Farautar Mutunci

Chapter 7

by @oumfatayat

FARAUTAR MUTUNCI

Marubuciya:

Na’ima Sulaiman Daƙayyawa ( Oum Fatayat)

Page: 7


Madam Karima ya samu a zaune, a kusa da Nuri tana faman murmushi,tana mata sannu kallon Mahmud ta yi kana ta masa albishir da Nurin na ɗauke da juna biyu.

Batare da sun an karaba Mahmud ɗin ya matso da sauri ya ɗauke nurin cilak yana za gaye da ita a tsakiyar falon, farinciki yake sosai, don ya ma manta da Madam KARIMA a wajen, wutsilniya Nuri ta fara yi tsayawa ya yi cak, don yaga tana meman yi masa a sara a cewar sa.

“Haba Nuri ya za ki min asara Amani tun kafin ta fara warwarewa a cikin na ki, ki bari mana”. 

Kwantar da ita yayi akan kujera, yana ƙoƙarin buɗe mata ciki wai yana so jin motsin Baby, taɓa shi ta yi da hannu ta yi, nuni ta masa da Madam Karima da ta kusa fucewa daga falon, kunya ce gaba ɗaya ta rufe shi nan ya bi bayanta yana sosa ƙeya.

“Madam don Allah ko za ki rubuta min Maganin da Nurin za ta ɗan sha na je nasiyo mata saboda aman nan da ta yi”. Dariya kawai Madam Kariman ta yi kana ta dawo ‘yan rubuce-rubuce ta yi ajikin ƙaramar takkada ta bashi, shi kuma ya futa da sauri.

“ A gaskiya Nuriyya kinyi matuƙar dacen miji, don na lura idan Mahmud yana tare da ke tom ba ya iya ganin kowa sai ke, don haka ya kamata ki cigaba da masa biyayya, ki kuma taya shi ya rabu da Hajjo lafiya, ki sake dagewa sosai wajen kula da shi da kuma rayiwarsa, don Allah kar ki ba ni kunya”. Shi ne abuda Madam Karima ta faɗawa Nurin

“In sha Allah Madam zan dage, na kuma gode da irin kulawa da shawarwarin da nake samu daga gare ki” 

Murmushi Madam Karima ta yi sanan tace “ Ai na lura da Hajjon ta sa, akwaita da rigima, shi yasa na miki maganinta, na kuma miki hakane saboda ta barki kisamu sukunin zama ke da mijinki cikin kwanciyar hankali, amma hakan ba shi yake nuni da ki zuba ido kawai ba, zama bai kama ki ba, dole ki sake ɗaura ɗamara wajen yi mata biyayya tare da kyautata mata sosai da sosai, ki kuma dage da addu’a don kuwa bacci bai kama kiba”.

“Na gode sosai Madam zan kuma ƙara jajircewa a kan hakan”.

“Yawwa Nuri, haka nake son ji”.

Ƙarar wayar Mahmud ce ta sa su yin shiru da maganar, alamar yana shigowa kuma ana kiransa ba tare da ya ɗaga ba ya ƙaraso falon.

Da ganinsa Madam Karima ta miƙe ta kuma musu sallama za ta fita, shopping ɗin da Mahmud ɗin ya mata ya bita da shi ya kuma rakata har ƙofar gida, yana mata godiya, nan ta sake masa nasiha akan Hajjo, kana ta wuce cikin gidanta.

Bai tsaya wata-wata ba ya koma gidan, da mamaki yake kallon inda take kwance, babu Nuri babu alamunta, motsinta ya ji a cikin Kicin ga kuma gidan ya haɗe da wani ƙayataccen girki wanda kana iya jiyo ƙamshin sa tun da ga waje, binta ya yi don ganewa idonsa.

Juyowa ta yi da idanuwata ta masa wani fari  mai ƙara kiɗima shi, yadda ya ga ta sake wani kyau ne yasa ya sake susucewa,abunda ya sake ruɗa shi yadda ta ɗaure gashin kanta ta kuma P. Cap jelar gashin ta kwanto mata har gafon bayanta, wata ƙaramar riga iya cinya ta sa mai ƙaramin hannu.

Ƙungunta ya riƙe, ta fara yar waƙa tana jujjuwa a hankali gaba ɗaya Nuri ta gama rikita Mahmud, janyo ta ya yi sosai jikinsa ya rungumota, jigina ta yi da bango nunfashin su yana fita da sauri.

“Nurina na gode miki wai ashe dama kin cire tsarin iyalin nan ban sani ba, mai yasa ki ke gane abunda nake so ne tun kafin na furta”.

Hura masa iska tayi a ido, ta kuma sun bace shi a goshi, sanna ta fara magana

“Kasan me? A rayiwata ba bu wani abu da na fi karanta irin abunda kake so, duk wani motsinka ina iya gane shi, Hubbyna ka sani kai ɗin rayiwata ne kuma babu wani abu da zuciyar ka za ta buƙata wanda ban jishi a jikina ba tun kafin ka furta”.

“ Nuri Allah ya dasawa zuciyata Sonki, Kin san me? Wani lokacin har kasa aiki nake a Office, sai na shafe tsawon a wanni ina tunanin ki kuma duk da nasan ina gamawa gida zan dawo”.

“ To ni dai ba ruwana, idan aka ce wani baya kammala aikin sa kullum”

Lakuce mata hanci ya yi “ Ai kuwa kina da Ruwa tunda dai ke ce sila”

Rungumota ya yi a jikinsa sosai, ita kuwa abunka da laƙwaiƙwaya, ta sake sosai ta lafe a jikinsa, shafa cikin na ta yake wani farin ciki da nutsuwa ne suke ratsa shi, ji yake tamkar abar shi daga shi sai Nuri a  cikin Duiyarsu don kuwa ba don Hajjo ba, ba wani sauran ƙalubale kuma.

In da ya ke sake godewa Allah Nurinsa mai hankali ce, kuma tana kaffa-kaffa da duk wani abu da ya dangance  shi.

Kallonsa ta yi “Hubby bacci uhum”.

Yadda ta faɗi maganar cikin salo, da yadda zazzsƙar muryarta mai sake angiza shi ne yasa ya ji wani daɗi ya sake ratsa shi.

Ɗakko ta ya yi cilak ya kawo ta falo ya ɗora ta akan kujera, zama ya yi a ƙasa ya ɗakko ƙafarta ya fara danna mata su a hankali yana mata tsusa a haka har ba…….

بقلم أم فتيات 👧👧👧✍🏼……