EELHAM🌹

58&59

by @rabearhwakili

Episode 58& 59📲




بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai



__________________
                               Zuba mishi ido tayi babu ko ƙeftawa,,,cikin dauriya da basarwa ta cire idon  akan su,,,wanda kallon da tayi wa AS ba ƙaramin tsarguwa yayi da haka bah sai yaji babu daɗi kaman baiyi dai-dai,amma wata zuciyar na gaya masa ai ya kai lokacin ta,,,yana cikin saƙe saƙen shi yaji muryan ta a bazata ta furta "no need mommyn Anwar, na bar miki kwanan duka". Tana gama faɗin haka tasa kai ta bar musu daki,,shikuwa AS he was very shock da batun ta, hakan kuma ba ƙaramin ɓata mishi rai yayi ba,mubeena kam dan murna ta ji take kaman ta goya EElham tayi ta gudu da ita,,,cikin zafin zuciya ya tashi ya hau sama da alwashin zata sani kuma zai bata mamaki..
      Tana shiga ɗakin bata tsaya wani bata lokaci ba ta shiga toilet tayi alwalla tazo ta gabatar da nafila bayan ta idar ta daura da tilawa wanda hakan ya ja ta tsawon lokaci sai da taji bacci na fin ƙarfin ta ne sai ta miƙe ta na cire hijab daga nan sai ta kwanta babu jimawa bacci yayi gaba da ita.
    Gudu take sosai dan ganin ta tserewa wannan babban halittar da ke binta a baya gudu take wanda da kaga gudun kasan ta cetan rai ce, haka ta dinga fasa daji bata ko jin zafin ƙayar da take takawa ga ƙafar sai jini take amma bata damu ba, burinta ta samu ta gudu ma wan nan halittan kar ya kamata.
   Babban halitta ce wacce bata da kyau na gani ko kadan ga jikin shi duk gashi ta ko ina, ga kanshi ɗan ƙarami kamar lizard sai dai jikin shi tana da girma kamar giwa,duk da jikin shi hakan bai hana sa gudu tuƙuru ba,yana saura kadan ya kamata Allah ya bata ikon furta addu'a a bakin ta wanda nan da nan wannan halittan ta dakata daga binta,ganin hakan da tayi ne sai ta tsaya tana sauke nunfashi da addu'a a bakin ta har yanzu bata dai na ba,,,sadab sadab yazo gareta ya cafke mata ƙafa,cikin razana take son ta ƙwaci kafarta amma ina,,,, cikin babban murya da babu daɗi ji yake faɗin "Khadijah ki barni na cika burina,wannan shine dai-dai lokacin cikan burina wanda na ɗauki shekaru ina jira....." Ƙatuwar sandar da ta kwaɗa mishi a bazata yasa ya saki ihu mai rikitarwa,dan  kafin ta buga masa Saida ta karanta addu'a sannan,,, tana tsaye Allah ya cire mata tsoro taji ya fara sakar mata ƙafa can kuma taga wannan abun ya fara rikiɗa yana zama mutum,,,,, a mugun zabure ta falka da addu'a a bakin ta, jikin ta sai rawa take,ga ya jiƙe shankaf da zufa, da addu'a ta tashi ta shiga toilet tayi alwalla tazo ta dinga azkar tana kai kukanta ga Allah.
    Sai da tayi sallar asuba sannan ta koma gado tayi bacci,,,sai wajajen 10am ta tashi, shima ba wai baccin ya ishe ta bane, gyaran ɗakinta tayi tsaff sannan ta fita falo nan ma ta gyara shi ta saka Tulare masu daɗin kamshi, kicthen ta shiga ta daura ruwan zafi da su citta a ciki yana tafasa ta juye a cup, shan shi ta hauyi haka babu komi a ciki,daman dan cikon cikin da take ji ne,,,Saida ta gama shan ruwan ne ta shiga daki tayi wanka ta haɗe cikin shirin ta ta doguwar riga ta atamfa.
Kitchen ta koma ta haɗa cornflakes ta fito falo, har zata fara sha sai ta aje cup ɗin kan center table dake anan ɗin,ɗaki ta shiga ta dauko wayarta ta dawo,zama tayi tana Shan cornflakes ɗin, dake bata haɗa da yawa ba nan da nan ta shanye ta daure cup ta maida shi ma'ajiyar shi,falon ta dawo ta zauna tana duba abu a wayarta,,,tana nan zaune wajen hour 1 da rabi taji cikinta ya taso mata da ciwo lokaci guda,,, cikin azaba ta aje wayar tana dankam cikin,nan da nan zufa ya jiƙeta,jikinta sai rawa yake,da abun yafi karfin ta ta zube A nan ƙasa jini na fita daga jikinta wanda hakan shi ya haddasa mata fita daga cikin hayyacin ta,tun tana gani kadan kadan har idanun ta suka rufe ruf jini na cigaba da zuba daga jikinta.....
     Har ya nufi parking lot sai yaga idan yayi haka bai kyauta ba shi yasa ya dawo ya shiga ɗakin eelham yana ta danna door bell amma shiru ya kusa 10 mint a tsaye a nan har zai juya sai yayi tunanin tura ƙofan, yana turawa kuwa kofa ta buɗu kutsa kai yayi a ciki yana kallon falon da yasha gyara ga sai kamshin ke tashi, kamar ance ya dubi ta gefen cushion ya hango eelham kwance cikin jini sosai dan har yanzu babu abinda ya dauke daga jinin dake zubar mata.da sauri ya dauke ta ya nufa mota yana bata wuta ya bar gidan.
Ko kafin ya isa yayi kiran family doctor ɗinsu su yasa yana isowa aka daura ta akan abin daukan majinyata suka nufi emergency yaso ya shiga amma doctor ɗin ya dakatar dashi. 
Alhamdulillah sun samu sun tsayar da jinin harda numfashin ta da ya dauke, cikin nasara, bayan sun fito ne suka nima ƙarin jinin, ba musu AS yace a diba nashi jinin cikin Sa'a yazo ɗaya.maƙala mata karin jinin akayi shi kuma ya kira su Ummi ya sanar musu ga eelham batada lfy suna hospital,cikin tashin hankali tace gasunan zuwa.....
    "Haba Aziza ke da baki gama warkewa ba ina zaki kuma,ba jimawa aka baki sallama daga hospital ba fah?". Cikin taɓe baki tace "inace kafata da jiki na ne? Dan haka just put eye idan kaga baza ka iya ba,take it off". Tana gama faɗin haka tasa kai ta wuce daga ɗakin zuwa parking lot, bata yadda driver ya kai ta ba, da kanta tayi driving, a daidai ƙofan gidan Ruqqy tayi parking,Saida ta tabbata babu fuskan sani sannan ta shiga cikin gidan kamar wacce tazo sata, daman an bar mata gidan a buɗe alamun dai an san da zuwan ta, kofan falon shima ta tura, inda ta samu Ruqqy a falo, ganin ta da ruqqy tayi ne yasa cikin fara'a ta tarbe ta dayi mata sannu da hanya,cikin Tata fara'an tace "amarsu Kinga yadda kika yi kyau kuwa? Anya ba'a samo mana baby ba?". "Innalillahi baby fa? A'a". Saida Aziza ta dara sannan ta furta "uhm sai mun gani dai". "Ni dai babu ruwa nah". Cewar Ruqqy cikin dariya, tashi tayi ta dauko mata abu mai sanyi suna ƙara gaisawa, "ashe abinda ya kuma faruwa kenan sister?". Cewar Ruqqy "kedai bari abun sai a hankali, Ni kar ma aje a nakasa mutum a banza a hofi". Cikin dariya Ruqqy tace "haba dai sister waye zai nakasa ki? Ai da zaman garin Kano ya gagare shi". "Wannan tsohuwar muguwan nan mana". "Surukar taki kuma?". Wata harara ta sakar mata tana cewa "a inda babu surukai ba, ga dai ɗanta babu ruwan shi amma kin ganta nan muguwa ce ta ƙarshe". "Allah ya ganar da matar nan dai". Cikin taɓe baki Aziza tace "Amin idan ita mai shiryuwa ce ba". "Daman ina ta biɗan ki sis, har ma ina cewa ko zan zo can gida in same ki ne ko ya abin zai kasance, dan na kira wayarki kashe, nace ko lafiya, ashe dai aika aikar da matan nan tayi miki kenan". "Ai gwara da baki zo ba, kinsan duk ta saka ana bin mata sawu na, duk da dai ba sanin ki sukai ba amma sai sun bin ciko ko ke wace! Yanzu ya ake ciki?". "Al amarin sai hanklai......" Nan ta zaiyane mata abinda zata faɗa sannan ta tashi zata tafi, rakiya Ruqqy yayi mata har wajen gate sallama sukai ta koma ciki.numbern eelham ta kira amma har ta gama ringing bata ɗauka ba Saida tayi mata 3 miss call nan ɗin ma not answer,ganin haka ne sai ta barshi da tinanin kilan ko tana bacci ne ko bata kusa da wayar.
   Elham ta farka jiki da sauƙi sai dai complain na jiri da tayi, nan ɗin ma sunce ba komi bane zata daina ji,sun dai ƙara mata allura ta samu bacci bata tashi ba sai gab da magrib lokacin su ummi sun daɗe da zuwa harda grandma,taimaka mata ummi tayi ta samu tayi wanka,bayan ta fito Ummi ta miƙa mata cup din tea mai zafi,ba musu ta karɓa tana sipping a hankali,da sallama ya shigo cikin ɗakin, Ummi ce ta amsa amma grandma ko kallon shi batayi ba,gaisar da Ummi yayi yana tambayan ta mai jiki sannan ya juyo wajen grandma ya gaisheta, murya ba yabo ba fallasa ta amsa tana aika mishi da kallan banza wanda shi bai san mi yayi da take mishi wannan kallon bah, "Ahmad mi doctor yace yana damun daughter?". Amsawa yayi da cewa "sun ce sai result ya fito sunyi mata test akwai abinda suke tunani". "Toh shikenan Allah yasa muji alkahiri". Da Amin ya amsa yana maida duban shi ga eelham da ta nuna kaman bata san da zaman shi a gurin ba, so yake ya tashi ya je gare ta amma fuskar Ummi ya hana sa inda grandma ce da tuni an wuce wajen, kaman kuwa sun san abinda yake so sukace zasu koma gida daman jiran shi suke yazo, cikin girmamawa ya amsa da toh, maida duban ta ga eelham tayi ta furta "daughter mi kike son na taho Miki dashi idan zan dawo?". Sai da ta lumshe idanun ta sannan tace "bana jin daɗin bakin na a haɗa mun  abu mai dan tsami". Cikin sauri AS yace "a'a ummi a dai yi mata pepper soup, zai fi wannan abun dan gudun ulcer".  "Toh sannu isashen,abinda take so shi zata ci, ba taka ra'ayin ba ahemm". Cewar grandma da tayi maganar kamar dama tana jiraye dashi, "atoh, kaida ba kai zaka ci ba amma kana wani bada excuse na banza, toh shi zanyi mata, idan na kawo karka bari taci". Shi fa sun fara bashi mamaki shi bai san abinda yayi ba, to Kodai ita ta gaya musu wani abun,kulle kofan da yaji ne ya maida shi hankalinsa daga tunanin da ya faɗa,ganin sun wuce ne, ya ƙarasa zuwa wajen ta yana zama a gefenta da riƙo mata hannu, cikin murya mai sanyi ya furta "ya jikin naki?". Murya a cinkushe ta amsa da "lafiya". Kallan kyakwar fuskar ta yayi ganin bashi take kallo ba sai yasa hannun ya juyar da fuskar ta zuwa gare shi,datse idanun ta tayi alamun bata son ganin shi,"open ur eyes". Yi tayi kaman bata san mi yake cewa ba, yasan ta da taurin kai harda na bala'i,ganin dai baza ta buɗe bane sai ya ƙara matsawa kusa da ita, cikin muryan raɗa ya furta "dejarht nayi laifi ne da baki son ki kalle ni?". Cikin son ta tura mishi haushi tace "nikam mi kayi min,bare na ƙi kallan ka, kasan ai sai mutum ya kai ake kallan sa, inaga dai kaman da sau........" Cikin razananniyar tsawa ya katse ta ta hanyar faɗin "enough for u, kinsan am not ur mate, karkumakiga ina lallaɓa ki kiyi tunanin wani abun daban, tun wuri U better back to ur senses! Stupid". Yana kaiwa nan ya fita harda bugo mata ƙofa da ƙarfi kamar zai karye ta, taɓe baki tayi tana samun waje ta kwanta, ɗan zaman da tayi ta jita duk ta gaji,,,koda ummi ta dawo ta iske babu AS a ɗakin cikin mamaki tace "daughter ina mijin naki yaje?". Sunkuyar da kai ƙasa tayi sannan tace yaje ya dawo dan yanzu ya fita". "Amma shi ma dai! shine bazai jira har na zo ba zai wuce? Idan kika buƙaci wani abun fa?".  "Kiyi hakuri ummi". Shikenan to! Tashi kici abinci zaki ji daɗin shi babu musu kuwa ta miƙe zaune Ummi tana feeding ɗinta kamar wata baby, suna a haka sai ga umma ta shigo, cikin fara'a suka gaisa Elham ma ta gaida ta, amsawa tayi da kulawa da tambayar ta jikin nata.  "Allah ya ƙara sauƙi daughter!, dawowa ta kenan Hajiya mama take ce min ai Elham bata ji daɗi ba, nace bangan ta zama ba". "Jikin da sauki ai ba kaman ɗazun ba". Fatan samun lafiya sukai yi mata suna masu canza fira irin nasu na iyaye...bayan wucewar umma Elham ta matsa sai an sallame ta ita ta gaji da zaman asibiti, ba musu kuwa ummi taje ta sanar da doctor, cewa yayi su dan jira result sai su tafi da shi gaba ɗaya,,, AS ya dawo amma ko kallan inda eelham take baiyi ba dan Maganarta ta ɗazu ba ƙaramin zafan shi tayi ba, Ummi tayi mishi bayanin doctor zai sallame su dan eelham ta buƙaci haka amma yace su jira result sai su tafi dashi,cikin gamsuwa ya gaɗa kai yana kwashe kayan da yake nasu yana kaiwa mota haka dai har ya gama,,, suna nan a zaune sai ga doctor ya shigo, musabaha sukai da  da AS, sannan ya miƙa mishi papern haɗi da cewa "alhamdulillah ga result nan ya fito, saidai ba ƙaramin Sa'a tayi ba dan maganin da tasha suna da ƙarfi wajen yin abotion, wanda ko ɗaya mutum yasha sai a hankali bare ita da tayi over does ɗinshi,dan haka sai haƙuri cikin da yake jikin ta dan wata ɗaya ya zube"............✍️
   
Kuyi haƙuri da wannan pls ban samun zama kwana biyun nan afwaan