80&81
{🌹 EELHAM🌹}
Rabe'arh wakili
80 & 81
بسم الله الر رØÙ…Ù† الر ØÙ‰Ù…
"Yanzun nan banda zalunci duk abinda nake yi maka baka gani, ba ka ko ji kunyan idanu na ba kake gaya min zaka dauƙo lovelies dinka? Lailai Ahmad". Tana kai wa nan ta fashe da kuka mai cin rai da zuciya, shi kuwa tun sanda tace masa azalumi ya rintse ido da karfi yana jin zuciyar shi na kuna dan ya tsani wannan kalmar ga kuma ta danganta shi da ita, cikin nutsuwar sa ya buɗe oily eyes ɗin sa da suka yi red dan ɓacin rai, tashi yayi ya fita daga ɗakin ko damuwa da halin da take a ciki baiyi ba, da niyan shi zuwa next week zai koma Nigeria amma tunda tazo da haka zai nuna mata shi yake gaba da ita, zuwa da safe zai fita yaje yayi ciku-cukun visa, bayani kuma bazai yi mata ba duk abinda take tunani haka ne, haka dai har ya gama abinda zai yi sanna ya kwanta yana jin zuciyar shi babu daɗi badan halin da ya bar mubeena ba a'a sai dan ce masa azalumi da tayi, yana a haka dai bacci yayi awon gaba dashi, alarm ɗin wayar sa shi ya tasar dashi alamun dai subhi tayi, toilet ya shiga yayi abinda zai yi sannan ya fito shimfiɗa sallaya yayi ya gabatar da sallar bayan ya idar ya daura da tilawa da lazumi wanda ya dauke shi tsawon lokaci ko sanda ya duba time yaga 7 yayi sai yayi addu'a ya miƙe, maida komi ma'adanar shi yayi sannan ya shiga toilet yayi wanka yana fitowa ya shirya cikin ƙananan kaya ba tare da ya kalli kofan mubee ba yasa kai ya bar gidan gaba ɗaya. Mubee taci kuka har ta gode wa Allah da kyar bacci ya ɗauke ta sabida tsananin kishi irin nata dan ita da taji yace lovelies tana tuna nin ko dai eelham yaba wannan suna, ko da ta tashi da safe idanun nan sunyi luhu-luhu dan kukan da tayi bana wasa bane ba daukar waya tayi tayi kiran zeena duk da tasan ba shiga zai yi ba, as usual wayar is switch off jefar ta wayar tayi bisa gado tana tunanin wa zata kira ta samu shawara ba za kuma ta iya kiran yayarta bah dan tasan wa'azi zatai mata daga karshe wata bacci ta fige ta wanda batayi niya ba,..... successfull AS ya samu Flight da zai tafi Nigeria zuwa jibi shi yasa yana komawa gida ya shirya kayan shi bayan ya gama ya fita cikin gari dan yayi wa yar rigiman shi tsaraba..... Ummi ce a ƙasa a ɗakin goggo "ikon Allah faɗi mana muna sauraren ki". Cewar grandma tana kallon ummi "ba ki ga yadda na tsaya ina kallon ta ba? Tana abu kamar ta ga surikan ta a wajen". Cewar goggo "uhm daman su EElham nake son ayi mun alfarma in tura su Abuja ita da Aziza da ruqqy". Ta ƙare maganar zuciyar ta na bugawa dan idan suka tambaye ta mi zasuje yi bata sani ba dan jiya Abbie ya kirata ya bukaci haka daga gareta, ganin da su grandma sukai bai kamata a hanata ba yasa sukace "shikenan yaushe ne tafiyar". Cikin farin ciki Ummi tace "ko zuwa gobe ko jibi" "sai su tafi a goben Allah ya tsare hanya". Tayi murna sosai ta kuma ta zuba musu Ruwan godiya da addu'a gamawa lafiya sannan ta baro part din dan tanason ta shirya musu kaya koda ta gama haɗa musu komi sai tayi kiran Ruqqy tace idan mijinta ya dawo ta kirata, "Ummi yana nan". "Ok toh bashi wayar". Miƙawa Umar waya tayi bayan sun gama gaisawa tace "son aron daughter zaka bani zasu danyi tafiya zuwa Abuja". Ba tare da jayayya ba ya amince da faɗin "ni ma tafiya zanyi kuma zan ɗauki lokaci a can".godiya da albarka Ummi ta rinƙa zuba masu har sukai sallama,wajen umma tayi ta gaya mata, itama ɗin bata nuna damuwar komi da haka ba sai fatan sauka lafiya da tayi musu,... Tun daga kofa Ummi ta jiyo dariyar Aziza tura ƙofan tayi ta shiga inda ta sa me su suna fira a tsakanin su dan yanzu kam eelham ta saki jiki da Aziza sosai sun zama kaman wasu kawaye, ganin ta da sukai ne yasa ta yi shiru saidai da sauran murmushi a face ɗin ta tayi wa ummi sannu d zuwa har suna haɗa baki da eelham, amsa musu tayi da kulawa, "daman zuwa nayi na sanar muku zamu je Abuja idan Allah ya kai mu" a kusan tare ƙirjin Aziza da eelham ya buga nan da nan mood ɗin su ya canza amma basu bari ta fuskanci halin da suke ciki ba ita kuwa ummi tana faɗin haka ta bar musu ɗakin ba tare da ta jira amsar su ba, su kuwa saƙe saƙe kawai suke barin ma Aziza da tafi eelham shiga tension, fakan idanun eelham tayi ta shige ɗaki wai zata toilet, tana shiga kuwa ta faɗa cikin toilet tayi dialing number ogan ta, yana dab da katsewa aka yi picking bata jira cewar ta ba Aziza tace "ance zamu taho Abuja nida eelham" daga dayar gefen aka amsa da "eh karki damu lokacin baiyanarta yayi daman ina da niyan yin haka" "amma......" "Karki damu Allah will protect you! idan Flight zaku bi zan sa escort su taho airport ɗin dan su luran min da motsin komi" doguwar ajiyar zuciya taja kafin ta amsa da "toh" tana sauke wayar jin daga can bangaren an yanke,,,,, washegari karfe 12pm Flight ɗin su ya daga zuwa Abuja koda suka sauka driver ya kwashe su zuwa gidan inna daman Abbie ne ya turo da driver ɗin, abinda su Ummi basu sani ba ana nan ana bin su a baya da wasu mota guda biyu amma da yake Aziza ta san da zaman su yasa ta lura da su eelham ma dai ta fahimci cewa ana bin bayan su amma bata ce komi ba ta dai zubawa mirror idanu, waɗan nan mutanen ba su suka bar binsu ba Saida suka kawo gate ɗin gidan su inna sannan suka juya suka koma, hakan kuwa sosai ya tsayawa eelham a rai, bayan gate man ya buɗe ne driver ya shiga yana yin parking duk suka fito duka su biyar da Ummi, Aziza, meenal,Ruqqy,sai eelham, part din inna suka wuce direct dan a gidan babu wanda yasan da zuwan su sai Abbie kawai daman kuma shi ya bukaci haka, mufeeda ce kwance a kan cushion dake a falon inna tana kallo dan jiya aka sallamota daga hospital shine Abbie ya bukaci da a dawo da ita nan wajen inna, ansawa tayi tana mikewa zaune a hankali ga cikin nan yayi girma tubarkallah, gaisuwar da takewa ummi katsewa yayi ganin eelham da tayi bata ko ji nauyin jikin ta ba ta karasa wajen eelham da sarsarfa tayi hugging ɗinta ruwan hawaye yana tarar mata a ido ganin haka da tayi ne cikin wasa tace "a'a dan Allah karki kayar da ni Mrs sadeeeq" goge dan hawayen da ya sauko mata tayi da murmushi mai ɗauke da farin ciki tace "ki dai ji tsoron Allah Ni bance zaki kayar da ni ba sai ke?" Bata amsa mata ta bi ta gefen ta ta wuce, "matar yaya ina wuni" tayi maganar a ɗadɗare dan tasan halin Aziza sai dai ta ba ma wani labarin ta amma for her surprise sai taji Aziza tayi hugging ɗinta tare da faɗin "maman twice oyoyo nayi kewar ku fa ina inna?" Ta ƙare Maganar tana raba mufee da jikin ta mufeeda kuwa cikin murmushi mamaki tace "tana ciki" "ooo ni ba'a Sanni ba ko?" Zuwa tayi gare ta tana cewa "ummi nayi mamakin ganin ku ne barin ma o'a" harara eelham ta zuba mata mi zu ummi zasuyi idan ba dariya ba dan yadda tayi hararan kamar idon zasu faɗo daman gasu tubarkallah, dariyar su shi ya fito da inna daga cikin ɗaki tana faɗin "ke kuwa kina lafi....." Ai maganar ta maƙalewa tayi ganin su eelham itama din da mamaki tace "iliyam kece kuwa? Kodai ɓatan hanya kikayi?" Sosai taji kewar wannan mata daukar ta take kamar goggo da grandma buɗe baki tayi a hankali tace "mai kama da ita ne" "ke kika sani Ni dai bazan biye miki ba dan baƙon ka annabin ka" gaisar da ita Ummi tayi sannan Aziza itama ta mika Ta'ta gaisuwar suna a haka sai ga Abbie ya shigo da sallama dauke a bakin shi,har kasa su eely suka miƙa gaisuwa ga Abbie inda ya amsa da kulawa sosai yana yi musu sannu da jiki Ummi ma ta gaisar da shi shima ya gaida inna,nan dai suka ɗan taɓa hira kafin su miƙe jin ana kiran sallah,...... Tun jiya bai ƙara saka mubee a ido ba dan bai cika zama a gida bah yana shirye shiryen tahowa gida dan gobe Flight ɗin su 6am zai daga zuwa Nigeria, shigowan shi kenan gidan dakin shi ya shiga bai ko kalli na mubee ba, haɗa sauran kayan shi yayi,bayan ya gama ya shiga wanka, yana fitowa ya gabatar da shafa'i da wuturi da addu'oi sannan ya bi lafiyar gado, kamar kullum alarm shi ya tasar da shi a gurguje ya shiga toilet yayi wanka yana fitowa bai je masallaci ba ya gabatar da Sallar shi a gida bayan ya idar ya haɗe cikin shigar shi ta ƙananan kaya sosai kuwa yayi kyau faffaɗan ƙirjin shi sai ya ƙara baiyana muscles dinsa ma sai suka ƙara fitowa dan sai hannu rigan ya kama shi, fitowa yayi daga dakin cikin sauri ya shiga dakin mubeena saidai ya iske tana nan tana bacci bai tada ta ba ya aje mata farar paper da ATM a kan mirror sannan ya fito daga dakin yana barin gidan gaba ɗaya dan ya kusa makara, koda ya isa airport ba jimawa Flight ɗin su ya daga zuwa Nigeria..