EELHAM🌹

96&97

by @rabearhwakili


{🌹 EELHAM🌹}
Rabe'arh wakili 
96 & 97
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
Sauke wata boyayyar ajiyar zuciya tayi sannan ta furta "hmm amma cewa akayi wai baza ka tafi da matar cushe ba" babu shiri ya ɗago ya dube ta yace "wa ye ya faɗa miki haka, ko waye yace ke matar cushe ce a waje na? Bari na faɗa Miki abinda baki sani ba, koda su bappi basu aura min ke ba ni zan Nima auren ki da kai na daman ina da niyan haka, dejarht tun kina a jaririyar ki nake son ki, tun ban san so ba, na fahimci haka ne bayan barin mu ƙasa da mukayi, na wahala da rashin ki dejarht a kuma lokacin da na ganki sanadin su Anwar nafi kowa murna da farin ciki ƙara ganin ki a rayuwata" yana kaiwa nan ya rungumota ƙam cikin yin ƙasa da murya yace "dejarht baki ba zai  iya furta iya adadin da nake son ki ba,kalmomin sunyi kadan, i love you Khadijah, and I will continue till my last breath"unexpected hug yaji daga gare ta, kam ƙam ta rungume shi hawaye na zuba daga fuskarta na farin ciki, ganin yana kokarin fito da ita daga jikin shi ne yasa ta cire hannu ta goge hawayen tas kamar basu wanzu ba, kallon ta yayi da murmushi yace "Madam to ni ana so na kuwa?" Da sauri ta maida fuskar ta a kan chest ɗin shi tace "a'a ba'a sonka" murmushi yayi dan muryan ta ya bai yana komi, "mi yasa baki gaya min u're pregnant ba?" Dagowa tayi ta dube shi "pregnant?" Bai ce mata komi ba ganin dai bata sani ba "dauko hijab ɗinki mu koma gida" "uhm uhm ummi zata yi magana" "ita ma tana nan tare da mijin ta" da kanshi ya tashi ya dauko mata hijab ta saka suka bar ɗakin, ta baya suka bi har suka iso wajen parking, mota suka shiga ba tare da kowa ya gansu ba suka bar gidan zuwa hotel, washegari yana yi suka bi Flight suka koma Kano, a can Abuja kuwa an Nima eelham sama ko ƙasa babu ita Saida suka kira AS shikuma ya shaida musu suna Kano yana faɗin haka ya yanke wayar, ummi har zata ɗauki zafi da lamarin su umma suka bata baki da kuma ta bisu da fatan alkhairi, haka kuwa akayi ta zubda makaman yaƙin ta, suma babu wani jima suka koma Kano dan su haɗa kayan su, a washegarin ranan da suka koma ya ɗauke ta suka je hospital inda akayi mata test aka gano tana dauke da juna biyu, sosai sukai murna da hakan koda suka koma gida AS ba kunya yayi kiran grandma ita kuwa amsa masa tayi da "sai yan zu kake sani kenan" sosai yake kula da duk wani motsi na eelham gaba ki ɗaya kula da tattali yake gwada mata. haka rayuwa yake ta tafiya gashi yanzu har sun koma Abuja gaba ki ɗayan su da zama a babban family house ɗinsu, as ya koma england tini bisa yarjewan eelham tunda babu yadda zai yi da mata biyu a ƙasan mutane, tunda ya wuce ko sau ɗaya basu taɓa fashin yin waya ba wani zubin harda mubee da ta sauko ta gane gaskiya bisa shawarwari da yayarta ta bata ku ma alhamdulillah duk ta dauka da yake kuma Allah ya nufe ta da shiryuwa.kamar haɗin baki yau su yusrah, Raihana,Sarah, suka tashi da labour, Raihana ta fara sauka ta sulluɓo kyakyawar yarta mace mai kama da iyayen ta, can bayan la'asar Yurah itama ta sauka inda ta haifo yarta mace itama, a tsakanin yusrah da Sarah babu wani jimawa ita ma ɗin mace ta haifo mai kama da baban ta sak, sosai gidan suke cikin murna da farin ciki da yake duk an dawo dasu ɓangaren su inna yasa kusfa kusfa haka aka ɗinga zuwa gaishe su da ganin baby, angwayen ƙarni ai ba'a magana sun kasa tsaye sun kasa zaune, ana gobe suna mubeena ta iso, washegari aka radawa yara suna, bayan suna mubeena ta tafi garin iyayen ta,haka rayuwa yake ta tafiya yau daɗi gobe kuma a kasinta. su Aziza suma ɗin duk sun haihu mufeeda da ummi ma tun bayan sunan yaran su Raiha suka haihu duk ɗinsu maza ne,Aziza ɗin ma mace ta haifa, sai Ruqqy da meenal suma maza suka haifo Masha Allah family fa ya ƙara faɗaɗa, suna kuma zaman so da kaunan juna su, Abba kuwa ana can gidan yari ana karban wuta. Yau tun safe eelham take jin ta some how some how.