20
*NANNY...!*
(Mai Reno..)
*Na*
*AISHA ALTO*
*JAMILA UMAR (Janafty)*
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.
*BABI NA ASHIRIN*
Ɓangaren Kayan Haihuwa Kuwa Babu Abunda Tahir bai gama Siya ba Kuɗi masu yawa ya Ware ya bama Matar Ishaq Zahra ta sayo komai da komai Kayan jariri kuwa komai Biyu ta Siyo na Mace Dana Namiji Tace Saboda Tahir bai yarda an mata Scanning ba, balle aga mai Zata Haifa.
Kuma Zahran Da kanta ta kawo Kayan Gidan, Abunda Ya ƙarama Farida Ciwo yanzu Har Takai matsayin da Bata da Wani amfani Wajen Tahir, ya maida kanshi dashi da 'yan'uwansa da Iyayensa Wajen Tattalin Mufeeda, Sai dai Tayi Wuni Cikin Ɗakinta Taita kuka bamai lallashinta Ita baga kulawan Miji ba Haka Zalika ma Su Bassam banda Gaisuwa babu Abunda Ke Haɗasu Koda yaushe Suna Ɗakin Mufeeda suda Iya da Innaro Wani Lokacin Tana Falo sai dai Tajiyo hirarsu Da Dariyansu Mufeeda kuwa Ko ta ganta ta gaisheta Farida bata amsawa Sai dai Ta bi Cikin Jikinta da kallo Cike Da Kishi ganin yadda yayi Girma yana Neman Rinjiyan Mufeedan, Burinta da Fatanta Allah Ya Sauke Mufeedan Lafiya ta ƙara gaba Allah barshi abunda Zata Haifa In Ta gama Shayarwa akaisa gidan Marayu Domin ba Wanda Zai Gurɓata mata 'ya'ya dana Shege
******
Yau ɗin takama Jumma'atu Babban Rana ce, Misalin ƙarfe 9 na Safe Duka suna Zaune A falo Suna Hira Innaro, Iya da Basma sai Bassam Dake wasa da Naila Wacce Take Tafiyanta yanzu Sai Mufeeda dake Zaune kasan Cafet Ta Buɗe ƙafa Hannayenta na Baya ta Dafa ƙasa Ga Cikinta nan Wani Randa guda yayi girma sosai har yayi ƙasa, Ta kumbura Ko'ina na Jikinta ya Buɗe ya ƙara Girma, In ka kalleta Farat Ɗaya kamar ba Mufeeda ba Domin Ta Cika Ciki ya sakata tazama ƙatuwa, su Basma suna Hutun Ƙarshen Shekara in suka koma zasu Shiga jss3 hadda kawai Suke Zuwa yanzu da Islamiya.
Aya ce agabanta Tana ci Tana Dariyan Labarin da Iya ke basu na Matar ƙaninta da Ta faɗa masai, Basma Saboda Dariya Harda Riƙe Ciki, Mufeeda ma Dariyan Take lokaci Ɗaya tana Cin Ayanta, Farida Data Sauko Daga Sama ta bisu da kallon Takaichi Da ƙyar ta iya Buɗe baki Ta gaida Innaro, Iya ta gaidata Hakama Su Basma Duk ta amsa amma Mufeeda na Gaisheta tayi kamar bata jiba ta Shige Kichen Abunta Mufeeda bata damu ba Domin Inda Sabo ta Saba da Hallayar Farida.
Ruwa ta Ɗauko Kafin Ta sake Haurawa Sama Ƙofar Bedroom D'in Tahir Tabi da kallo, Tun Jiya Daya Dawo Daga Lagos bai sake Fitowa ba, Buɗe Ƙofar tayi Ta Shiga ta Iskeshi kwance Cikin Bargo yana barci Ƙyalesa Tayi Ta Fito Daga Ɗakin Tana Tunanin gajiyace Domin Wajen Satinsu Daya achan Shida Ishaq ne Suka Tafi Taran Sabbin Motocinsu da Zasu zo ta Jirgin Ƙasa, Toh basu iso ba Sai Shekaran jiya Da Daddare Su kuma jiya suka taho Zuwa Kaduna.
Ɗakinta ta koma ta Sha Ruwa kana Ta Koma ta kwanta Tana Tunanin Da Zarar Mufeeda Ta Haihu Ta bar mata gida Zata gyara Duka mu'amalanta da Mijinta Harda 'ya'yanta Batasan Cewa Lokaci Tuni ya Ƙure mata ba.
Mufeeda Dake Dariya Ƙasa ƙasa, Taji kamar bayanta ya amsa Da Sauri ta gimtse Dariyan Tana jin Lokaci Ɗaya maranta ya Ƙulle, Cije baki tayi ganin ba Wanda ya lura da Halin Data ke ciki Ta Dafa Kujeran Ta Miƙe A hankali Tana Cije baki Lokaci Ɗaya Innaro da Iya Suka kalleta kafin Innaro taceb"Mufeeda lafiya..? Ina zaki Haka..?"
Saurin Sakin Murmushi Tayi kafin tace "Bakomai Innaro Toilet zan Shiga.." Innaro tace "Ayyah..Jeki Dawo.." Ta faɗa Tana kallonta da Sauri Mufeeda ta Fara Taku Zuwa Ɗakinta Tana Daurewa amma Fa Cijewa kawai take saboda yadda Ƙugunta ya Riƙe ga Maranta ta Ƙulle Waje Ɗaya,bHar ta Shige Ɗakinta Innaro na Binta da kallo kamar tana so Ta Ɗago Wani Abu...
Mufeeda Da ƙyar Ta iya kai kanta Tsakiyar Ɗakinta kafin ta Durƙushe Tana Riƙe gadon Hannu Biyu Jin Ƙugunta kamar zai Tsage gida Biyu, Zufa ce ke Keto mata kamar Wacce Ake Gasawa Salati Mufeeda ke Saki Cikin Ranta Lokaci Ɗaya Hawaye na Wanke mata Fuska ko Bata sani ba Wannan Azaban Data keji Ta Gane Naƙuda ce, Tun Abun na Ƙasa ƙasa Har ya gagari Tunanin Mufeeda Kuka Take Wurjajan da Majina Domin Tagama Yanke Kauna wallahi Mutuwa Zatayi domin Wannan Azaba Ta mutuwa ce.
Innaro ce Taga Shirun na Mufeeda Yayi yasa Ta kalli Basma Tana Faɗin "Ke Basma Maza Tashi ki Dubo min Mufeeda najita Shiru ne.." Da Hanzari Basma Ta Miƙe Ta Nufi Ɗakin Mufeeda Halin Data Tarar da ita ya bata Tsoro Cikin Firgici Tace "Innaro kuzo kuga Mufeeda.." Ta fada da Ƙarfi Jin Haka yasa Innaro da Iya Suka fara Rige Rigen Shiga Ɗakin Mufeeda Hankalinsu a Tashe, Bassam Dai Naila ya Ɗauka Wacce Ta Fashe da Kuka lokaci Ɗaya bai bisu Ɗakin ba ya dai Tsaya A falon yana Tunanin ko lafiya...
Kallo Ɗaya Innaro Tama Mufeeda Ta Fahimci Tana kan Gwiwa Basma Ta kallah Wacce Har Ta fara Hawayen Tausayin Mufeeda tace "Maza kije ki kira min Daddynki.." Da gudu Basma Ta Fita ta Haura sama Tahir na kwance Cikin Barci Yaji Basma na Faɗin "Daddy Daddy...Ka Tashi Innaro na Kira Mufeeda Zata Haihu Tana ta kuka.." Take Faɗa Tana Kuka Itama.
Zumbur ya Miƙe Daga Kwancen Yana Kallon Basma Ido ya Zaro yana Faɗin "Zata Haihu kika ce Basma..?" Kai ta gyaɗa mai tana Share Ƙwallah da Hanzari ya Dirko Daga kan gadon Da gashi sai Dogon Wando Jallabiyansa ya Laluba ya saka ya zari Key ɗin Mota ya Fita Da Sauri Basma Tabi Bayanshi Fitowarsu Da Hanzari ya Fito Da Farida Daga Ɗaki Ganin Tahir da gudu ya Sauka Ƙasa yasa Itama Tabi Bayansu da Sauri Tana mamakin Me ya Razana Tahir Lokaci Ɗaya Haka..?
Tahir ko na Shiga Ɗakin Mufeeda Yaga ba yarda Take Innaro na mai magana bai Saurareta ba kawai ya Cicciɓi Mufeeda Zuwa Waje yana Faɗin "Innaro ki Ɗauki Mayafi mutafi Asibiti.." Farida Dake Ƙoƙarin Shiga Ɗakin Mufeeda Tayi Baya ganin Tahir ya Ɗauko Mufeeda Tana Faman kuka tana Yarfa Hannu, suman Tsaye Tayi Cike Da Takaichi da Kishi Wai Tahir ne ya Ɗauki Mufeeda da Hannunsa Niko Nace Yamata Cikin ma balle Ɗauka.
Bata gama Mamaki ba Iya da Innaro Da Suka Rufa mai baya Da Gudu Mayafai A hannu Saboda Zullumi sai ga Basma Ita ma da Hijabi Ta Runtuma tabi Bayansu, baki ta Riƙe Cike da Baƙin ciki Lokaci Ɗaya kuma Falon ya ƙara Ɗaukan Kukan Naila, Daga Nailan Har Bassam D'in Da Harara Ta Bisu kafin Ta Saki Tsaki ta koma Sama Tana Ƙunƙuni Ita kaɗai.
Tahir ko Garzali bai Saurara ba ya Kai Mufeeda Bayan Mota, Ya Dawo Gidan Gaba Mazaunin Direba ko Su Innaro Dake Fitowa Haraban Gidan bai Jira ba ya Kunna Mota yayi Reverse da Ƙarfi lokaci Ɗaya ya saki Hon ya Fice Da Gudu, Su Innaro basu Tsaya ba Suka Faɗa Mota Basma Ta Shiga Gaba Innaro Tace "Garzali bi mana bayan Attahiru..." Cikin Bin Umarni Garzali yaja mota Yabi Bayan Tahir Daya Nufi Asibitin Iyali Hospital Dake Kusa Dasu.
****
Koda Tahir ya gama Faka Motarsa Cikin Haraban Asibitin Bai Jira Wani ba, Ya Fito Daga Mota ya Buɗe Baya ya Cicciɓo Mufeeda Dake kuka Wurjajan Lokaci Ɗaya Da Salati Domin Ji Take kamar Zata mutu da Gudu ya Nufi Cikin Asibitin Da Ita ganinshi Haka ne ya saka Nurses Da Gudu suka gungoro Gadon Ɗaukan Marasa Lafiya Zuwa Gareshi ganin kamar ya Fita Daga Hayyacinsa yana Kiran Likita.
Kan Gadon ya Ɗora ta da Hanzari Suka Shiga Turata yana Bin Bayansu cikin Tashin Hankali Labour Room Suka Shiga da Ita Suka Rufo ƙofa Dole Tahir ya Tsaya Awaje yana Safa da Marwa sai ga Su Innaro Sun Shigo Asibitin Hankalinsu Tashe Cikin Fargici Innaro Tace "Attahiru Ya Ake Ciki...?" Numfashi ya Sauke yana Faɗin "Bansani ba Innaro Sun Dai Shiga da Ita Ciki..." Gefe Suka Koma kowa na Addu'a Cikin Ransa Basma ko Hawaye Take Sharewa Suna nan Tsaye Wata Nurse Ta fito da Gudu Ta Wuce Office d'in Likita, Sai gashi Sun Fito A tare Cikin Hanzari Sun Koma Cikin Ɗakin Daga Wajen Suna Jin Salatin Mufeeda Da Kukanta Lokaci Ɗaya Tahir yaji Jikinsa ya Saki Ƙwalla Ta Cika mai ido yana Fatan Allah ya Sauki Yarinyar nan lafiya kada ta Mutu Da Cikin nan ya Shiga Uku.
Tsawon Awa Ɗaya Likitoci na Shige da Fice kan Mufeeda Haihuwa Shiru nan da nan Suka mata Scanning Nan Suka gano yan Biyu ne A cikinta amma Sun Galabaita, yunƙurin Fitowarsu da kansu Matsala ne, Nan da nan Wani Likita ya Fito Yana Faɗin "Ina Mijinta...?" Da Hanzari Tahir ya Isa Gabanshi yana Faɗin "Gani Dr..Hop ta Sauka lafiya.." Kai ya girgiza mai kafin yace "Biyoni Office da Sauri bamu da Lokaci.." Jin Haka yasa ya bishi da Hanzari, Zuwa Cikin Office Ɗinshi Suna Shiga Ciki ko zama baiyi ba ya Miƙa mai Wata Takarda yana Faɗin "Muna Buƙatar saka Hannunka anan, zamu Shiga da Ita Aiki ne yanzu Domin Ceto Rayuwarta data yaran Dake Cikinta.." Tahir na Zufa ya karɓa Takardan Haɗe da Biron ya Rattaba Hannu, kafin Likitan ya karɓa yana miƙa mai Wata ƙaramar Takarda yana Faɗin "Ka biya Kuɗin Aiki yanzu..." Tahir bai Tsaya ba ya Fito da Sauri su Innaro Dake Zaune Suka miƙe Suna kallonshi Kanshi ya Shafa yana Faɗin "Sun ce aiki zasu mata yanzu...Ku zauna anan Bari naje na Biya Kuɗin Aikin Na Dawo.." Innaro tace "Toh kana da Kuɗi A hannunka..?"
Yana Tafiya yake Faɗin "A'a Sai dai Atm ɗina zanyi Amfani Dashi.." Ya faɗa yana Ƙara Sauri Cikin Minti goma Sai gashi ya Dawo da Resit ya Riga ya Biya Kuɗin Aikin bai Daɗe da Isowa Wajen ba Sai ga Mufeeda An Gungurota Zuwa Ɗakin Tiyata an Chanza mata kaya, Kuka Take da Salati Lokaci Ɗaya Suna kallo Aka Shiga Da Ita Gefe Suka koma Kowa Da kalan Addu'an Dake Ranshi barin ma Tahir da Abun Duniya Suka Taru Suka mai yawa...
Shuɗewar Awa Biyu Kafin wasu Nurses Guda Biyu Su Fito Daga Ɗakin Tiyatan Ɗauke da Yara Guda Biyu Cikin Wasu Showels, da Hanzari Suka miƙe Suna kallonsu Cikin Fara'a Ɗaya Tace "Congratulation ta Sauka An Samu Twins, mace da Namiji..." Gaba ɗayansu Suka Haɗa baki Wajen Faɗin "Alhamdulillah." Innaro Ta karɓi Namijin Iya kuma Ta karɓi Macen Dukkansu bakinsu yaƙi Rufuwa Shiko Tahir Hamdala yake Acikin Ranshi kafin yace "Ina ita Maman Yaran..?" hope tana lafiya.." Ɗayar tace "Eh ana gyarata ne da Zarar an kammalah zamu maidata Ɗakin Hutu.." Daga Haka Suka Wuce, Chan sai ga Likitocin Suma Sun Fito Suna Cire Safan Hannu, Musabaha sukayi da Tahir Suna mai Murna, Bakin kowa yaƙi Rufuwa, Bai Ɗauki yaran ba Domin Wani Tausayinsu ne ya Tsirga mai na Ya samar Dasu Ta Hanyar da bai dace ba, Ashe Dalilin Daya sa ya Afkama Mufeeda Kenan Rabon samun Waɗannan ne ya Kawo Haka.
Ba ɓata Lokaci aka Gunguro Mufeeda Zuwa Ɗaki na Mussaman Domin Hutu, Suka ce Kar wanda ya Shiga Inda Take Sai ta Farfaɗo bayan Awa biyu da wani Abu, Yanzu aje azo da kayan Jarirai da Kayan Tea d'in da Mai Jego zata Buƙata in ta Farfaɗo, Tahir ne ya barsu anan ya Koma gida, Farida na Jin Dirin Mota ta Zabura ta Fito Falo Suka Ci karo da Tahir Cikin Rawan Baki Tace "Ta Haihu..?"
Bai kalleta ba yace "Eh amma C.s Aka mata an Ciro 'Yara Biyu mace da Namiji.." Dafe ƙirji Farida Tayi kafin Tace " 'Yan biyu fa kace...?" Ta faɗa Tana kallonsa Bai mata magana ba illah binta da Kallo Da yayi kafin yace "Eh Abunda Kunnenki ya jiye miki..." daga Haka ya Wuceta ya Barta sama ya Koma ya Ɗauko Wayarsa ya Sauko, Ɗakin Mufeeda ya Shiga Inda ya Tatarro Duka kayan Babies, Sai kuma Dogayen Riguna da Riga da Zani, ya Fito Nan ya Wuce Farida Tsakiyar Falon Tana Binshi da Kallo, Bassam ne ya Biyosa yana Tambayansa Mufeeda Ta Haihu Cike da Fara'a Tahir ya Ɗaga mai kai kafin yace "Kun samu ƙanne Bassam 'Yan'uwanku ne Twince ne Suma.." Washe Baki Bassam yayi Harda Tsalle yana Faɗin "Daddy Zan Bika.." Bai ce mai komai ba sai ma Miƙa mai Jakar Kayan Mufeeda da yayi Suka Fice Daga Falon.
Sai da Tahir ya kawo Kayan Kana Aka maida Yaran Ciki aka Sake Gyarasu aka Shiryasu Cikin kayan Sanyi pick masu kyau Ɗakin da Mufeeda Suke Suka maidasu, suka ce suma abarsu Su Huta Haka nan, Bakin Basma da Bassam yaƙi Rufuwa saboda Murna Sai Lokacin Tahir ya samu Damar Kiran Baba Hakimi yake Sanar Dashi Baba Hakimi Dake Shirin Fita Sallar Azahar ya Washe Baki yana Faɗin "Kai Masha Allahu...Allah ya inganta.." Daga nan Abba ya Kira Shima ya Sanar Dashi, Shima ya Saka albarka, Daga Abba sai ya Kira Ishaq ya Sanar mai, Wanda ke Zuba kabbara Cikin Waya kafin Kace me Haihuwan Mufeeda Ta isa Kunnan Wanda ya kamata Farin ciki kamar bata Gurɓattaciyar Hanya aka samesu ba.
****
Baba Hakimi Na gama Waya da Tahir ya Shiga Cikin Turakarsa ya Ɗauko Huhun Goro da Dabino Cikin Wata Leda Waje ya Fita Zuwa Masallacin Kusa da gidan nashi Lokacin Har An Tada Sallar Jumma'a Domin Babban Masallaci ne Wanda ke Jikin Gidan nashi Inda Suke Gudanar da Sallar Jumma'a.
Bayan An idar da Sallah Baba Hakimi Ya bada Sanarwan Akwai ɗaurin Aure nan da nan ko Kowa ya Matso kuɗi ya Fito Dashi Duba 30k ya bama Liman yana Faɗin "Ina so kazama Wakilin Ɗana Tahir, ni kuma zan zama Wakilin Mufeeda A Ɗaura musu Aure.." Liman ya Washe baki ba tare Da bata Lokaci ba nan Take Shaidu Suka Shaida Ɗaurin Auren Tahir Mansur Ɗanbatta da Mufeeda Bello Ɗanbatta, Auren Daya bama Kowa Mamaki Domin Mutane Da dama Sun san Mufeeda A matsayin Wacce ke Reno A gidan Tahir, Cikin Fari ciki Taro ya Watse bayan an Raba Goro da Dabino Baba Hakimi ya ɗibi Wasu ya Shiga Dasu Cikin Gida Har Ɗakin Goggo Abu Wacce ke Cike da Murnan Wayar Da Tahir ya mata yanzu Yana sanar da Ita Haihuwan Mufeeda, goro da Minti ya miƙa mata yana Fadin "Na Ɗaura ma Tahir Aure da Mufeeda Yanzu bayan Mun Sauko Daga Sallar Jumma'a..." Baki Goggo Ta Washe kafin tace "Mallam kamar kasan Abunda Ke Raina kenan...Allah ya basu zaman lafiya.." Da Ameen ya amsa Cikin Jin Daɗin Haɗin kanta Duk Da yasan bazai Samu Matsala ba.
******
Har Yammah Su Innaro na Asibitin Sun cika Ɗakin da Mufeeda Take bayan ta Farfaɗo, Basma da Bassam Sun ƙanƙame yara Ko Tahir basu Bari ya Ɗauka ba, sai da Innaro ta karɓe Macen Ta Hannun Basma Ta Miƙa mai ya karɓa Cikin Jin kunya Lokaci Ɗaya yana Tsurama Jaririyar Ido Sak Basma Tana Jaririya, Lokaci Guda Idanuwansa Suka kawo kwallah yayi Saurin Mayar Dasu Mufeeda Dake Jingine da Gado Tana kallonshi yana Dagowa Suka Haɗa ido sai tayi Saurin Kauda kai Murmushi yayi ya ƙarasa Kusa da Ita yana Faɗin "Mufee ya Jikin..?" Kanta na Ƙasa Tace "Da Ɗauki Daddy..." Kai ya gyaɗa kafin yace "Masha Allah...Allah ya ƙara baki lafiya.." Da Ameen Ta amsa Ƙasa ƙasa, kan Jikinta ya Ɗora mata Jaririyan Yana Faɗin "Kina Sonta...?" Kallonsa Tayi kafin tace "Kaifa kana Sonsu...?" Kai ya Gyaɗa mata kafin yace "Ina sonsu Sosai kuma Zan Cigaba da Ƙaunarsu Har Ƙarshen rayuwata.." Murmushi Ta Saki kafin tace "Nima ina sonsu...." Dariya yayi yana kallonta kafin ya Miƙa Hannu ya karɓi na Hannun Bassam ya Ɗora mata Bisa Jikinta yana Ƙoƙarin Zama Kusa Da ita Wayarsa ta Shiga Ƙara Miƙewa yayi ya Zarota Ciki Aljihu sai yaga Hakimi ne Da Hanzari ya Fice Mufeeda ta Bisa da Kallo Cikin Wani yanayi.
Fita yayi Haraban Asibitin kana Ya Ɗaga Kiran Cikin Farin ciki Baba Hakimi yace "Ya Wajen Maijegon da Sabuwar Amarya don bazan Tambayi sabon Megidan Salamatu ba Tunkafin ya Fito Duniya Take Nuna min Son kai.." Dariya Tahir yayi kafin yace "Duk Suna lafiya Ranka ya Daɗe.." Baba Hakimi yace "Madallah kafin ya Zarce da Faɗin "Attahiru na yanke Wani Hukunci ba tare Da nayi Shawara Da kai ba Domin ina ganin Hakan Shine Daidai.." Tahir ya Jinjina kai yana Faɗin "Ka isa ne Ranka ya Daɗe kowani Hukunci ne zan karɓa Hannaye Bibbiyu.." Baba Hakimi ya saki Murmushin Jin Daɗi yana Faɗin "naji Daɗin Haka ba Komai Illah Ɗazu bayan sallar Jumma'a Na Ɗaura maka Aure da Mufeeda yanzu Haka tana Matsayin Matarka ne Attahiru..Bata da wanda ya fika ku Haɗu ku Rungumi 'ya'yanku Karsu Tashi suga bakwa Tare Su Tuhume ku Wata rana.." Ajiyar Zuciya Tahir ya Sauke kafin yace "Hakane Baba...Allah ya bani ikon Adalci.." Da Ameen Baba Ya amsa kafin Su yanke Kiran Bayan Baba Hakimi ya tabbatar mai Suna Tafe ko yaushe.
Bai koma Cikin Asibitin ba yayi Tsaye yana Tunanin Wannan Al'amarin Guda Biyu Lokaci Ɗaya Haihuwa da Aure, Dafe kansa yayi yana Faɗin "Alhamdulillah...Allah ne Abun Godiya.." Yana Cikin Wannan Halin ya hangi motar Ishaq Ta Shigo Cikin Asibitin Bai Matsa daga Wajen Ba Har Suka ƙaraso Shida Zahra ta gaisheshi Bayan Ta mai barka, Shi ya musu Jagora zuwa cikin Ɗakin Suka Gaida Mufeeda Suka kuma Ɗauki Yaran Bayan Sun gaisa da su Innaro Nan Suka bar Zahra Tahir yaja Ishaq suka Fita Waje Cikin Damuwa ya labarta mai Abunda Baba Hakimi ya Kirasa ya gaya mai Baki Ishaq ya Washe kafin yace "Finally...Baba Hakimi ya gama maka Komai Friend...Mufeeda Ta Chanchanci Haka Domin Bata da Wani Gata Nan Duniya bayan kai...Gaskiya Allah sakama Baba Hakimi da alheri Yayi Abunda ya Dace.." Tahir dai Shiru yayi yana Jin Ishaq Shi kuma yana Cigaba da Bashi baki basu koma Cikin Ɗakin ba sai da Sukayi sallar Mangariba, suna komawa Tahir yace Su Basma Su Shirya su Koma gida, Harda Iya gobe da Safe sai su Dawo Innaro kaɗai Aka bari zata kwana da Mufeeda, Zahra tayi musu sallama Bayan ta ijiye musu kwandon Abincin Da tazo Dashi. Tare Suka Fita Bayan Tahir yayi musu Sai da Safe Mufeeda kuwa na Kwance Tana Binsu da kallo har Suka Fice Daga Ɗakin.
Nanny(me reno) Free book ne amma ga waɗanda ba za su iya jira ba akwai completed documemt 1k ne ku tura ta wannan acct ɗin 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK ko tuntuɓar waɗannam lambobin ***
***.
*Janafty*
*Aisha Alto..*