94&95
94 & 95
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
Ganin ya miƙe ne yasa Abbie yayi kokarin tsaida shi amma bappi ya hana, haka dai ya fice babu wanda yace masa uffan,,,bayan sun kammala break ne grandma da goggo suka yanke shawarar kowa ya shirya aje a ga gidan da zasu koma, idan yaso ko zuwa next week sai su koma sai kowa ya fara shiri, nan kuwa kowa ya watse a ka bar kayan masu aiki suka kwashe, daman duk sunyi wanka, Bus da karin mota uku ya kwashe su suka wuce chan gidan through location da suka gani a takardun, su eely da sauran yayin su mata gaba ɗaya suna a cikin Bus ɗin sai sauran motan iyayen su da su inna, sai motar su samari shima guda huɗu. suna kawowa dai dai gate ɗin gidan kuwa sukai parking, haka kowa ya fito daga motar eelham ce karshen fitowa daga cikin Bus ɗin tana fitowa idanun ta suka faɗa a na AS amma sai tayi maza ta ɗauke nata tana basarwa, shikuwa qur ya zuba mata ido babu ko kyaftawa har ta fito daga motar gaba ɗaya, kowa ya shiga ciki kusan eelham ne ma gaba gaba, tundaga wajen gidan zaka gane cewa anguwa ce guda, cikin tsakiyar gidan kuwa ai ba'a magana dan faɗin sa, gashi anyi wa ƙasar kwalta ɗodar, ga part part nan jere amma sai dai ko wanne yana da tazara da ta ɗan uwan shi, ta baya can wasu part din ne suma gasu nan, sama sama suka shiga ko wani part shima ba duka ba suka fito, suna ta santi da yabon girma da tsarin gidan aikuwa baba yasha addu'a sosai shi da Ammie, haka dai suka fito suka wuce, suna komawa gida aka ƙara zama, inda cikin mazan ko wanne an bashi part ɗaya ɗaya da yake ta baya ya zauna da matar shi, su ma su yaya fadeel ance zama dai harda su dan haka suma sai su shirya su Anty Maleeka kam sai daɗi ake ji za'a dawo kusa da iyaye, Umar ma haka, suma iyayen nasu kowa an bashi dama ya ɗauki ɗaɗ-ɗai masu mata biyu kuma ya zama uku, AS ma tashi uku kenan daya nashi, ɗaya na mubee, ɗaya na eelham, bayan sun gama rabon aka sallami yaran bayan duk sun fita ya rage iyaye kawai "Toh daman dalilin tara ku da muka yi anan shine muna son muƙara haɗa zumunci mai ƙarfi ne tsakanin mu da Anne gata, ba tilastawa ba Kuma tursasawa ba kuma umarni bane sai alfarma da muke biɗa a wajen ki" shiru Anne tayi kafin ta amsa da "ku masu zartar da hukunci ne akai na ni kuma tawa biyayya insha Allah" "Masha Allah Allah yayi miki albarka! Daman alfarman da muke Nima shine muna son a daura muku aure keda Abbien su Alhaji Muhammad" dum haka taji ƙirjinta ya buga sunkuyar da kai ƙasa tayi kafin ta buɗe murya tace "duk abinda kuka yanke dai dai ne a gareni" sosai suka ji daɗi furucin ta inda su inna suka buƙaci Abbie da ya miƙa sadaki kuma sun hana kowa ya bi ya masa, nan ya aje kuɗin suka tsayar bayan sallar azahar sai a daura auren a masallaci dama ga lokaci yayi, duk fita sukai zuwa Masallaci, bayan sun idar da salla aka daura auren Abbie da Anne yaran kuwa sunyi murna da jin wannan labarin sabida shaƙiyanci irin nasu harda wasu haɗa kwarya kwaryan walima ta dare bayan an idar da isha'i suka haɗa wannan walima tsakiyar gidan sukai ta gefe suka shimfiɗa carpet masu tsawo aka jera abinci a tsakiya ga haske ko ta ko ina shagali,kowa yana wajen amma babu eelham da Anwar dan su na wajen su goggo, eelham kuma na ɗaki, da sauri ta fito dan tasan yanzu suna nan suna jiranta ta tafiya take tana daura agogo bata ankara ba sai jin gwaf da tayi taci karo da mutum, ja baya tayi kadan tana taɓa goshin ta dan ta ƙwalu kafin kuma ta ɗago kai dan sam bata gane mai tularen jikin sa ba, ido huɗu sukai da AS da ya zuba mata ido ya harɗe hannu a ƙirji, cikin fiskewa tace "sannu" ta ratsa ta gefen shi zata wuce amma sai ya hanata wannan damar, ba dai ta ɗago ba dan ta kula so yake ta kulasa ita kuma bata shirya ma wannan ba, ganin fa bazai matsa mata ba kuma ba za ta iya masa wata magana ba yasa ta gwammaci gwara ta koma, haka kuwa ta juya ta koma inda ta fito, sai da ya bari ta shiga sannan shima ya take mata baya,zaune ya same ta gefen bed tana kokarin kwance rolling Vail ɗin da tayi,ganin shi kuma bai hana ta ci gaba da abinda take ba, zama yayi daga gefen ta babu wani space mai tsawo a tsanani, yace "dejarht hala baki san nayi tafiya bane?" Cikin rashin damuwa da son cusa masa haushi tace "auu I'm sorry yaya AS nayi busy ne ya hanya da kuma mommy su Anwar?" Ba haka ya so ba, baison wannan sabon salon da ta ɗauka yanzu, zuba mata ido kawai yayi yana ganin rashin damuwa akan fuskar ta, kallon da yake bin ta dashi ne yasa tace "yaya ko kana son wani abu ne?" Ɗan datse labban shi yayi tunanin ko dai magana ta gaya masa wato bai zuwa wajen ta sai da dalili kuma kusan haka ne. "Khadijah mi yake damun ki neh?" "Babu komi yaya" shi dai eelham ɗin da ya sani ba haka take ba, tafiyar da yayi sai yaga kamar an canza masa ita gaba ɗaya bayan wannnan harda ƙiba yaga ta ƙara masa ga fatar ta sai glowing take ta kuma ƙara buɗewa irin ta masu ciki, kasa ɗauke idanun shi akan ta yayi, da yaga kamar ba zai iya jurewa ba sai ya koma kusa da ita daman ta bar mishi wajen, sata yayi a jikin shi, bai jira komi ba ya daura hannun shi kan cikin ta, da sauri ta dauƙe masa hannu tana banka masa harara wanda kadan ya rage dariya ya kufce masa, "a'a Ni kar ki cinye ni da wannan idanun pls" cikin basarwa ta ɗauke idanun ta daga kanshi, "Madam wai me sirrin ne naga kin wani ƙara zama madam? Ko dai akwai ne Uhm?" Bata fahimci inda ya dosa ba yasa tayi shiru bata tanka masa ba, sauke nunfashi yayi yace "dan Allah dejarh fushin nan duk na mene? Ni ina can na kasa sukuni tunanin ki duk ya hana na maida hankali inyi abinda ya kai ni yasa na dawo ina zumuɗin ganin ki amma ke sai naga ba haka ba kamar ma baki so na dawo ba keda kakannin ki da iyayen ki barin ma Ummin ki da bappi" "ƙilan kuma haka ne fah" cikin daure fuska lokaci guda yace "ƙilan haka ne mene?" Tashi tayi daga jikin shi tace "ban sani ba, da ka koma inda ka fito ina ganin kaman haka zai fi" dafe kai yayi dan shi sai yanzu ya fahimci inda ta dosa wato kishi take kenan, sosai yayi farin ciki da haka alamu dai sun nuna tana son shi, cewa yayi "taya za'a na koma inda na fito na bar matata anan ai in Kinga na koma to ƙafata ƙafan ki" "a'a fah tana can" cewar EElham, sauke nunfashi yayi ganin ta dau da zafi cikin sanyin murya yace "zauna muyi magana pls" ƙi tayi sai da ya ja hannayen ta sannan ta zauna a gefen shi cikin sanyin murya yace "khadeeja kiyi haƙuri Ni nasan nayi miki ba dai dai ba da na tafi na barki a halin rashin lafiya, ba yin kai na bane aiki ne ya taso min to kuma nace zan tafi dake grandma ta hana wai baki ji sauƙi ba, shi yasa na ɗauki mubeena muka tafi tare amma ba dan na ɓata miki nayi haka ba".