farin ciki........✍️