74&75
{🌹 EELHAM🌹}
Rabe'arh wakili
74 & 75
بسم الله الر رحمن الر حىم
Sosai yaji daɗin addu'an nan da tayi mishi duk da a gajarce tayi shi, amsawa yayi da "Amin ya rabb, sai munyi waya". Da ok ta amsa masa dan duk perfume dinsa ya cika mata hanci, shima lura da haka ne sai ya tashi, har ya kai ƙofa unexpected tace "sauran idan kaje kamanta da zamata! Take care". Tana gama hadin haka ta faɗa cikin toilet shi kuma ya juyo yana bin bayan ta da ido har ta ɓace ma ganin shi, wajen mirror dinta ya nufa ya dauki pen da joter da ya gani, falla yayi ya rubuta mata short message ya aje mata bisa bed ta yadda zata gani da wuri,sannan ya fita da ɗan sauran murmushi a face ɗin shi, a tsatsaye ya sallami goggo ya fice zuwa part ɗin umma shima a tsatsaye yayi gaisuwa ya fito ya shiga na ummi kamar sauran bai zauna ba dan sun kusa makara bayan ya gama gaida ummi ya dubi nubeena da ta cika tayi fam kamar zata fashe, bai kula da hakan ba dan shi gani yayi samun wajen nata yayi yawa, yace "tashi muje" a kunbure ta mike tana ficewa daga palour ko sallama Ummi batayi ba,shima bin bayan ta yayi bayan ya sallami Ummi, driver ya kaisu har airport suna zuwa babu jimawa Flight ɗinsu ya daga zuwa england.... da farko taso ta sakawa kanta damuwa amma daga baya tayi wa kanta karatun ta nutsu, sannan ta saki abin ta maida shi kaman ba komi bah, Saidai cin abincin da take a yanzu nan ya fara bata tsoro dan harda abinda bata ci a da a yanzu shi take so, gashi yanzun nan tuwo take so ta shinkafa miyar bitter leaf ga bata jin zata iya da kanta dan haka ta tashi ta shiga dakin goggo inda ta same ta zaune tana gyara kayan ta, sannu da aiki eely tayi mata cikin rashin gaskiya tace "dan Allah goggo tuwo nake so ta shinkafa da miyar bitter leaf". Tun da ta fara magana goggo ta saki abinda take ta zuba mata ido baki sake da annashiwa sosai a face ɗinta tace "tuwo kuma EElham? Keda baki cin tuwo barin ma miyar ɗaci? Mi zakiyi dashi?". "Ci zanyi fa goggo". Tayi maganar hawaye suna zubar mata, goggo kuwa cikin zuciya fadi take "abun ya zo ga ma iya". A fili sai tace "nikam ba zan iya shiga kitchen yanzu ba atoh". Wannan karan fashewa tayi da kuka kamar wacce aka daka cikin kukan tace "in da zan iya yi da kaina da ai bazan zo wajen ki ba! Dan Allah goggo kiyi min". Ta kare da saukar da murya dan goggo ta tausaya mata. Saida goggo mulu dan kanta sannan tace zata yi mata badan halin ta ba sai dan abu ɗaya, a fakaice eelham ta taɓe, amma a zahiri sai tace "toh Nagode goggo , bara naje part din grandma dan banson naji kamshin girkin,idan kin gama zan dawo ko kuma ki kira ni". "Toh a dawo lafiya". "Amin" ta amsa tana fita daga sashen zuwa ta grandma ba, ba tare da tayi sallama ba ta shiga sai wani huhhura hanci take ta samu waje ta kwanta a ƙasa, grandma kuwa tun da eelham ta shigowa ta zuba mata ido har yanzu kuma bata ɗauke ba, cikin niman magana irin ta grandma tace "nifa idan za'a shigo ana yin sallama, a daina fado min cikin ɗaki haka". Cikin tsiwar da take dashi a kwanakin nan tace "toh ki fidda ni mana, ba ma ki gode an shigo miki waje ba, yen yen yen yen". "Kinwa mijin ki AS badai ni ba ehem, eh Ahmad ba,da ya wuce da matar so ya bar ta cushe eh shifa". Bata ce mata komi ba ta tashi ta bar mata dakin nata duka ta koma ta umma, tana zuwa ta faɗa jikin umma tana sakin siririn kuka tace "umma Kinga grandma gori ta koma tana yi min, wai yaya ya wuce da matar so ya bar wacce akayi masa cushe, dani takeyi fah? Bayan ita ta hana yaya tafiya da Ni, ai ya gaya min". Sauke nunfashi umma tayi tana kuma gode wa Allah da eelham ta fara dawowa kan hanya, tace "karki damu kinji auta? Da kanshi zai zo yana niman ki insha Allah, amma ba grandma ce ta hana ya tafi dake ba, ganin daman shi ne kawai, dan haka kema U have to shine ur eyes am I clear?". Cikin gamsuwa da maganar umma ta gaɗa mata kai dan da kanta itama ta shirya tayi fighting akan mijin ta, dan lokacin haka yayi,,,, nan umma ta zauna ta dinga bata shawarwari sosai kuma alhamdulillah eelham tana daukan su tsaff a kanta,har dai tazo bacci ya dauke ta, ganin haka ne umma ta gyara mata kwanciya hadi da faɗin "Allah ya raba lafiya"..... Saida ta sha bacci sosai wuraren biyu saura ta tashi, toilet taje ta wanke fuska koda ta fito bata tsaya komi ba ta fice daga sashen zuwa ta goggo inda ta iske ta gama yi mata tuwon ta jera su a dining sannu da aiki tayi mata ta tafi dining, sarving tayi sannan ta hau cin tuwo ba ƙauƙautawa, sai da taci ledar biyu sannan hankalin ta ya kwanta, barin wajen tayi ta koma ɗaki toilet ta shiga ta wanko hannu daga nan ta ɗauro alwalla tazo ta gabatar da sallar azahar. Ko bayan da ta idar wata baccin ta koma dan wanda tayi bai i'sheta ba, ta danyi nisa a bacci ta ga an danne mata ciki ga wani abu yana yawo a cikin a lamar dai matsan da akayi masa shi ya kawo haka ga ita ma eelham dakyar take jan numfashi cikin wahala, cikin ikon Allah ta fara karanto addu'a ta neman tsari sannan ta fara jin sausauci daga nan bata Kuma sanin inda kanta yake ba..... Kamar yadda take a bangaren eelham haka take a bangaren Aziza, itama ɗin cikin mafarki taga an danne mata ciki ga yaron da yake a cikin sai motsi yake alamar shima dannan ta shafe shi kamar an ƙwaci bakin ta ta furta addu'a nan da nan taji komi ya wuce a gigice ta farka da sauran addu'a a bakin ta, cikin tsoro ta bar dakin tana tafiya a hankali dan ji take jikin ta na ciwo ga kuma tana jin abu na bi mata ƙafa koda ta duba taga jini ne cikin rikicewa da fidda rai shikenan ta rasa wannan cikin shima ta durƙushe anan ta fashe da kuka, tana kuka tana rokan Allah, ganin tana da sauran ƙarfi kuma jinin ba rushing yake ba yasa ta ɗauki key na moto ta fito tana ƙwala kiran driver Allah yasa suna waje cikin sauri ya taso ba tare da tayi masa magana ba ta mika mishi key, fahimtan mi take nufi ne sai ya karba ya buɗe motar itama ta shiga ya bama motar wuta, Saida suka bar anguwar ne yace "Hajiya ina zamu". A wannan lokaci jinin da ke zubar mata ya ƙara rushing, dan haka dauriyan ta ya kusa karewa, ga bata gani sosai biyu biyu take ganin shi, murya na rawa tace "hospital mafi kusa". Jin haka da kuma halin da yake a ciki ya kara bama motar wuta suka nufi wata private hospital da Sauri ya fita ya shiga ciki babu jimawa ya fito shi da wasu nurses su uku da gadon daukan majinyata, bayan sun daura ta a kai suka nufi ciki da ita ganin tana son ta dauke wuta... Chan Abuja haka ta kasance ga mufeeda saidai ita ta fisu jin wahala dan cikin ta ya girma sun shiga watar haihuwar su, nunfashi take ja da karfi kamar zata yi yaya ga dannar cikin da akayi mata cikin mafarki ga kuma labour ta tasar mata lokaci guda, bata yanke kauna ba haka ta dinga fighting da nunfashin ta ga hannun ta nan saman ciki tana ture wanda ya danne mata ciki tun tana da karfin ta har tazo ta gaji tana a wannan halin Allah ya kawo yaya sadeeeq, cikin tashi hankali ganin halin da take ciki da sarsarfa ya karasa wajen ta yana girgiza ta amma kamar karya taɓa ta cak numfashin ta ya tsaya a dai dai lokacin jini ya barke mata kamar an kunna fanfo nan da nan tayi haske tayi fayau,rasa mi zai yi yayi ya kasa taɓuka komi dan ya ruɗe sosai, yana a haka yaji murya aunty Billy tana sallama, ai babu shiri ya miƙe ya fita zuwa falo cikin tashin hankali yace "Anty ki taimaka kar mufeeda ta tafi ta birni dan Allah, cikin bugawar zuciya da ya saka ta ta wuce direct zuwa bedroom inda ta samu mufee a yadda yaya sadeeeq ya barta ga jini har ya bata gefen da take sosai,, dake zuciya aunty Billy tayi ta fita ta kira yaya sadeeeq tace "dauko ta". Babu musu ya dauke ta suka fito zuwa parking lot, Anty Billy ita tayi driving zuwa hospital da niyan ta su tafi wanda suka buɗe file a nan amma wata zuciyar bata aminta da haka ba sai ta share kawai ta canza izuwa wata, suna zuwa aka tafi da mufee emergency unit, wanda yaya sadeeeq yaso ya shiga amma doctor sun hana,.... Abin duniya ya taru yayi mata yawa ta rasa yadda zata saka kanta, dan labari ne yazo mata akan farmakin da aka kai wa su EElham tana cikin wannan halin sai ga wani kiran nan, ɗauka tayi ji tayi ana cewa ga "Abbie nan shima sun farmake sa saidai basuyi nasara a kanshi bah dan shi bai yi bacci ba a zahiri suka je masa alhamdulillah Allah ya kunbtar da...." Bata karasa ba sai jin ihun da tayi daga ɓangaren mai maganar cikin tashi hankali ta rinƙa kiranta tana "mamyn yara" daga ɓangaren mamy kuwa, ihu take tana "dan Allah kayi hakuri,kar ka taba marainiyar Allah, na yadda kayi min koma mi,amma dan Allah karka taba ta dan Allah na roke ka, ta ƙare maganar da fashewa da sabon kuka hadi da haɗa hannayen ta alamar roƙo, dan har cikin zuciya take jin soyayyar eelham kamar ita ta haife ta.babu ko tausayi ya ƙara wanke mamy da sabuwar mari yace "ina eelham take munafuka". "Wallahi ko kashe ni zaka yi bazan taba barin kasan inda take ba, banda ma ƙaryan rashin kunya ku nimo inda take m..." Marin da ya ƙara dauke ta dashi shi ya katse mata maganar ta, shafa bakin ta tayi ta kalla jini alamun dai ji mata ciwo, daga can bangaren matar can kuwa recording ta kunna dan Allah bai Bama wannan mutumin daman hango wayar da mamy ta wurga karkashin gado ba.. ɓangare mamy da wannan mutumin kuwa daka mata tsawa ya ƙara yi yace "zaki faɗi inda eelham take ko sai kinje inda mahaifiyarta taje?". Bakin mamy ba ya mutuwa yan zu dinma cewa tayi "koda yanka nama kake bazan faɗa ba wallahi". Finciko ta yayi yana ja a kasan ƙiiiiiiii kamar yana jan kayan wanki, ganin zata tona masa asiri sai ya shaka mata abu a hanci daga nan tayi takab bargo ya ciro ya nade ta a ciki ya daura ta a kafada kai baza kace mutun bane dan yadda ya kanannaɗe ta babu tausayi, haka ya fiddata daga gidan gaba ɗaya, daman kafin ya shigo Saida ya shaƙa ma gate man wani abu shine har yanzu bai farfaɗo ba, yana fita ya jefa ta cikin motar kamar ba mutum ba wanda sai da kanta ta kwale da kofa, a 360 yabar area din,cikin ƙanƙanin lokaci ya kawo wata anguwa wacce tafi tasu mamy shiru, cikin wani danƙararren gida ya danna horn da gudu gate man ya taho ya buɗe, shiga yayi yana parking a lot, wannan gient din kuwa ganin shine yasa suka ƙarasa wajen shi suna mika gaisuwar su fuskar nan a lullube yace "ku fidda ta daga garin nan gaba ɗaya, ku gana mata punishment har sai ta faɗa waye abokan aikin ta da kuma ina eelham take". Amsa masa sukai cikin girmamawa, shi kuma ya jefa musu key yana shigewa zuwa cikin falon, sukuma babu bata lokaci suka fita da mamy daga gidan suna ɗaukan hanyar barin gari...... Goggo ce ta shiga dan ta tada eelham lokacin salla tayi amma tana shiga ta fara cin karo da jini a bakin kofa, cikin ruɗu ta tura kofa inda ta samu eelham bisa gado ga jini yayi mata kaca kaca, goggo tana da dakiya dan haka yanzu ɗin ma dakewa tayi ta koma falo ta ɗauki waya tayi kiran bappi daman yanzu ya bar part din,, yana ɗauka tace "ka wuto da key". Tana gama faɗin haka ta yanke, wayar tana maida akalar kiran ga grandma cewa tayi ta shirya ta fito fita ya kama su, tana a haka sai ga bappi ya shigo, ba tare da ta dube shi ba tace ka shiga ka ɗauko eelham, ba musu ya shiga dakin nata saidai daskarewa yayi a kofa ganin jini maida duban shi yayi ga eelham nan dinma gani yayi duk tayi stain,jin murya goggo yayi tana cewa "ka dauko ta mana". Haka ya karasa jiki a sanyaye ya karasa gare ta ya dauke ta yana dauke hawayen da ya makale masa a ido,, haka suka fito inda suka samu grandma wajen mota, ganin an dauko EElham haka ne ga har kayan bappi sun ɓaci tace "innalillahi wa'inna alaihi raji'un, la'ilaha ilallah Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, mi ya sami namecy?". Tayi maganar muryarta ta na rawa sosai ga hawaye na zubar mata, dan duk wanda ya kalli eelham a lokacin sai ya tausaya mata, babu wanda ya tanka mata dan duk basu cikin nutsuwa, shigar da ita mota bappi yayi cikin sauri suma su goggo suka shiga bappi ya tada motar suka wuce hospital a 360, koda suka je daman yayi kiran doctor din su shi yasa suna zuwa aka daura eely akan gadon daukan majinyata aka tafi da ita zuwa ciki.... AS sun sauka a kasar england babu jimawa, bayan sun sha tafiya a sararin samaniya, hotel ɗin da yayi bucking ya samu moto taxi ya kaisu har can, biyan mutumin yayi dan yana da kuɗin su na nan,kama hannun mubeena yayi suka shiga ciki, yana jin zuciyar shi babu daɗi ya kuma rasa mike damun shi, koda suka je wanka yayi ya ranka sallah dake kashi, ga mubeena ma haka ta kasance, bayan sun idar ne suka samu waje suka kwanta dan duk a gajiye suke, Mubeena ta fara bacci AS kuwa, gaba daya tunanin shi ya koma ga eelham dan haka kawai tunanin ta ya rinƙa zuwan masa kamar dai eelham bata lafiya, kudira yayi da safe zai kira ta, haka dai bacci ya dauke shi da tunani barkatai cikin zuciya kuma duk ta eelham ce......
Alhamdulillah, Alhamdulillah,anan zan dakata sai in kuma Allah ya kai mu bayan salla in sha Allah, dan Allah wanyenda nayi musu ba dai dai ba kuyi mun afwaan hakan na daga cikin ajizanci na ɗan Adam.
Allah ubangiji ya dawo da mu lafiya, Allah yasa yadda muka hadu har zuwa yau Allah ya ƙara haɗa mu haka cikin koshin lafiya mai albarka, Amin ya Arrahman Rahimin 🤲
Falalar Kwanaki Goma Na Farkon Watan Zul-Hajji
.
An karbo Hadisi daga ibn Abbas (R.A) ya ce Annabi (SAW) ya ce: ranar daya ga watan zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya gafarta wa Annabi Adam (A.S). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah(SWT) Zai gafarta masa kowane irin zunubi tsakaninsa da Shi.
.
(2) Ranar biyu ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya karbi Addu’ar Annabi Yunus (A.S) Ya fitar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi. Wanda ya azimci wannan rana yana da lada kwatankwacin wanda ya raya shekara da ibada .
.
(3) Ranar uku ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya karbi addu’ar Annabi Zakariyya (A.S) Ya ba shi haihuwa. Duk wanda ya azimci wannan rana Allah (SWT) Zai karbi adduo’in sa.
.
(4) Ranar hudu ga Zulhijja ita ce ranar da aka haifi Annabi Isah (A.S). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah Zai kare shi daga talauci da musibu.
.
(5) Ranar biyar ga Zulhijja ita ce ranar da aka haifi Annabi Musa (A.S). Duk Wanda ya azimci wannan rana Allah (SWT) Zai kare shi daga munafunci ko azabar kabari.
.
(6) Ranar shida ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya Yi budin alkhairi ga Annabi (SAW). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah Zai dube shi da rahama, kuma ba Zai azabtar da shi ba.
.
(7) Ranar bakwai ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Zai sa a rufe kofofin wuta, ba za a bude su ba har sai wadannan kwanaki goma sun wuce. Duk wanda ya azimci wannan rana Allah Zai rufe masa kofofi talatin na tsanani a rayuwar sa, a bude masa kofofi talatin na sauki.
.
(8) Ranar takwas ga Zulhijja ita ce ranar da ake cewa, ranar tarwiyya. Duk wanda ya azimci wannan ranar, babu wanda ya san adadin sa sai Allah.
.
(9) Ranar tara ga watan Zulhijja ita ce ranar hawan Arfa. Allah Yana gafartawa duk Alhazan da ke wurin Arfa. Wanda kuma ba ya wurin aikin Hajji, idan ya azimci wannan ranar, Allah Yana gafarta masa zunubansa na shekarar da ta gabata, da kuma shekarar da ke tafe.
.
(10). Ranar goma ga Zulhijja ita ce ranar layya. Duk wanda Allah Ya horewa abin da zai yi layya, idan ya yanka dabbarsa, digon jini na farko da zai fara diga a kasa zai zama gafara gare shi da iyalin sa. An so wanda zai yi layya da wanda ba zai yi ba ya kame bakinsa sai bayan an dawo daga sallar idi, ya ci abinci ko wani abu daga cikin layyarsa. Allah Zai ba shi lada wacce ta fi Dutsen Uhud girma da nauyi. Kuma ana so ya raba naman sa kashi uku. Kashi na farko sadaka, kashi na biyu kyauta, kashi na uku kuma domin iyali.
.
Allah Ya ba mu Ikon azumtar dukkan wadannan ranakun, kuma Ya sada mu da falalar da Ya tanadar ga masu Ibada a wadannan ranaku. Amin.
Ya Allahu ka tsare hanyar duk wani matafiyi, ya Allah ka kare mu, da iyayen mu, da yayun mu, da kannen mu,da mazajen mu da ƴaƴan mu, yah Allah kasa duk wata hidima ta sallah da za'ayi Allah kasa muyi shi lafiya da kwanciyar,Allah yasa muyi sallah cikin wadata da koshin lafiya, Allah ka karɓi ibadun mu Amin dan darajan fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam 🤲
Dan Allah ku saka Ni a addu'a yan uwa🙏🙏
A sha shagalin sallah lafiya🤲💃💃💃💃ina jiran yan yawan salla fah☺️🤭🤭a kuma ɗan tausaya wa ciki gudun kar ya saka or saki zawaro,🥺🥺😅 wai wata tausayi kuma?😁🤔inace shi ma zai ƙaru? Dan haka no sausauci, no sausauci nace,😂🤣🤣🤣amma nace bah? sai a dan tanadi ja da yalo a gehe da tocila mai haske dan patro na dare🤣🤣🤣🤣🤣🤣😅😅😅 a Toh babu ruwana yauwa 😂😂😂amma waɗan nan kasusuwan kar a raga musu hillis ayi dugudugu da ita har sai ta zama kamar hoda, 🤸🤸🤸🤸😂 🤣🤣🤣😅😅Ni na gaya miki🤭🤭🤭 amma kuma nace no my water 🤣🤣🤣🤣saidai a dan tausayawa hakori, wai wata tausayi ma🤔🤣🥺 inace shike tauna har yasa bakin ka gajiya to kar a daga mishi kafa🤣😅😁😁🤣 amma abi shi a sannu atoh ba ruwa na, no my wara 🤣🤭🤭🤭😂😂😂🤣🤣🤣😂🤸🤸🤸🤸🤸 till we meet again bye bye yan aljanna 👏👏👏👋👋👋👏👏👏
Wannan page ɗin taki ce AUNTY BILLY ABDUL🫶🫂Allah ya ƙara sutura yasa kifi haka, Allah ya kara daukaka, da basira, da karfin gani, Amin ya hayyu ya Kayyum 🤲❣️
Over luv lodi-lodi yan uwa yan aljanna 😍❤️🫂🫶
Sai Allah yayi mana dawowa bissalam ma'assalam.☺️