EELHAM🌹

68&69

by @rabearhwakili

 

Assalama Alaikum mutanen kirki mutanen kwarai amincin Allah ya lullube Ku a duk inda kuke, kamar yadda kuka sani yawan talla ta yi yawan roko a yau ma na zo muku da sirrukan gyaran fata, Idan matsalar bushewar fata ko matsalar tsakewar fata ko kuma su kike yi fatarki ta yi glowing ta yi kyau da santsi kamar bayan fiki wannan post din na ki ne don kayanki sun tsinke a gindin kafa kin kawo kuka gidan mutuwa. Don ban dalilin kina da damar mallakar extra ordinary ki je ga ordinary ba

 

Super lightening soap

Organic lightening soap 

Baby soap 

Lightening dilka soap

Attractive soap

Morocco soap

 

 

Muna maraba da masu siyan daya ko sari muna aikawa ko ina a faɗin duniya cikin aminci 

 

 

Gamai buƙata ya  tuntuba wannan number  ***

 

Dan Allah idan baki shirya siyan kayan mu ba toh babu buƙata kira ko chatting dan ɓatawa juna lokaci

 

68 & 69

بسم الله الر رحمن الر حىم 

Safa da marwa kawai take ta faman yi tsakin tsakiyar falon, ga fuskarta tayi jaa abinka da fararen mutane,tana da bukatar shawara ta rasa wa zata kira ga tayi wa zee walaƙanci bare ta kira ta, tana da bukatan ganin ta,daure zuciya tayi dai ta hau kiran zeena,,abin duniya ya taru yayi mata yawa ta rasa yadda zata koma ma mubee dan sai in tana kusa ne aikin da take son aiwatar wa zaiyi, sosai tayi zirfi cikin tinani har wayarta ta gama ringing bata sani ba sai ana ukun ne ta farga, jiki na rawa ta dauka dan a koda yaushe tana expecting kiran mubena ya shigo wayar ta, cikin farin ciki ganin mubeena ce mai kiran ta hau rawa tana jin daɗin, daga wayar tayi tana kara shi a Kunni, daga ɓangaren nubeena bata jira cewar ta ba tace "dan Allah zeena ki taho gida ina cikin tashin hankali pls it's urgent". Kadan ya rage ta sake ihu amma sai tayi controlling kanta, "shikenan ƙawa gani nan tafe". Godiya tayi mata tana yanke call ɗin, daman cikin shiri take vail kawai ta yafa ta fito tana kulle dakin ta, bakin titin anguwan su ta fita dan ta samu abin hawa amma shiru babu,tana tsaye anan sai ga wata mota taci tinted sauke glass na ciki yayi hadi da faɗin "yan mata bismillah bai kamata kamar ki suna tsayuwa a rana ba bayan gamu a gari". "Noo thank you kaje". "Dan Allah kiyi hakuri dai na dan samu ladan kinji kyakyawa?". Saida ta gama iya yin ta sannan buɗe front sit ta shiga, tana rufe kofa taji saukar hanky a fuskarta daganan bata ƙara sanin inda take ba,, su kuma suka Bama motar wuta suna masu fashewa da dariya barin ma yadda sukaga zeena tana yi wato ita a dole tayi sabon kamu;..."Kedai bari ba'a magana, abin sai godiyar Allah, ai Nima duk hakan yakan dawo min cikin Kunni sarai, sai dai in toshe inyi kamar banji ba atoh". Daga dayar bangaren aka amsa da faɗin "hakan da kike shine dai-dai aminiya, Allah dai ya shiga tsakanin mu da maƙiya". Da Amin Anne ta amsa mata, "Kinga zan mance kuma! akace kwanaki mijin Maleeka ya binciko inda su eelham suke gaske ne ko karya, dan kin san ba yadda da maganar yaran nan nake ba". sam sam sam Anne batada yarda ko kadan duk da wacce suke wayar tare suke aiki amma bata jin zata iya faɗa mata gaskiyar magana cikin wayencewa tace "ikon Allah, aikuwa banji ba, da an gan su da nafi kowa farin ciki, shi da ya gaya musu bai faɗa sunan gari da anguwa ba?" "Kin san sha'anin su inaga duk shirme ce, wai bai faɗa ba, amma nikam nace shima ya faɗa ne dan hankalin su ya kwanta badan komi bah". Sauke boyayyar ajiyar zuciya tayi tace "tayu haka ne, Allah dai ya baiyana mana su". Da Amin aniyar Anne ta amsa nan sukai sallama suna aje wayar, kiran wayar autan ta tayi ringing biyu yayi aka daga daga dayar gefen tace "Anne ina wuni?". "Alhamdulillah ya gidan da sauran yan uwan ki masu taurin kai da mazajen su?". Cikin dariya  tace "suna nan kam sai abinda ya ƙaru, dan Kinga fadil kullum cikin saka min ido yake". Dariya suka kwashe dashi kafin cikin dariyar Anne tace "nasan badan wadan nan mutanen ba  da hashem ya sa anyi ram da ni tini, dan naga shi yafi daukan abin da serious, shi faɗil dan gulma ne tunda shike aika masa da saƙo". Ta ƙare da dariya sosai dan sha'anin nasu dariya yake bata dan duk basu san a tafin hannun ta suke ba "Anne ga radio mai jini ya dawo sai anjima". Kitt ta katse kiran Anne kuwa dariya ta hauyi jin abinda autan ta ta kira mijinta dashi, Saida ta gama shan dariyar ta sannan ta miƙe tana shiga ciki dan tana son ta ɗan huta..... Tun jiya taso suje Abuja wajen su momma amma sai hydar yace a bari sai yau,, haka kuwa akayi wajajen 12 suka sauka a Abuja ba tare da kowa ya sani ba harda momma din, a gidan su dake a nan suka sauka, Saida suka huta sannan suka nufa gidan su momma wanda shi bai san nufin Aziza da zuwan nasu ba, part din inna suka fara shiga inda suka same ta zaune a ƙasa tana cin tuwo dawa da miyar kuɓewa danya, wacce tasha man shanu ga Nama masu taushi a ciki, ganin haka da azeeza tayi ne bata yi mata magana ba taje ta wanko hannu ta zauna tana kai tuwo bakin ta hadda wasu gaɗa kai take wato abin yana gingering nata, sake  yaya hydar yayi da baki yana kallon ikon Allah dan shi kam yafi kowa sanin cewa Aziza ba ta son tuwo ko kadan, amma a mamakin shi kuma gata tana ci hadda wasu gaɗa kai, nan take wani farin ciki ya kama shi dan ya kiyasto wani abin, itama inna nan take ta gane ko mi yake nan, amma sai tayi shiru bata ce komi ba har suka gama cin tuwo, bayan ta kai kayan kitchen ta dauraye ne ta dawo ta gaisar da inna, ya mutsa fuska tayi hadi da faɗin "ooh sai yanzu kika san da zama ta kenan? Ko sai yanzu yaron naki yasan da wanzuwata?". "Wani yaro kuma inna? Yunwa dai tasa ban gane kowa, Kinga yanzu da na koshi ba gashi na gane ki bah?". Haka ne kam, yunwan taɓa Kunni bah?". Nan fa ta fara hangen maganar inna shiru tayi tana tunani, da sauri kuma tace inna ciki ne da Ni?". "Mutum da abun shi kuma yazo yana tambaya? ". "Dan Allah inna akwai?". Tabe baki tayi tana cewa "yaran yanzu sam babu kunya tare dasu! Ciki ne dake Allah ya inganta". Jin haka ne yasa Aziza saukowa tana yin sujudu shukur, bayan ta dago ne ta daga hannu sama tana gode ma Allah daya ƙara bata wani rabon a kurkusa, kallan inna tayi hadi da faɗin "dan Allah inna ina niman alfarma a gare ki". Kallon ta tayi kafin tace "ina jinki". Dan jin tayi kafin ta furta "inasan ne kar wanda yasan da zaman cikin jikina bayan ke da yaya hydar! Dan Allah kuyi min wannan alfarman". Shi dai yaya hydar hakan ba sabon abu bane a gare shi, amma ga inna sai abun yazo mata a sabo "kamar ya kar a bari kowa ya sani bayan abin farin ciki ne hakan?". Cewar inna "eh inna inada dalilin yin haka dan Allah goyon baya zaku bani da kuma rufe wannan maganar". Kan inna ya kulle tana ganin kamar an canza Aziza daga wanda ta sani, "shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi". Da Amin suka amsa hadda yaya hydar, amma sai inna ta katse shi tana cewa "mallam dakata ban gayyace ka a maganata ba, ahem". Sha'anin inna sai addu'a kawai bai ce mata komi ba yace "Aziza tashi muje". girgiza kai tayi ta ce "noo ina nan, sai an jima zan fita gaida mutanen gidan". Bai ce komi ba ya sa kai ya fice daga part ɗin zuwa na momma..Yana ganin shigar goggo ya taso daga inda yake zuwa wajen ta, ganin tana kokarin guduwa, cafke ta yayi fuska babu wasa yace "zauna". Ganin haka yasa ta zauna a gefen shi tana cin magani, "dan baki da kunya a gaban ido na kike fira da wani ƙaton banza dake baki ɗauke Ni da mahimmanci bah! Shi yasa kike gaya min magana san ranki". Ni dai besty ba ƙaton ban....." Ɗalle mata lips yayi cikin jin zafi ta aza hannu a kan lips ɗin ga hawaye sun tarar mata a idanu, ba wata wata ta mike tsaye Saida ta bari ta isa kofa taja masa Allah ya isa sannan ta gudu zuwa part ɗin grandma dan nan kawai tasan zata ta tsira,,, rintse ido yayi da karfi jin wai EElham ta ja masa masa Allah ya isa, mike wa yayi yana cewa zata ja mai dalili kuwa tashi yayi ya bita har wajen grandma inda ya same ta kwance a jikinta, rayawa yake "sai son jiki kamar mage". Amma a zahiri sai ya gaida grandma cikin ladabi kamar ba dazun nan ya gama mata rashin mutumci ba, ita kam ganin hakan da tayi ne sai tayi tinani ko ya tuba ne ita ma ɗin da fara'a ta amsa "alhamdulillah ya aikin". Yauwa anzo wajen ya raya a zuciya a fili kuma yace "aiki kam sai godiya! Grandma wai babu kowa a gidan ne?". "Kaji ka fah ina zaka gansu duk suna gidan mazajen su". "Eh haka ne meenal bata zo ba kenan?".  "A'a nikam babu wacce tazo yau! Mi kake so halan?". Cikin jimami yace "wani abokina daga Dubai zai zo, dan yanzu haka Flight ɗinsu ya kusa landing, so gashi nace kar yayi logging din hotel dan anan nake so na sauke shi, wato a part dina na nan". "Masha Allah, kayi dai-dai kuwa, daman baƙon ka annabin ka, yanzu bara a kira masu aiki su shiga su gyara". "A'a grandma ki barshi kawai dan banson suna shigar min part bari dai idan na tashi nayi da kai na". Nan take grandma taga hakan bai dace ba bayan mutum da matar shi kuma gata kusa, bata yi dogon tunani ba tace "namecy taimaka ki gyaro masa part din kinji". Tura baki tayi gaba dan haka kawai taji hankalin ta bai kwanta da zuwan nata ba, bata ce komi ba ta tashi ta shiga dayar ɗakin grandma wanka tayi ta zo tabi jikin ta da humra masu sanyin kamshi ta saka doguwar rigar material mai tsantsi, kwanciya tayi saman gadon har bacci ya fara daukan ta sai taga kamar bata kyauta ba zata tashi sai wata zuciyar tace "ina zaki? Koma kiyi kwanciyar ki ooo". Aikuwa with out second thought ta kwanta, tana datse ido, jin an bude kofan ne bai sa ta buɗe ido ba dan tasan grandma ce, "namecy ta haba mana taso ki tai maka masa, ya tafi ya dawo, ga key nan". Ta ƙare maganar da miƙa mata key, jin tace bai nan yasa ta tashi ta dauki hijab ta fice zuwa part din, har ta gama zata fito taci karo da AS da shima ya kawo jiki zai shigo, matsa mishi tayi amma sai yaƙi matsa mata, murya na rawa dan haka kawai taji yanzu wani tsoron shi ya rufe ta, murya na rawa tace "yaya zan wuce". Shigowa yayi ya kulle kofan hade da bama masa key, "yaya ni wuce wa nace maka zanyi fah". Bai kulata ba ya zare key ya shige cikin bedroom da yake kal kal ga sai kamshin yake tashi, wanka yaje yayi ya fito ya saka kaya ya gabatar da sallar azahar da ake ta yi, bayan ya idar ne ya fita falo yace ma eelham taje tayi salla "Ni zanyi a wajen goggo". "Ban isa dake ba kenan". Da sauri ta girgiza kai tace "a'a yaya" tayi maganar muryanta na shaking "ok! Shiga kije kiyi salla". Wannan karan ba musu ta shiga ciki,Saida ya dai-daita lokacin sannan ya shiga dakin, EElham na ganin shi taji kirjinta ya buga da karfin nan da nan tsoro ya rufe ta lokaci ɗaya,, ƙarasawa yayi zuwa inda take, ba tare da yayi mata magana ba ya cire mata hijab yana aje wa a gefe, cikin muryan raɗa yace "u're so special to me dear wife". Yana gama faɗin haka ya dauke ta chakk zuwa bed hankali eelham idan sunyi dubu to fah duk sun tashi, wutsil-wutsil ta dinga yi da ƙafa wai ya sauke ta amma ya ƙi bayan ya aje ta ne, ya sauke dukan coutins da Bob ɗin dakin EElham kuwa tsoro firgici sun hanata tashi daga inda ya aje ta......... Grandma kuwa duk zatan ta ko EElham ta koma wajen goggo ne daga nan shi yasa bata damu ba, har ma ta manta da batun ta saka Elham gyaran part din AS lokacin wuraren 5 ummi ta shigo bayan ta gaisar da inna, take gaya mata ai eelham tana asibiti anyi mata ɗinki, cikin rashin fahimta goggo tace "wani kalan dinki kuma?". Cikin kunya ummi tace "ta shiga kwaryan manya....✍️

       Tsokaci; wasu suna ta tambayar wace Anne? "Anne dai idan ba'a manta ba matar baba ce, yayan Ammie wato yaron goggo, su Maleeka yaran shi ne su uku Allah ya mallaka mishi, fadil da hashem kuma surikan Anne ne su". Fatan an fahimta