76&77
{🌹 EELHAM🌹}
Rabe'arh wakili
76 & 77
بسم الله الر رØÙ…Ù† الر ØÙ‰Ù…
A can asibi wajen eelham kuwa doctor sun yi kokarin ganin sun tsaida jinin cikin ikon Allah da taimakon sa jinin ya dauke dib kamar anyi ruwa an dauke, sai dai har yanzu bata dawo cikin haiyacin ta ba sanadin jinin da ta zubar babu ƙauƙautawa, haɗa mata da allura ta bacci sukai dan ta samu hutu sosai,sannan suka yi mata karin jini, bayan sun tabbatar da komi yayi musu yadda suke so sai suka fito daga dakin inda suka samu su bappi a tsaye cirko-cirko a kofa, babban doctor din cikin su ne shi ya bukaci ganin bappi shi kuma ya wuce zuwa office dinsa, a daidai lokacin sai ga Abba shima yazo daga gida yake ya kira bappi shine yake gaya masa ai suna asibiti eelham babu lafiya, baiko gaya wa umma ba shima ya wuto kenan, a tare suka shiga office ɗin doctor bayan ya gabatar musu da wajen zama ne sai ya dora da yi musu bayanin cewa "sun yi nasarar tsaida jinin da yake zubar mata kuma Alhamdulillah cikin dake jikin ta babu abinda ya same shi dan shi bai masan anyi haka bah yana lafiya qalau a kuma wajen da ya kamata ya zauna, yanzu dai munyi mata allura ta bacci ne yadda zata huta sosai". Duk da su bappi basu san da zaman cikin ba amma sunyi farin cikin jin bai zube ba ba kuma abinda ya same shi, amma wani gefe na zuciyar su tana tunanin to mi ya same ta da bleeding haka, kasa daurewa bappi yayi Saida ya tambayi doctor yace "amma doctor mi yayi causing haka?". Dan jan numfashi yayi kafin yace "a iya binciken da mukai a yanzu bamu ga komi ba amma dai muna kan bincika har yanzu". Cikin gamsuwa su bappi suka gaɗa kai da mamakin wannan lamarin, haka suka tashi suka fito inda suka gayawa su grandma abinda ke akwai, fatan samun lafiya sukai mata....suna a haka sai sukaga Hydar ya shigo cikin asibitin shima a birkice dan driver da ya kawo aziza shi yayi kiran shi yanzu babu jimawa yake gaya masa ga Aziza nan a asibiti babu lafiya, daga wajen aiki yake shine ya biyo tanan, haɗe fuska grandma tayi dan ta zata ko yazo duba jikin eelham ne shi yasa, amma abinda bata sani ba shi bai ma lura dasu ba dan har ya gitta su bai sani ba, ganin haka ne yasa bappi ya yi kiran sunan shi "hydar?" Yayi kiran cikin mamaki dan yadda yaga kaman baya a hayyacin sa, Juyowa yayi yana kallon su bappi wanda shi a da sam bai gansu ba sai yanzu da akayi kiran sunan shi, amsawa yayi da "na'am bappi" da dan guntun murmushi akan fuskar shi, amma da ka gani kasan cewa aranta yayi ya yafa ma fuskar shi. "Ina zaka haka kake duk a birkice? Baka ma ko ganin gaban ka". Cikin dauriya yace "daman Aziza aka kawo asibitin nan yanzu driver yake gaya min wai sun zo asibiti" "Subhanallah, Allah yasa kaffara ne muje can ɗin". Ba musu kuwa suka tafi can wajen Aziza aka bar goggo da grandma wajen eelham. Koda suka isa can ward din da aka kwantar da Aziza shiga sukai bisa jagorancin driver, baiwar Allah kwance take sanbal duk ta rame ta ƙara haske dan itama sosai ta zubda jini wanda doctor har sun fidda rai daga baya kuma jinin ya tsaya,nan da nan idanun hydar suka cika da ruwan hawaye dan yadda ya ganta ba karamin bashi tausayi tayi ba, amma sai ya boye hawayen dan bai san su Abba su gani saidai ya makaro dan sun gani, baki suka bashi sannan Abba yace "ya kamata muje muji mike damun ta" Cikin gamsuwa bappi ya gada kai inda hydar yaji daɗin haka ganin sun nuna damuwa akan matar shi dashi karan kansa, haka dai suka rankaya zuwa office ɗin doctor,same doctor ne da wanda ya duba eely, dan Saida ya fara attending ma Aziza, yana fitowa akace masa ga wata patient nan an kawo emergency. ganin su Abba da yayi ne yasa ya ɗan saki murmushi yana cewa "Alhaji kunyi mantuwa ne?" Suma ɗin da murmushi Abba yace "a'a mun zo akan batun dayar diyar mu ce" duk da bai fahimta ba ya dai gabatar musu da wajen zama, musabaha sukai da hydar kafin ya zauna, bayani bappi yayi masa yadda zai gane ta Hanyar faɗa masa sunan Aziza da yayi, checking file doctor yayi ya gansa a sama sama, da mamaki ya jiyo yace "ikon Allah, Alhaji ai kusan matsalar su ɗaya da yar uwarta Khadijah" Cikin rashin fahimta har suna haɗa baki wajen faɗin "kamar ya doctor! Wa ce yar uwar ta?". "Khadijah dai wacce kuka zo ɗazun nan akanta" "Ikon Allah" cewar bappi, bayani yayi musu sosai, inda sukai duba sukaga matsalar Aziza da eelham daya, dan itama duk jinin da ta zubar hakan bai sa ya shafe cikin ta ba yana lafiya lau, ba ƙaramin farin ciki Hydar yayi da jin wannan daddadan labarin ba, fuska a sake ya hau yiwa doctor godiya su Abba ma sunyi masa godiyar sannan suka fito daga office ɗin, wajen su goggo Abba suka koma inda yaya hydar ya ya koma wajen matar shi. "Ya mai jikin,? Fatan dai jikin da sauki Koh?" Cewar goggo, "jiki kam alhamdulillah, abin mamaki ma wai matsalar su ɗaya da eelham...." Nan ya kwashe komi ya gaya wa su goggo, inda suka shiga shock da jin wannan batu da kuma yi musu fatan samun lafiya duk da grandma tace alhakin eelham ke binta, "goggo ya kamata kuje ku huta hakanan" "Muje ina ai muna nan daram, kar ma ku fara da wannan zancen dan ko gezau ba zan yi anan ba, idan kuma Hajiya hauwa zata biku ku koma ne toh?" "In koma ina? Ai muna nan a tare yauwa, idan ku kun gaji ne the door is Open kuna iya tafiya, dan mukam muna nan har sai anyi sallama kokuwa Hajiya Khadijah?" "Aikuwa dai duk wanda yaga bazai iya zama ba ko ba zai iya jure zaman mu nan ba shi ya tattara ya koma can inda ya fito! Wai tsaya da nufin ka mu tafi mu barwa namecy waye?". Daman su Umman su na kan han...." Zancen shi katsewa yayi ganin shigowar su ummi ga kaya nan riƙi riƙi a hannun su, gaida su grandma sukai cikin girmamawa da kuma yi musu ya mai jiki, ansawa sukai suma fuska a sake, "goggo nace tunda mun iso da sai kuje ku huta" "Iyeee lailai, kora da hali ƙiriƙiri, eh mana kora da hali mana Hajiya Khadijah duba min fa" Kinga shi yasa nayi gum da baki na dan shiru ai shima babban magana ce, maganar da suke na mu tafi ai saidai su din su tafi ba dai mu ba, Toh mi zasu iya mata bayan kowacce tana fama da ƙiba su wani ce" Su dai su umma basu ce komi ba dan halin goggo da grandma babu wanda basu sani bah, cikin kufula grandma tace "ina kuma kuka kai yaran wannan mutumin? Dan nasan tsaff zai iya shiga Court damu idan yaran nan su ka ɓata" Danne dariya ummi tayi dan lamarin wannan mutanen sai fatan rabuwa lafiya cikin ƙasa da murya da girmamawa tace "suna gidan Antyn su Ruqayyah, da zamu fito ne nasa driver ya wuce da su can" "Atoh haka ma tafi ai" Cewar goggo "yauwa ga matar hydar can itama an kwantar da ita sai kuje can nan mun yi yawa" Ba musu kuwa suka tafi can da sauran kayan da suka taho dashi.
sosai hydar yayi farin cikin ganin su, bayan sun gama gaisawa suka tambaye shi mai jiki inda ya amsa musu da "jikin nata da sauƙi saidai har yanzu bata tashi ba". Cikin tausayawa sukai mata fatan samun lafiya, "ka kira su yaya ka sanar musu kuwa?". Cewar ummi "a'a ban kira ba, dan Allah ummi kema karki faɗa musu" Kallon shi kawai tayi zata yi magana kenan sai ga wayarta ta fara ringing hakan shi ya katse ta daga abinda zata ce, ciro wayar tayi daga bag dinta dan ganin wake kiran, koda ta duba sai taga Abbie ne yake kiran ta, ɗauka tayi da ƙawataccen murmushi a fuskar ta, gaisar dashi tayi daga can gefen ya amsa da fara'a dan baison tasan yana dauke da damuwa saidai ya makaro dan tsaff ummi ta fahimci yana cikin damuwa amma sai bata ce komi ba jikin ta dai yayi sanyi ji tayi yana cewa "ga mufeeda nan a hospital tun dazu take ta bleeding sai yanzu aka samu jinin ya tsaya" dummm haka hydar yaji ƙirjin shi ya buga dan yana jin duk abinda yake fadi da yake yana zaune ta gefen da ta kara wayar shi yasa, ƙara nutsuwa yayi yana maida hankalin shi dan ya gano kan zaren, "subhanallah, amma yaya mi yayi causing haka ko labour ne?" "Ai da labour din ne da da sauƙi, dan da abin haka ya taso mata kamar labour ashe bashi bane, sun dai yi test sunce basu ga komi ba dan cikin jikin ta yana nan cikin koshin lafiya" qTashin hankali da ba'a saka wa date shi ya dirar wa yaya hydar cikin subutan baki yace "inaaa akwai lauje cikin naɗi akwai abinda yake faruwa, lalura kala ɗaya su uku?..." Shapp ummi ta mance waya suke da Abbie tace "son mike faruwa kake magana haka mi ya sami mutane ukun?" "Ummi abinda yake damun eelham shike damun Aziza da mufeeda, kuma duk cikin su na nan lafiya qalau? Wannan abin a duba ne, idan kin kula duka abun ya same su ne kusan lokaci ɗaya" Abbie da dama shi ma ankai masa farmaki yasa tuni ya halbo jirgin maganar da Hydar yake, cikin maida kan shi caml dan kar su fahimci halin da yake ciki yace "hydar bakin ka kanin ƙafan ka, kayi shiru kar kuma ka gayawa kowa su eelham na asibiti, kuma ko waye ya kira ka kace komi na lafiya kar ka sake ka....." Maganar Abbie makalewa yayi ganin mommy da yayi a asibiti bayan yasan shi bai gayawa kowa ba kuma wannan ba hospital da suka buɗe file bane sannan bai ba su Anty billy daman fada ma kowa ba. sanɗa ta rinƙa yi tana yi tana kallon bayan ta alamun akwai abinda take kullawa ko kuma bata son wani ya ganta ga sai kakkare fuska take, da mamaki Abbie ya rinƙa kallon ta daman shi tun ba yanzun nan ba yake mata kallon zargi da Rashin Gaskiya a tare da ita, ai mancewa yayi yana waya yabi hanyar da tabi dan shi kam abin ya bashi mamaki ta ya ya akai mommy ta sani? Ƙara sauri yayi ganin zata ɓace masa saidai duk saurin da yake a banza dan ta ɓace masa bat, haƙura yayi ya kamo hanya zai koma bakin kofan dakin da aka kwantar da mufeeda dai dai wani lungu yaji murya ƙasa ƙasa, da kamar ba zai tsaya ba sai yaji kamar ana tsaida shi dan haka dole ya tsaya ya samu waje ya laɓe yana sauraran abinda suke faɗa....