88&89
{🌹 EELHAM🌹}
Rabe'arh wakili
88 & 89
بسم الله الر رØÙ…Ù† الر ØÙ‰Ù…
Ba su suka samu suka zauna ba sai da akayi isha'i nan kowa ya fito, amma Ummi ta hana eelham fitowa wai sai inhar ita tace tazo,ta dai aika mata da nata dinner da nasu Anwar, hakan kuwa sosai yayi ma ta daɗi duk da ita bata san da AS aka zo ba, kawai dai bata son kowa ya fuskanci halin da take ciki, a can falo kuwa bayan sun kammala dinner ne suka daura da bude taro da addu'a inda inna da kanta ta shaida masu grandma ɓacewar su Aziza "wayan gari mukayi muka iske babu aziza babu iliyam, babu inda bamu duba su, shima Abbie din su da Abbu dinsu sun fita niman su amma shiru, sai kuma yau muka ga sun dawo su da Mutanen da muke ta nema ruwa a jallo, saidai abinda ya hana mu sanar da ku gudun kar mu tada muku da hankali da kuma rashin fuskan da zamu dube ku da wannan maganar" "asha abu baiyi daɗi ba, ai Hajiya Khadijah ba'a haka ai an riga da an zama ɗaya Allah dai ya ƙara kiyayewa" cewar grandma da Amin duk suka amsa inda goggo tace "Toh tunda shima dan nawa bai san da ɓacewar matar ba ai ya kamata a shaida masa baiyanar ta ko kuwa?" "Eh kam haka za'a yi! Kai Abbie din su kira dan uwan ka idan da hali ma ya dawo kasan ko zuwa gobe ne" ba musu kuwa Abbie ya danna ma number Abba kira ɗauka yayi bayan sun gaisa amma muryan Abbie wani iri kaman wanda yake acikin tashin hankali shiru yayi ya kasa cewa komi sai can Anne ta karɓi wayar daga hannun Abbie tace ma Abba "yanzun nan aka aiko mana da gawar matarka daman kuma an dade ba'a ganta ba sai yau ake aiko mana da gawanta gatanan ba'a kai ta ba ana jiran isowar ka" ta ƙare maganar da shesheƙar kuka kamar gaske, shi kuwa da yake basirar tashi ta toshe kuma bai gane ko Muryar wace ba duk zatan shi ko momma ce, cewa yayi "gani nan zuwa yanzun nan, ai da kun kaita ko kuma kunyi kirana tun dazu da aka kawo ta" ya ƙare maganar cikin farin ciki, nan zuciyoyin mutanen falon ya buga a lokaci ɗaya ciki kuwa harda na momma miƙe wa tayi tace "ina zuwan ku" da sauri Anne ta miƙe tace "kina zuwa kije ina? Ai idan Kinga kin bar nan maciyin amanar dan uwan shi ne yazo nan!dan haka maza ki koma ki zauna daga inda kika tashi" eelham ce ta fito har ta ɗan haɗawa da gudu tana fita wajen gate tana zuwa ta warce wayar hannun mai gadin inda ta duba taga da ogan sa yake son yayi waya dan daga window ta hango shi shine tayi sauri fitowa kar ya ɓata musu shiri,katse call ɗin tayi fuska babu wasa tace "yanzun nan ka kuma kiran sa kace masa matar sa ta mutu an kawo ta" yana kokarin ya yi mata musu ne yaji an zuba masa mari wanda ba kowa yayi masa haka ba sai Umar gefen shi Hashim da fadeel da sauran ma'aikatan su, ai nan da nan mutumin ya ruɗe daka masa tsawa sukai da ya nutsu yayi kiran ogan nasa, ai nan da nan ya nutsu tsaff kuwa wanda bai san daga ina nutsuwar ta zo masa ba ko dan ya gansu da bindigu ne? Daga kofan falon inna kuwa duk mutanen cikin sun fito sakamakon fitowar eely a guje wanda hakan yasa momma ta samu hanyar tsarewa saidai rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ta mai kaya yanzu ɗin ma mommy ce tayi ram da ita tana banka mata wata muguwar harara, mai gadi kuwa ƙara kiran ogan shi yayi cikin Sa'a wannan karan ya ɗauka "fatan komi dai lafiya da irin wannan kira haka ba ƙauƙautawa?" "Toh yallabai lafiya ba lau ba mai ɗakin ka da suke tunanin ta ɓace To yau de gata an samo ta a mace ga can cikin gida sai ihu da koke koke suke" wata ƙatuwar dariya ya saki "na gode na lado gani nan zuwa gidan yanzu, naji ma wannan katon banzan wai shi yaya na naji kaman kuka shima yake Koh?" Makut ya haɗiye kaukauran yawun da ya tsaya masa a maƙoshi kafin yace "eh yallabai ai duk kuka suke, sai an jima kar wani cikin su ya fito" "eh kuma haka fa sai nazo nan da mintina goma" nan sukai sallama yana ji kamar yace masa kar yazo amma is too late for that, Abbie kuwa da dama ya karaso wajen yana jin komi daman a hand free aka saka yasa yaji komi inda maganar ya girgiza shi ya girgiza jin shi da ganin shi ya girgiza tunanin shi amma da yake Abbie akwai shi da dakiya sai hakan bai nuna a fuska ba yana ta karanto addu'a dai, cikin girmamawa Umar yace wa su Abbie da su shiga ciki ba musu kuwa suka shiga ciki,sauran ma'aikatan su Umar kuma suka shiga dakin mai gadi suka ɓoye sai dai anbar fadeel da mai gadi, suna anan sukaji knocking din kofa nan take kuwa fadeel ya Saita gun dinsa a gefen cikin mai gadi,shikuwa sanin mi yake nufi da haka sai ya natsu suka isa wajen gate ɗin yana gaf da buɗewa fadeel yayi maza ya ɓoye, ta yadda babu yadda za'ayi wanda zai shigo ya gansa, Abba kuwa cikin badda kamarsa sukai musabaha da gate man yana nufan ciki, ganin shigar shi ne yasa suka bar mai gadi da sauran ma'aikatan su suka bi bayansa, Abba yana shiga kuwa idon shi bai sauka akan kowa ba sai a na mamy da ta zuba wa kofa ido ga kuma kowa ya zubo masa ido ana yi masa kallon tuhuma, ai habawa bai tsaya jiran komi ba ya juya zai fece sai ji yayi gwaff yayi karo da mutum, nan kuwa sukai ram da shi, yana ganin haka kuwa ya sakarwa hasheem wata bahaguwar mari, ba shiri ya sake sa daman shine karfin rikon, nan kuwa ya samu hanya gudu saidai yana daf da gate yaci karo da hydar da AS wanda dowowar su kenan, ba wata wata tunda akan aikin sa yake hydar ya cafke sa ganin alamun da Umar yayi masa "zaka sake Ni Ko sai uwarka ta haifi wani ba kai ba?" Oho bai kula ba ya ja sa har zuwa falo inda AS ya bisu da ido, suna zuwa kuwa Umar ya riƙe shi, mamy kuwa sai hawayen take ta sharewa eelham kam kallon mafi tsana ta rinƙa jefawa Abba, Abbie kuwa kallon sa kawai yake yana kin yadda da abin da idanun sa da kuma abinda kunnen sa suka jiyar masa, Abbu da inna shiru sukai suna kallo wani sabon al'amari da ya girmi sanin su,,, da wata fusatacciyar kallo Abba ya dube su Umar yace "baza ku sake ni bane? Ko sai jikin ku ya gaya muku?" Ba kunya ba komi hashem ya ɗaga handcuff yace "u're under arrest" yana gama faɗin haka ya Kamo hannun shi sai saka masa, amma inna ta iso wajen tace "kamar ya anda ares? Mi yayi muku sabida Allah mutum daga zuwan shi zaku biyo shi har gida kuce zaku tafi dashi? Haba kuna rinƙa tsoron Allah mana" duk cikin su babu wanda ya damu har sun fara kici kicin daura masa handcuff ɗin Abbu ya mike da sauri ya isa ga dan uwan sa ya riƙe sa kam dan kar a tafi dashi Saide mene Yana riƙe sa Abba ya hankaɗa sa da iya karfin da Allah ya bashi, AS yana ganin haka yayi sauri ya tare bayan Abbu yana fadowa sai ya faɗi a jikin AS wanda kowa ya sadakar shikenan Abbu sai kariya,ganin abun yazo da sauƙi ne yasa suka rinƙa sake hamdala, duk Abba bai damu da halin da suke a ciki ba ya juyo a fusace yace "koda bakin wasa wani cikin ku ya ƙara tabani tabbas sai ya raina kansa, ba ina gargaɗin ku baku ji ba ko?" Itama mamy cikin ta ta fusatar da tsana tace "ai da baka barshi a haka ba mara mutumci mara tsoron Allah, wlh ka kiyaye, duniya ce kuma batada tabbas ka tuba ka komawa Allah kar ka bari ka mutu kana aikata wannan aikin, ga ka kuma da nauyin da ka daukar wa kan ka ta cin amanar dan uwan ka da kake yi a bayan idon sa, ko a haka a ka Barka rayuwar ka tana cikin hatsari, kafin kuma a tafi da kai ka bani takarda ta dan bazan iya zama da mutum fasiƙi kamar ka ba, macuci, fasiƙi kawai nayi da na sanin sanin ka a rayuwa, nayi da na sanin haɗa jini da kai, ai da lokacin da ka ɗauke Ni daga gidan nan ai da baka bar ni a raye ba,Allah ya isa tsakanina da kai" "ban san shashancin banza mi kike faɗa haka?" Cewar Abba, "Aziza" Anne tayi kiranta dan ganin Abba yana son ya raina masu hankali su kuma so suke ayi komi a gama a daren nan, amsawa Aziza tayi da "na'am" "bani record ɗin nan", ba musu kuwa Aziza ta miƙo mata mcard din da take saving din duk abinda Abba yake, Anne kam ba jira ta yi connecting da Bluetooth nan akaji muryan Abba yana cewa..