64&65
Episode 64& 65📲
بسم الله الر رحمن الر حىم
Da sunan Allah Mai rahma Mai Jin Kai
Ba musu kuwa ya miƙe ya shige dakin da EElham take, ba tare da yayi knocking ba ya buɗe ƙofan ya shige ciki,, waya take da Ruqayyah da gani na sirri ne, ganin AS da tayi ne sai ta kashe wayar da sauri da fatan Allah yasa bai ji mi take cewa bah, kallon ta yayi ganin yadda ta daburce lokacin ɗaya, takawa yayi zuwa inda take, zama yayi yana jawo ta zuwa jikin shi, karɓan wayar hannun ta yayi, dubawa yayi yaga ashe da Ruqayyah take waya, taɓe baki yayi, yana jujjuya wayar a hannun shi murya can ƙasa ya furta "wa ya siyar miki waya?". A takaice ta amsa masa da "kuɗi" gaɗa kai kawai yayi zai yi magana kenan sai suka ji knocking, kwacewa tayi da sauri tana matsawa gefe, dan daga murya AS yayi yace "shigo" buɗe kofan Anwar yayi yana kallon ɗakin ganin eelham da yayi ne sai yace "umm" cikin zumuɗi, murmushi dauke da kyakyawan fuskarta ta amsa da "na'am boy! Ykk". "Alhamdulillah! Umm I miss u" "same dear! Taho". Ƙarasawa yayi zuwa gare ta, daukan shi tayi ta aza kan ƙafafunta ta furta "ina Anam da mommy?". "Anam tana gida ita da mommy, bamu zo da su bah". Shafa kanshi tayi haɗi da faɗin "send my regard, kaji?".zuba musu ido yayi yana kallon su cikin birgewa, kafin ya miƙe a hankali yace "Boy zo mu wuce". Da sauri eelham ta dago ta dubi AS wanda tunda ya shigo bata kalle shi ba sai yanzu, cikin muryan ladabi tace "dan Allah yaya ka barmin shi ko da safe ne sai ya koma". "A she kina magana? Ai ban sani ba". Zunburo maki tayi kadan cikin shagwaɓa tace "dan Allah yaya" "na ƙi! idan kin yi fushi ki haifi naki". Yana kaiwa nan ya kama hannun Anwar suka fita Anwar na ta ɗaga mata hannu har suka bar ɗakin,,, da kallon takaici ta bi bayan shi.har ta zauna kuma ta fita falo wajen goggo, "amarya magulmaciya an samu fitowa kenan". Zaro ido tayi haɗi da faɗin "Allah ya tsare ni da shi". A'a kinji ni na haɗa ki da wani? Rufa min asiri! Ga wayar ki nan mijin ki yace a baki". Amma goggo da niman magana take bata ce mata komi ba ta karbi wayar tana komawa daki dan ta lura kwana biyun nan goggo ta saka mata ido da yawa,,,Saida ya biya yayi wa su mubeena takeaway sannan suka koma gida,dinner sukai sannan mubeena ta tasa su Anwar daki har sukayi bacci ta dawo falo wajen AS,,, "ka tashi muje mu kwanta ni bacci nake ji". Mubeena tayi maganar cike da shagwaɓa, "kije idan na gama abinda nake zan shigo". Bata ja zancen da tsawo ba dan bacci take ji sosai, tashi tayi ta wuce ɗakin ta,Saida tayi wanka ta shirya cikin Kayan bacci masu santsi tabi lafiyar gado,tana kwanciya babu jimawa yayi gaba da ita..... Sai da ya tabbatar da baccin nata yayi nisa lokacin shaɗaya saura ya dauki wayar shi ya hau kiran eelham....tun tuni ta kasa bacci dan tana ta tunanin yanzu AS yana nan tare da matar shi ko? Idan ta tuna da haka sai taji ranta ya ɓaci, tana cikin juye juyen ne taji wayarta tana ringing koda ta duba taga an saka "HUSBAND MHIE!!!" Da mamaki ta dubi wayar kamar baza ta dauka ba sai tayi receiving call ɗin amma ba tai magana bah, shima ta bangaren shi bai ce komi ba,,,,cikin jin haushi tace "idan baza'ayi magana ba zan kashe wayata". Murmushi yayi kafin a hankali yace "dan Allah kashe toh". Dan tsamm tayi jin dirar muryan shi, ita dai tasan batada numbern shi how comes yanzu kuma gashi a wayarta, shima a ina ya samu, katse mata tunanin yayi ta hanyan faɗin "yaushe zaki dawo gidan ki?". Haɗe fuska tayi kamar yana ganin ta haɗi da faɗin "Ni kam wani gida nake da bayan wanga?". "Gidan mijin ki" cewar AS "Allah ya kiyaye" dan ƙaramin dariya ya saki wanda ita ma taji sautin fitar shi, "ashe fa haka ne!! Baki shirya samun naki yaran ba kenan?". Taɓe baki tayi tace "daman Ni ban ce maka ai ina...." katse ta yayi ta hanyar faɗin "Toh Ni kuma ina so" "nikuma nace baka so"cewar EElham tana hararan wayar "kin yanke hukunci da kanki kenan? to mu zuba mu gani, idan ma baki dawo ba kin san ina iya biyo ki har nan gida ko?". Shiru tayi bata ce masa komi ba dan bata gane inda ya dosa ba, ji tayi yana faɗin "ba dan Kinga grandma tana daure miki bane shi yasa kike min haka ba, karki damu daga ke har ita zan yi maganin ku inhar bata yadda kin dawo gida ba". Ba'a dawowa inace kana da mata a gidan? Toh kaje na bar mata...." "Dejarht mi yasa baki tsoron gaya min magana haka?nasha gaya miki kibi a sannu dan ina gudar miki ranan da zamu cire wannan rainin". Dan shiru yayi kafin ya cigaba da faɗin "kar kuma na ƙara ganin ki da Wannan kayan na NYSC, ki rinƙa saka kayan gida is better! Umarni nake baki ba Shawara ba, idan kin gadama ki saka kiga yadda zanyi dake". Yana kaiwa nan ya katse wayar shi,,,sauke wayar tayi tana jan doguwar numfashi da sakin dan guntun murmushi, juyawa tayi ta samu waje ta kwanta tana jin relief a tare da ita...... Tasss tasssss haka taji ƙaran saukar mari akan fuskar ta wanda ya dauke mata jinta da ganinta at once, kafin ta gama dawowa cikin hayyacin ta taji yana faɗin "wannan shine kashedina na karshe a gare ki, kafin nan da 48 hours ina bukatar sanin inda take kokuma ki kawo min ita". Matsowa yayi kusa da ita daf yace "failure to do so....?". Jiki na rawa sosai YAYA ta gaɗa mishi kai gefe ɗaya na zuciyarta tana jinjina rashin imanin shi, daka mata tsawa yayi yace "disappear". kamar kyaftawan ido ta wuce fit, tafiya take amma duk bata cikin nutsuwarta haka har ta fito bakin titi da yake dare ne babu wasu abin hawa duk sun dauke kafa haka dai ta dinga tafiya a gefen titi batayi nisa ba taji an watsa mata abu a fuska daga nan bata ƙara sanin mike wakana ba, fitowa sukai daga mabuyan sa suka saka ta cikin mota dayan cikin su ya fidda waya yace "it's done Hajiya!!" Yayi Maganar cikin girmamawa, daga can gefen aka amsa masa da "good job!!keep it up". "Yes mar". "u should take her to the other house and u take care of her! Don't did something that will harm her, she's with u guys for her safety". Cewar hajiyar nan, "by god grace,we will do all we can". Cewar wannan gient ɗin da suke waya, sauke wayar yayi jin ta kashe daga ɓangaren ta,maida akalar kiran tayi ga Aziza..... Tun dazu daman Aziza take jiran call ɗin ta, ganin call ɗin ya shigo yasa jiki na rawa ta dauka tana fita zuwa falo,, bata jira cewar Aziza ba tace "daughter fatan kina saka mun ido a kan wannan amanar da na danƙa miki?" "Insha Allah, ina kokarin haka saidai kwana biyu ban ji wani update daga ɓangaren su ba". Sauke nunfashi matar tayi tana cewa "and u support to" "eh daman zuwa gobe nake son na shiga can ɗin kinsan ma makasudin da yasa na tilasta masa dawowan mu nan kenan". "Haka ne! Allah ya bamu Sa'a" "Amin ya Allah",kit ta katse wayar wayar, sauke wayar Aziza tayi ta koma daki saidai tana shiga ta iske hydar a zaune alamun dai ya daɗe da tashi cikin rashin gaskiya tace "honey when did u get up?". Zuba mata manyan idanun shi yayi kafin ya dauke su a hankali yana maida su gefe cikin son ya gano ta yace "since". Dummm haka taji kirjinta ya buga da ƙarfi amma da yake akwai ta da muguwar wayau cikin wayencewa tace "ayarh let go to bed". Da ido ya bita yana rasa gano gaskiyar ta, ba musu suka je suka kwanta, Aziza na ta sauke ajiyar zuci a boye........washegari,, shirye eelham take cikin doguwar abaya onion color sai tayi rolling da vail ɗin shi dan ya kasance yana da girma handbag ɗinta ta dauka bayan ta sallami goggo, batare da ta shiga wajen grandma ba ta wuce parking lot ta shiga motarta ta bar gidan, driving take a hankali kaman bata son yi ga murmushi dauke a fuskar ta, daidai wani roundabout taga kaman ana binta, bata tabbatar da haka ba sai da ta shiga wata hanyar, farat ɗaya taji tsoro ya shige ta amma ta dake zuciyar ta tana ƙara bama motar ta wuta, suma ɗin ƙara ma tasu wuta sukai suna bin bayan ta a guje, haka eelham ta dinga rough drive dan ganin kawai ta tsare musu amma ina, cikin kariyar ubangiji da tsarewar shi ya kawo ta cikin company, wanda suna ganin haka sai suka dakata da motar har sai da suka ga shigan ta sannan, gudan cikin su ya dauki waya yayi kiran ogan su as usual "Hajiya the lady is so scared". Daga can bangaren cewa tayi "how did u let her kno u're following her back". "We're Sorry mah" amsa musu tayi da "hmmm is ok" . "are we to wait for her?". Cewar wannan guy ɗin yana tambayar hajiyar nan, "don't worry she's safe, cos she's with her husband!! Don't worry u can come back". "Yes mar". Bayan sunyi sallama ne ya gayawa yan uwan shi suka bama motar wuta suka bar wajen.......duk da a firgice take hakan bai hana nutsuwarta bayyana ba har sai in kayi mata farin sani zaka gane tana cikin firgici tana zuwa ba wata wata ta shiga office ɗin AS, ganin shigowar ta ne da kuma yanayin ta yasa ya miƙe yana isowa gareta amma kafin ya ƙaraso ta danyi gudu ta faɗa jikin shi tana sauke ajiyar zuciya a jejere kamar wacce tayi gudu,tarban ta yayi da hannu biyu cikin damuwan halin da take a ciki yace "baby what's wrong?". "Wasu ke ta bin baya na har na shigo cikin company". "Wasu!?" gada mishi kai tayi kawai,cikin zurfin tunani yace "who are they". (littafin yaya azeema, marubuciyar sarki sameer). Ganin dai bazai samar ma kanshi da answer ba sai ya share raba ta yayi daga jikin shi ya kama hannun ta suka koma kan sofa da ke a office ɗin, zaunar da ita yayi ya kawo mata ruwa ba musu kuwa ta karba tasha tana sauke ajiyar heart (yau su eelham an tsorata) maida cup ɗin yayi zuwa ma'ajiyar shi sannan ya dawo ya rinƙa kwantar mata da hankali har dai ta hakura, duban ta yayi yace "dejarht yanzu Kinga da kin koma gidan ki da tare zamu rinƙa zuwa amma kince ba haka ba, Kinga abinda nake ta yi miki gudu". "Babu inda zan koma! Kuma zuwa Company na aje shi daga yau, ai daman saura mana 2 month mu kammala". "A Company waye zakiyi wannan? Ni dai ban iya cin amanar ƙasa ba, dan haka dole ki ƙarƙare aikin naki". Yayi Maganar da sigar da tayi magana, fadawa tayi jikin shi tana rufe ido haɗi da sakin dan dariya dan yadda yayi ɗin is so funny and attractive. "gulmammiya! ni ɗaga ni karki karya ni". "Ni da bani da wata nauyi". Tabe baki yayi hadi da faɗin "ke kike ganin haka amma kaman buhun cement haka kike". Kallon shi tayi fuska kamar zata yi kuka tace "yaya fear god". Zai bata answer kenan sai suka ji knocking na door tashi tayi tana komawa gefe dashi sosai, shi kuma AS yana jin haushi wanda yayi knocking din,murya a daƙile yace "come in". PA ɗinsa ne ya shigo hannun shi riƙe da file da mamakin ganin eelham a office ɗin kuma kan cushion office ɗin oga,ga kuma oga shima yana zaune gefen ta, kallansu yake tayi ta gefen ido yana mamakin wannan lamarin,miƙawa AS file ɗin yayi har zai juya ya fita AS ya dakatar dashi, matsawa AS yayi kusa da Elham da tayi kaman bata a office ɗin, dai dai kunni ta yace "madam hijab za'a siyo miki saiki fadi wanda zai fitting da kayan ki". Cikin zumbura baki tace "ba wani hijab ɗin da zan saka, ana fa zafi?". Bai saurare ta ba ya ɗago ya dubi PA ɗin sa da ya kura musu ido babu ko kyaftawa yace "ka siyo hijab". Yayi Maganar yana miƙa mishi ATM card dinsa hadi da faɗa masa color da yake so. Bayan ya fita ne ta juyo tana kallon shi tace "ni ka matsa kar wani ya sh......" Maganar ta maƙalewa tayi ganin mubeena..........✍️
Dedicated to my yar uwa sister Hajara, and sister mhie Ruqayyah, u're so special to me, really appreciate how u support me, an love this book, a big thank to u dearest sisters, ❣