52&53
Episode 52 & 53📲
***
BARKA DA JUMMA'A YAN UWA
ALLAH YA ƘARA MAIMAITA MANA MASU YAWA
YA KARƁI IBADUN MU AMIN YA HAYYU YA KAYYUM 🤲
JK🕋📿
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
Wuraren ƙarfe huɗu 4 grandma ta shigo ɗakin dan tunda suka fita daga cikin bata dawo ba tana falo, yanzu ɗin ma akwai abinda ta zo dauka ne ta koma,
Tura kofan da zatayi idanun ta sukai mata kyakyawar gani, kauda kai tayi tana mamakin yaran zamani, haka dai ta dauki abinda tazo dauka ta fice tana ja musu ƙofa.
Tun sanda grandma ta buɗe kofan ya farka buɗe ido ne kawai baiyi ba, sai da ya ga fitar ta sannan ya buɗe oily hair ɗinsa yana dire su akan eelham dake ta baccin ta peaceful, ganin ta fara motsi ne alamar zata tashi sai yayi sauri rufe ido kaman mai bacci.
A hankali ta gama buɗe lulu eyes ɗinta da suka ɗan kunburo kaɗan,jin ta tayi kaman tana a jikin mutum yasa ta ƙara waro ido dan ta tabbatar ilai kuwa saman jikin ma namiji ai ba shiri ta miƙe tana zare ido, dube dube ta shiga yi dan kar ace akwai mutum a dakin, ganin babu kowa shima gashi yana bacci sai ta gode Allah tana silalewa ta bar dakin asirin ta rufe waɗan nan tsoffin basu ganta ba,
Tana fita kuwa tayi kicibis da grandma, cikin fiskewa ta sa kai zata wuce sai taji muryan grandma tana faɗin "namecy har an tashi bacci kenan? Kin dai tasar da shi ko, dan la'asar tayi".
Wayyyo Allah ina ƙasa ya tsage ta shige dan kunya.
AS da yake bayan su sai murmushi yaƙe ta faman saki, cikin muryan wanda ya tashi daga bacci yace "kema kin san zata tasar dani mi na tambayar to".
"A'a ba sai ka gwada min rashin ta idon ka ba ehem"
"Idan ba so kike a gwada miki ba mi na tambayar to"
Bai jira amsar ta ba ya kama hannun eely suka fita daga falon jiki duk a sanyaye, inda Allah ya taimake ta babu kowa duk sun wuce.
Saida suka kai ƙofa sannan ta ƙwaci hannun ta tana hararan shi ƙasa ƙasa dan wannan abun ai duk shi yaja, batare da tace mishi komi ba tasa kai ta wuce tana kunkumi,
Jin kiran da ake ne yasa ya shige part ɗinsa dan dauro alwalla.
________________
bayan sallar isha'i
Zaune suke a ƙasa duk su uku Ruqqy meenal Elham,su Abba na yi musu nasiha akan haƙuri a gidan aure, sai da suka gama su ummi suka daura nasu,sosai sukai musu nasiha mai ratsa jiki da sanyaya ta.
Kiran Anty Hanan da Anty Billy Ummi tayi suka kama su suka fita zuwa part ɗin grandma wanda sai kukan rabuwa da iyayen nasu suke,su aunty billy na ta basu baki har suka isa, itama grandma tayi musu faɗa mai harshen damo wanda duk kukan da suke bai hana su ji ba,saida ta gama musu faɗan sannan ta kama su zuwa part ɗin goggo, ita ma dai tayi nata wanda suke gaya musu dabarun riƙe miji cikin hikima sai da suka gama musu faɗan sannan suka raka su har cikin mota, Saida a kazo shiga mota ne eelham ta ƙanƙame goggo tana kuka da gani dai kukan da uku take, da kyar aka samu ta sake goggo,Shigar da ita mota akayi, driver yaja motar sauran yan rakiya suna bin su a baya, Saida aka fara sauke meenal, batare da su eelham sun shiga ba driver ya ja motar suka wuce anguwar su Ruqqy itama a ka shigar da ita gidan ta da yan rakiyan ta, daganan aka wuce gidan da eelham zata zauna dan su bappi sun tanadar mata komi anyi mata jere tun da rana a gidan AS da ya kasance sabo dan yana chan yasa akai ta gyarawa dan nufin shi daya sauka a chan zai tare da ƴaƴan sa da yar matar shi, ashe dai eelham ke da rabon shiga farko.
Koda suka sauka fito da ita Anty Hanan tayi da wata baba Sa'ade, sai da suka zo kofan shiga falon ne baba Sa'ade tace "ki shiga da ƙafan dama tare da Bismillah".
Kamar yadda tace mata kuwa haka tayi amma ta ƙara da sauran addu'oi sannan ta shiga da ƙafar dama, ɗaki aka wuce da ita direct.
Nasiha dai suka ƙara yi mata sannan suka fito suka barta amma Anty Hanan w nan aka barta sai AS ya dawo zata wuce, taimaka mata tayi ta gyara abinda bai yi ba,sai da ta gama ta haɗa mata ruwan wanka, ba musu kuwa ta tashi taje tayo, zama tayi a kujerar dressing mirror tana tsane jikin ta, lotion ta shafa sama sama sannan ta bi jikin ta da humra da ta gani saman mirror, tashi tayi ta dauki kayan da ke a kan gado wanda Anty Hanan ce ta aje mata doguwar shadda kalan sky blue taji stone work ga sai daukan ido take, cikin sauri ta zira rigan ba tare da tayi dauri ba ta daura White Vail mai ɗan girma saman kai.
Designers perfume tabi jikin ta dashi masu kamshin gaske, komawa tayi tana zama gefen bed tana ta wasa da hannun ta da suka sha desing sukai kyau, knocking Anty Hanan tayi mata cikin yin ƙasa da murya tace "Anty na gama".
Jin haka ne ta turo kofan ta shigo.
"Masha Allah U look so adorable".
Cikin kunya ta duƙar da kanta ƙasa tana "na gode Anty".
"Ahmad sun shigo zan bi abokin shi ya sauke ni! saida safe Allah ya bada zaman hakuri".
"Na gode Anty" tayi maganar muryanta na rawa
"My pleasure dear! Koma ki zauna abinki bye". Tana gama faɗi ta fice daga ɗakin.
Ita kuma EElham komawa tayi bakin gado ta zauna tana jin ta duk a takure.
Tana zaune a nan AS ya shigo bakin shi ɗauke da sallama, akan labba ta amsa wanda bai zama lailai a ce yaji ba.
Aje ledojin da suke hannun shi yayi yana zama gefen ta, saka hannu yayi yana ɗago da fuskarta,datse ido tayi da sauri dan wani irin kunyan shi ya dirar mata at once.
Cikin murya ƙasa ƙasa yace "Barka da zuwa Mrs Ahmad"ya ƙare da hura mata iskar bakin shi akan face ɗinta, ƙara rintse idon tayi.
Cikin yin ƙasa da murya yace "buɗe ido".
Ƙin buɗewa tayi, ganin dai baza ta buɗe bane sai yace "tashi muje kiyi alwalla muyi sallah" .
"Ni nayi sallah"
Zuba mata ido yayi haɗi da cewa "Ni nace ba kiyi bah! Common tashi kije kiyi alwalla".
Tashin da taje yi sai gyalen da ta daura ya zame sanadin zaman da AS yayi a kai, dan tura baki tayi tace "my Vail".
Ba tare da yace komi ba ya ɗaga mata, ita kuma ta nufi hanyan toilet tayo alwalla ta fito,samu tayi ya shimfiɗa sallaya biyu waldrop ta nufa ta ɗauki hijab ta saka.
jansu sallah yayi raka'a biyu, bayan an idar ya dafa kanta yana karanta addu'a da ake,daura mata da tambayoyi akan addini yayi, inda take bashi amsa dai-dai cikin ikon Allah.
Linke sallayan tayi tana maida su cikin waldrop. Fita yayi daga ɗakin ba jimawa ya dawo hannun shi dauke da plate da cup,dauko ledar da ya shigo da shi yayi yana aje wa a center table dake a ɗakin juye naman yayi a plate sai hollandia ya zuba a cup, maida duban shi yayi ga eelham yace "zo nan".
Sai da ta ja class sanna ta taso tana daga tsaye tace "gani"
"Zauna" yayi maganar yana nuna mata gefen shi.
Zama tayi amma nisa da shi dan cushion ɗin ya kasance 3 siter.
Matsawa yayi zuwa gefen ta,cikin daure fuska yace "haaaa" cikin murtike fuska itama tace "na ƙoshi".
"Mi kika ci"
Shiru tayi bata tanka masa ba.
Babu wasa yace "ki buɗe baki Koh".
Cikin ɗan gundira ta buɗe baki.
A hankali ya dinga feeding ɗinta,yana cikin bata wayar shi ta hau ringing, ɗan dakatawa yayi yana cewa "excuse me" ita kuwa haka ta zuba masa ido dan haka kawai taji shigowar call ɗin ya ɓata mata rai.
Daga wayar yayi yana ci gaba da bata naman a baki yana yi suna waya da mubee wacce sai narke masa take.
Cikin saita kanta ta miƙe tana nufan toilet dan yin brush, dago wa yayi ya bita da ido har ta shige cikin toilet ɗin, suna nan suna waya ta fito bata dube shi ba ta shiga cikin waldrop ta canza kaya zuwa na bacci,daura hijab tayi akai sannan ta fito ta kwanta kan gado tana yin rufa da blanket.
Tashi yayi ya kwashi kayan ya maida su kitchen ɗakin shi ya shiga yayi brush ya canza kaya zuwa na bacci daman yayi wankan shi, kashe wutar dakin yayi ya ja ƙofan ya koma na eelham wanda har yanzu waya yake da mubee.
Murɗa ƙofan yayi amma sai yaji ƙofan ɓam ta datse da key, sosai hakan ya bakanta mishi, dan mi zata kulle masa ƙofa mi take nufi.
Cikin ɓacin rai ya datse wayar da suke da mubee yana komawa ɗakin shi zuciya duk a dagule.
Ɓangare Elham ma haka ya kasance cewa take dan mi zai na rinƙa yin waya da wata a ɗakin ta,ai wannan kaman cin fuska ne, shi yasa yana fita ta tashi ta datse ɗakin da key idan waya zai yi ya tsaya a ɗakin shi.
Haka dai ta kwanta ba jimawa bacci ya ɗibeta .....
_____________
Washe gari
"Na shiga uku ni zeeena, wayyyo Allah na, Ahmad mi yasa zaka yi min haka? Baka san tsananin kishin ka da soyayyar ka da nake ɗawainiya dashi ba,wallahi ina sonka har cikin ƙoƙon zuciya ta bana iya rayuwa ba tare da kai ba Ahmad! Ka taimaka ka dube ni ka aureni, ina kishin ka! Ina kishin ka! Ina kishin ka, bana iya jure inganka da wata mace, bana na iya jurewaaaaa" ta fashe da kuka tana cigaba da surutun ta ita ɗaya kamar wata sabuwar kamu a hauka, zumbuuuuur ta miƙe kamar wacce aka muntsila "mubee kece zaki zama kwallon buga wasa ta! Har sai na kori wanchan sannan in dawo kanki, ni zeeena gani nan tafe zuwa gareki".
Saita kanta tayi sosai sannan ta ɗauki waya tana trying number mubee.
________________
MUBEENA
Sharan tsakar gidan take wanda da gani kasan dan dole take yinshi.haka dai tayi sharan har ta gama, bakin ƙofan ɗakin mama ta tsaya tana cewa "mama na gama sharan".
"Sannu da kokari Allah yayi albarka! Ga wankin mallam nan ki wanke mishi".
Can ciki ta amsa da toh.
mubeena bata son aiki ko kaɗan, sai Allah ya taimake ta ya haɗa ta da mai kuɗi,dan a gidan AS komi yi mata ake, amma idan tazo gida an ta saka ta aiki kenan ba dare ba rana, hakan yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa bata son zuwa.
Kwasan kayan tayi tana zuwa makwarara ta diba ruwa daga durum ta fara wanki, bayan ta gama wankin ne, tana cikin shanya sai taji wayarta na ringing, cikin sauri ta aje kayan dake hannun ta,
Kan window ta dauki wayar ganin mai kiranta yasa ta saki murmushi.
"Hajiya zeena muryan ku kenan?".
"Abubuwan ne sai a hankali kinsan na koma gida kuma babu network a garin sai jiya nake dawowa".
"Eh haka fa! Toh ya su ba-ba?"
"Kedai ba wannan ba mubeena, daman kinsan AS zai ƙara aure shine babu ko labari, sai jiya da na dawo nake ji a shanun talla! Nace to mi nayi wa wannan matar?".
Jinta,ganinta,tunaninta toshewa yayi, ita kuwa zeena cikin son ta daura mata hawan jini tace "jiya aka daurawa Mijin ki Ahmad aure, a kuma jiya ta tare a sabon gidan shi........"
Tasan cewa maganar nan tabbatacciya ce tunda har ya fito daga bakin Amintacciyarta, wurgar da wayar tayi cikin buɗe baki ta fasa wata ihun fitan hankali, faɗi take "wayyyyyo! wayyyo! wayyyo! Ka cuceni kaci amanata Allah ya isa tsakanina da kai, hmmmmmmm heeeeeeeeeee niiiiiiiii niiiii niiii inaaaaaaa bazata ta saɓu ba wallahi bazan ɗauka ba........"
Cikin tashi hankali mama ta fito daga ɗakin ta jin ihu da surutan da mubeena take kamar wacce ta zare dan sunbatun yayi yawa.
"Ke mubeena natsu mana,mi akayi Miki kika cikawa mutane gida da ihu kamar wata ƙaramar yarinya".
Gaban mama ta tsaya tana pointing kanta tace " kishiya fa kishiya fa mama! Ahmad ya yaudare ni, yaci a manata, yaci amanata mamaaaaaaaa..."
Kuka yana kufce mata, mama cikin daka tsawa tace "zaki nutsu ko sai na kira mahaifin ku ya zo?".
"A kira shi ya bi min hakki na! Ai Nima ƴa ce kaman kowa, ko a kwai wacce aka taɓa yima kishiya a gidan nan? Ko shi Mallam yayi Miki kishiya ne, sai ni da Ahmad ya raina zai yi wa sakayya da haka inaaaaaa Allah ya........" Cikin fusata mama ta ɗauke ta da mari cikin kaukuaran murya tace "sai yau na tabbatar baki da hankali, wawiya kawai, kina hauka ne zaki na rinƙa ja wa mijin ki Allah ya isa? Ko tsoron ki yake da bazai yi aure ba, bazan roƙe ki da kishiga hankalin ki ba mubeena, ki cigaba karki fasa, wawiya kawai mtwws". Ta ƙare maganar da jan doguwar tsuka tana shige wa ɗaki ta bar mubee nan riƙe da fuska dan marin ya shigeta fiye da zato.
Da sallama dauke a bakin shi Mallam ya shigo cikin gidan, ganin mubeena yayi tsaye dafe da fuska cikin dattakon sa yace "mubeena lafiya kike kuka mi akayi Miki?".
Jin muryan Mahaifin ta ne yasa ta saita kanta murya na rawa tace "malam Ahmad ne ya ƙara aure".
"Alhamdulillah Masha Allah, abu yayi kyau Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya, ya kuma bashi ikon yin adalci".
Sagade tayi da baki tana kallon mahaifin ta,idan kuma idanun ta ba karya sukai mata ba kaman murna yake da auren da AS ya ƙara!, tana cikin wannan tunanin taji Mallam yana cewa "tabawa fito kiji abin arziƙi". Fitowa tayi tana washe baki haɗi da faɗin "yanzu ma nake tsumayin shigowar ka! Ashe har ta gaya maka?".
"Ganin ta nayi tsaye nake tambayan ta mi ke faruwa take gaya mun! Allah dai ya sanya alkhairi".
"Amin ya Allah Mallam"
Kallan mubeena yayi yana nuna mata gefen shi yace "zauna" yayi maganar babu wasa a cikinta, ba musu kuwa ta zauna tana danne kukan da ke taso mata, to dole tayi kuka mana ganin iyayen ta suna farin ciki da auren da mijin ta yaƙara kaman daman jira suke hakan ya faru.
"Ke mubeena" firgigit ta dawo cikin haiyacin ta "na'am Mallam"
"Da farko Kunni zan fara ja miki, da ki shiga hankalin ki, kiyi mishi biyayya da fatan zaman ku lafiya ke da yar uwarki, karki kuskura na ga kinyi tashin hankali akan haka, dan Allah ne ya halasta masa yin mata ɗaɗ-ɗai har huɗu, dan haka banso kiyi jayaiya da haka, idan kuma kince baki ji maganata ba kije kiyi duk abinda kike ganin shine daidai a gare ki, ni nazan hanaki ba kuma bazan ce karkiyi ba! amma idan labarin hakan ya zo mun zanyi mummunar saɓa miki! Kina dai jina?".
"Anya mutanen nan suna sonta kuwa? Akwai soyayya a nan kuwa? Taya za'ayi ayi mata kishiya sannan suce karta dauki mataki? Tab ai se dai suyi abinda zasu yi amma sai ta dauƙi mataki, ina dalili...."
"Wai ba da ke ake magana ba kinyi banza da mutane? Toh idan ma wani abun kike kullawa Allah ya baki Sa'a kiyi shi tunda ke ba'a faɗa miki kiji, Nasha gaya miki kibi duniya a sannu". Cewar mama ranta a ɓace da halin mubeena.
"Tabawa ai basai kin ɓata yawun bakin ki ba, taje tayi duk abinda zuciyarta ke raya mata, ba ita zata sani ba, ki zuba mata ido kawai".
"Shi kenan kuwa".
Cikin sauke murya tace "Nagode insha Allah zan kiyaye! Ina son na koma gida yau na bar su Anwar".
Kadan ya rage dariya ya kufcewa mama, wato bata tashi tuna ta bar yara ba sai a yau, bayan ta kusa wata a gidan bata ko maganan su, amma da yake ba tada ta ido shine zata ce ta bar su Anwar a gida.
"Allah ya tsare hanya! A kuma kiyaye kar labari yazo min akan kinyi ba daidai ba".
"Insha Allah Mallam za'a kiyaye na gode".
"Ma dallah tashi kije".
Miƙewa tayi cikin ɗaki ko kaya bata tsaya ɗauka ba ta fito sanye da vail sai pos da waya da ta riƙe a hannun, durƙushe ta kai tana sallamar su wai zata wuce, ba tare da sun hanata ba sukai mata fatan sauka lafiya, har ta fita daga gidan ta dawo ta dauki wayar da ta yasar da shi a ƙasa dan tanason tayi kiran zee dan number ɗinta na kan sim ɗin da ke wayar, tana fita ta tare a dai-daita ya kaita tashan mota dan yau ba magana bin Flight dan bazata tsaya jiran lokacin tashin nasu ba, motar Kano ta samu sai da aka cika sannan suka ɗauki hanya.
cire sim tayi ta saka a ɗayar wayar tayi kiran zee, inda ita kuma ta dinga tunzura ta tare da cewa idan sun sauka ta wuto gidan ta kawai, cikin gamsuwa ta amsa da "shikenan sai mun sauka".nan sukai sallama kowacce tana aje wayar ta......
______________
Zaune take a falo ita da baƙi yan biki, zasu wuce ne shine grandma tasa jawaher tayi musu rakiya dan su ga gida. Tashi sukai zasu wuce ta rasa abinda zata basu, tunawa tayi tana da ɗan canjin ta a pos kuma suna da yawa, tashi tayi tana ce musu tana zuwa ɗaki ta shiga inda ta fidda duka 50k din koda ta fito kitchen ta nufa ta haɗa musu snack ɗin da aka aiko mata dashi, sosai ta ɗibar musu, sannan ta fito.
Miƙa musu ledar tayi 50k ɗin kuma tace "yace a baku"
"Hadda ɗawai niya haka, to mun gode kwarai Allah yayi albarka! Ki taya mu yi masa godiya" cewar dayar.
Ita dai murmushi kawai tayi, ganin sun tashi ne sai ta miƙe itama tayi musu rakiya har wajen mota, kallan jawaher tayi tana cewa "yanzu ke ma wucewa zakiyi?".
Kiji min mata fa, da nufin ki in zauna? Sannu to".
"Toh mi a ciki idan kin zauna".
Cikin dariya tace "a'a babu".
tayi maganar tana shige mota, ita kuwa eelham ba tare da ta ƙara kallan ta ba tayi ma matan nan biyu sallama, ganin tafiyar su sai ta koma ciki tana jin ta duk wani iri, shiga tayi cikin falon tana nufan hanyan ɗakin ta ba tare da ta tsaya kallon komi a falon ba.
"Zo nan" tsammm tayi a tsayen da take, ita sam bata lura yana falo ba, jiyowa tayi tana ƙarasawa inda yake, zaune yake akan 2sitter dake a babban falon.
Batare da ta ƙara kallan sa ba tace "ina kwana?".
Taɓe baki yayi, yana nuna mata gefen shi, ita kuwa yi tayi kaman bata gane abinda yake nufi ba "eelham" salon da yayi amfani wajen kiran sunan nata sosai hakan ya narkar da ita, amma sai ta basar dan yau da yan miskilanci ta tashi.
Tashi tayi kaman zata zauna ɗin ta gudu zuwa ɗaki, tana haɗawa da sanya wa kofan dakin key daman da sauran fushin jiya a tare da ita, kuma sai tayi maganin shi, wanda ko gobe idan a kace ya ɗaga wayar wata a gabanta bare kuma a ɗakin ta bazai yi ba, dan ita ta ɗauki hakan da yayi a matsayin cin fuska gare ta.
Datse lips ɗinsa yayi, wato eelham gudun shi take amma tana iya bin wani ƙaton banza su bar gari, amma zai yi maganin ta, ta yadda zata dawo cikin hankalinta dan yaga raini ke son shiga tsakanin su.
Daga karshe ma ya tashi ya fita daga gidan ba tare da ya ƙara bi ta kanta ba..............✍️