78&79
{🌹 EELHAM🌹}
Rabe'arh wakili
78 & 79
بسم الله الر رØÙ…Ù† الر ØÙ‰Ù…
A sannu a hankali eelham ta fara buɗe idanun ta wanda taji su duk sunyi mata nauyi sosai,cikin ikon Allah ta buɗe su duka sai kuma ta kuma kulle su dan haske yayi mata yawa a cikin idanun nata, sai da ta ƙara daukan wasu mints sannan ta ƙara buɗe su duka tana zubawa pop da ke a dakin ido kamar wacce take kokarin ta gane da mi akayi su, grandma ce ta fito daga toilet, ƙarasawa wajen bed ɗin eelham tayi dan sam bata lura da cewa ta farka ba Saida tazo gab da gab da ita sannan buɗe baki tayi tace "Allahu Akbar, namecy?" Tayi kiran cikin surprise and happiness, da kyar eelham ta iya juyo da wuyar ta zuwa ga bangaren da taji muryan grandma, da dan sarsarfa grandma ta karasa gareta tana zuwa ta dinga taba fuskarta kamar wacce take son ta tantance ita din ce ko kuwa?,cikin bata fuska eelham tace "a'a ni karki ya mutsa min fuska" tayi maganar da kyar kamar wacce a ka tilasta ga kuma bai fita da kyau dan ba ƙaramin jin jiki tayi ba, grandma kuwa cikin bata fuska at same time kuma tana share hawayen fuskarta na farinciki tace "ja'ira kawai! Kin ji sauƙi kenan rashin kunya ya tashi" bata kula da maganar ba sai cewa da tayi zatayi wanka, tashi Grandma tayi ta shiga toilet ta haɗa mata ruwan wanka sannan ta fito, taimaka mata tayi already an riga da an cire mata drip, ta shige toilet, tana shiga babu jimaw sai ga goggo da Aziza sun shigo ciki daman goggo ta raka Aziza motsa jiki ne da doctor yace a rinƙa fitar da ita, ganin da tayi babu eelham a gadon ne yasa suka ci birki har taune harshe take wajen furta "Hajiya Khadijah ina namecy din ki take?" Da murmushi dauke a fuskar grandma tace "Allah ya kawo sauki bayan fitar ku Allah ya bata ikon farkawa cikin koshin lafiya, yanzu jira ma nake ta fito idan ta shirya sai a kira doctor yazo ya duba jikin nata" nan fa goggo ta hau kabbara cikin farin ciki marar misaltuwa, Aziza itama tayi farin ciki da farkawar eelham sosai, su na a haka sai ga ta ta fito daure da sabon towel wanda ya kai mata har gwiwa, kallon goggo tayi ta tura baki gaba sannan ta ɗauke kai, mi zasu yi idan ba dariya ba hadi da faɗin "iyeee dan baba da abin sa ya tashi kenan?" Bata fahimci abinda suke faɗa ba yasa bata ɗauke shi komi ba, gefen gado ta zauna tana haɗe fuska kamar wacce akayiwa dole tace "kaya" Aziza ta miko mata kayan hade da cream,da ɗan guntun murmushi ta saka hannun ta karɓa sai da ta kammala saka kayan sannan suka hau yi mata ya jiki da tambayar mi ke damun ta kuma, Ansar ɗaya ce shine da sauƙi, Aziza da kanta ta kira office ɗin doctor babu jimawa yazo yayi dan gwaje-gwaje inda ya shaida musu da komi lafiya qlau, godiya sukai masa har zai fita eelham tayi karab tace "dan Allah dan Annabi doctor kayi discharge dina pls" ta ƙare maganar da marairaicewa ba musu kuwa ya rubuta musu sallama da tunanin ko cikin jikin ta baison warin hospital ne saidai ya basu bedrest for good 2weeks, su goggo suma sunji dadin sallamar, nan suka fara hada kaya suna kaiwa mota ganin hakan da driver da su Abba suka bari ne shima ya shiga ya rinƙa taimaka musu har suka gama amma Aziza da eelham ba su ɗaga komi ba, duk da motar bai yi musu ba haka dai sukai manage, koda suka kai gida part ɗin grandma suka wuce su duka wanda ita grandma taso a je part din goggo amma goggo tace sam su tafi can, har suka huta a cikin gidan babu wanda yasan da dawowar su,.... Ummi ce da Umma a parking lot da basket ɗin delicious zasu hospital amma sai driver yake gaya musu ai su grandma sunce a gaya musu an sallamo su, ba musu bare nuna ɓacin rai sai farin cikin da sukai haka suka kwasa sai part din grandma, zaune suke a falo dukan su su hudu, duk da babu wata shakuwa tsakanin eelham da Aziza haka dai suke dan tasu firan sama sama, bayan su umma sun gaida su goggo ne sannan suka hauyi musu ya masu jiki, da dau rawa da tambayar "ashe eelham ta farka" nan suka gaya musu komi, sukuma sukai musu fatan samun lafiya. da kyar ummi ta cire kunya tace "dan Allah goggo a taimaka a aramin su eelham" ba musu ba jayayya suka yaddar mata, sosai Ummi tayi farin ciki da haka duk da bata san dalilin da yasa suka Amince mata a lokaci guda ba,..sun dade a nan suna ta fira kafin kuma kowa ya waste sanadin kiran sallar da ake eelham da Aziza suka bi bayan ummi zuwa part dinta, umma kuma ta koma nata part ɗin da yi wa Ummi wasa wai tayi mata wayo ta kwashe yara di ka........ Baƙin dukan da waɗan nan mutanen suka rinƙa yi wa mamy yasa ta koɗe ta fita hayyacin ta,da yake fara ce sai jini da shaidar duka duk suka kwanta mata a jiki, cikin tsananin azaba da raɗaɗi da Kuma yunwa uwa uba kuma ƙishin ruwa su suka disasar mata da murya wanda ba lailai wanda yake kusa da ita ya iya jiyota ba bare kuma na nesa da ita haka dai ta rinƙa ambatan "Ruwa!Ruwa! Ruwa" sai dai kash ba bu wanda ya ji ta, har ta fidda tsammani taji an buga ƙofa da karfin gaske, saidai bata motsa daga in da take ba dan ta saba daman hakan suke bugo ƙofar kamar zasu karyata, ba tare da ta buɗe ido ba dan sunyi mata nauyi ta buɗe baki da kyar ta furta "Ruwa dan Allah" Allah da ta kira shi ya sakar mishi da jiki lokaci ɗaya sai yaji ya zubda makaman yaƙin shi, jiki a suɓule ya fita babu jima sai gashi nan ya dawo da ruwan gora masu sauƙin sanyi yana bata ta kafa baki ta kwankwaɗe shi tass dan ƙishi ba na wasa ba taji ta, kallon ta ya rinƙa yi cikin tausayawa a kuma lokaci daya yaji zai iya sadaukar da komi ko dan ya taimaki wannan matar idan kuma ya taimake ta shi kuma ya samu uwa daman rashin ta ya kawo shi wannan halin da yake a ciki, horn ɗin da yaji an danna ne shi ya katse masa tunanin sa nan da nan ya ɗauki bottle da tasha ruwa yayi watsi dashi cikin wani lungu murya na rawa yace "ki rinƙa ihu kamar ina dukan ki" gaɗa mishi kai kawai tayi, nan fa ya hau dukan shirgin kaya, ita kuwa mamy sai ihu take iya karfin ta wanda idan wani yaji zai ɗauka ko dukan gaske ake mata na fitar hayyaci, shigowan su falon kenan suka ci karo da kukan mamy wanda azaba ya boye muryan, ogan su kuwa nan ya fashe da wata dariya babu daɗin ji mabiyan shi su ma suka daura nasu non stop, Saida su gaji dan kansu sannan ogan cikin su ya fara dakatawa mabiyan nashi suma suka dinke tasu, "ku kira min yaron nan lailai ya iya riƙon amana" duk abinda suke tautaunawa ya kasa Kunni yana saurara jin za'a shigo yasa ya saita nustuwar shi saidai cikin Sa'a da nasara bai shigo ba sai knocking da aka yi masa, cikin buɗe ta sa muryan yace "waye?" "Oga yayi kira" ɗan sakon ya faɗi haka, shikuwa gane ma'anar shi yasa ya wurgar da abin dukan yasa kai ya bi bayan wannan ɗin. Yana fitowa oga da kanshi ya hau tafa mishi ganin ba wani babba bane dan bazai wuce irin 27 years ɗin nan ba, risunar da kai ƙasa yayi yana miƙa gaisuwa ga wannan mugun mutumin wanda tunda suke tare dashi bai taɓa ganin asalin fuskar tashi ba, tarban shi oga yayi sosai inda ya bashi ragamar punishing mamy har sai ta fidda abinda suke son ji daga bakin ta, bawan Allah cikin nuna fake happy ya rinƙa zubawa ogan shi kirari da godiya har dai ya sallame shi...... "Dan Allah Anne ki fada mana abinda yake damun ki, kwana biyu kullum doctor yazo yace blood dinki is still high, dan Allah Anne ki fada mana ba ki da wasu wanda zaki faɗawa damuwar ki bayan mu" sam bata jin abinda Anty maleka take faɗa dan gaba ɗaya tana nan ta faɗa a duniyar tunani ga hawaye sai sintiri suke a kan fuskar ta wanda ita sam bata san da fitowar shi ko wanzuwar shi ba, auta da batada dauriya nan ta kwanta jikin Anne ta fashewa da kukan halin da mahaifiyar su ta ke a ciki, ruwan hawaye da ke sauka a jikinta hakan shi ya taimaka ta dawo cikin duniyar mutane, tana mai binsu da ido kafin ta shafa kan autar ta alamar lallashi har dai tayi shiru, sosai tayi jarumtar danne damuwar ta gudun karta jefa yaran nata cikin wani hali hakan da ta nuna sosai kuwa ya taimaka dan duk sun saki jiki suna ta shan sha'anin su, sai dai ga Anty Maleeka ba haka bane ba dan duk wani motsin Anne akan idonta ne dan tasan boye wa kawai tayi dan kar su kuma tambaya amma ta sha alwashin zata bi da ita haka har ta gano damuwar ta, dan abinda zai saka Anne kuka ba karami bane shi yasa ya tsaya mata a rai........ Kwance mubeena ta ke saman bed shi kuma AS yayi busy operating system so yake ya gama aikin kafin ya kwanta gefe ɗaya kuma suna fira jifa jifa da mubee dan itama ji take da ta ta wayar, Saida ya kammala abinda yake sannan ya furta "zan je Nigeria zuwa next week" unexpected haka maganar sa ya zo mata hade da kuma faduwar kirji, ai bata san san da ta miƙe zaune daga kwancen da take ba murya har zuga take wajen furta "Nigeria kuma? Yin mene? Yaushe yaushe muka zo?" Da kallon eh lailai kam ya bita kafin ya dauke yana danne dariyar qetan da ke taso masa, jin bai amsa mata ba yasa ta fashe da kuka wanda ba na komi bane sai na kishin mijin ta, tana kuma tunanin ƙilan idan yaje ya kuma dawo da eelham, nan fa ta ƙara volume kamar wacce aka zagarwa iyaye ko kuma wacce aka nakaɗawa duka, sam bai son hayani ko ko ko kadan shi yasa ya taso daga inda yake ya isa inda take yana zuwa ya jawo ta jikin shi ya rinƙa lallashin ta amma kamar ƙara mata patro yake, ta ke dibara ta fado masa cikin kwantar da murya da sigar lallashi yace "pretty darling! Ki kwantar da hankalin ki ba komi zai maida Ni zuwa Nigeria ba kawai dai ina san naje na dawo da lovelies dina k......" Fisgewar da tayi da ƙarfi shi ne yai nasaran katse masa zancen sa, ita kuwa mubeena a mugun fusace da tafarfasan zuciya tace.......