19
*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_
*NA*
*AISHA ALTO*
*JAMILA UMAR(Janafty)*
M.A JUMARE FOOD AND SPICES
Pure and Natural hygienic tasty.
Muna da garin Ɗanwake da yaji mai kyau dakan hannu, akwai kuka, tsamiya, garin tamba, kuɓewa da daddawa.
Muna aikawa da kayanmu a ko'ina
Anguwan Ma'aji new millennium city kaduna
Phone number ***
*HIJABS CORNER BY JANAFTY*
*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design, muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*
*BABI NA GOMA SHA TARA*
Ƙarfe 2:40pm. Ta isa Ɗanbatta, Tahir da Hakimi da sauran mutane suna zaune a ƙofar gidan suna karɓar gaisuwa gurin jama'a masu zuwa musu ta'aziyya, haka ta ratsa tana sunne kai ta shige cikin gidan, tana shiga direct ɗakin Goggo Abu ta dosa.
Tana shiga da Umma suka fara haɗa ido, rass taji gabanta ya faɗi tana turo baki ta ƙarasa ciki ta zauna a kusa da Goggo Abu ta duƙar da kai taƙi kallon kowa dake ɗakin, Mufeeda kuwa tana ganin Farida ta shigo tayi maza ta miƙe ta fita falon Goggo ta zauna, don bata son abinda zai haɗasu da Farida guri ɗaya, gani take zata iya rufeta da duka don haka take jin tsoronta.
Miƙewa Goggo Abu tayi itama ta fito falo gurin Mufeeda ta zauna akabar Umma da Farida kaɗai a cikin uwar ɗakin, ɗagowa Farida tayi tana kallon Umma tace "Umm..." Da sauri Umma ta dakatar da ita tana watsa mata harara take faɗin "Uban me ya kai ki gidan Bilkisu Farida...? Wato dai ke har yanzu bazaki natsu kiyi hankali da duniya kisan me take ciki ba ko Farida.? Yanzu da kika je gidan Bilkisun uban me kikaje tayi miki? Me ma yasa kika saka ƙafa wai kika bar gidan mijinki da 'ya'yanki bayan duk irin faɗan da nayi miki ranar kafin mu tafi? Wato baki ji ba shine kika shure kika tafi gidan ƙawa har na tsawon kwanaki huɗu kina can a zaune saboda gaki ballagaza ko...? To uban me kika je yi gidan aurenta tayi miki..? Tana zaune da mijinta lafiya ke da baki san mutunci da darajar naki mijin ba shine kika kwashi jiki kika tafi gidanta tayi miki maganin taki matsalar ko?" Ta faɗa a hasale tana ji aranta kamar ta tashi ta rufeta da uban duka saboda takaicinta, ita ko Farida wani bala'in haushin Bilkisu ta ƙara ji a zuciyarta, take wasu hawaye suka fara zubowa daga cikin idanunta Umma na kallonta tace "Ai kuka kam yanzu kika farashi Farida..tunda dai kince ke ba mai hankali da tunani bace balle kisan ya kamata, na ɗauka zaki yi nadama ne saboda abinda sakacinki da toshewar tunaninki ya janyo muku ke da mijinki, ashe ba haka bane, ke inda tunaninki yake daban, abinda kika ɗaukarwa zuciyarki tun farko shi zaki ci gaba da yi. To kiyi Farida, bance ki fasa ba kici gaba..." Haka Umma tai tawa Farida faɗa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, Farida kuwa in banda kuka ba abinda take yi har da shassheƙa, sai yanzu ne ita da kanta take ganin aibun abunda tayi a rayuwarta, bata kyautawa kanta da 'ya'yanta ba, uwa uba kuma mijinta, bata tashi sanin babban kuskuren data tafkawa rayuwarta ba, sai data je gidan Bilkisu taga yanda take yiwa mijinta take kaffa kaffa dashi, bata haɗa komai da mijinta ba. Ita yanzu wace riba zata ce taci na irin halayen dasu Bilkisu suka dinga zigata suna ɗorata akai kuma tana bi...?
Umma ce ta katse mata tunanin da take da faɗin "Yanzu a irin waɗannan abubuwan da kike yi wace riba kika samu? Me kuma zaki ɗorar? Miji ya gaji da halinki, har ya daina damuwa da duk wasu lamura da suka shafeki, kin kaisa bango halayenki sun gama isarsa, kin tafi kin bar gidan mijinki da 'ya'yanki kin tafi gidan ƙawa kin zauna har tsawon kwanaki, kin gama fallasa kanki da zuri'arki a gaban ƙawayenki, sirrin gidanki da komu bai kamata mujishi ba kin gama tallatashi a titi ga wasu can kinyi terere da mijinki, don nasan sai kin gaya musu duk abinda yake faruwa, tunda tunaninki ya gama toshewa..." Ta faɗa tana murmushin takaici, wani kukan baƙin ciki Farida ta fashe dashi tana girgiza kanta, kafin ta ɗago hawaye na tsirarowa daga cikin idanunta tace "Umma don girman Allah..." Sake dakatar da ita Umma tayi da faɗin "Komai kika yi fa kanki kika yiwa, nidai zanci gaba da tayaki addu'a Allah ya shiryeki yasa ki gane gaskiya. Don haka maza ki tashi kije ki yiwa Mufeeda gaisuwa..." Ta faɗa tare da miƙewa, itama Faridan tashi tayi tana share hawayen fuskarta tabi bayan Umma suka fito falo, inda Goggo Abu da Mufeeda suke sai Nailah da Iya da Maman Lantana, Umma zama tayi a kusa da Mufeeda tana kallon Farida da tayi tsaye tana kallon Mufeeda a sace tana turo baki alamar bazata iya ba an takura mata, wani kallo Umma ta watsa mata ba shiri ta dubi Mufeedan data sunkuyar da kai ƙasa tana wasa da bakin hijabinta, sai data zabga mata uwar harara kafin ta ɗauke kai tana faɗin "Ya ƙarin haƙuri...Allah ya jiƙanta ya gafarta mata.." Ta faɗa a tare tana zama a kujerar dake falon.
A hankali Mufeeda ta ɗago ba tare da data kalli inda take ba tace "Alhamdulillahi...Momy mun gode Allah, Ameen na gode.." Ta faɗa ƙwalla na taruwa a cikin idanunta, janyota Goggo Abu tayi jikinta tana share mata hawaye, taɓe baki Farida tayi tana kallonsu kafin ta ɗauke kai tana sakin siririn tsaki.
Ranar a nan Umma ta kwana yayinda Abba kuma suka juya shida direba suka koma wanda sai ranar addu'an uku sannan zai dawo bayan anyi addu'an uku da safe sai su koma tare da Umma.
************
Yau akayi addu'an ukun Inna Fulera, bayan mutane duk sun watse yayi saura sai yasu yasu a gidan, suka taru dukkansu da Baba Hakimi da Goggo Abu da Innaro da Tahir da Ashe dasu Basma da Bassam sai Farida da Mufeeda da Umma da Abba.Sai Ishaq da Zahra da Suka zo Suma, Sai da suka haɗu gaba ɗayansu kafin Baba Hakimi yasa Tahir yayi addu'a aka shafa, sannan ya fuskanci Mufeeda wacce ke zaune a ƙasa ta duƙar da kanta ƙwalla na zubo mata, nan ya shiga yi mata nasiha sosai da nuna mata ta dinga yiwa mahaifiyarta addu'a ta daina mata kuka, kanta ta gyaɗa masa kafin ta ɗago tana share ƙwallar tausayin kanta.
Umma ce ta gyara zamanta tana kallon Abba take faɗin "Gata nan Alhaji ka tambayeta inda ta tafi tabar gidan mijinta da 'ya'yanta tsawon kwanaki bata gidan aurenta...ba tare da tazo gida ba, ba kuma tazo nan Ɗanbatta ba..." Ta faɗa tare da nuna masa Farida da tayi tsuru tsuru tana raba idanu, wani kallo Abba yayi mata yana faɗin "Au wato bayan mun tafi shine tabar gidan tayi wani guri, saboda bata ji maganar da mukayi mata ba..?" Gyaɗa kai Umma tayi tace "Ai kuwa babu abinda ta ɗauka a faɗan da akayi mata.." Ta faɗa tana kallon Farida.
Gizgiza kai Baba Hakimi yayi yana faɗin "A'a bafa kusan dalilinta na barin gidan ba, ƙila dai akwai abinda shi Attahirun yayi mata ne..." Da sauri Abba ya katseshi da faɗin "A'a Mansur, karka ce haka, ai yana gaba da ita, kuma ko ba haka ba ai mijinta ne shi, kuma kome zaice mata ai bai kamata ace tayi fushi tabar gidan ta tafi wani guri daban inda ba'a sani ba..."
Baba Hakimi na kallon Abba yace "Ka bari muji abinda ya faru a bakinta tukunna..ke Farida faɗa mana abinda Attahiru yayi miki da yasa kika bar gida..?" Ya faɗa yana kallonta, ƙara sunkuyar da kai tayi ta shiga rattabo abinda ya faru ranar bayan tafiyarsu tana haɗawa har da sharri tana ƙullawa, tunda ta fara maganar kawai Tahir ya girgiza kai yana sakin murmushi bai ce komai ba, har ta dasa aya...
A harzuƙe Abba yace "Wato a ranar da muka gama magana akai miki faɗa a ranar kika sake shuka wata tsiyar ko Farida..? To ki sani wallahi tallahi babu inda Mufeeda zataje tana nan zaune daram a gidan anan zata zauna ta haihu, sai dai ke kibar gidan don ubanki kije duk gidan ubanda zaki amma banda gidana, kuma wallahi duk ranar da kika sake fita kika je wani waje bada yawun mijinki ba ko kika fita saboda nuna kinfi ƙarfinsa Allah ya isa bamu yafe miki ba, tunda ke bazaki taɓa yin hankali ba..." Ya faɗa a zafafe yana sauke numfashi, sake rushewa da kuka Farida tayi har tana jan numfashi kamar zata shiɗe saboda baƙin ciki, nan Umma ma ta ƙara dasawa sukayi mata tass, abin mamaki Goggo Abu na zaune tayi laƙwas sai bin kowa da kallo kawai take ta kasa magana.
Baba Hakimi ma yayi mata faɗa sosai sannan ya haɗa har da Tahir shima yayi musu faɗa kafin ya ɗora da faɗin "Kiyi haƙuri Farida ki rungumi Mufeeda ki tausayawa rayuwarta, ki zauna da ita lafiya kinga marainiyace, ki ƙara riƙeta kamar yanda kika fara riƙeta ada..idan cikinta ya isa haihuwa watan ya tsaya Innaro zata zo can gidan naku ta zauna don ta riƙa kula da ita har ta haihu.." Ya faɗa yana ƙara lallashin Farida kan ta zauna lafiya da mijinta ta kula da 'ya'yanta.
Daga ƙarshe dai Baba Hakimi ya saka musu albarka tare da yi musu fatan alkhairi da gamawa lafiya dukkansu.
Nan Tahir ya matso gaban Abba ya duƙar da kai bai ce komai ba, lura da hakan da Abba yayi yasa yace "Me yake faruwa ne Tahir.? Ko akwai wata matsala ne kuma...?" Jinjina kai Tahir yayi alamar Eh.. Abba na gyara zama yace "Ka faɗa min ko mene ne Tahir insha Allahu indai inada dama Allah ya bani iko zanyi maka maganinsa..." Cikin jin daɗi Tahir ya ɗago yana faɗin "Dama Abba inaso ne ka roƙi Baba ya yafewa Goggo Abu.." Ya faɗa yana jin ƙwalla na taruwa a cikin idanunsa, saurin ɗagowa Abba yayi yana kallon Baba Hakimi, kafin yayi magana Baba Hakimi ya rigasa yana murmushi yace "Na riga na yafe mata duniya da lahira, Allah kuma ya yafe mana baki ɗaya ya kiyaye gaba.." Da Ameen duk suka amsa, kafin Tahir ya fara miƙewa Shida Ishaq suka fita daga ɗakin suka nufi ƙofar gida gurin Sauran Jama"an Dake Wajen Wadanda Suka zo Addu"arku Uku ba Dadewa sai ga Su Abba Suma Sun Fito Suna Tattaunawa shida Baba Hakimi.
A ranar Umma da Abba suka koma Kano, da yamma suma su Tahir da Farida da Iya da Mufeeda da yara duk suka tattara suka yi shirin komawa Kaduna, mota biyu sukayi Tahir da Farida da Mufeeda suka shiga motar Ishaq, su kuma Basma da Bassam suka shiga motar Tahir da Garzali ya tuƙo suka ɗauki hanya, bayan sun bar motar Farida a nan gidan Baba Hakimi akan washegari Garzali zai dawo ya ɗauka.
******
A hankali abubuwa suka fara daidaita, sai dai Farida tana tsananin kishin Mufeeda, amma tana ƙoƙarin dannewa bata son a gane, don irin tsantsar kulawar da Tahir ke nuna mata kwata kwata bata so, amma tana yi tana dannewa, bata so a gane tana jin haushi.
Haka a ɓangaren Tahir shima kwata kwata baya ganin hasken Farida, don ta gama sire masa gaba ɗaya a ransa, daurewa kawai yake yana nuna kulawarsa a kanta, kuma yana ƙoƙarin sauke hakkinta dake rataye a wuyansa, amma duk ɓoyewarsa sai data gane, don a komai ya ƙara canza mata sosai, kusan rabin kulawarsa gabaki ɗaya yanzu duk ya ɗorata akan Mufeeda ne.
A lokacin ne kuma su Mufeeda suka shiga Jss2 suna ci gaba da karatunsu, bata da matsalar komai ta ƙara wani kyau da haske, sai dai kusan kullum kafin tayi barci sai ta tuna da Innarta, idan tai kuka sai ta share hawayenta kuma tayi mata addu'a.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya wani lokaci aji daɗi wani lokacin kuma aji akasin haka,Farida Bata Kaunar Ta Bude Ido Taga Mufeeda da Ciki Acikin gidannan Tsoronta Daya ne Abba da Umma Tasan yanzu Abu kadan Zatayi Suyi Fushi da Ita Sosai,Abunda kuma ke karamata Kishin Mufeeda Shine ganin yadda Tahir ya Watsar da al"amarinta bai Cika damuwa da Al"amarinta ba,gasu Bassam Sun ki marata baya Sun bi Bayan Mahaifinsu,Haka Suke Kafa kafa da Mudeeda kamar su lasheta komai take bukata tana samu Koda yaushe Cikin Tallalinta Sukeyi.
Tuni Farida ta Watsar Da Shawaran Kawayen banza,Tunda Agroup Dinsu Billy Taje Tana bada Lbrin Zata kwatar mata yanci Ta gayamata mgana Ranta ya baci,ta Shiga group din Ta maida mata martani Tamata Wankan Tsaki Billy Tasan bata da gaskiya Sai ta kama kame kame,anan Akayita bata Hakuri Daga karshe Fitama Farida Tayi Daga Group Wasu Dadama Sun Bita Suna bata Hakuri Suna Fadamata Kowa Data gani Anan yana lallaba Aurensa ne,ba wani mai Sakaci,sai Lokacin Farida Tagane tayi Wauta babba..Wato Duk Acikinsu itace Sakarya Tayi Kuka Sosai kamar Ranta zai Fita Tayi Nadama sanda bashi da amfani,Tadaina Fita kwata kwata Wanda Ta gyara Domin Shi ko kallo bata Isheshi Ba Domin yafi Nuna kalawarsa Akan Mufeeda Fiye Da Ita,Abunda yasa Farida Rama kenan Atsaye Duk tayi Wani Zuruzuru Da Ita.
***********
*BAYAN WATA SHIDA*
Cikin Mufeeda ya ƙara fitowa sosai yayi girma gwanin ban tausayi, Tun yana Wata Hufu Tafara Zuwa Awo Anan Iyali Hospital,kuma shi yake kaita watarana In yana da Lokaci Ranar dai bai samu Zuwa ba sai Garzali ya kaita ita da Innaro,tsufan cikin nata ne, yasa Tahir ya hanata zuwa islamiya yace ta riƙa zama a gida makarantar boko zata rinƙa zuwa kaɗai, duk ranar da ba makaranta tana zaune a gida, hakan yana ƙona ran Farida sosai ya baƙanta mata zuciya, don ta tsani ganin cikin bata ƙaunar tayi tozali dashi kwata kwata a rayuwarta, jira take kawai Mufeedan ta haihu Tahir ɗin yasan nayi da ita.
Baba Hakimi ya cika alƙawari Tahir na sanar Dashi Cikin Mufeeda ya Cika Wata Tara yace ya Aiko Garzali ya Ɗauketa, nan da nan kuwa ya aikashi sai ga Innaro Ta Iso Abunda ya ƙara baƙantama Farida rai ganin Ɗakin Mufeeda Tahir yace A sauketa Suna Murna kamar ba Ɗan Shege za'a Haifa ba, Haka Tazo da Jiƙe jiƙe Saboda Maganin sanyi, Take Ta bama Mufeedan Ita da Iya ba'a san Wanda yafi Wani kula da Mufeedan ba, Goggo Abu kuwa Batama ta Farida yanzu Domin Da ƙyar ta samu bayan Abba ya saka Baki Hakimi ke Kulata Ko a hakan ba kamar baya ba, Shiyasa Take ƙoƙarin gyara Kuskuranta ta kuma Ƙudirci Wani Abu A ranta Jira kawai Take Allah ya Sauke Mufeedan lafiya Ta Aiwartar da Ƙudirinta Domin yanzu Tausayin Mufeedan Take Kullum Cikin Kira Take awayar Innaro Ana bama Mufeeda Tana Tambayanta Me take ji..? Wani Lokacin Dariya kawai Mufeeda keyi bata cewa komai Domin Yawanci Tambayan Tahir kenan Inya Shigo Dubata da Safe da Kuma bayan Ya Dawo ko Shi bata bashi Amsa sai dai ta Sunkuyar Da kai Aranta Tana Jin Daɗin yadda Daddy ya fara maida Jikinshi ba kamar Farkon Al'amarin ba.
Nanny(me reno) Free book ne amma ga waɗanda ba za su iya jira ba akwai completed documemt 1k ne ku tura ta wannan acct ɗin 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK ko tuntuɓar waɗannam lambobin ***
***.
*Janafty*
*Aisha Alto...*