EELHAM🌹

83&84

by @rabearhwakili


{🌹 EELHAM🌹}
Rabe'arh wakili 
82 & 83
بسم الله الر رحمن الر حىم
Alhamdulillah AS sun sauka Nigeria a airport din Kano koda ya fito ya iske driver dinsa yana jiran sa dan ya kira shi ya faÉ—a masa time É—in da zai sauka shi yasa, gidan su goggo yace a wuce dashi koda suka isa gida part din shi ya wuce direct dan dare ta riga da tayi duk da farkon dare ne kuwa, part din na nan fes dan ummi ta kan sa masu aiki su gyara masa duk da baison masu aiki na shigar masa part, wanka yaje yayi ya shiga kitchen ya haÉ—a liptea ya fito falon, Saida ya kammala sannan ya maida cup É—in ma'adanar ta bayan ya dauraye, É—akin shi ya koma ya na kwanciya kuwa bacci yayi awon gaba dashi  daman ga gajiyan tafiya.... Gidan shiru baka jin motsin komi sai na kukan tsuntsaye, eelham ce jikin window tana kallon gate É—in gidan daga dakin inna dan har tayi bacci farkawa tayi, tana tsaye a nan taga gate man ya buÉ—e karamin kofan gate yana matsawa wanda ya shigo, a lokaci daya kirjin  eelham ya buga dumm dumm dimmm dimmm,dafe kirjin tayi tana karanto duk addu'ar da tazo bakin ta, jikin ta ya hau É“ari dan ganin abinda idanun ta sukai mata gani ji tayi kanta ya kulle zargin shi nan da nan ya mamaye mata zuciya da tsanar sa, haka ta kasance ga Aziza da take tsaye wajen window itama dan an sanar mata da abin harin su zai shigo cikin gidan yau,amma tunanin ta bai taÉ“a hasaso mata wanan fuskar bah,shikuwa wannan mutumin daidai wajen window dakin inna ya tsaya yana kara waya a Kunni sakamakon kiran da akayi masa daga É“angaren can, ba'a jira cewar ba aka ce "karka shiga da akwai matsala ka dawo yanzun nan". Kit aka katse kiran bai ko Æ™ara ko second É—aya a wajen ba ya kama hanya da niyan barin gidan a kusan tare Azizaa da eelham suka bi bayan sa, amma saidai Azizaa ta riga eelham fita shi yasa basu haÉ—u da juna ba haka suka rinÆ™a bin bayan sa sunayi suna laÉ“e cikin ikon Allah sam bai lura da ana binsa ba burin shi kawai ya koma can wajen yan kungiyar su ya ji mike faruwa dan wannan kiran na gaggawa da gani ba daidai ba, Saida sukai tafiyan wajen hour 1 and half sannan suka ga ya shiga wani lungu, yana shiga itama Aziza ta shiga wanda eelham ta É—auka ko tare suke duk da dai bata hango ko fuskar waye ba, Saida ta tabbatar sun shige sannan itama ta shiga tanayi ta na laÉ“ewa, abinda basu sani ba fadil da hashem da umar suna biye dasu a baya saidai suma É—in basu san ko su waye a nan É—in ba, wajen shiru sai kukayen tsuntsaye da kwaÉ—i da suke a ruwa dan wajen ya kasance kamar daji ne duba da manyan itacuwa dake a wajen da kuma grasses da sukai wa wajen kawanya, can nisa da kofan shigowa haske ne na fitilar aci balbal ake hangowa, can wannan mutumin ya nufa suma É—in haka suka rinÆ™a take masa baya cikin taimakon Ubangiji da rufun asirin sa, ai Æ™ame wa sukai bayan sun iso wajen Inda suka iske wata mata daure ta igiyoyi masu kauri ga jikin ta nan duk jini alamun dai ba karamin azaba aka gana mata ba, Saida wannan mutumin ya tsaya a post dinsa sannan cikin girmamawa yace "shugaba gani, naga kiran gaggawa ayayin da komi yake gab da kammaluwa" cikin É—acin rai da kunan zuciya yace"wannan matar ita da yaron aikin ka sukayi kiran wata akan tafiyar ka cimma aikin mu, ganin da yayi ba haske yasa yayi kiran ka"   wata tsana mafi tsanani yaji yana dirar sa akan wannan mata ba tare da tunanin komi ba ya Æ™arasa gareta ya ca kuma wuyan ta ya shaÆ™e shaÆ™a bana wasa ba da kyar sauran members suka kwace ta wajen wannan mutumin faÉ—i yake "kin san shekara nawa nayi ina farautan wannan yarinya ko kinsan abubuwan da na tsallake dan sabida wannan yarin yan? Ko kin san buri na akan haka?" Ai komawa yayi ya rinÆ™a kai mata duka kamar an aiko shi da yake zuciya na kusa yake mata wannan dukan yasa dakyar aka banbare shi daga gareta ita kuwa sai maida numfashi na wahala take Wanda a yanzu da kyar yake fita,,, a harzuÆ™e ya nuna ta da yatsa manuniya yace " kenan a kwanakin da muka harar wa cikin su uku kece kika É“ata mana aiki? Ke ce ko ba ke bace?" Ya kare maganar a tsawace yana kokarin rikiÉ—a ya koma wani babba kwaro, eelham da take video recording nan da nan komi ya fara dawo mata na mafarkin da take yawan yi da wannan halittar, jikin ta rawa ya kama yi numfashin ta har yana yi kamar zai É—auke hannu tasa ta danne bakin ta jin tana kokarin tona wa kanta asiri addu'oi ta fara jerowa cikin ikon Allah ta samu natsuwa, haka ta ke ga É“angare Azizaa kadan ya rage ta fasa ihu sai dai taji anyi sauri an rufe mata baki, hadi da faÉ—in "ki nutsu" cikin yin Æ™asa da murya, ba shiri da juyo da sauri ta kalle ta ba kowa bane face eelham, sauke ajiyar zuciya tayi da mamakin ganin ta anan amma bata ce komi ba duk suka maida hankali wajen abinda yake faruwa, cikin sauyin halittar nan ya isa gare ta yana buÉ—e katon bakin shi kamar kada, ganin haka da tayi ne yasa ta kama addu'a a sarari kowa naji, shi kuwa wannan mutumin da ya rikada duk da yana jin karfin addu'an a jikin shi haka bai sa ya daina nufo ta ba, cikin members dinsu kuwa babu wanda yayi gigin riÆ™o shi a wannan karan dan duk wanda yaje wajen yasan sauran Saida maman mutum ta haifi wani ba shi ba, ganin zata nakasa sa yasa ya hura wuta ya wurga mata, da yake Allah ba azzalumin bawan sa bane ba Allah ya taimake ta aka É—auke ta daga wajen nan da nan kuwa wajen ya kama da wuta balbalbal, daga saman jet aka wurgo da Roop mai karfi shi wannan ya kama ya hau da wannan matar a kafaÉ—an shi har suka shiga cikin jet É—in, shima wannan halittar tashi ya rinÆ™a yi sama yana kaÉ—a fifigen shi kadan ya rage ya cimmusu sai ya kasa ya fado Æ™asa sabida karfin addu'a da wannan mata ta rinÆ™a yi, cikin wani tsananin a zaba ya juyo, sauran members kuwa nan kowa yayi ta kansa dan sun san idan ya riÆ™e mutum a halin nan da yake tsaff zai farkawa mutum ciki, aziza taga abinda yafi karfin Æ™waÆ™walwar ta kuwa nan ta Æ™amÆ™ame eelham tana da ta sani bin shawaran da akace ta biyo shi, shikuwa wannan halittar jin da yayi zuciyar shi na kaishi ga wajen su eelham ne yasa ya tafi i zuwa wajen, Azizaa da eelham kuwa Æ™afa mi naci ban baka ba ganin yana kusanto gun da suke, nan suka kwasa a sittin, gwaff Azizaa tayi karo da mutum wata razananniyar kara ta saki tana sumewa, cak hydar ya É—auke ta aka wurgo da Roop ya dare zuwa cikin jet dan ganin wannan halittar ta kusanto su, eelham ma dai haka ta rinÆ™a gudu har ta fita daga cikin wannan wajen gudu take har ta iso titi wani ta hango rakube wajen wani icce da alamun shi ma dai taimako yake biÉ—a yana ganin ta kuwa shima ya hau binta a baya suka rinÆ™a gudu Saida sukayi nisa da wajen sosai sannan suka samu waje suka fake suna maida numfashi,.... Cikin dajin kuwa masu jet É—in nan kuwa sai É—auki É—aÉ—-É—ai suka rinÆ™a yi wa mugayen nan har Allah ya basu ikon kwasan su duka harda ogan su, wanda kwata kwata dibara ta kwace masa, haka dai yana ji yana gani ya mika wuya aka tafi dashi Saidai sun kasa da wannan mutumin haka dai aka barshi da saka ran shima zuwa gobe insha Allah zai shiga hannu haka dai suka bar cikin dajin nan cikin nasara batare da ko kwarzanen ciwo a jikin su ba,,,... Su eely suna zaune a nan sai ga mota tana danna musu horn har sun mike zasu kwasa a guje taji ance "daughter" a zabure ta maida duban ta zuwa ga Anne da take hakimce a back sit dan daga cikin motar sun kunna haske ta yadda na waje zai gan na ciki, buÉ—e Æ™ofan Anne tayi ta fito da murmushi dauke a fuska tana zuwa tayi hugging din eelham haÉ—i da shafa kanta, breaking hug din tayi ganin fa ba lokacin haka bane janta tayi zuwa cikin mota a back sit shikuma wannan namijin ya shiga front sit duk da dai Anne bata san shi ba za ta taimaka mishi ne kawai, direct gidan ta dake anan Abuja aka wuce da su duk da babu haske sosai a garin haka bai hana su gano kyawun gida na Anne ba,wani giet ne yazo ya buÉ—e musu gate suka shiga ciki,bayan yayi parking suka fito suna nufin cikin gida, a falo suka yada zango eelham kuwa kwanciya tayi tana jin jikin ta da cikin ta na dan yi mata ciwo, Anne da kanta ta shiga kitchen ta kawo musu ruwa masu saukin sanyi nan kuwa suka kwankwaÉ—e duka lafewa tayi a jikin Anne tana sauke ajiyar zuciya shima wannan guy É—in da basu san shi ba kwanciya yayi kan cushion yana maida tashi ajiyar zuciya dan yau sun ga abinda basu taÉ“a gani ba haka kuma sun tirÆ™a gudu, ganin da Anne tayi ne kaman suna son suyi bacci yasa ta katse su tace su bari idan sukai subhi sai su kwanta gaba É—aya dan lokaci ya kusa sauran yan mintina..