EELHAM🌹

86&87

by @rabearhwakili


{🌹 EELHAM🌹}
Rabe'arh wakili 
86& 87
بسم الله الر رحمن الر حىم
Saida ya koma bacci ya tashi sannan yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya sannan ya fito ya shiga kitchen ya haÉ—a tea mai kauri, nan da nan ya shanye ya wanke cup É—in ya maida shi ma'adar shi sannan ya fito ya shiga mota ya bar gidan gaba É—aya bayan gate man ya buÉ—e masa gate, gidan anty hanan ya nufa daman gate man É—in gidan ya san shi yasa ya buÉ—e masa shi kuma ya kutsa da hancin motar sa cikin gidan, yana yin parking ya fito ya shiga entrance É—in shiga falon door bell ya danna babu jimawa aunty Hanan tazo ta buÉ—e ganin shi ne yasa ta fadada murmushi ta "a'a brother yaushe a gari? In ji maÆ™i baÆ™o" shima É—in da dan murmushi yace "jiya da dare" ya bata amsa yana kaiwa zaune akan É—aya daga cikin kujerun falon, aunty Hanan bata zauna ba ta shiga kitchen ta haÉ—o masa break fast mai lafiya ta dire masa a gaban sa, godiya yayi mata haÉ—i da faÉ—in "Anty kamar kin san ina jin ta" "ai nasan kanin nawa baya wasa da cikin sa yasa" dan guntun dariya ya saki sannan ya fara loda wa cikin sa abinci dan AS bai wasa da cikin sa, Saida ya kammala sannan ta shiga É—aki ta fito da Anam da Anwar suna ganin baban su kuwa suka kwaso a guje sukayi hugging disa, nan shima ya tarbe su yana masu kiss dan sosai yayi kewar su, Anwar Sarkin magana cewa yayi "papa umm fah?" "Umm tana gida kunyi kewarta ne?" ÆŠaga kai sukai masa dan da gaske su na cikin kewan eelham wanda basuyi ta mahaifiyar su haka ba, kallon Anty Hanan yayi yace "Anty Bara muje" har zaka gudu brother?" "Ina da aikin da zanyi ne! Yauwa wani gari Ummi taje?" "Ai yau ma zata dawo insha Allah" kallon ta kawai yayi bai kuma cewa komi ba tunda jin abinda take gaya masa saÉ“anin tambayar sa, "ya mubeena fatan tana lafiya?" "Tana gaishe ku, a can na baro ta ma" "ooh Allah sarki" tashi yayi ya kama hannun yàran shi suka miÆ™e suna fita daga falon har wajen mota aunty Hanan tayi masa rakiya su kuma suka bar gidan .... Alhamdulillah Azizaa ta farka cikin koshin lafiya inda ta bukaci da a sallame ta ta gaji da zaman asibiti, ba musu kuwa yaya hydar yaje ya karÉ“o mata sallama amma kafin su wuce Saida suka shiga É—akin matar da suka É—auko daga wajen mutanen can, kwance take ta juyawa kofa baya hakan yasa basu ga ko wace ba sai da suka karasa kusa da ita sannan, ai ja da baya Hydar yayi bakin shi na rawa yace "mamy?" Cikin mamaki, da hanzari ta buÉ—e idanun ta jin kamar Muryan yaya hydar aikuwa shine nan ta saki murmushi mai faÉ—i na farin ciki ganin Allah ya Æ™etarar da ita daga hannun wannan mutumin "hydar? Azizaa" a kusan tare suka amsa mata Azizaa kuwa saboda tausayin ta sai da ta share kwalla dan mamy ta kasance ma'aboyciya son kwalli ce amma jibe ta yau yadda ta koma, duk ta fita a hayyacin ta ta koÉ—e ta rame ga jiki duk shedar duka muryan Aziza na rawa tace "mamy waye yayi miki haka? Wani azalumi ne wanda babu tsoron Allah a ranshi? Mi kika yi masa har yayi miki haka mamy?" Wata murmushi mai É—aci da ciwo mamy ta saki wanda kai da ka ganshi kasan babu komi a cikin shi sai bakin ciki da dana sani amma sai bata tanka mata ba "Aziza ba lokacin tambaya ba ce yanzu, idan muka koma gida ta huta sai ayi, bara naje na karÉ“o mata sallama sai mu tafi gida gaba É—aya" haka kuwa akayi yana karÉ“owa suka wuce office akayi mata wasu yan tambayoyi sannan suka fito suna barin ma'aikatar gaba É—aya zuwa gidan inna da hankalin su yake a tashe, suna shiga ciki sai ga wata motar kuma a bayan su itama ta shigo a kusan tare sukai parking suna fitowa daga cikin motar ba kowa bace face Anne da eelham sai wannan guy É—in, ai Anne na ganin fitowar mamy ta Æ™arasa gare tayi hugging É—inta kafin tayi breaking hug din tace "ina kika shiga haka mamyn su? Mi ya sami jikin ki haka?" Answer É—in mamy dariya ce kawai gareta ganin haka ne sai Anne tayi shiru bata kuma cewa komi ba, dan ta lura tana a cikin wani hali, mamy kuwa da kyar ta buÉ—i baki tace "Abdul?" Shima da kallon ta yake yace "na'am umma na" yana Æ™arasawa zuwa gare ta, eelham ma dai da take a daskare ganin halin da baiwar Allah take ciki mamy tayi kiran ta haÉ—i da buÉ—a mata hannu alamun ta iso gareta ba musu kuwa ta je tayi hugging É—inta kam kam kamar za'a kwace mata ita,a wannan lokacin kuwa kasa jurewa mamy tayi Saida ta zubda kwalla masu zafi da kuna masu kuma cin rai, sai da Anne tayi magana sannan fa suka saki juna dan ko wanne su sunyi kewar juna kwarai da gaske, haka dai suka ranÆ™aya zuwa cikin gidan koda suka isa sun iske duka family members É—in duk suna nan cikin tashin hankali tun daga kansu yaya sadeeeq ya Adam ya khaleel ya muzammil da sauran mazan cikin matan ma duk su anty billy sun zo aunty narnarh, anty sadiya da sauran matan harda wayenda suke nesa da gari inna tasa duk anyi kiran su da yake fligh suka bi yasa tafiyar tayi musu sauri su Sarah masu ciki suna nan zaune waje É—aya abin duniya ya taru yayi musu yawa, shima Abbie da ya fita ya dawo ganin har 4 tayi babu labarin su, suna a haka  sukaji sallama daga kofa a kusan tare duk suka maida duban su ga kofan dan jin kaman sanannun murya, zumbur duk suka miÆ™e inna kuwa tafa hannu ta yau yi tana sallallami kafin ta zube anan Æ™asan tana yin sujudu shukur ta daÉ—e a haka kafin ta mike bakin ta É—auke da hamdala,karasawa sukai cikin falon suna miÆ™a gaisuwar su ga inna, inna ta amsa fuska da sakewa da kuma farin ciki lulluÉ“e a cikin ta daga nan ta fidda wayar ta tace "ke meenal lalubo min lambar Hajiya hauwa, idan kuma bata shiga ba ki lalubo ta Hajiya Khadijah" ba musu kuwa tayi dialing number goggo ringing biyu tayi picking karba inna tayi tana karawa a Kunni bayan sun gaisa inna take shaida mata "ai ga Anne ta baiyana, ita da takwarata da suka É“ace a jiya da dare ita da Aziza da kuma mamyn su", ai ba wata zance tace ga sunan zuwa, da yake suna tare da grandma yasa suka shirya tafiya a yanzu nan take sukai kiran su bappi da Abba suna zuwa kuwa suka shaida musu da "su shirya zasu tafi Abuja a kuma siyar wa kowa tashi ticket din harda mai baÆ™in halin can ba dan halin shi ba" ba musu kuwa akayi haka cikin nasara sun samu Flight É—in da zai tashi amma sai 5 nan da 1 hour kenan nan suka hau shirya kayan su, umma da Anty Hanan ma duk an faÉ—a musu zasu Abuja da yake mijin aunty Hanan bai da matsala yasa ya yarda jin kuma wai ashe eely sun É“ata amma an gansu toh shima dai yayi niyan zuwa to saidai akwai wani aiki ta gaggawa da ya taso masa, lokaci yana kusa suka kwasa suka wuce airport harda su Anwar,inda Anty Hanan ta bar yaranta wajen kakan su, da yake a can gida an san da zuwan su yasa aka turo da mota uku, duk da shi AS bai san mi ya kawo su garin ba dan yana zaune Abba yake gaya masa ya shirya tafiya ta gaggawa ta kama su, a dai-dai gate É—in gidan sukai horn gate man ya buÉ—e nan motar suka samu damar shiga ciki, anayin parking suka fito suna nufan sashen inna, sai da aka basu izinin shiga sannan suka shiga, Abbu da Abbie ne sai kuma inna sai mamy, ummi da mommy wanda shi Abbie sam bai yarda da ita ba, bayan sun shigo ne suka gaisa sosai Ummi da mommy kuwa suka tashi suka kawo musu abu mai sanyi suna Æ™ara musu sannu da zuwa, Anty Hanan kam bata zauna ba tayi kiran wayar aunty billy, gaya mata inda take tayi ta kwasa tayi can, AS kuwa sai wani cin magani yake da yaga kaman suna kokarin kara masa ciwon kai ne barin ma su goggo yasa ya bar part din ya tafi garden hannun shi riÆ™e da na Anwar dayar kuma Anam wanda su mommy sunyi sunyi su zauna amma fir sunÆ™i, yana zama yaya hydar ya karaso wajen, musabaha sukai duk da AS sai wani É—auke kai yake yana wani shan kanshi shi kuwa hydar dariya ma ya bashi amma sai bai yi ba ya maida hankali ga su Anwar kafin ya É—aga waya ya kira aziza yace ta zo garden ta É—auki su Anwar, suna a haka sai ga meenal ita tazo dan Aziza tace tana jin jiri, da mamaki AS ya ke duban kanwar shi amma miskilanci ya hana sa tambayar ta, ita dai gaishe su tayi tana rike hannun su Anam suka bar nan É—in, shi kuwa yaya hydar haka dai yake ta dan sako ma sa fira duk da dai ba wai fira ta dame shi bane dan  baida yawan hayaniya, haka dai AS  ya biye mishi, daman kuma can ba wani inuwa É—aya suke sha ba, a can cikin dakin inna su mufee ne suka kafa da'irar fira ciki kuwa harda yayin su,, "wai yanzu yaran nan marasa ji su suka kusa zama iyaye iyeee akwai shagali fah" cewar aunty narnarh nan aka hau dariya aunty sadiya tace "dey play ai mun kusa baki ga haihuwa yau ko gobe ba" anan fa su yusrah aka hau rufe fuska wai kunya, ita kam eely tana gefe tayi shiru tana jin bakin cikin sanin wannan mutumin da tayi tana jin da ta sanin sanin wannan mutumin da tayi, tana jin tsana mafi girma akan shi, daga karshe ma daukan su Anwar tayi suka bar dakin zuwa dayar dan ji take kanta na juya mata, cikin su babu wanda ya lura da fitar ta daman da suke fira bata saka musu baki ba itama Aziza bata saka ba dan sunga abinda idanun su bai taba zato ko tsammani ba,su kuwa haka suka cigaba da tsokalan kannen su har suka gangaro kan su Ruqqy da meenal "amare na wata nawa nawa ne mu fara bucking kar a riga mu" cewar Anty inteesar "a'a ba ruwan mu mukam" har su mufeeda zasuyi masu caaa sai ga kiran sallar magrib duk taron watsewa yayi cikin farin ciki...