EELHAM🌹

85&86

by @rabearhwakili


{🌹 EELHAM🌹}
Rabe'arh wakili 
84 & 85
بسم الله الر رحمن الر حىم
Kamar yadda Anne tace kuwa basu suka kwanta ba sai  da sukai sallar asuba sannan suka kwanta suna kwanciya babu jimawa bacci yayi awon gaba dasu,... Tun a cikin jet É—in yaya Hydar yake ta zubawa Azizaa ruwa amma inna taÆ™i ta farfaÉ—o dan ba Æ™aramin tashin hankali ta shiga ba,zuwa wannan karan hankalin shi ya fara tashi da wannan É—auke wuta da Azizaa tayi ta wani bangaren yana tunanin mi ya kawota cikin wadannan mutanen, haka dai har jet É—in su ya sauka ma'aikatan su, inda aka hau kwasan wadan nan mutanen anayin ciki da su, shi kuma hydar daukan matan shi yayi ya kai ta clinic bayan sa kuma wadan da suka É—auko dayar matar ne wanda sam hydar bai tsaya ya duba ko wace ba dan dare kuma baiyi ta kanta ba, suna shiga cikin wajen nan da nan suka karÉ“e su inda suka basu taimakon gaggawa cikin ikon Allah nunfashi su ya dawo saidai Azizaa ta farka a firgice sai buge bige take Saida sukai mata allura ta bacci sannan aka samu salama, shima É—in sai sannan ya samu kwanciyar hankali, masallaci yaje yayi Sallah sannan ya dawo ya cigaba da tsareta bai kuma yi wani azancin ya kira yace suna tare ba danshi mancewa yayi sam.... Achan gidan inna kuwa tun asuba da inna ta tashi salla take ta faman jiran fitowar eelham amma shiru ganin haka ne yasa ta karasa masifar ta ita É—aya sannan ta shiga dayar É—akin tayi abinda zata yi ta dawo dakin ta, da mamakinta eelham bata fitoba cikin masifa tace "dan Allah idan kin ga dama karki fito, idan ta ni ne ma nayi abinda zanyi dan haka ki shekara baki fito bah, yo har ni za'a kawo wa salalan tsiya? Mtssssw". Ta Æ™are maganar da jan tsuka, shimfiÉ—a sallaya tayi sannan ta gabatar da sallar ta har ta idar da lazimi babu eelham babu dalilin ta, tashi tayi ta tura kofan toilet É—in Saidai shiru babu eelham babu dalilin ta, ba tare da tunanin komi ba tace "yanzu haka guduwa tayi tun cikin dare daman ni naga a terere na kwana kofa hanhai ita ta jiyo atoh" ta Æ™are maganar da taÉ“e baki,.Mufeeda ma ta tashi amma bata ga Azizaa a dakin ba tunanin ta ko tana wajen Ummi ne yasa itama É—in bata damu ba ta ci-gaba da harkan gabanta, Saida aka zo wajen break fast Ummi take tambayan ina su Azizaa? "Ummi ba tana wajen ki ba? Ita daman eelham a wajen inna ta kwana" Abbie da yake shigowa yayi cikibis da wannan zancen nan da nan yaji kirjin shi ya buga "a'a nikam babu wanda ya zo mun É—aki" cewar ummi nan kuwa mufee tace "tunda na tashi ban ganta ba na dai ga kofa a buÉ—e kuma ba'a rufe ba shi yasa nace tana wajen ki" "a'a bata nan dubo su a É—akin inna kila suna can suna ta fama da bacci" mikewa tayi ta shiga É—akin inna inda suka kusa cin karo da ita tana kokarin fitowa ita kuma mufee tana kutsa kai, janye wa mufee tayi tana ce mata "sannu" a masifance inna tace "nace da ya mutu sarakan nawa kika bashi iyee?, yanzu da ace na bige ki da wannan rusheshen cikin naki kinje kin fadi babu wanda zaki ce yayi Miki haka sai inna,toh aniyar ki ta biki, haka wancan o'a ta barni a hanhai ta wuce nata ke kuma kinzo kina kokarin daura taki a kai!, mi ma kika zo min a É—aki?" duk Maganar nan na inna mufeeda bata damu dashi ba dan idan inna ce sai ta faÉ—i mafi yin haka "eelham da aunty Azizaa Ummi tace inyi kiran su" "Nima ban gansu ba, ba ita iliyam tana wajen ta ba? Dan nikam babu inda ban duba ba amma bata nan bare kuma Azizaa" bata kuma ce mata komi ba suka fito zuwa falon mufeeda ta miÆ™a gaisuwa ga Abbie inda ya amsa da kulawa da tambayar ta jikin ta amsa masa tayi da sauÆ™i, gaida inna yayi amma gaba É—aya hankalin shi na ga kofa yaga fitowar eelham amma shiru kasa jurewa yayi ya tambayi mufeeda "ina eelham?" "Abbie wai inna tace tana wajen ummi wai bata a nan part din" "a'a inna babu wanda yazo min dan tunda muka rabu anan ban kuma saka su a ido ba" da kallon mamaki inna ta bita dashi kafin tace "mi kike nufi toh" shiru ummi tayi batace komi ba, carab mufeeda tace "laa ummi ko suna part din mommy?" "Ta iya yiwa bara ace ta turo su" daukan waya Ummi tayi ta danna kiran mommy É—auka tayi inda suka gaisa ummi ta bukaci da a turo su eelham budan bakin ta tace "eelham ai tun jiya rabo na da ita, meenal kawai take nan" cikin sauri ummi tace "Azizaa fah?"  "A'a itama bata nan" Kitt Ummi ta yanke wayar Abbie kuwa ya fara shiga tashin hankali ga momma bata nan tana hospital dan an kwantar da sister dinta ita ke zaune da ita karshe ma ita bata san da zuwan nasu ba, inna kuwa cikin sallallami tace "oooh Ni yar su Allah ka rufa min asiri ga matar dan uwanka itama ta bata har yau babu labarin ta, sanin kan ka ne kuma bamu gaya ma dan uwanka ba dan kar ya shiga wani hali a kasar mutane, yanzu kuma ace daga zuwan mutane su ma a nime su a rasa sai kace wasu kudade? Ya Allah ka tsare bayinka a duk inda suke" har haÉ—a baki suke wajen furta"Amin ya Rabb" ita kuwa inna sai sharan kwalla take abinci ya kasa ciwuwa a gareta, Abbie ma dai yana cikin tension sosai ganin zaman ba zai haifar masa da É—a mai  ido ba yasa ya miÆ™e ya bar wajen shima ko break baiyi ba dan ji yayi cikin shi ya cushe, bangare Ummi ai ba'a magana lumi lumi ta aro yara yanzu kuma sai ta koma tace musu sun É“ata kaii inaaa ai sai ga hawaye sharrr wani na koran wani, mufeeda ma ba'a barta a baya ba ita din ma tana cikin jimamin rashin ganin su, Abbie kuwa kafin ya bar gidan sai da ya tambayi gate man yace "ko yaga fitar su eelham ko kuma akwai wanda ya shigo?" Amma da yake mara mutumci ne cewa yayi "babu wanda ya shigo kuma babu wanda ya fita", cikin gamsuwa Abbie yayi masa godiya sannan ya bar gidan gaba É—aya da tunanin ta ina zai fara.... Tunda sassafe AS ya shiga part É—in goggo inda ya same ta zaune a palour da hisnul Muslim a hannun ta, ganin shi ne yasa ta saki faffaÉ—an murmushi ta hau yi mishi lale marhaban da zuwa "Ahmad ne a Æ™asar? Saukan yaushe?" Da dan murmushi a face É—in shi yace "Jiya da dare,ina kwana fatan na same ku lafiya?" "Alhamdulillah ya gajiyar hanya?" "Gajiya tabi jiki goggo" "Masha Allah, ya iyalai?" Ai ji yayi kunya ta rufe shi ganin kamar gatse tayi masa a haka dai ya amsa da "tana lafiya ai achan ma na barta" "oo to to to Allah ya taimaka" da Amin ya amsa yana jiran fitowar eelham kokuma goggo tace masa ya shiga tana ciki amma sai yaji shiru ganin dai bazata yi masa magana bane yasa ya tashi ya bar mata part É—in ta gaba É—aya, ita kuwa goggo da ido ta raka sa tana faÉ—in "yaro man kaza, mu zuba mu gani ai baka Æ™ara saka eelham a ido sai randa kasan darajan ta" shi kuwa part É—in grandma ya nufa saidai ita tana a bedroom room anan ya same ta, da yake ita yar kwartukwar ce cewa tayi "daga ina haka? Kodai kayi É“atan hanya ne?" Da so yayi ya rama amma tuna yazo ganin eelham ne kamata yayi ya bita a sannu cikin kwantar da murya yace "ina kwana antashi lafiya?" "Lfy qlau Alhamdulillah " daga nan bata Kuma cewa komi ba, shima shiru yayi "grandma su Anwar da Anam fah?"  Itama din cikin rashin damuwa tace "suna gidan yayarka Hanan" "taya za'a yi a rinÆ™a zaga gari da yara na, inda an san baza'a riÆ™e mun su ba ai da sai ta fito ta gaya min" "daman wa ka bar ma rainon yara" ba kunya yace "Khadijah mana" "tayi maka kama da mai rainon yara ne?" Shiru yayi bai ce komi ba ganin haka ne yasa grandma tace "ita din ba mai  raino bace ba, ita ma É—in yace kamar kowa shi yasa na saka aka wuce dasu wajen Ruqayyah ita kuma da tafiya ya kamata na sa ta tura su gidan antyn su dan namecy Wallahi tafi Æ™arfin rainon Æ´aÆ´an ka" tana kaiwa nan ta bar mishi É—akin dan wannan karan da gaske take sai ya gayawa aya zaÆ™in ta, taÉ“e baki yayi shima ya baro dakin ya shiga na Umma inda ta tarbe shi ba yabo ba fallasa amma ita din aiyana wa kawai take a rai zasu kwatar wa eely yancin ta,  tashi yayi ya bar mata part din ya shiga na ummi inda ya samu bappi yana karanta daily trust gaisar dashi yayi cikin girmamawa inda bappi ya amsa masa a daÆ™ile shima É—in AS bai kuma cewa komi ba sai can yace "bappi ummi tana ciki ne?" "Tayi tafiya" "ina taje bappi?" "Baka da contact din ta?" Hakuri ya bashi sannan ya baro part din ya koma tashi da tunanin ko mi yayi wa mutanen gidan da suka wani juya masa baya?..