EELHAM🌹

56&57

by @rabearhwakili


Episode 56& 57📲




بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai



__________________
                              Kukan da tasha cikin dare shi ya haddasa mata ciwon kai mai tsanani ga sai rawan ɗari take,tanason ta kashe ac ta kasa tashi tayi haka,cikin ikon Allah bacci mai nauyi yayi gaba da ita wanda ya jata tsawon lokaci sai wajajen 2 ta tashi,ciwon kan ya dan saukar mata hakan dai ta lallaɓa ta tashi ta shiga toilet tayi wanka haɗe da alwalla dan lokacin azahar tayi, jallabiya ta zira ta dauki hijab ta gabatar da salla, koda ta idar bata tashi ba Saida tayi addu'a sosai sannan ta tashi, dressing mirror ta nufa ta ɗan gyara fuska da shafa lotion, doguwar riga ta material ta saka dan bata iya saka kaya masu  nauyi.
Fita tayi dan ta samu abinda zata ci ta sha magani, noodle ta dafa sai Golden morn,fitowa falo, da ta gama sai ta kwashe kayan ta kai su kitchen ta wanke su ta fito.
Kallon falon tayi taga babu abinda ya same shi har yanzu yana nan kal kal daman jiya da yamma ta gyara, abin shara ta dauka ta shiga dakin ta ta gyara tana yi tana hutawa haka dai har ta gama.
Har ta kwanta ta miƙe kamar wacce ake muntsila ta tashi ta buɗe waldrop ta dauko ATM ɗinta zira hijab tayi ta fita zuwa gate.
Bayan sun gaisa da gate man ɗin ne cikin rashin hayaniyar ta da ya ƙaru tace "dan Allah baba ina driver yake".
"Bara a kira miki shi Hajiya".
   "Nagode baba"
Dakin da driver yake ya shiga ya kira shi,tare suka fito tanimu driver yana gaida ta cikin girmamawa,
  "Alhamdulillah! Daman dan Allah "zaka siyo min waya da sim ne"
Cikin girmamawa yace "ba komi Hajiya wata product". "Samsung sai sim".
 "Insha Allah Hajiya".
Godiya tayi mishi tana komawa ciki.
Tana zaune a nan taji ƙaran door bell tashi tayi ta buɗe, Mallam tanimu driver ne,miƙa mata ladar hannun yayi, karɓa tayi tana yi mishi godiya dan taji daɗi. Kulle ƙafan tayi ta koma cikin bedroom, duba wayar tayi taga ba karamar waya ya siyo mata ba dan tana da kuɗi a account ɗinta sosai,saka sim tayi sannan ta saka charge dan ya haɗo mata da igiyar chaji.
Saida wayar ta cika sannan ta ciro tayi kiran goggo sun daɗe suna fira kafin suyi sallama,kiran Ruqayyah tayi taji wayar a kashe, meenal ma tayi kiran ta amma bata yi picking bah.
Tashi tayi taje ta daura abinci kodan masu aikin gidan.......

_____________________
                                      "Aziza kiyi haƙuri ki bar kukan nan haka,idan Lokacin da Allah yayi zaki haihu za kiyi, dan haka ki kwantar da hankalin,ki cigaba da rokan Allah masu albar kinji?".
"Shikenan Allah ya kawo masu albarka".
Da Amin ya amsa yana mai jin tausayin ta cikin zuciyar shi dan soyayyar Aziza da yara Allah kadai yasani.
"Cikin bata ƙarfin gwiwa yace insha Allah kafin nan da kwana 7 zan ƙara baki wata ajiyar in Allah ya yarda".
Cikin jin kunya kaman ba Aziza ta kife kanta a jikin shi tana dariya murya can ƙasa tace "Amin".
"An shige su wai amsaw kikayi?".
Ɗagowa tayi tana mishi hararan wasa tace "to da kar na amsa? Inace addu'a kayi?".
"A'a fah ni bance karki amsa ba! Ba ruwa na".
Yadda yayi maganan ya bata dariya cikin dari ta furta "better for u"
  "Kin dai manta better for us dai"
Dukan wasa ta kai mishi shi kuma ya goce,nan dai suke ta firan su kaman ba Aziza masi bah, "yauwa baby nace ya kamata a gayawa su momma dan su san halin da ake ciki ko?".
Dan ɓata fuska tayi tace "a'a ni bance ba, ai nariga da naji sauƙi nikam, a barshi ba sai anyi min terere ba".
Shi dai ya rasa dalilin da yasa Aziza da momma jinin su bai gamuwa waje ɗaya cikin kauda maganar ya furta "shikenan! Doctor ma yace za'a bamu sallama zuwa anjima".
"Allah ya kaimu daman zama cikin shi duk ya ishe ni".
"Anya kuwa".
"Anya mi ne?".
"A'a babu"
"Ni ba wannan ba gwara muyi ta da waje wa tun yanzu ahem".
"Toh ina jin ki"
"So nake daman idan Allah yasa zan ƙara samun wani cikin kar ka gayawa kowa kuma ko Hajiya (momma)ban yadda ka gayawa ba".
"Aziza rigima,toh shike nan Allah ya kawo rabo mai albarka". Da Amin ta amsa, suna ci gaba da firan tasu.....


_____________________
                                     "Dan Allah ka rabu da ni, haba Ni na fara gajiya da kai ina dalili kullum abu ɗaya, kai ni daga yau karka ƙara zuwa min gida idan kuma kace ba haka ba mu zuba mu gani, banda ma rashin zuciya nace maka na gaji haba ko ana dole......" Katse ta yayi ta hanyar faɗin "haba sarauniya ta farin cikin zuciyata! Ki yi haƙuri nasan tsoro kike ji dan kar wannan shashashan mai gidan naki ya gano, to ki kwantar da hankalin ki komi yazo karshe mun kusa kauda shi nan kurkusa, Kinga daga nan kin zama mallaki ta daman kwace yayi min".cikin samun nutsuwa tace "da gaske kake ko dai kawai kana son na kwantar da hankali ne?".  "Haba ke kuwa! Kema dai kin san bazan faɗa abinda ba haka yake ba a gare ki,dan haka ina mai ƙara miki albishir nan kusa zai ware". Cikin ƙatuwar dariyar farin ciki ta furta shi yasa nake ƙara sonka, Allah ya bar min kai,amma aikin ya zama cikin sauri dan na gaji da ganin sa".
Kar ki damu uwar ƴaƴa na! Wai wannan garan yana ganin fa kaman yaran nan nasa ne Koh?". 
Aikuwa dai kasan ba wai ya cika hankali bane". Kai sarauniya ta mijin ki ne fa ki k....." Ƙaran faɗiwar abu ya katse mishi maganar shi cikin tashin hankali suka miƙe jiki na rawa barin ma shi, cikin ruɗu da tashin hankali suke, suna cikin wannan halin suka ƙara jin sawun tafiya alamun wanda yake musu laɓe ya gudu,tashin hankali sun shige shi fiye da zato da tsammani sai kuma Allah ya hanasu su leƙa wa ke a wajen. Cikin tashin hankali tace "kaga abinda nake ta gaya maka kenan ba, na hanaka zuwa da rana amma kaƙi kaji, yan zu ya zamuyi? Waye ya ke yi mana laɓe? Na shiga uku". Cikin lallashi ya furta "Ki kwantar da hankalin ki, ko waye ya yi haka sai yayi da ya sani,kin san sabida sonki da nake babu abinda bazai iya ba, koma waye zan kawo miki shi har gaban ki ki yanke masa hukumci da hannun ki, kinji?". Tasan zai yi abinda yace ɗin cikin sauke ajiyar zuciya tace "har naji hankali na ya kwanta". "Da yake ke natsoraciya ce ke ba?". Ya ƙare maganar da tsokalan ta "eh naji nidai zoka wuce tun kafin mai gida ya dawo". Oo sabida wannan wawan kike korata?". "Ni ban kore ka ba, ga waje zauna idan aka kama mu ba shikenan ba". Cikin dariya yace"abin bai kai nan ba Bara naje".
Sai bayan kwana biyu kuma, idan kace ba haka ba koda kazo ba za ka i'she ni kallo ba".
"Ok ba damuwa sai an jima". Nan sukai sallama suka rabu,,,yana fita daga gidan ya fashe da dariya yace "wawiya kawai kina tinanin zan aure ki ne? ina gama samun abinda nake so kema zan aika ki inda zan aika mai gidan naki da ƴaƴan ki hhhhhhh". nan ya ƙare maganar da ƙatuwar dariya yana ganin burin shi ya kusa cika.....

____________________
                                   Tunda sakon nabil ya shigo mishi sai ya canza salon tafiyar tashi dan yasan yanzu haka akwai idon yan bin ciken su a kan shi, yanzu haka baida ikon yin wayar sirri dan sun saka mishi tsaro a waya yan zu duk wayar da zai yi suma ta bangaren su zasu ji, ga baida ikon fita ya siya wata dan duk inda ya shiga yana ganin gient suna bin bayansa wanda shi bai ma san inda ta samo su ba, dakin sirrin shi ya shiga yana barin wayar shi a falo, daki ne dauke da su systems wajen computer ya nufa cikin kwarewa ya fara aiki a ciki,typing yayi ya tura ta sms,yana turawa ba jimawa sai ga kiran waya ya shigo cikin wayar shi ta sirri,,, dauka yayi bayan sun gama gaisawa ne yayi shiru alaman yana sauraran dayan bangaren, can ya furta "a yanzu dai zan  dakatar da bincike ta waje na, dan sun sa mun ido,ga wayata ma sunyi min kutse a ciki". Shiru yayi yana ƙara sauraran abinda ake faɗa can yace "toh shike nan Allah ya taimaka mana". Nan ya aja waya sukai sallama shi kuma ya fito daga ɗakin zuwa falo inda ya samu matar shi zaune, zama yayi suna ta firan su gwanin birgewa....


________________
                           Da niyan sati ɗaya ya tafi zuwa Abuja amma yanzu kwana uku da zuwan shi yaji garin ya ishe shi gaba ɗaya dan kewar EElham ke nuƙurƙusan shi cikin zuciya, ganin dai ba zai iya daure wa ba sai yayi bucking flight wanda zai tashi da 7pm,,, koda yayi sallar magrib bai koma gida ba airport ya wuce lokaci ta kusa, da zuwan shi babu jimawa Flight ɗinsu ya daga zuwa Kano batare da ya sanar da mubeena ba,,,,d suka sauka ya fidda waya ya kira driver ɗinsa akan ya taho ya same shi a airport,,, yana a wajen sai ga driver yazo, shiga yayi suka dauƙi hanyan gida lokacin har anfara kiran sallah, isar su gida sai bai shiga ba ya wuce zuwa Masallaci dan gabatar da sallar isha'i..  
     idar da sallan ta kenan ta fito falo dan taci abinci,koda ta saka abinci taji kuma baza ta iya ci ba dan yau haka ta wuni da tashin zuciya ga kuma kwaɗayin da take ji, ganin dai baza ta ita ci bane sai ta shiga kitchen ta haɗa mai da yaji guri guda ta fito falo ta rinƙa dangwala tana sha har da su lumshe ido,,, daukar wayar ta tayi ta kira Ruqayyah cikin Sa'a kuwa ta shiga ,,"amarya bakya lefi ykk ya gida?".
Daga ɓangaren Ruqqy ta amsa da "alhamdulillah amarsu ya amarci?". "Angonci dai".
Kiji min Mallama daga tambaya zaki gaya min baƙa?". Ta ƙare maganar cikin shaƙiyanci.
"Allah ya shirya ki, ya yaya Umar?"
"Wai habitty?".
"Ke dai kika sani" cikin dariya Ruqqy tace "yana lafiya qlau ya naki angon?". 
Cikin taɓe baki tace "angon momy su Anwar dai" daga jin yadda tayi Maganar zaka gane akwai kishi a ciki, shikuwa as da yaji maganar sai yaga kaman dan bata son shi ne yasa ta  faɗi haka, danne zuciyar shi yayi yana ƙarasawa wajen ta, batare da ta ankara ba taji an zare wayar  dake kunnin ta,, da sauri ta jiyo dan taga waye wannan,, shikuwa ƙara haɗe fuska yayi yana katse call ɗin,aje mata wayar yayi a gefe da mamakin ko a ina ta samu wayar, danshi dai yasan batada waya duk suna wajen shi, wata zuciya kuma ta gaya mishi ai tafi ƙarfin ta tsaya jiran ka kawo mata shine ta siya wata. Kauda tunanin yayi daga ran shi fuska babu wasa yace "ki sa me ni a part ɗina kafin nan da mint 10". Yana gama faɗa yasa kai ya fice daga part ɗin,,,bata son kayan kace nace yasa ta shiga ɗaki ta dauki hijab sannan ta bi bayan sa, sashen da take tunanin nasa ne ta shiga, zaune ta ganshi yana ta fama da dannan waya, koda tayi sallama a kan labba ya amsa ba tare da ya dube ta ba, ita ma cikin shan ƙamshi ta biɗa waje ta zauna kujerar da ke nesa da shi, tana zama babu jimawa mubeena ta shigo sai iyayi take,cikin makirci tace "amarya barka da dare". Elham bata iya muna funci ba, shi yasa bata amsa mata ba tayi kaman bata ji ba, as ya lura da haka sai bai ce komi ba, mubeena kuwa cikin nuna bata damu ba ta samu waje ta zauna gefen shi, can kuma ta tashi ta dauko masa ruwa ta zuba a cup ta miƙa mishi, cikin jin daɗi yayi mata godiya duk da ba ƙishin yake ji ba amma yasha kaɗan, Saida ya aje cup ɗin hannun sa ne, sannan ya fara da addu'a kafin yayi musu nasiha da su haɗa kawu nan su dan shi bai son faɗa,ya kuma buƙaci da su girmama junan, amsawa mubeena tayi da "insha Allahu zamu zama masu kiyayewa Allah ya bamu ikon haɗa kawunan mu".
"Amin Amin" kallon eelham yayi ta ƙasan ido yaga sai dannar wayarta take wato ta ba ma banza ajiyar su, kauda kai yayi yana jin babu daɗi. Cigaba yayi da faɗin "sai maganar kwana, kune masu yanke hukunci, ya kuke son ta kasance?". Wannan karan sosai mubeena tayi kokarin danne zuciyar ta, tace "Ni dai a nawa ganin ko kwana uku uku, ko ya kikace amarya?". Idan eelham ta tanka cushions da suke falo suma sun amsa, ganin da AS yayi baza ta amsa ba, sai yace "shikenan haka yayi". Bayan sun gama maganar ne mubee ta miƙe tana yi musu Saida safe amma as ya katse ta da faɗin "pretty ina zaki? Ai yau ke kike dani" yayi maganar cikin gayya, wanda babu shiri eelham ta ɗago tana duban shi........✍️