72&73
72 & 73
Assalama Alaikum mutanen kirki mutanen kwarai amincin Allah ya lullube Ku a duk inda kuke, kamar yadda kuka sani yawan talla ta yi yawan roko a yau ma na zo muku da sirrukan gyaran fata, Idan matsalar bushewar fata ko matsalar tsakewar fata ko kuma su kike yi fatarki ta yi glowing ta yi kyau da santsi kamar bayan fiki wannan post din na ki ne don kayanki sun tsinke a gindin kafa kin kawo kuka gidan mutuwa. Don ban dalilin kina da damar mallakar extra ordinary ki je ga ordinary ba
Super lightening soap
Organic lightening soap
Baby soap
Lightening dilka soap
Attractive soap
Morocco soap
Muna maraba da masu siyan daya ko sari muna aikawa ko ina a faɗin duniya cikin aminci
Gamai buƙata ya tuntuba wannan number ***
Dan Allah idan baki shirya siyan kayan mu ba toh babu buƙata kira ko chatting dan ɓatawa juna lokaci
بسم الله الر رحمن الر حىم
Zaune ya kai gefen sofa da take a kai yana kallon fuskar ta da ta haɗe su tamau kamar bata taɓa sanin mi ake kira da dariya bah, sauke boyayyar ajiyar zuciya yayi dan he really miss her, rabon shi da ita since when they discharge her from hospital, idon da ya zuba mata ne yasa ta ji duk ta dan daburce, ganin hakan da shima yayi ne sai ya saki dan guntun murmushi amma bata ga hakan ba, tashi tayi zata bar wajen ya riƙo hannayen ta yana komar da ita zaunen da take, shima haɗe tasa face ɗin yayi yace "baki iya tarban miji bane?". Can ƙasa ta furta"baka koya min bah". Karab kuwa a kunnin shi, dan Allah ya bashi ƙarfin ji sosai, amma sai ya nuna kamar bai ji mi tace ba, "Madam". Yayi kiran ta kamar yadda ya saba, idan ta tanka cushion da take a kai shima ya tanka, Saidai ta kara daure fuska fiye da farko dan bata son wannan sunan da yake laƙaba mata, duba time yayi yaga lokaci ya ja dan daman yau da niyan ya ganta ya zo "dejarht". A kan maƙoshi ta amsa masa da "uhm". Yaso a ce ta kalle shi dan yaga reaction ɗinta amma taƙi ganin haka ne yasa yace "tafiya ta kamani zuwa england zai kuma dauke Ni tsawon lokaci har na wata uku ko biyu is depend dai, so zan tafi da mubeena tunda ke iyayen ki sunce bazaki ba, shi yasa nazo nayi Miki sallama, sannan gobe za'a kawo su Anwar sai ki taya mu rikon su kafin mu dawo". Addu'oi ta rinƙa jerawa a cikin zuciya tun sanda ya fara magana, Allah da ikon shi sai taji ta fara dawo wa dai dai cikin rashin damuwa da haka da fake smile on her face amma u will never kno cewa it's fake, cos she's wise, "yauwa kaman kasan nayi missing ɗin su, Ni daman tun yau ka kawo min su". Tayi maganar with full of excited" with full of worries on his face ya dube ta, yana kokarin gane da gaske take or not,amma ina ya kasa gane her current mode, bai gama dawo wa normal ba tace "ko na bika na karɓo su ne?". In angry voice yace "da in kika taka ƙafan ki zuwa can ke da dawo sai baba ya gani, ban riƙe ki ba ki tafi ki dauko su,wacce bata san inda yake mata ciwo ba mtssssw". Ya ƙare maganar da jan tsuka, ya aje mata ledar hannun shi sannan ya fita without saying a gud bye....Yana fita itama ta tashi ta shige ɗaki da gudu ta faɗa bisa bed ta fashe da kuka da take ta riƙe shi tun dazu...Goggo da fitowar ta falo kenan taji kuka kuma daga dakin eelham yake fitowa yasa babu shiri ta nufa can ba tare da tayi mata knocking ba ta tura kofa ta shiga, inda ta samu eelham sai kuka take kamar ranta zai fita "subhanallah, ke Khadijah mi ke damun ki da kika samu waje kika zauna kina yiwa mutane kuka ko waye ya buge ki?". Faɗawa tayi zuwa jikin goggo tana ƙara wata sabuwar kuka, goggo dai bata kuma magana ba tana dai ta buga bayan ta alamun lallashi, haka dai har ta samu tayi shiru tana sauke ajiyar
zuciya...."Khadijah! Mi akayi miki kike kuka?". Ba ta taɓa boyewa goggo komi ba kuma a yau baza ta fara ba, cikin sanyin murya tace "goggo yaya ne wai zai yi tafiya zai je england zai kuma yi 2 or 3 month a can shine wai zai ɗauki mommy su Anwar ya tafi da ita". Ta ƙare Maganar wasu sabbin tears suna ƙara zubar mata.... Ka dan ya rage goggo ta fashe da dariya dan eelham ta bata dariya sosai,one side kuma tana tausaya mata "banda abinki eelham,mi na kuka, tunda kin san kina son ki bi shi mi yasa baki gaya masa bah?"."Goggo taya za'ai nace zan bisa bayan yace da matar shi zaije, salon ma su raina ni, kina ji ma dan baza shi dani ba cewa yayi zai kawo min su Anwar nayi rainon su"."Ooh ke kuma ai ba fito masa zakiyi ki ce zaki bah,a siyasance a ke yi ke kuwa". Sauke nunfashi tayi dan bata jin zata iya yin haka dan kamar da zubda class din ta neh. Kamar goggo tasan mi take kullawa tace, "nasan zaki ga kamar yin haka zubda class ne, a'a zakiyi abin ne da dubara ta yadda ba za'a gane ba, wai ma kina abu kamar ba mace ba". Sam bata jin zata iya yin haka, sai dai ace mata ita ba mace bace, dan bata cike da rashin kama class. "Daman taurin kai ne da ke kamar naman kai, karkiyi mana ba kece zaki sani ba, kiyi duk abinda kike ganin shine dai dai". Tana kaiwa nan ta tashi ta bar mata dakin da jin haushi, dan ita taso EElham tayi yadda ta faɗa mata amma sai dai ta san jin kai irin na ta ba zai bari tayi hakan ba..Tashi tayi taje tayo wanka tazo ta saka kayan bacci masu dan nauyi dan garin yau akwai sanyi na damuna, shinfiɗa sallaya tayi ta gabatar da shafa'i da wuturi bayan ta idar ta daura da tilawa Saida tayi abinda ya samu sannan ta tashi bayan ta kaiwa Allah kukan ta, kwanciya tayi tana kwantawa babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita......Zawaro ya dinga yi tsakanin falo dan cikin kwanaki biyun nan ya rasa gane kanshi ya rasa control ɗin shi, at all, momma ce ta fito daga cikin dakin shi, dan ta duba taga baya cikin ɗaki kuma bata ji motsi a toilet bah shi yasa ta fito zuwa falon, tana fitowa kuwa ta ganshi sai Safa da marwa yake,tsaya wa tayi ta na kallon shi ta lura kwana biyun nan cikin damuwa yake, amma sai ta share kamar bata san halin da yake a ciki bah, cewa tayi "yallabai". Juyowa Abbie yayi cikin nutsuwar sa yace "na'am". Cikin nuna halin ko in kula tace "kazo muje mu kwanta kaga dare ƙara nisa take". Zuba mata ido yayi kawai yana kallon sabon canjin da ya gani daga gareta, ganin hakan da tayi ne sai ta dauke kai kamar bata fahimci kallon da yake mata ba taja ƙafa ta wuce bedroom, shima ɗin dakin ya shiga yana jin kanshi duk babu daɗi.ganin da yayi kwanciyar duk ta i'she shi yasa ya tashi ya dauro alwalla yazo yana kaiwa Allah kukan shi, ya dade a nan kafin daga baya ya kwanta a nan babu jimawa kuwa bacci ya dauke shi cike da mafarkai barkatai....Washegari,Wuraren ƙarfe 7 AS da nubeena suka shigo gidan su ummi dan sun kawo su Anwar ne, fuskar mubee kuwa a sake yake babu wata damuwa a kai, kallan mubeena yayi yace "ki shiga wajen Ummi ina zuwa". dan jim tayi kamar tace suje tare amma da ta tina da ita za'a sai ta sauke nunfashi still dai tana jin kishin eelham na taso mata, babu yadda ta iya ta kama hannun Anwar,Anam a hannun ta suka wuce part din ummi, shi kuma AS ya shiga na goggo.Da sallama dauke a bakin shi ya shiga, sai dai ya tadda babu kowa a falon sai dan motsin da yake jiyowa daga kitchen, can ɗin ya nufa, tura kofan yayi ya shiga idanun shi suka sauka akan eelham da tayi busy frying fara, daga kofa ya zuba mata ido dan ba komi ya dauki hankalin shi ba sai yadda skin dinta ke dauka ido yayi luwai duk da ta kasance ita din ba fara ba ce amma hakan bai boye komi daga glowing ɗin da tayi bah, sauke nunfashi yayi yana ƙarasawa wajen da take ganin ta nuna kamar bata san da shigowan mutum ba, kuma tsaff ta San da zuwan nashi ta hanyar kamshin Tularen shi ta dai share ne kawai, ji tayi yace "gud morning wife". Tabe baki tayi a zuciya kuwa sai tace "su wife anji jiki". Amma a fili sai tace "ina kwana?". Bai amsa gaisuwar ba sai cewa da yayi "mi kike da soya fara da farar safiyar nan?". Cikin nuna kamar maganar gaskiya za tayi tace "goggo ce ta saka Ni". Tayi maganar kamar wacce a ka saka aikin akan dole bayan kuma ita ta saka kanta dan haka kurum taji tana son cin fara daman akwai sai ta diba, kallon faran yayi ganin yadda tayi fresh tayi jan gashi yace "yau zata ci daɗi kenan? Nima ki saka min tawa a take away Dan Nima naji inasan ci duk da ban taɓa ba,gada kai kawai tayi dan i zuwa yanzu ta kai nakura dan Tularen da AS yasaka ji tayi yana tasar mata da zuciya ganin dai zata Cutu yasa cikin sanyin murya kamar ba ita ba ga hawaye har sun cikar mata a idanu, cikin kwanakin nan bata da wuyan yin kuka cewa tayi, "yaya dan Allah ka fice ni tularen ka yana tasar min da zuciya". Ta ƙare maganar daidai hawayen na saukar mata a fuska. Da mamaki yake duban ta ganin ba duka ba zagi amma tana yi masa kuka, cikin lallashi yace "baki son tularen ne?". Hannun ta toshe da hanci ta gada mishi kai alamar eh, cewa yayi "amma wannan ai shine perfume din da nake amfani dashi". "Toh ni ban san shi". "Wanne kike so toh?". "Ni dai ban sani ba amma dai ka canza pls". Sauke nunfashi yayi yace "ok shikenan consider it done ma'am". Harara ta banka mishi tana barin wajen sai da taje kofa tace "ga faran nan kama juye duka". "Goggo fah?" "Bata so" "ok Nima bana so". Cewar AS, ita kuwa daga kafaɗa tayi alamar she don't care cikin sauri ta buɗe kofan ta fita daga kitchen ɗin ta shige dakin goggo tana fadawa cikin toilet, goggo da taga shigowar ta haka sai ta bita da ido kawai sai da taji kakarin amai ne sannan ta mike ta shiga toilet ɗin tana "assha! Khadijah mi yake faruwa dake ne, ko baki da lafiya ne?". Cikin sauke nunfashi ta girgiza kai alamar a'a sannan tace "perfume din yaya ya saka ni amai". Zuba mata ido goggo tayi dan tun ba yanzu ba take lura da some changes da ta gani tattare da ita,amma sai ta dauke kai tana taimaka mata, a tare suka fito inda suka samu AS a zaune ya zuba wa kofa ido yana kallon EElham, ita kuwa dauke kai tayi kamar bata san mi yake yi ba, bed ta karasa ta kwanta tana sauke nunfashi, idanun shi na kan eelham yace "goggo daman bata da lafiya nah?". "Lafiyar tayi karanci kam Ahmad dan kwana biyun nan jikin nata sai a hankali, ta kuma ƙi fadin abinda yake damun ta aje asibiti". Sauke nunfashi yayi yana cewa "zuwa anjima sai taje idan jikin ya dan sauka". Ita dai duk tana jin su ta dai saka kanta a ƙarƙashin pillow dan bata son tana shaƙan kamshin Tularen shi a yanzu, wanda a da kuma tana so, tashi goggo tayi ta bar musu dakin,wannan daman yayi amfani ya karasa inda take, yana zama kuwa ta fashe masa da kuka bilhakki da gaskiya kamar wacce ya kama ya daka, wanda shi da kanshi ya san ba haka take ba dan saurin kuka ba nata bane "wife! Ki faɗa min abinda ke damun ki kinji? Ko jikin ne?". "Ni ban san perfume din nan fa shi ya saka nayi amai". "Elham wani rigima kuma kika bijiro dashi, ok sai ki faɗa min wani perfume kike son nayi amfani da shi". Kanta dai na a karkashin pillow ɗin bata dago ba ta ƙara amsa masa da "Ni dai ka canza". "As u wish ma'a..." Ai bai ƙarasa ba ta fashe da kuka kamar wata ƙaramar yarinya. Shi kam abin nata ya koma bashi dariya, "nikam wannan kukan bada Ni ba, bara naje kar muyi late". A gundure ta ce "Allah ya tsare".......✍️
Alhamdulillah Masha Allah, dazun nan wata yar uwa take gaya min ta saka wa yarinyan yayarta sunan EELHAM wanda nayi farin ciki da haka, dan Allah ku saka wa diyar mu EELHAM albarka dan Allah kar ku wuce wannan page ɗin baku yi mata addu'a ba ita da mahaifiyar ta.
Mommy EElham Allah ya ƙara Miki lafiya ya kuma hore abinda za'ayi wa EElham hidima Alfarman Annabi Muhammadu saw.
Allah yayi wa rayuwar ki albarka
Allah ya rayaki akan sunna eelham baby I really love u dear daughter.
I dedicated this page to lovely daughter EELHAM❣️ Allah ya raya ki a kan sunna, Allah yama Rayuwar ki albarka, dana sauran yayun ki 🤲