EELHAM🌹

90&91

by @rabearhwakili

{🌹 EELHAM🌹}
Rabe'arh wakili 
90 & 91
بسم الله الر رحمن الر حىم
A dai dai lokacin da Abba zai fara magana ta wannan record É—in momma tayi sauri ta miÆ™e kamar wata wacce ta zare, har zata Æ™wace Bluetooth É—in Anne ta riÆ™e Æ™am haÉ—i da banka mata wata Æ™asÆ™antacciyar kallo wanda hakan yasa babu shiri nan ta ke momma ta muzanta, saÉ—ab saÉ—ab tasa kai zata bar Æ™ofan amma su Umar sun yi cirko cirko sun yi kane kane sun tare ko ina, cikin fusata da Abbie bai san daga inda yake zuwar masa ba kuma haka kawai yaji yana jin haushin ta sosai cikin muguwar tsawar da tunda take dashi bai taÉ“a yi mata ba, lokaci É—aya tsawar tashi ya girgiza tunanin ta, ai bata san sanda ta koma wajen da ta tashi dazun ba ta maÆ™ure waje É—aya, Anne kuwa ba ta Æ™ara jiran komi ba tayi playing nan fa aka ji muryan Abba yana cewa "haba sarauta ta wai har so nawa zan gaya miki ki kwantar da hankalin ki kin kusa zama mallakina? Kina yi kamar baki yadda da wannan future husband to be É—in ki ba ko? To karki wani saka damuwa a rai komi ya kusa kammaluwa kinji my mata?" Cikin kissa momma tace "haba har sai yaushe zan ta jin wannan zancen daga bakin ka amma ka kasa ai watar da komi kullum sai magana daya wajen shekara goma sha kenan!ai inda  wannan maganar haddace  yaci na haddace shi hakanan". "Ba Ni nace karki damu ba? kuma nace ki dai na barin wannan mutumin mijin nan naki yana taÉ“a ki any how dan gaskiya ina da kishi" "mtwws maganar banza inace kaima kana fita daga nan wajen matayen ka zaka je?, sannan ka wani kokarin kafa mun dokan da ni ban kafa maka ba? Toh gaskiya haram". bai ce komi ba akaji ya ja doguwar tsuka sai kuma Æ™aran kulle kofa da akaji gwaff, kamar daukewar ruwan sama haka falon yayi tsit babu abinda yake motsi sai Æ™aran ac da suke aiki, Anne kam bata tsaya bi ta kansu ba ta kunna na gaba nan É—in ma duk cin amanar dan uwan sa yake haka tai ta kunna wa duk dai akan yadda ya tsani abbie ne da kuma yadda  yake cin amanar sa, har dai recording É—in yazo Æ™arshe. a dai dai lokacin da Bluetooth yayi shiru a nan take inna ta zube a Æ™asa sumamma, nan fa hankali gaba É—aya yayi kanta, momma da dama tun farkon abin kuka take irin ta da ta sani da nadama kuka take irin ta kaico tana ina ma ace za'a yi canza hannun agogo baya, cikin kukan itama ta duÆ™ufa kan inna tana kuka tana girgizata tare da faÉ—in "dan Allah inna karki mutu ki barmu cikin wannan halin tabbas nayi da na sanin aikata haka" hankaÉ—ata grandma tayi ta dube ta da idanun ta sukai jawur murya babu wasa babu sausauci tace "in har ba so kike ki Æ™arÆ™are ta ba toh ki tashi ki bar nan kafin ranki yafi haka É“aci"gum tayi shiru ta matsa daga kan inna saidai bata bar falon ba. Yusrah, yaya khaleel, yaya  Adam, ba Æ™aramin girgiza sukai da wannan al'amarin ba,tunda yaya khaleel yasa kanshi akan kujera ko motsin kirki bai Æ™ara yi ba, yaya Adam ma dai shiru ne dan wani irin kunya yaji yana lulluÉ“e shi jin abinda mahaifin shi ya aikata da matar yayan shi dan haka kuka yake son yayi wanda ba iya gidan su ba gaba É—aya anguwar sai  anji sautin fitar ta amma taÆ™i tazo yaÆ™i ya bashi wannan haÉ—in kai sai na zuci da yafi na zahiri ciwo, Yusrah mufeeda da sauran yan matan É“arkewa sukai da kuka barin ma mufeeda da Yusrah tunda su abin tafi shafa, kuka suke wanda yake tafe da baÆ™in ciki hawaye wani na koran wani, yaya hydar kan kasa jurewa yayi sai da AS ya riko shi daga tsayen da suke ya fashe da kuka jin abin kunyar da mahaifiyar su ta aikata,Abbie ma dai mutum mutumi ya zama, a falon fa an rasa wanda zai lallashe wani ganin haka ne sai grandma da goggo sai kuma Abba (Abban Ruqqy)da bappi suka maze suka hau basu baki duk da suma abin ya buge su, ruwa aka dauko aka shafawa inna nan take ta kawo nunfashi, Abba kuwa ganin an gano shi ne yasa ya fito a salin sa na mugu inda ya rinÆ™a sake dariya yana tafa hannu kafin kuma yazo ya daure fuska ya dinga faÉ—in abinda yayi a gidan tundaga barar ma da Aziza ciki da yake har zuwa wannan farmakin da ya kawo musu su uku, da inda ya sha farmakan Abbie da kuma inda yake farmakan rayuwar eelham amma Allah ya kubtar da ita daga dukkan sharrin sa, ya kuma shaida musu shine nan ya saka momma ta saka hydar ya rabu da eelham dan biyan tashi buÆ™atar, sosai mutanen falon suka firgita inda tsoro al'ajab mamaki suka dabaibaye su ba su gama dawo wa dai dai ba suka ji muryan shi yana faÉ—in "kai kuma" yayi maganar yana pointing Abbie cigaba yayi da faÉ—in "tunda kun  tsira a baya to a yau a kuma yanzu ga ni ga  ku" wata Æ™ara ya saki wanda haka sai da ya girgiza falon, eelham da take É—aki da su Anwar da sukai bacci bata san sanda ta miÆ™e ba har zata fito sai ta juya da baya ta É—auki Anam da Anwar tayi musu kyakkyawar shimfida a waldrop da ya kasance mai faÉ—i ta dauki rechargeable fan ta saka musu a ciki sannan ta aje qur'ani daga gefen su ta kulle waldrop É—in da key tana daukan wata qur'anin ta fita, koda ta fita falo gani tayi ba gaske da yake tasan kan falon inna yasa ta isa wajen light din ta kunna, tana kunna wa kuwa Abba ya Æ™ara yin wata karar da tafi ta farko daga nan ya rikaÉ—a ya koma abinda yake zama. Har kowa yayi ta kanshi cikin karaji eelham tace 'kar wanda ya motsa addu'a shine makamin mumini dan haka addu'a shine zai zama makamin ku dan ko ina kuka shige sai ya biku" Allah da ikon sa nan kuwa kowa ya fara duk addu'a da tazo bakin shi daman cikin mazan babu wanda ya motsa jin haka ne suma suka hau addu'a, nan kuwa Abba ya fara gurnani yana jin ana masa azaba cikin jikin sa amma hakan bai sa ya dawo dai dai ba, shifa sai ya cika abinda yake ran shi koda daga nan zai mutu ne, Æ™ara yunÆ™urawa yayi a fusace ya chakumi Abbie bawan Allah da bai san duk abinda yake faruwa ba dan yayi nisan nisan kiwo sam duk wannan abun da yake wakana bai san anayi ba sai da yaji shaÆ™a har na wuce misali sannan kuma ga nauyin da yaji jikin shi yayi masa lokacin É—aya, a wannan suffar Abba ya Saita hannayen sa masu zarozaron farce zai karci Abbie a ciki, a dai dai nan eely ta gama tofin da tayi a cup ta watsa masa tana karanta ayatul kursiyu lokaci É—aya nan ya saki abbie ya fara murÆ™ususu a Æ™asa, eelham kam bata barshi ba haka ta dinga zuba mishi wannan ruwan addu'a, Abba kuwa jin azaba tayi azaba tini ya rikiÉ—a ya dawo mutum sai dai hancin sa da bakin sa sai fidda jini yake cikin muryan shi da bai gama dawowa dai dai ba ya sauwaÆ™e wa mamy, wanda tayi farin ciki da haka ji take kamar ta zuba ruwa a Æ™asa ta sha,su  Umar basu Æ™ara jiran komi ba suka tafi dashi, wani cup eelham ta samu tayi ma Abbie tofi ta miÆ™a mishi yasha, tass kuwa ya shanye ita kuma ta karbi cup É—in ta maida shi ma'ajiyar shi sannan tayi saÉ—ap saÉ—ap ta koma inda ta fito wannan karan harda su murza key dan ganin oga ya ganta kuma bata son ganin shi.. achan falo Abbie ba tare da ya kalli momma ba bai kuma dubi yaran da suke anan ba ya sauwakewa momma sauran igiyar da yake tsakanin su sannan ya bukaci da ta bar masa gida yanzun nan, da yake tasan ba ta da gaskiya yasa ba musu ta tashi ta shiga part É—inta  ta É—auki abinda yake nata masu amfani wanda tasan zai yi mata anfani ta bar gidan hawaye sai ambaliya suke mata a fuska, Abbie cikin jarumtan nan tasa ya yi musu nasiha mai shiga jiki da bargo sosai kuwa hakan tayi tasiri a gare su sai dai fa wannan tabon yana nan daram cikin zuciyar su, suna a wannan halin na jugum jugum sai ga su zeena da yayar Anne, yan falon kuwa sai kallon su suke irin kallon rashin sani, a dan rakuÉ“e suka zauna, suna gaida mutanen falon É—aiÉ—aikun cikin su suka amsa sauran kuwa ko kallo basu i'she su ba irin ma AS da Hydar, cikin marairaice fuska zeena tace "dan Allah eelham nake nema" ai nan suka Æ™ara yi mata Æ™ur da ido wanda hakan yasa nan da nan ta tsargu, goggo ce ta amsa mata da "eelham tana ciki ya akayi ne?" "Dan Allah a taimaka a kira min ita inasan nayi muhimmiyar magana ce da ita" Saida suka Æ™ara yi mata kallon tsaff sannan grandma ta saka meenal zuwa kiranta..