98&99&100
{🌹 EELHAM🌹}
Rabe'arh wakili
98 & 99 & 100
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
Ganin yanayin ta yasa AS bai je ko ina ba dan yana ganin kamar labour ne,da ya tambaye ta tace mishi ita lafiyarta qalau, amma da abin tazo mata da gasken gaske nan fah ido ya raina fata, kafin AS yayi wani yunkuri har ta yunƙura da ƙarfi ta sulluɓo ɗanta, nan kuwa wata nishin ya ƙara taso mata, ga yaro nan a ƙasa sai kuka yake tsalawa, ummi da take a falo ai ruɗewa tayi ta faɗa ciki tana zuwa ta nufi wajen eelham dake a gefen gado, AS da yake gefe saboda ruɗewa ma kasa sanin yadda zai yi yayi, "maza kamata muje hospital" ai bata rufe baki ba, nan yaro ya ƙara wata kuka a kuma dadai nan Allah ya ƙara bata ikon haifan wani yaron shi dai tunda yayi kuka sau ɗaya bai kuma ba, kabbara ummi ta fara tana godewa Allah sannan ta dubi AS tace masa ya samo rezor, wajen mirror ya tafi ya dauko duka kwalin ya bata, ummi kuma ta yanke musu cibi, haka dai ta zage ta gyara yaran tayi musu wankan tsaff, eely ma ta gyara ta sosai, sai da ta ɗan huta sannan suka ɗauki eelham da yaran nata twince suka tafi asibiti, koda suka je aka duba ta komi lafiya qalau hakan yasa basu zauna ba suka dawo gida inda suka iske yan Barka dankam a part ɗin inna, duk wanda ya ɗauki yaran haka zai ta santi dan yara kam sun sha kyau sunyi kama da maman su da kuma AS Saidai basu dauko chocolate skin din eelham ba sai sukayo hasken AS kamar su Anwar, yaran they're identical twins kamar su har ta ɓaci sosai wanda mutum bazai iya banbance waye wane a cikin su ba. AS kam duk da ba wannan bane haihuwar shi ta farko ba amma sosai yayi murna da farin ciki kamar wannan ɗin sune farkon yaran sa, dan Allah ya zuba masa son yara kamar mi, ga ya kasa zama sai buge buge waya yake yana sanar da ƙaruwar da ya samu. Ranan suna yara suka ci sunan baban eelham da Abban Ruqqy, amma ana ce dasu Nawaf, da Nawaz, yara sun yi goshi alhamdulillah mahaifiyar su itama ta samu gata sosai sunyi kokarin ganin sun kore mata maraicin ta, sosai sukai mata hidima wanda ko iyayenta suna nan iyaka kenan. Haka dai taro ya tashi lafiya cikin Aminci. bayan sunyi arba'in eelham ta koma ɗakin ta bayan ta ji gyara ciki da waje wajen likitar mata Hajiya maimuna, tayi kyau ta koma tai bulbul kamar ba wata mai shayarwa ba. Haka rayuwa yake ta tafiya inda gaba ɗaya rayuwan su Nawaf suna yin shi a part din mubeena ne, idan ka gansu a wajen eelham sun zo cin abinci ne, da kuma ta yaye su da kanta ta tattara kayan su ta miƙawa mubeena, ta cigaba da kula da su Anwar dinta dan tace sune ya'yan ta... Bayan yayen su Nawaf ta ƙara samun juna biyu Saidai wannan kam taji jiki wajen laulayi, har dai Allah ya sauke ta lafiya ta haifi mace mai kama da ita harda skin din su, wannan karan ita AS yace ta zaɓi sunan da take so a sakawa yarinya, ita kuma tace a sa Ruqayyah dan kaunan da sukewa juna... Yau da gobe asarar mai rai, rayuwa nata tafiya daga Safiya kaji ance rana tayi ranan ta juye zuwa dare, dare ya haɗa kwanaki, daga nan satika,shima ya juye ya koma watanni, watanni suma su juye zuwa shekara daga nan kaji ana maganar shekaru. BAYAN SHEKARA 23 abubuwa da yawa sun faru na farin ciki da akasinta, ciki kuwa harda rasuwar Abba dake a gidan yari,da auren su Anam da sun zama cikakkun yan mata, tsoffin nan suna nan sai dai tsufa ya ƙara kama su, family ya ƙara faɗaɗa inda zaman lafiya ya ƙara wanzuwa a tsakanin su gwanin birgewa. Tun bayan haihuwar auta Ruqqy AS bai ƙara samun haihuwa ba, yanzu haka duk anyiwa su Anam aure da su auta Ruqqy. Sosai umm da mommy suka haɗa kansu sun zama kaman yan uwa ba kishiyoyi ba. Hakan ya taimaka sosai wajen haɗin kan yaran su, shima papa ya samu kwanciyar hankali sosai da haka kuma yana alfahari da su. Duk dare a part din papa familyn shi suke haɗuwa gaba ɗaya ayi dinner sannan kuma su yi fira cikin fahimtan juna, yau ma hakan ta kasance, bayan sun kammala dinner suka koma falo gaba ɗayan su suka kafa cambar fira haka dai suke ta yi cikin nishaɗi duk da yanzu sun manyanta, daga bakin kofa akayi sallama da murya can ciki kamar wanda aka tilasta, umm (eelham)ce ta amsa da fara'a dauke da fuskarta, ƙarasawa wannan matashin yayi wanda a shekaru zai kai 30 yrs yayi ciki yana gaida iyayen shi wanda mommy (mubeena) ko kallon shi batayi ba dan wannan halin nashi sai umm ɗin sa, gefen umm ya zauna yace, "umm I'm hungry" "boy wai kai sai yaushe zakai aure ne? ga Sa'annin ka duk sunyi, amma kai baka ma maganan haka" dan bata fuska yayi dan shi bai son ana yi masa maganar aure, "wai sai kin tsaya bata yawun bakin ki ne? Masallaci zan kaishi ayi sadaka dashi, ko na samo masa cikin dangi, koda yake ai ke ke daure mishi" Cewar AS, da sauri Anwar ya dubi mahaifin sa jin abinda yace, su twince kuwa abin nema ya samu kyalkyalan dariya suke barin ma yadda suka ga hankalin Anwar ya tashi, "aure lokaci ne idan tasa lokacin yayi ai zai yi" cewar umm, ita dai mommy bata ce komi ba dan tana nuna kawaici akan Anwar sosai idan ba faɗi akayi ba baza ka taɓa cewa ita ta haife shi ba. "Papa BB boye muku kawai yake amma yana da..." Hararan da Anwar ya sakar masa ne shi yasa ya haɗe maganar babu shiri, yana kuma toshe bakin shi ɗan dariya "faɗa muji ooo" cewar papa shikuwa dama abin Nima ne ya samu baki har rawa yake wajen faɗin "surayyah yarinyar aunty Ruqqy" jin asirin shi ya tonu yasa yace "umm Saida safe! Kai ba gulma ba zamu hudu anjima" "akan me zaka taɓa min yaro? Daga ya taimaka maka?" Cewar mommy tana hararan Anwar, dariya su umm da papa suka sanya mata ganin yadda take ita a dole za'a taɓa mata ɗan so shi kuwa guduwa yayi yana murmushi, toh iyayen shi ma sunji daɗin wannan haɗin nasu saidai kawai su bisu da fatan alkhairi.....
Tammat bi hamdullah.
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Alhamdulillah
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, na gode Allah da ya bani iko da daman kammala littafin nan cikin ƙoshin lafiya Alhamdulilla, inda nayi kuskure Ubangijin mu Allahu ka yafe min dan alfarman Annabi Muhammadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallam 🤲
ina Neman afuwa ga dukkan Wanda Na yiwa ba daidai ba yayin rubuta wannan littafi cikin Sanina ko'a rashin sani dan Allah ayi mun afuwa.🙏🙏🙏
EELHAM FAN'S ina matukar godiya ina kuma alfahari daku da irin yadda kuka karɓi littafin nan da hannu biyu,da yadda kuke yi min addu'a, da yadda kuke comments ina godiya mara adadi Allah ya saka maku da mafificin alkhairi, gaba ɗaya masoya littafin EELHAM ina miƙo muku jinjina yan uwa.
Anty Billyn Abdul
Ammey laylah
Anty A'isha Aliyu garkuwa
Yaya azeema
Ummu maheer
Tabbas kun cancanci godiya mara adadi, ina godiya sosai da sosai,Allah ya saka muku da mafificin alkhairi, Allah Ubangiji yayi sakayya da jannatul Firdausi 🤲.
Yar uwa sister Ruqayyah
Yar uwa sister Hajara
Allah ya saka da alkhairi tabbas ina godiya da irin ƙwarin gwiwan da kuka bani Allah ya saka da alkhairi
Allah ya saka da alkhairi yar uwa sister khairatuh Allah ya ƙara miki lafiya.
ina rokon Allah ya ƙara haɗamu cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali🤲
I will really miss you fan's
Allah ya sada mu da alkhairin sa
Bissalam ma'assalam👏