54&55
Episode 54& 55📲
***
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
__________________
Sosai ya samu tarbar da ya bashi mamaki daga mubeena,abinda bata yi a da shi tayi mishi a yanzu wanda hakan ya faranta masa kwarai.
Kallon mubee na yayi cikin farin cikin canza warta yace "pretty darling".
Cikin kisisina da makirci tace "na'am my one"
Riƙo mata hannu yayi yana duban fuskarta yace "yaushe zaki tare can gidan?". Mubeena kuwa cikin kissa tace "Ni dai gaskiya nan ya ishe ni, ba sai naje na takurata ba, dan ni ma ai kafin tazo ni ɗaya na zauna a gidan nan, dan haka itama a barta taci lokacin ta".
Ƙuriii yayi mata da ido yana mamakin canjin da ya gani tare da ita wanda baiyi expecting bah.daure fuska yayi yace "yaushe zaki tare can?". Itama ɗin cikin kissa tace "Ni babu inda zan koma".
Tashi yayi tsaye sai da ya isa wajen ƙofa ba tare da ya juyo ba yace "gobe nake buƙatar ki bar gidan nan zan aiko a kwashe abin amfani! Idan kuma kince ba haka ba zamu ga waye gaba ni da ke".yana gama faɗan haka ya buɗe kofan ya fita daga falon zuwa wajen motar sa, shiga yayi ya bar gidan gaba ɗaya zuwa gidan eelham.
Ganin fitar shi ne sai ta daka tsallen murna tana jin daɗin fara cin nasara a kan shi,daukar waya tayi ta kira zeena,babu abinda ta manta bata gayawa zeena ba, itama ɗin cikin jin daɗin fara ganin shirinta na tafiya dai-dai babu wata matsala tace "gaskiya ƙawa kinyi ƙokari, ni fa banyi tunanin zaki iya ba".
"Lailai ma zeena mi kika maida ni ne? Ai fiye da haka ina iyawa".
"Atoh gara da kika jajige dai! Kinga sai da safe ina tare da mutumin ne".
Bata jira cewar ta ba ta datse wayar cikin happy.
__________________
Cikin bacci yaji yana jin nishin mutum wanda yake fita sosai daga ji kasan mutum yana cikin ciwo mai tsanani.
A firgice ya tashi yana laluba gefen shi ko zai ga Aziza amma bai gano ta ba haka yasa babu shiri ya kunna bed side lap, hakan ya taimaka masa wajen ganin bata anan ai bai san sanda ya miƙe ya nufi cikin toilet ɗin ba.
Kwance ya ganta cikin jini kaman an yanka ƙaramar dabba ga wani yana ƙara fita bul bul bul bul, cikin tashin hankali ya nufa inda take, girgiza ta yake haɗi da kiran sunan ta yana cewa "Aziza! Aziza! Aziza, mi ya same ki?". Ina bata ma san yana yi ba a hankali ta dinga kulle idanu har ta gama kullewa rufff alamar babu rai tare da ita.
Ganin haka da hydar yayi bai san sanda wani jarumta da karfi da yazo masa ba, tashi yayi ya dauke ta ya fito ya ɗauki key mota, cikin Sauri ya fita daga ɗakin zuwa parking lot, back sit ya buɗe ya saka ta sannan ya shiga motar ya jata a sittin daman mai gadi ya buɗe masa tuni.
Bayan sun isa asibitin bai jira komi ba ya ƙara saɓanta ya nufa ciki wanda har yanzu jini na zuba ga kayan shi duk sun ɓaci.
Wata nurse ce ta turo gadon daukan marasa lafiya ga wasu a bayan ta, daura Aziza yayi akai,sukuma suka tura ta zuwa emergency unit, wasu doctors biyu suna shiga cikin ɗakin
Safa da marwa kawai yake a tsakanin ɗakin da Aziza take, yana kuma yi mata addu'a samun lafiya.
Sun ɗauki tsawon lokaci kafin su fito daga ɗakin, babban doctor din ya buƙaci hydar da ya bisa zuwa office.
Koda suka isa bayani yayi masa Yana cewa "alhamdulillah mun samu mun tsaida jinin, Sai dai cikin jikin ta sai hakuri! Sannan a dinga kiyayewa gaskiya, indai kun san tana da juna biyu ta daina aiki mai yawa kaga miscarriage na 6 da tayi kenan kai ma kasani, idan kuma haka ta faru zata iya taɓa mahaifanta wato haka zai bata matsala". cikin sauke ajiyar zuciya yace "shikenan doctor insha Allah za'a kiyaye".
"Allah yasa! Yanzu dai ga wannan magungunan muna buƙatan su yanzu".
Hannu ya saka ya karba yana yi mishi godiya sannan ya bar office ɗin, tausayin Aziza sosai ya kama shi cikin zuciya, dan yasan duk rashin mutumcin Aziza tana son yara sosai, barin ma da ta kwallafa rai a wanna cikin, ashe dai shima ɗin ba rabon ta bane, haka dai ya je pharmacy ya siyo.magungunan ya miƙawa doctor.........
__________________
Wajajen sha ɗaya AS ya dawo gidan,Saida yayi wanka ya canza kaya sannan ya nufi sashen Elham.
Koda yaje ya iske tayi bacci sai ya ja mata kofa ya fita, ita kuwa idon ta biyu dan da taji motsin shi ne ta rufe ido kaman mai bacci, yana fita kuwa ta tashi ta saka wa ƙofan ta key ta dawo ta zauna saman gado hawaye mai zafi yana silalowa daga kyakyawar fuskar ta,ganin dai zata daura wa kanta pleasure ne sai ta miƙe ta shiga toilet tayi alwalla tazo ta gabatar da salla sannan ta dauki qur'ani ta rinƙa tilawa wanda hakan ya ja ta tsawon lokaci,sai da ta fara jin bacci ne sannan ta kwashe sallayan, lokacin wajajen 2 na dare, rage hasken wutan ɗakin tayi sannan ta kwanta.
Wajajen 7am eelham ta tashi daga baccin bayan sallan asuba, gyran gidan ta hauyi,sosai ta kalkale gidan yayi kyau, Tularen wuta ta saka masu ƙamshi
kicthen ta shiga ta haɗa abinda zasu yi break dashi, cikin kankanin lokaci da kammala daman ba wani mai wuya tayi bah, wanka ta shiga tayi ta haɗe cikin shirin ta na atamfa ɗinkin riga da zani sosai yayi mata kyau ga sai kamshi take zubawa.
fitowa falon tayi ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun falon,ta zuba tagumi ta kafe waje ɗaya da ido, ba komi ke damun ta ba sai kewan su goggo da su Ruqqy da Anwar, gashi batada waya bare tace zata kirasu, kaman ance ta kalli wajen TV stand wata paper ta gani da kuɗi a kai, wanda lokacin da take gyara bata gan su ba kuma ta goge wajen, amma da ta tina hankali ke gani sai ta watsar ta tashi ta dauko, da kaman bazata buɗe ba sai kuma ta buɗe, cin karo tayi da handwriting mai kyau wanda hakan shi ya jata ta karanta abinda ke ciki, "na tafi Abuja! zanyi 1 week". Iya abinda ta gani kenan a rubuce, danne zuciyar take son tayi dan kar ta zubda hawaye a kan haka, amma ina ta kasa jurewa kwata-kwata, nan kuwa ta zauna ta sha kuka har ta gode Allah, tana kuma mamakin chanza Warshi lokaci guda,wata zuciyar kuma raya mata yayi wai dan matan shi ta dawo ne.
Tana a cikin wannan halin taji ƙaran shigowar mota, tashi tayi ta leƙa ta window, kwarai kuwa mota ce tayi lodin kaya, a dayar part ɗin motan ya paka, tana tsaye a wajen taga suna ta shiga da kaya kuma da gani kasan sabbi ne, tana nan tsaye sai ga wata motar ta ƙara shigowa itama shaƙe da kaya suma duk sabbi, haka dai suka rinƙa shigar da kayan,, sake labulan tayi ta koma ta zauna tana tunanin ko mi yasa ake saka kaya a dakin, dan ita tunanin ta bai bata mutum ne zai zauna a ciki ba,kusan 2 hours tana zaune har taji fitar motan alaman sun gama, tashi tayi ta shiga ɗaki ta dauko vail ta fita daga falon.
Part ɗin da taga ana jera kaya nan ta nufa dan taga wani wainan suka toya tunda Ahmad baya nan hakkin kula da gidan na a hannun ta,tura ƙofa tayi tana kutsa kanta ciki, idanun ta suka mata kyakyawar gani, ta bangon shigowa taga an saka "u're highly welcome pretty darling uwar gida sarautar mata" ga kuma hoton ta da akayi mata unexpected kaman ma ba a Nigeria akayi hoton ba, sosai kuwa mubeena tayi kyau a hoton,dan anyi hoton ne tana dariya idon ta na wani guri.
Allah sarki eelham cikin danne zuciyarta ta ja kofan ta koma inda ta fito,tafiya take bata ma ganin gaban ta da kyau, haka dai har Allah ya bata ikon shiga cikin dakin ta, tana shiga kuwa ta faɗa kan bed ta fashe da kuka, ita ba dawowar mubee bace damuwar ta ba a'a, abinda ya ɓata mata shine da AS zai gagara ya gaya mata sai dai kawai taga ana shigowa da kaya, na biyu kuma yayi tafiya kuma zai kai har tsawon sati ɗaya amma ya gagara faɗa mata da baki sai a paper a paper ɗin ma a gajarce,,, daga karshe ma tashi tayi ta nufi toilet ta dauraye fuska da alwashin baza ta ƙara zubda hawaye a kan su ba.......
___________________
Karfe biyar mubeena ita da tawagar ƙawayen ta suka iso gidan, zeena ce yar kanzagi wajen bude ƙofan amma tini ta maƙale ta kasa gaba ta kasa baya, maganar bakin ta yana maƙalewa a maƙoshi,, Shamsiya ce tace "zee tashi mana mu shiga kin wani tsaya a ƙofa".
Wayencewa ta yi ta juyo tana cewa "abin surprise ne ya dakatar dani! Dan nayi saurin shiga".
"Mi wannan abin mamakin da kika gani?" cewar mubee "idan kina son ki gani close ur eyes". Ba musu kuwa mubee ta rufe ido, zeena ta kama mata hannu suka shiga,duk wannan abin da take danne zuciya kawai take amma ba dan haka bah da anyi abin kunya.
"Toh yanzu Buɗe ido" slowly ta buɗe har ta gama buɗe su akan hoton ta da welcoming da yayi mata duk da baya nan.
nan fa ƙawayen ta suka dinga koɗata, ita kuwa kanta ƙara ƙato yake tana jin ita ta isa.
Bayan sun zauna ne barra tace "amma ya kamata muje muga wace kishiyar kawar mu, ko kuwa?".
"Maganar ki haka take barra ku taso muje". Cewar Shamsiya dan itama taji zafin kishiyar da akayi wa mubeena wai tana taya ta kishi.
Aikuwa gaba ɗaya suka tashi suka tafi can hadda mubeena,a daidai ƙofan falon sukai knocking.
Elham dake kitchen tana aiki jin ƙaran door bell ne yasa ta aje abinda take ta wanke hannu tans fita daga kitchen ɗin.
ɗaki ta shiga ta yafo vail sannan ta fito tana nufan ƙofan, buɗe musu tayi tana yi musu sannu da zuwa duk da bata gane ko su waye su ba, shiga sukai suna wani kare ma falon kallo ana yi ana gatsine fuska amma dai ya burge su barin ma da falon yake a gyare tsaff ga kuma sai tashin kamshi yake.
Saida suka gama kalle kallen su sannan suka zauna,
Elham daman tunda tayi musu sannu da zuwa ta shige kcthen, abu mai sanyi ta kawo musu tana ƙara yi musu sannu da zuwa.
Cikin iyayi zeena tace "dauke ruwan ki bashi ya kawo mu ba".
Ita kam ba dan taga hoton mubeena ba zata ce wanna ce abokiyar zaman ta saboda kishin da take hangowa a kwayan idanun ta, ba dai tace komi ba, ita kuwa shamsiya ji tayi eelham ta burge ta ganin ba ta da hayaniya,,mubeena kuwa kallo ɗaya tayi wa eelham bata ƙara ba, sai taga ita ɗin ba komi bace a gaban ta, nan kuwa ƙirjinta ya fara bugawa da ƙarfi shiyasa ta sunkuyar da kai ƙasa tana pressing wayar ta.
"Amarya ga yar uwarki mubeena, daman munce bara mu zo a gaisa ki kuma san da zuwan nata duk da dai mun san ya gaya Miki".
Dan guntun murmushi tayi haɗi da cewa "eh haka ne! Sannun ku da zuwa! momy Anwar ina wuni". Danne zuciya tayi sosai sannan ta amsa mata kaman babu komi,,
"Amarya mun gaishe ki bara muje Allah ya bada zaman haƙuri". Tashi sukai suna fita, rakiya tayi musu zuwa ƙofa sannan ta dawo ta koma kicthen tana cigaba da abinda take.....
_____________________
mi yasa kike son ki ɓata muna shiri ne? Kin san shekaru nawa muna wannan shirin? Sai da abu ya zo gab da gab zaki nimi ki wargaza min aiki? Karyar ki,na baki nan da kafin lokacin ki kawo min abinda ake da buƙata".
Da ga chan ɓangaren aka amsa da "ɗan iya! babu inda ban shiga na gaza a cikin garin nan ba amma shiru ba"...... Katse ta yayi cikin tsawa wanda ya rikita ta "Da kata babu abinda zaki gaya min,daga yanzu bazan ƙara sauraran ki ba sai kin kawo wannan abin harinn namu da ya zama ƙofan cikan burin mu". Yana kaiwa nan ya datse kiran,sauke wayar tayi tana ta Safa da marwa da kuma tuna nin ta ina zata fara waye zata saka yayi mata aiki cikin sirri, ta shiga tashin hankali dan tasan halin sa babu abinda bayi iyawa tunda ya riga da ya faɗa haka kuma doka ce.......
____________________
AS ya shiga damuwa akan abinda yayi wa eelham, dan shi da kanshi yasan yayi ba daidai ba, ga ba tada waya bare ya kirata,yasan ko karen hauka ya cije shi bai isa ya kira mubee yace ta kai wa eelham waya ba duk da yaga changes tare da ita.
Kiran mubeena yayi suka sha hira wanda har lokacin zee tana gidan.
Ɓangaren mubeena kuwa sai faman iyayi take wanda zeena take ganin kaman da gayya take tana dai kallo ta ta ƙasan,
Sun ɗauki tsawon lokaci suna waya kafin suyi sallama tana aje wayar.
"Dan walakanci kinsan dai ina jiran ki ne amma kin wani kama yin waya kin manta da batu na,koda yake laifi na ne da na ƙi bin su barra".
"Haba ƙawa ba haka bane,shi ne ya riƙe ni".
"Idan ya riƙe ki baki yanke wayar idan na wuce sai ku cigaba".
"Sorry zee ta, mun tuba".
Tashi tayi tace "ni na wuce masu miji". Wannan karan da mamaki ta dubi zee dan reaction din da ta nuna ya ɗan bata tsoro.
Zee kuwa ko damuwa batayiba tasa kai ta wuce ba tare da ta sallami mubee bah, dan zuciyarta duk s kuntace take.
Ganin fitar ta ne mubeena ta taɓe baki da ɗaga kafaɗa alaman ko a jikin ta.......
____________________
1am
Bayan gari ne sosai baka jin motsin komi a wajen sai na tsuntsaye, daga can nisa kuma wuta ke tashi ga mutane da baƙaken kaya sun zagaye wutan, cikin mutanen nan ba ka ganin fuskan kowa cikin su.
Wani babban mutum ne ga jiki ga kuma tulelen tumbi kamar zata fashe, hakimce yake saman kujerar mulkin sa shima ɗin baka ganin fuskar ta shi, cikin kaukauran murya yace "ɗan yanka! a fiddo da shi"
Nan suka tasa ihu, kafin wani cikin su ya shiga wani ɗaki yana tafiya yana juye-juye, da ƙafa ya buga kofan dakin sannan ya shiga ciki.
Dakin baƙiƙirin ne baka ganin ko tafin hannun ka dan tsananin duhun dake a cikin, ga kuma tsananin warin da yake tashi, wannan mutumin kuwa ko a jikin shi haka ya taka har ya fara jan wani abu a ƙasa ya fito, ashe mutum ke hannun shi, tsakiyar taron nan ya jefa shi cikin rashin imani da tausayi.
"Shugaba ga shinan". Ya ƙare maganar da risunar da kai, yana komawa Wajen shi, shikuwa wannan sarkin tashi yayi daga saman kujerar yana tafiya da kyar har yazo gaban wannan mutumin, sauran mutanen kuwa kan su na ƙasa dan girmamawa ga ogan su.
Cikin ƙatuwar muryan shi yace "Daudau!".
Wanda aka kira da sunan ya amsa da "Shugaba" yana ƙara risunar da kai, sannan ya fita daga Layin shi zuwa wajen da ogan su yake, buɗewa wannan mutumin fuska yayi nan fuskar mutumin ya bai yana, Dattijo wanda a ƙalla zai shekara 65 ya jigatu sosai dan ba ƙaramin azaba suka gana mishi ba,ga numfashi da kyar yake iya fidda shi.
Miƙar da shi tsaye wannan mutumin yayi.
Ogan su ƙara duban dattijon yayi fuska babu rangwame,murya a cinkushe yace "su waye suka aiko ka kayi wa mutane leƙen asiri?".
Ya ƙare da danna masa mahaukacin marin da sai da wajen yayi amsa kuwa.
Cikin gigita da fitar hankali yace "baaa baaa bu ba bu babu wan wan wanda ya aiko ni".
Ba tare da ogan nasu ya ƙara magana ba ya isa gare sa yana soka hannun shi a kirjin wannan dattijon, zurub hannun shi ya shige, nan mabiyan shi suka hau ihu suna murna da tsalle.
Da ƙarfi ya fidda hannun shi, da jini ya ɓata caɓe caɓe "sunɓuƙai!" Yayi kiran sunan wani.
Cikin girmamawa yace "shugaba"
Bai jira komi ba ya dauki wannan mutumin ya miƙawa dodon su.
Saida waje ya natsa ne sannan shugaban nasu yace "godiyar mu ta kusa kaiwa shekarun da muke ta jira muna tsumayi,dan haka kowa ya shirya za'a jajige, hhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhh".
Nan suma suka hau ihu dan wannan ranan suka dade suna jira.........
_________________
Magana take kasa ƙasa dan kar mai gidan ta yaji abinda take cewa "ki na a zaune kin sake baki, bayan ga Hashim nan ya binciko inda suke, yanzu haka rana suke ƙoƙarin sakawa su tafi".
Daga can bangaren aka amsa cikin ɓacin rai tace "shi Hashim har wuyan shi ya kai wannan wajen, wato baiji gargaɗi na a kanshi ba kenan? Shikenan mu bashi last chance muga, sannan ki rinƙa samun ido a kansu har shi mijin naki".
"Zan yi haka! Saida safe" Kitt ta yanke wayar tana samun waje ta kwanta a gefen mai gidan ta, abinda bata sani ba idon shi biyu kuma tun fara wayarta yaji komi, kuma ya gane akan mi take magana, Saida ya bari baccin ta tayi nisa ya rubuta text message da wayar shi na sirri ya turawa Hashim sannan yayi deleting nashi, tashi yayi yana maida wayar ma'adanar ta....
__________________
Zaune take akan sallaya tana kai kukan ta ga Allah mai kowa mai komi,ta daɗe kan sallayan sannan ta miƙe ta kwashe ta samu waje ta kwanta, babu jimawa bacci yayi gaba da ita.
ammie ta gani cikin fararen kaya ga fuskarta dauke da murmushi, duban eelham tayi tace "daughter ki dage da azkar da addu'oi niman tsari daga duk kan wani abin ƙi, duk da nasan bakya wasa da haka, amma ki dage yafi na da, karki kuskura ki zauna babu alwalla a tare dake, ki zamo mai yawan kai kukan ki ga Allah dan babu abin da ya gagare shi,karkiyi wasa da azkar,da addu'oi, Allah ya kare ki, ya tsare ki, Allah yayi miki albarka, Allah yayi miki albarka".
Tashi tayi a gigice da addu'a dauke a bakin ta,zaune ta mike tana kifa kanta a kafarta ta fashe da kuka mai cin rai, kuka take kaman zata shiɗe, kuka ne dake tafe da kewa da soyayyar mahaifiyarta.
tunda Ammie ta rasu bata taɓa yin mafarki da ita ba sai yau a yau ɗin ma a yanzu, nan kuwa ta ƙara volume ɗin kukanta babu mai lallashi sai da ta gaji dan kanta sannan ta miƙe tana shiga toilet ta ɗauro alwalla tazo ta shimfida sallaya tana kai kukan ta ga Allah, har akayi kiran asuba a kunnin ta, gabatar da sallan tayi sannan ta samu waje ta kwanta dan zuwa yanzu bacci ya fara fin ƙarfin ta.........✍️