EELHAM🌹

62&63

by @rabearhwakili


Episode 62& 63📲
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
     
             Ƙarar kulle kofan ne ya ankara da shi fitan tata, har ya mai da hankali zai fara aiki kuma ya fasa ya miƙe ya fita daga office ɗin, office ɗin Elham ya nufa, ba tare da yayi knocking ba ya shiga ciki,,, madara da sugar take sha ta haɗa su guri ɗaya tana saka spoon tana kai wa bakin ta, ko da taji an shigo mata office bata juya ba tunanin ko Ruqqy ce dan itama ta dawo aiki,,,, takowo yayi zuwa kujerar da take,,,ita kuwa ta tabbatar ba Ruqqy bace ta hanyar jin kamshin Tularen AS, haɗe fuska tayi tana cigaba da shan madarar ta,,,,shi kuwa ta gefen ta ya tsaya yana ƙare mata kallo dan yadda take shan madarar ba ƙaramin jan hankalin shi yayi ba, cikin ƙasa da murya yace "baki iya karrama mutum idan yazo office ɗinki ba ne?" Yi tayi kaman ba taji abinda yake cewa ba, ba zato ba tsammani taji ta a sama ya daga ta daga kan kujerar zuwa jikin shi kaman ya dauki jaririya zama yayi a kujerar sannan ya a zata kan ƙafafun shi, mutsu mutsun kwacewa ta dinga yi amma ya hanata wannan daman, a bazata taji hannun shi kan cikin ta, a mugun fusace ta daga tana ture hannun shi cikin muryan fusata tace "ka dai na tabani nace maka banaso". "Daman a wuya yake da ita cikin son ya guma mata ya furta "na dai na taɓaki baki so, amma kina iya kai kanki wa wani ƙato can daban ai". Zuba mishi ido tayi tana kallon shi ga hawaye ya cikar mata ido da sauri ta kauda fuskar ta daga gare shi tana jin tsanar shi yana shigar mata zuciya lokaci ɗaya,, da karfi ta miƙe daga jikin shi murya na rawa sosai tace "wannan da kake tunani ya fika kima da daraja a waje na, dan haka ka daina danga...." Maganar ta katsewa yayi ganin ya nufo ta a fusace ja da baya ta dinga yi shima yana binta haka har ta danga na da bangon office ɗin,rintse ido tayi tana jira taji wani hukun ci zai mata,, shi kuwa matso wa yayi da fuskar shi zuwa gare ta daf da daf,cikin Muryar mai daci ya furta "ki kiyaye gaya min magana son ranki, sannan uban waye yayi miki cikin da kika barar". Cikin kauda tsoro tace "na ƙarfin mutanen da ne, bazan faɗa ba idan kana da karfi ka tilasta Ni nayi haka". Tana gama faɗa ta Shammace shi ta tsugunna ta fita daga wajen, handbag kawai ta dauka ta fita daga office ɗin tana jin tsanar shi na ruruwa a zuciyar ta,,,datse lips ɗin shi yayi kamar zai taune su,jingina yayi da bango yana harɗe hannu a ƙirji, numfashi ya rinƙa saukewa a hankali haɗi da addu'a har yaji ƙirjin shi ya dan sauka,,barin office ɗin yayi yana kulle mata ƙofar da key, parking lot ya nufa driver yana ganin shi ya taso ya tada mota suka bar Company zuwa gidan su ummi....cikin kwana kin nan mubeena ta kasa gane kan AS dan kwata kwata baida wani walwala, hakan da yake abin ya na damun ta, shiyasa tayi kiran shamsiya a waya sai dai bata same ta ba sai ta juya akalar kiran zuwa ga ta amanarta wato zeena, ringing biyu ta dauka daga ta chan ban garen tace "yar halas ta ƙi ambato yan zu nake cewa bara na shirya na taho gidan naki naji ki kwana biyu shiru babu sabon update". Cikin rashin fahimta mubeena ta amsa mata da "aikuwa ina da bukatar ganin ki ƙawa, dan Allah ki taho yanzu kafin zuciya ta ta buga". Da muryan farin ciki tace "zuciyar ki zata buga kuma? Toh gani nan tafe  amma ki shirya min better kafin na taho". "Wai ina gaya miki Matsalata kina wani cewa nayi miki better, babu abinda zanyi miki idan kin zo kyayi". "Shikenan on my way in next 15 mint"... Kamar yadda tace kuwa kafin 15 mint din ta iso. "lafiya kuwa mubeena naga duk kin fige? Kar dai ince ta kaicin AS ya saka ki a wannan hali". "Hmm zeena shine ba komi ba, yanzu bani gane kan AS, baya kula ni kamar da ba....." Katse ta tayi tare da fadin "ba sai kin ƙarƙare ba,tuntuni abinda nake miki gudu kenan amma kinki ki ɗauka Shawara ta,yanzu dai a je wannan a gefe abinda zaki yi ki fita daga sabgan shi kawai idan kika yi mai haka zai nutsu kamar yadda kikayi masa a baya, ke idan ma kika ga da takura haɗa kayan ki muje ki huta a wata ƙasar, kokuwa?". Ido ta zuba mata kawai dan a wannan karan bata jin zata iya daya daga cikin abinda ta gaya mata da da yanzu ba ɗaya bane... Kamar tasan abinda take kissimawa a rai tace "idan kuma Kinga bazaki iya ba shikenan, shawara ki ka biɗa kuma na baki, ya rage naki ki ɗauka ko akasin ta".  "A'a bazan iya daukan wannan ba gaskiya na gode, nikam tashi ma ki tafi zanyi kiran Anty salaha".  "Amma ke muguwa ce wata Anty salaha zaki kira? Ba dai yarki malamar nan bah?".  Cikin rashin damuwa tace "of course" a ruɗe tace dan Allah karki kira ta bazata baki shawara mai kyau ba, kila ma tana yi miki baƙin ciki kin fita a komi yan zu kina faɗa mata zata iya amfani da wannan daman ta kashe ......"  "Dakata zeena! Kina cikin hankalin ki kuwa? Kin san yadda Anty salaha take a gare ni kuwa? Ba ma wannan ba, yanzu baki ji kunyan gaya min yayata tanayi min bakin ciki ba, zata kuma iya kashe min aure, yanzu baki ji kunyan haka ba,ke bance zaki kashe min aure ba sai kece zaki kalli tsabar idona ki gaya min haka? Amma zeena baki da kunya baki da tsoron Allah, maza maza tun muna shaida juna zoki fitar min daga gida yar rainin hankali kawai mtwws". Ta ƙare maganar da jan doguwar tsuka tana watsa mata kallon banza, dan haka kawai yau taƙi yarda da zeena "haba mubee ba abinda nak......"  "I say out" mubee tayi maganar cikin daka mata tsawa kamar ba ita ba, dan bata da hayaniya ka dai barta da halin ta, sosai zeena ta tsorata da haka tuni ta kwashe kayan ta ta fita waje babu shiri, mubeena kam da harara ta raka bayan ta....... "Lafiya ke kuwa da dawowa da wuri kamar wata korarra?" Haɗe fuska tayi cikin magana ƙasa ƙasa tace "ni na gaji da aiki a wannan Company zan Nima transfer zuwa wata". "Oo maaikatar mijin ki kike gudu? Toh muga sauƙi, idan wasu suka guji Company abin ba zai dame ki bah".  "Nifa goggo ki dai na danganta shi da ni, kowa yayi harkan shi". Wata harara ta watsa mata tare da faɗin "na haɗa ki ɗin, ke ni kin ma ishe ni kizo ki koma ɗakin ki atoh".  "Zama daram ina nan, idan kin hana ni zama sai na koma gurin grandma". "Yanzu kuwa! tashi ki haɗo kayan ki daman ita ke goyar miki baya". Cewar goggo, tashi tayi ta nufi kofa hadi da faɗin "ga ki ga ɗakin goggo ni na tafi gurin kakata". Ta buɗe kofa zata fita taci karo da mutum, cikin sauri ta dafe goshinta hadi da faɗin "wayyyo Allah". Zuba mata ido yayi yana kallon rangwanta zalla tare da ita,  taɓe baki yayi ya ratsa ta gefen ta ya wuce,ganin da tayi AS ne sai ba tace komi ba ta sa kai ta wuce zuwa part ɗin grandma tana taɓa wajen dan ba ƙaramin zafi taji ba, "namecy mi ya sami goshin ne ake ta lilaya shi?" "Gwarewa nayi" "asha sannu, ki shiga ki dauko mantaleter ki shafa kar wajen ta tashi miki".  Tashi tayi taje ta shafa sannan ta dawo falon, "yau baki je wajen aikin bane?" Grandma tayi tambayar cikin taɓe baki, "naje na dawo ne, ina son a yi min transfer zuwa wata". "Atoh Saida nace miki tun farko a canza amma kince a'a, ni nasan ba jin dadin wajen nan zakiyi ba tunda wancan mai baƙin halin yana nan". "Ni dai ba shi ya hana ni ba, kawai dai a nima min transfer". "Oho ke kika sani, sai ki jira idan Abban ku ya dawo ki sanar musu". "Kiyi musu magana ke m......" Maganar ta katsewa yayi ganin shigowar AS, dauke kai tayi tana latsa wayar ta, grandma ita ma ko kallon Shi batayi ba,shifa sha'anin grandma dariya yake bashi, kauda kai gefe yayi yana gaisheta a daƙile, "ka ganni nan qlau nake alhamdulillah dan haka riƙe gaisuwar ka! Namecy tashi ki shige ciki ooo". Daman abin nima ne ya samu tana jin haka ta miƙe ta shige ciki, da kallon ƙasan ido ya bita,,,,,so take ta shiga ciki amma bata son ta tashi AS ya shiga dakin eelham dan ta gane take taken shi kenan, "mallam tashi kaje zamu kulle kofa". Kadan ya rage dariya ta suɓuce mishi sai ya fuske haɗi da faɗin "dare ne da zaku kulle ƙofa?". "Ina ruwan ka toh, haka nake da ra'ayi".  "Kije idan na tashi zan kulle". Wani kallon ta watsa nishin na ka ma raina min wayau amma sai bata ce mishi komi ba, tana nan dai a zaune har bacci ya fara kwasan ta, Saida bacci yaci karfin ta sannan ta tashi ta shige dakin ta ta kwanta ta bar AS anan,,, sai da ya ƙara minti goma sannan ya tashi ya shiga dakin da  EElham ta shiga, kwance ya same ta a gado alamun dai baccin take son tayi itama, "Elham! Elham". Shiru tayi bata amsa mishi ba tana kuma ji,zama yayi nisa da ita kaɗan yace "ina matsayin mijinki kina ji ina kiran ki amma kin maida ni banza wato idan na gaji na wuce Koh?". Nan ɗin ma bata kulasa ba daukar waya ma tayi tana operating abinta, tashi yayi daga inda yake yana komawa daf da ita, ganin haka ne sai tayi sauri ta matsa, cafke ta yayi ya saka ta a jikin shi murya babu wasa ya furta "dejarht! ban san rainin da ya fara shiga tsakanin mu ba,mma ina guje miki ranar da zamu cire wannan rainin, wanda ko kallan banza akace kiyi min baza kiyi ba". "Ni dai ka sake ni bacci nake ji". Saida yazo daf da kunnin ta yace "na riƙe ki? Kiyi baccin ki mana". "Ai ni ba yar iska bace". "Allah Koh? Shine kikaje kikayi ciki?". Babu shiri ta dago tana kallon shi idanun ta suna tara kwalla a ciki, cikin dakiya ta cire idonta daga kanshi tana datse su, ga ƙirjin ta sai sama da ƙasa yake, wanda tana da tabbacin yana jin haka shima, ga kuma yaƙi ya sake ta, a hankali ya rinƙa bubbuga bayan ta irin yadda akewa yara, tun Tana jin shi sama sama har bacci mai nauyi yayi gaba da ita a jikin sa a karo na biyu,jin ta daina mutsu mutsu ne yasa ya gane tayi kwana, Saida ya bari bacci ta yayi nisa sannan ya kwantar da ita akan bed a hankali kamar wata baby, da murmushi a face ɗin shi ya furta "yar rigimata". Tashi yayi yana manna mata sumba a goshi sannan ya fita dan yabar ayyuka da yawa a office,,, driver ya tada motar suka bar gidan zuciyar shi fees babu ko wata damuwa,,,tun bayan wucewar zeena taso ta kira yayarta amma Allah bai nufa ba sai yanzu ta samu tayi kiranta bayan sun gama gaisawa take gaya mata damuwar ta "mubeena kenan, kije kiyi ta hakuri kina kuma ƙara yi ma mijinki biyayya". "Anty ina yi fa bansan mi ya sa ya canza min haka bah?". "Toh shikenan! ki ƙara hakuri dai,daman zaman aure dan hakuri ne, idan kika yi sai kiga kinci riba". "Anty dan Allah ki bani shawara dai"  "shawaran kenan mubeena shi ne kiyi hakuri idan kuma kina yi to ki ƙara". Sabida haushi bata san sanda ta katse kiran ba,taya za'a yi mutum yana niman shawara a wani kama ce masa yayi haƙuri, ai bata ga zata iya wannan ba, daga karshe tashi tayi ta shiga dakin su Anwar inda ta same su suna bacci tunda yau babu islamiyya shi yasa bata tashe shi ba, ita ma kwanciya tayi a gefen su bacci yana yin awon gaba da ita....wuraren 6 na yamma AS ya shigo cikin gidan shi, part din mubeena ya shiga direct ya wuce zuwa dakin ta amma bata nan ɗakin su Anwar ya shiga nan ya same su sai bacci suke cikin kwanciyar hankali, tada mubee yayi sannan ya tada Anwar "mommy Anwar bacci yamma kuma".  Cikin Muryar bacci tace "ɗan kwanciya nayi shi ne bacci ya kwashe ni". "Kunyi kokari,! Boy ka tashi lafiya?". Alhamdulillah papa"  "masha Allah bara naje nayi shirin masallaci lokacin salla ta kusa". yayi maganar yana tashi sai da ya isa kofa sannan yace "a tada ummi na yamma tayi". Cikin bin shi da ido ta amsa da toh, tasar da Anam tayi sannan ta shirya Anwar cikin jallabiya ta yara wanda ta karɓe shi sosai kaman nin shi da AS ya kara fitowa,,, lekowa yayi cikin ɗakin ya furta "Boy zo mu wuce masallaci" ba musu kuwa ya miƙe yana yiwa mommy shi bye-bye "zamu gidan ummi daga masallaci". Cewar AS, Amsawa tayi da Toh sannan tace "ka wuto mana da take away". Da kai ya amsa yana yiwa Anam bye-bye,,,,bayan an idar da salla ya bawa motar shi wuta suka nufi anguwan su Ummi, part din ummi ya fara shiga a nan ya zauna sai da akayi isha'i sannan ya tashi ya wuce zuwa masallaci Anwar biye dashi, Saida aka idar sannan ya shigo shi dasu Abba, part din grandma ya nufa gaisawa sukai sannan ya fito jin kamar eelham bata ciki,,part din goggo ya nufa Anwar maƙale dashi, cikin sakin fuska ta karbi gaisuwar da yayi mata, wasa take yi wa Anwar wanda ganin ta da yayi sai ya dare mata kan ƙafafun, "Ahmad baka shiga ba ai tana ciki"......✍️

This page is for u yar uwa sister hajara, Allah ya dauwamar da farin ciki a gidan auren ki, Allah ya kawo zuri'a masu albarka, really appreciate your prayers 🙏😍