EELHAM🌹

60&61

by @rabearhwakili

Episode 60& 61📲




بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai


                             Tsamm ummi ta miƙe tsaye babu shiri,cikin rawar murya tace "ban gane ba,ban gane abinda kake nufi ba doctor?". "Kuyi haƙuri haka Allah ya tsara".yana kaiwa nan ya fice daga dakin. As kuwa kasa motsawa yayi daga inda yake zaune ya duƙar da kai ƙasa ga zufa sai tsatsafo masa yake, Ummi ma jikinta rawa yake sosai cikin rawan murya ta kalli eelham tace "eelham ya akayi? Daman kina da ciki ne? Ko cikin waye? Cikin wata daya fa EElham daga ina, du du du auren ku  kwana tara kenan". Cikin fitan hankali ta dinga jero mata wannan tambayar, kasa ta ƙara yi da kanta tana jero addu'oi,ta dake zuciyar ko hawaye babu a kan fuskarta, cikin daka tsawa ummi tace "baza ki buɗe baki kiyi magana ba,ko sai na saɓa miki". Yin Shirun shine mafi alkhairi a gareta shi yasa tayi shiru bata tanka wa Ummi ba to idan ta tanka mi zata ce?. Tashi yayi fuuu ya fice daga ɗakin ba tare da ya yadda ya ƙara kallon ta ba dan wani kuna yake ji a kanta, office ɗin doctor yaje babu sallama ba komi ya afka cikin office ɗin,cikin tafasan zuciya yace "taya akayi ta samu ciki har ya zube?". Ikon Allah, da mamaki doctor ke duban shi, to shi kam taya za'a yi nasan daga in da  ciki ya fito? "Haba dai as nikam Taya za'a yi na sani ni,abinda na gani kenan shi na faɗa,yadda a kayi ya samu ni ban sani ba". Huci mai zafi ya fesar yana jin zuciyar shi na tafasa koda ya fito daga office ɗin doctor bai koma dakin da su eelham take ba sai ya wuce parking lot ya tasar da motar shi yabar hospital ɗin a guje kaman zai tashi sama. Shirun da taji yayi yawa ne yasa tayi kiran driver yazo ya dauke su suka koma gida,part din grandma ta shiga amma bata same ta nan ba kama hannun eelham tayi suka koma part ɗin goggo, nan suka samu grandma da goggo suna fira irin tasu ta masu shekarun su. "Sannun ku da zuwa! Takwara jiki tayi sauƙi,toh Allah ya ƙara afuwa". Da Amin goggo ta amsa tana duban fuskan EElham da damuwa da tashin hankali ta cika a kanta ta,ga kuma fuskar ummi shima a cinkushe da tashin hankali. Cikin dattako irin ta goggo tace "in-law ya mai jiki?". Cikin jin kunyarta ta amsa da"jiki da sauƙi sai dai..." Sai kuma tayi shiru tana mai jin kunyar sanar musu. "Saidai mene muna jin ki". Cewar grandma, ta buɗe baki zata yi magana kenan sai ga AS ya shigo fuska babu annuri a cikin ta, daga tsaye da yake ya miƙa musu gaisuwa shima a cinkushe, bai jira komi ba ya daura da faɗin "ga tanan ku tambaye ta a gidan uban waye ta samo ciki". Wata muguwar faduwar gaba ya riske goggo baki na rawa tace "ciki kuma?". Bai tanka mata ba, ganin haka ne sai grandma ta furta "bansan shashancin banza da hofi, zaka fito kayiwa mutane bayani kokuwa?". Bai ce mata komi ba ya taka ya isa gare ta yana miƙa mata paper da doctor ya bashi, "bayani nace kayi min bawai ka miƙa min takarda ba, cewa nayi mike faruwa?". "Ba da kai ake magana ba ne Ahmad?". Cewar bappi da shigowan shi da Abba kenan daga masallaci suke shine suka biyo nan, cikin magana ƙasa ƙasa yace "bappi gata nan, ta faɗa muku abinda tayi". Cikin fusata grandma tace"Kai banson hauka taya za'a yi ana tambayarka kace wai a tambayi wata". Shiru yayi bai kuma cewa komi ba, dan idan yace zai yi magana akwai ƙura shi yasa ya zabi da yayi shiru kawai. "Ummi na mike faruwa ne?". Cewar bappi yana duban ta da tunda suka shigo bata dago kai ba, yanzu ɗin ma ita ma bata ce komi ba, cikin jin haushin ta as ya daka mata razananniyar tsawa yana cewa "baza ki buɗe baki ki fadi daga gidan uban waye kika samo ciki ba?". Sam AS bai cikin hankalin shi kishi ya rufe masa ido baya ji baya gani. Murya na rawa bappi yace "ban gane ina ta samo ciki ba?". Goggo da jikin ta yayi sanyi tace"Kaima dai ka tambaya,duk gasunan tun dazu ake tambayar su amma ko wanne yayi shiru harda ita in-law din". "Daman likita ne yace..." Sai kuma tayi shiru dan tana jin nauyin da za'a ce maganar nan ya fito daga bakin ta, lura da haka ne sai grandma ta ce "in-law faɗi ko ma mene kanki tsaye". Saida tayi ta maza sannan ta furta "doctor yace tasha maganin zubda ciki ne,kuma cikin ya zube dan wata ɗaya". Tashin hankali da jin abinda ba'ayi tsammani ba ya daskarar da goggo a wajen ta zama kaman mutum mutumi bata ko motsi, "innalillahi wa'inna alaihi raji'un, wani likita ya fadi haka?, Allah na tuba banda ma sharri irin na doctor ina eelham ina ciki bare kuma har ta barar auren su fa ko kwana goma batayiba bare ace har an samu ciki na wata ɗaya". Cewar grandma dan ita bazata dauki wannan shirmen ba, Abba da bappi suma basu yadda ba, dan sun shaida halin eelham bare tunda suka dawo nan fitar ta bai wuci so biyu ba shima ba ita ɗaya ta fita ba. "Haka ne kam Hajiya mama,sai indai yayi shirme". AS da yaga suna so su maida maganar ba komi bane yasa a fusace yace "ki buɗe baki ki gaya mun daga gidan uban wa kika samo ciki?". Ka sa jurewa tayi wannan karan sai da ta jiyo tana kallan shi da idanun, ga fuskar nan fayau babu komi Tare da fuskarta, cikin sanyin murya tace "tunda ba naka bane ina ruwan ka da sai kasan  daga inda cikin yafito? Kaga kuwa ba lailai kasan daga inda ta fito ba". Tana kaiwa nan ta miƙe ta shige ɗaki, wanka tayi ta saka kayan bacci tana kwanciya a gadon, grandma ce da goggo suka shiga dakin eelham, ganin su da tayi ne yasa ta miƙe zaune tana zama gefen goggo ta shige jikin ta ta fashe da kuka, mai cin rai cikin kukan take faɗin "goggo zaki yadda na zubda ciki? Wallahi goggo ban san komi ba, ban taɓa aikata abin da yaya yake tunani ba, ban san komi ba goggo...." Kuka ya kufce mata wanda ya katse mata maganar ta, goggo ma jikinta yayi sanyi qlau, nan suka fara lallashin ta amma ina kaman ƙara zugata suke, "goggo kin san yadda nake yi idan zan yi period, wallahi period nake ban san  komi ba bayan haka, ban aikata abinda yake tunani ba,ban aikata ba".  "Namecy baki aikata ba ko duka duniya sun yarda zaki aikata mu baza mu taɓa yarda ba, shima dan dai bai cikin nutsuwan shi ne, ki kwantar da hankalin ki".  "Kwarai kuwa mun baki dukkan yardan mu, koda kunnin dubu suke jikin mu bazamu taba ɗauka ba bare mu yadda". Cewar goggo,,,haka dai suke ta lallashin ta suna bata  baki har dai tayi shiru daga karshe bacci yayi gaba da ita..... Koda ya koma gida bai bi takan mubeena ba ya shige ɗaki zuciyar shi tana tafarfasa da ƙuna, kishi ya rufe masa ido bare har ya gane cewan eelham baza ta aikata haka ba, koda ya gama abinda zai yi sai ya kwanta amma bacci yace bai san wannan ba, tashi yayi ya dinga Safa da marwa ga kuma zazzaɓi yana ji,,jin knocking da akewa kofan shi ne yasa ya kai duban shi ga kofa, daga baya ya dauke dan bazai buɗe ba yana buƙatan privacy,Saida mubeena ya gaji da knocking sannan ta bar wajen da bakin kishin da ke nuƙurƙusan zuciyarta tinanin ta ko EElham tana ciki ne shi yasa AS ya saka key,, haka dai  tabar part ɗin gaba ɗaya tana danne kukan dake taso mata,, daukan waya tayi ta kira zeena amma bata ɗauka ba, wullar da wayar tayi bisa bed ta fashe da kuka mai cin rai wanda ba kukan komi take ba sai na kishin mijin ta... Sai da zazzabi yaci karfin shi sannan yasha magani ya kwanta, dan ba karamin ciwo yake ji ba tun daga zuciya har kai,,, yana cikin wannan halin Allah ya taimaka bacci yayi awon gaba da shi..... "A gaskiya ka bani mamaki, ƙaramar yarinya a ce ta gagare ka?, mu muna nan mun sake baki kana can kana farautar mana nasaran mu, amma zaka dawo mana da maganar banza, toh Bara kaji wannan shine last chance d zan baka duk yadda za kayi kayi kafin wannan satin ya ƙare idan kuma wannan satin ya shige duk ɗinmu ka sani babu wanda zai samu cikan burin shi, kenan aikin da muka yi na tsawon shekaru ya tashi a banza, dan haka ka dage ka maida hankali mu cimma manufan mu". "Amma ranka ya dade dadai an nimo inda take a zahiri bazan iya ta cikin mafarkin ta ba dan ina shan wuya, jiya ma kadan ya rage ta gane ni dan addu'an da ta dinga yi na fara rikiɗa zuwa normal ni". Sauke nunfashi mutumin yayi kafin yace "ina zuwa bara na tambaya ko an same ta,sai kaje ko da zuwa da safe zamuyi ma aika". Yayi Maganar yana shiga cikin dan kurkukun daki.ganin haka ne sai shi ma wannan mutumin ya ya wuce abin sa...... "Tun muna shaida juna yaya ki daina taɓa min dukiya ta, nasha gaya miki akan dukiya ta zan iya yin komi a kai". "Baki da tsoron Allah Anne, ke har kina da baƙin da zaki buɗe kice dukiyar ki ce? Banda sata ma taya akayi kudin suka zama taki? Toh ki sani inda kika samu dukiyar nan a banza nima haka zan tacin su a banza, tunda babu wanda ya kawo shawara sai ni, kai kikayi wasa ma zan iya ɓatar da ke naci dukiyar nan ni kadai ke ma kin san karamin aiki nane gwara ki bini a sannu". ji Anne tayi ƙirjinta ya buga dan tasan yarta tsaf zata iya yin abinda ya fi haka, ba ta kuma ce mata komi ba ta nufi stairs zata shige ɗaki, har ta kama handle zata buɗe kofan taji murya yayanta tana faɗin, "a wani gari su eelham suke?". Ba shiri ta juyo da sauri, "da kike niman inda take mi zakiyi da haka?". "Kin san dadin dukiya baki son a nimo inda suke Koh? Toh Ni ba wannan ba, Ni ma inada buƙatar su ne". Cikin kallon tuhuma ta kalle ta murya a dake tace "ko wuta ke fita daga bakin ki baza kiji inda take ba". Tana kaiwa nan ta tura kofa ta shige ciki tana banko shi da karfi, da ido kawai yayarta ta bita tana kitsa abinda zata yi mata...... Jikin eelham ya war-ware sosai kaman ba tayi jinya ba ta kuma watsar da batun AS a gefe dan tunda ya tafi ranar da aka sallamota daga hospital har yanzu bai dawo ba, itama ɗin bata koma ba, su goggo ma basu ce mata komi ba, dan grandma tace sai ta hora shi yasan darajan eelham sannan. Fitowa tayi daga ɗakin ta cikin shirin ta na NYSC daman ta koma tun Monday, dakin goggo ta shiga ta sallame ta ta fito ta shiga na grandma daganan ta shiga na ummi ta gaisar da ita ta fito zuwa waje, wajen motar ta ta nufa shiga tayi tana ficewa daga gidan zuwa wajen aikin ta,,, kamar yadda ta saba bata shiga harkan kowa ba ta nufi zuwa office ɗinta, komi na nan a tsaf din shi, tissue tasa ta ƙara goge kujerar da table ɗin, zama tayi tana fara aikin ta cikin kwarewa, tayi nisa a aikin taji landline dake a gefen ta yana niman a gaji cikin nutsuwa tayi picking,,ba tare da tace komi ba taji manager yana yi mata bayani, sai da ya gama ta aje wayar, itafa badan aiki take ba da babu inda zata, badan ranta yaso ba ta tashi ta dauki file ɗin ta nufi office ɗin oga kwata kwata, sai da PA dinsa yayi mata iso sannan ta shiga da sallama akan labba,karasa tayi ta gaishe shi with full of respect kaman yadda take tsakanin oga da yaron aiki, ta ƙasan ido ya gama ƙare mata kallo da mamakin halin nan nata, cikin basarwa shima ya amsa kamar yadda yake amsawa ma aikatan shi babu yabo babu fallasa, ba ta jira komi ba ta aje masa file tana yi masa bayani amma shi bai ma jin abinda take faɗa, sai da ta gama ne tasa kai ta fice daga office ɗin ba tare da ya ankara ba sai da yaji ƙaran kulle kofa ne.........✍️

Ga wannan babu yawa, ba anan na so dakatawa ba.
Dan Allah kuyi min uziri, ban samun time, Nagode 🙏