SAUTIN KARSHE

Chapter 14

by @amanarcool323

Shiru ba ta motsa ba. Tsura mata ido ya yi yana kallon fuskarta cikin yanayi na tashin hankali, ƙare mata kallo ya yi da kyau. Ya tabbatar da babu rai a jikinta, wani abu mai ɗaci ya tokare masa ƙarji. A hankali ya kwantar da ita ya sa hannunsa ya shafe mata fuska, ka sa ɗauke hannunsa ya yi daga saman fuskarta, kallon abin yake yi kamar ba gaskiya ba ne. Ya daɗe zaune a gurin yana kallonta ƙwaƙwaran motsi ya kasa. Ajiyar zuciya ya sauke. Ya furzar da iska mai zafi, ya ɗakko zani ya rufe ta, jiki a sanyaye ya tashi ya fita waje, tsayawa ya yi yana kallon Abida da ta fara bacci, runtse idonsa ya yi yana jin wani irin raɗaɗi da zafi a cikin zuciyarsa. Ɗakin Inna ya shiga, tana zaune saman darduma tana lazimi, Ma'u kuma na kwance a inda ta idar da sallah. Da sallama ya shiga ɗakin, yanayin yadda Inna ta ji muryarsa sai da gabanta ya faɗi. Zama ya yi a bakin ƙaramin gadon ƙarfen dake cikin ɗakin, Inna ta ce "Gadanga yaushe ka dawo? Ai na yi tunanin ma sai gobe za ka dawo da na ga har magariba ta yi ba ka shigo ba". Aliyu ka sa magana ya yi, jin shiru bai yi magana ba ya sa Inna ta haske shi da fitilar hannunta tana faɗin "Gadanga lafiya kuwa? Me yake faruwa ne ina yi maka magana ka yi shir...?" Yanayin yadda taga fuskarsa ne ya sa ta kasa ƙarasa maganar. Duk da hasken dake cikin ɗakin kasa kashe fitilar ta yi ta bar ta a kunne, "Me kuma ya sake faruwa?" Inna ta sake tambayarsa cikin sanyin jiki. 

"Inna Halima ta rasu!" shi ne kawai abin da ya iya faɗa. Shiru ta yi tana nazarin a cikin danginsu na ƙauye wake da suna Halima. Da ta ga ta kasa fahimta sai ta ce "Wace Halimar ce ta rasu, na kasa tuna wake da wannan sunan a ƙauye?". 

Ɗagowa ya yi ya dube ta da rinannun idanunsa ya ce "Halima ta nan gidan". A zabure Inna ta ce "Ƙalu Innalillahi wa inna ilaihim raji'un, Gadanga wace irin magana ce kake faɗa haka mara daɗin ji? Halimar da tare muka yi alwala da ita ta shiga ɗakinta za ta yi sallah shi ne ka ke cewa ta rasu?". 

"Inna ki yi istigifari, a cikin second ɗaya idan Allah ya so zai ɗauki ran bawansa, bawa shi ne yake ɗaukar kansa wata tsiyar, amma a gurin Ubangiji idan ya tashi ɗaukar ransa ba a bakin komai yake ba". 

"Innalillahi wa inna ilaihim raji'un, wayyo Allahna Aunty Halima don Allah kar ki mutu". Suka ji Ma'u ta yi maganar tana fashewa da kuka. Tashi Inna ta yi da sauri ta fita waje, ɗakin Halima ta shiga, nan ta tarar da ita a kwance. Gabanta ne ya faɗi, ganinta rufe da zani. Da sauri ta ƙarasa ta buɗe zanin daidai fuskarta. "Innalillahi wa inna ilaihim raji'un, innalillahi wa inna ilaihim raji'un, innalillahi wa inna ilaihim raji'un, Allahu Akbar, Allah ya jiƙanki da rahama Halima, Allah ya yafe miki kura-kuranki, Ubangiji ya sa mutuwa hutu ce a gare ki, ina fatan halinki na gari ya bi ki". Inna ta kai ƙarshen maganar hawaye masu zafi na zubo mata. Tashi ta yi ta fita daga ɗakin, Aliyu ta gani a tsaye ya jingina jikinsa da gini yana kallon Abida. A lokacin har an fara kiran sallar isha, Inna ta dube shi cike da tausayi ta ce "Ka yi haƙuri Gadanga, haƙiƙa mun yi babban rashi a gidan nan, Allah Sarki Halima mutuniyar kirki. Yanzu me ye abin yi?". 

Muryarsa har ba ta fita sosai saboda damuwa da tashin hankali, ya ce "Yanzu zan je masallaci, na san zan haɗu da Yayanta sai na sanar masa". 

"To shikenan sai ka hanzarta". Ba tare da ya sake yin magana ba ya bar gidan. Inna ta zauna a kusa da Abida tana kallonta cikin tausayi ta ce "Allah Sarki Abida, kina da shekaru goma a duniya Allah ya ɗauki ran mahaifiyarki". Ta yi maganar wasu hawayen na sake zubo mata. Ma'u kuwa na can ɗaki tana gunjin kuka kamar wata ƙaramar yarinya.

Tun a dare labarin rasuwar Halima ya zagaye dangi da jama'ar unguwa. Duk wanda ya ji labarin rasuwarta sai ya girgiza, saboda mace ce mai haƙuri da yawan fara'a, ga ta da girmama jama'a. A daren aka yi mata sitira sai dai aka ce jana'izarta sai gobe. 
Haka gidan suka kwana cikin damuwa da tashin hankali, musamman ma Aliyu da yadda ya ga rana haka ya ga dare. Washe gari ƙarfe takwas da rabi aka sada ta da gidanta na gaskiya. Sai a lokacin ne Abida ta fahimci abin da yake faruwa. Duk da ƙarancin shekaruta sosai ta shiga tashin hankali. Duk wanda ya ga halin da take ciki sai ya zubar mata da ƙwalla, haka dai jami'ar gidan da masu zaman makoki suka kasance cikin damuwa.

****

Babbar mace ce zaune a cikin katafaren falonta, ta yi shiga ta alfarma, kallo ɗaya za ka yi mata ka san hutu da jin daɗi sun gama ratsa ta. Lissafi take yi na kayan lefen da za a haɗo mata, kira ne ya shigo wayarta, cikin isa da gadara ta ɗaga kiran tana faɗin "Hello Hajiya Zulai ya kike?". 

Daga can cikin wayar aka ce "Lafiya ƙalau Alhamdulillah ƙawata, ya gida ya shirye-shiryen biki?". 

Matar ta amsa da "Alhamdulillah, gashi nan muna ta yi". 

Hajiya Zulai ta ce "Ma sha Allah, Allah ya taimaka" ta ɗora da faɗin "Da ma wani labari ne na zo miki da shi, sai dai ban san yadda za ki ɗauki abin ba, amma sanin halinki da na yi, da kuma ra'ayinki ya sa na ga ya dace in sanar da ke, saboda idan na ɓoye miki tamkar na ci amanarki ne". Hajiya Amina da ta ƙosa ta ji me a ka zo ma ta da shi ta ce "Yi sauri ki sanar da ni Hajiya Zulai, kin san ba na son jira". 

Hajiya Zulai ta ce "Da ma wani labari ne na jiyo, kuma a majiya mai ƙarfi na ji shi, wai matar da ake ƙoƙarin aurawa Saddik ba ta sonsa auren dole ne za a yi mata. Kin san Hajiya Munira muna mutunci da ita, ita ce da kanta ta sanar da ni cewar ita ta tursasawa yarinyar ta amince da auren, saboda ta gaji da bibiyar da take yi wa ɗan'uwanta yana wulaƙanta ta, wai ashe ita yarinyar Yayanta take so, ɗan gidan wan mahaifinta shi kuma ba ya sonta, shi ne uwarta ke son raba ta da shi, shi ya sa ta tilasta mata ta amince da auren Saddik, amma wallahi yarinyar ba ta sonsa. Sai kin ganta da na je gidan, kallo ɗaya za ka yi mata ka san cewar tana cikin damuwa da tashin hankali". 

Ashar Hajiya Amina ta yi, ta ce "Ni za a yaudara? A ci amanar yarona a haɗa shi da yarinyar da ba ta ƙaunarsa? Shi kaɗai nake da shi salon ta zo ta kashe mini yaro? To wallahi ba zai yiwu ba, aure saura kwana goma za a zo mini da zancen banza, ba da ni za a yi wannan abin ba, idan har na bincika na tabbatar da maganar nan gaskiya ce, na rantse da Allah ba za a yi auren nan ba". 
Hajiya Zulai ta ce "Da kyau ƙawata, wallahi gaskiya nake faɗa miki, amma dai ki ƙara bincikawa ki ji". Godiya Hajiya Amina ta yi mata, sannan suka yi sallama, nan ta ajiye batun lissafin da take yi ta shiga surfa masifa. 

****

Ba ƙaramar rama Ilham ta yi ba, kullum tana kwance a ɗaki ba ta da aikin da ya wuce kuka, Momy na ankare da ita amma ta yi share ta, a cewar ta idan aka yi aure duk za ta daina wannan abin. Lokacin da Dady ya ganta, ganin irin ramar da ta yi ya sa shi tambayarta "Ko dai ba ta da lafiya ne?". Ta ce "Eh Dady ina fama da ciwon kai ne". 

Dady ya ce "Subhanallah, shi ne ya ramar da ke haka? To kin je asibiti ne?". 

Jinjina masa kai ta yi alamar eh, bayan ya bar falon Momy ta ce "Ilham kenan, na san ba wani ciwo da yake damunki, kin ka sa haƙura ne ki cire wannan yaron a ranki. Yaron da ba ma take yake ba, amma ke kina neman kashe kanki a kansa, aure ne dai tsakaninki da Saddik babu fashi" cikin kuka Ilham ta ce "Wallahi Momy ba na sonsa, don Allah kar ki bari a aura min..." "Rufe mini baki ko na makeki a gurin nan" Momy ta katse ta, ta ci gaba da faɗin "Shashashar banza marar sanin ciwon kai, to ki bari idan a ka kai ki gidan kar ki zauna". Tashi ta yi ta koma ɗakinta tana kuka mai cin rai. Nan ta bar Momy ta shiga mitar ta ita kaɗai.

****

Kaɗan-kaɗan ta fara sakin jiki da jama'ar gidan. Duk da kwana biyu sun shiga cikin tashin hankali na rashin jama'ar da aka yi a garin. Zaune take ita kaɗai saman tabarma tana kallon Amir dake wasa da yaran maƙota, sai Inna Lantana dake duƙe a bakin murhu tana hura wuta. Baba Rabe ne ya shigo gidan da sallama, Inna Lantana ta amsa tare da yi masa sannu da zuwa. Zama ya yi saman tabarmar da take zaune yana faɗin "A'a ƴar Baba yau an fito waje?".

Murmushi ta yi ta ce "Eh Baba sannu da zuwa, ya kuma a ka ji da haƙuri?". 

Ya ce "Yawwa sannu, haƙuri Alhamdulillahi da godiya". Ta ce "To Allah ya jiƙansu da rahama, ya sa can ta fiye musu nan" ya amsa da "Amin". Ya na bin su Amir da kallo. Ya na so ya yi mata tambayoyi sai dai yana gudun ta fara yi masa kuka, hakan ya sa shi ya ƙyale ta ya tashi ya ɗauki buta ya shiga banɗaki. 

****

Sudais tun yana gajiya da kiran da Zuhura take zaman yi masa har ya zo ya fara sabawa, kullum sai ta kira shi, tana yi masa iyayi da shagwaɓa kala-kala, sai dai ya yi shiru yana saurarenta, daga "Hmmm, sai Umm" yake ce mata, haka za ta yi ta zubarta har ta gaji ta yi masa sallama. Ba laifi Zuhura kyakkyawa ce, kuma tana da sura mai kyau da ɗaukar hankali, sai dai shi ba wannan ne a gabansa ba. Zai kula ta ne kawai saboda yana jin kunyar mahaifinta. Amma ba don wani abu ba. A yanzu auren Ilham ne a gabansa, yarinyar tana ba shi tausayi sosai, bai son a aura mata wanda ba ta so, ya fi so a bari har ta samu wanda zuciyarta za ta kwanta da shi. Wanda zai iya canza mata ra'ayi, ya ɗauke hankalinta daga zancen sonsa ta take iƙirarin tana yi. Sai dai kashh, ba wata hanyar da zai bi domin ganin ya taimaka mata a fasa wannan auren, ya san idan ya yi wa Uncle magana zai amince, to amma bai son ta samu matsala da mahaifiyarta, tun da ita tana son auren. Haka dai yake zama kullum da tunanin abin a ransa ya rasa yadda zai ɓullowa lamarin. 

****

Gidansu Ma'u yau aka yi sadakar bakwai, har wata ƴar rama Aliyu ya yi. Duk dauriyarsa da jurumtarsa kallo ɗaya za ka yi masa ka ga raunin da ya bayyana a saman fuskarsa, mutuwar Halima ba ƙaramin shigarsa ta yi ba, tun da lamarin ya faru bai san ya kwanta ya yi bacci ba. Kullum tunaninsa wane irin ciwo ne haka da ya yi ajalinta lokaci ɗaya. A cikin kwanakin nan sau uku Jamila tana zuwa gidan gurin Ma'u, idan ta zo sosai take nuna tsantsar kulawarta ga Abida. 

Inna idan taga Aliyu ya yi shiru, zaunar da shi take yi ta yi masa nasiha mai shiga jiki. Da nuna masa muhimmancin haƙuri. 

Washe gari Ma'u ta koma makaranta, saboda tun da abin nan ya faru da ita ba ta sake fita ko ina ba. Sai ga wannan rasuwar an yi, dole ta ci gaba da zama a gida, damuwa biyu ta haɗe mata lokaci ɗaya. 
Da ta je makaranta ƴan ajinsu da sauran yaran makaranta suka dinga yi mata jajen abin da ya same ta, tare da yi mata gaisuwar rasuwar da aka yi musu. 

Bayan an tashi suna tafiya a hanya ita da Jamila, Jamila ta ce "Allah Sarki Aunty Halima, Allah ya sa kin huta, mace mai haƙuri da kawaici, ashe Allah bai ƙaddari zan yi zaman kishi da ita ba". 

Ma'u ta kalle ta ba ta ce mata komai ba. Ita ma shiru ta yi ba ta sake magana ba, sai da suka zo gurin da za su rabu sannan Jamila ta ce "Ma'u don Allah ki gaisar mini da masoyina, kuma ki ci gaba da kular mini da ƴata Abida kafin na zo". 

Cikin hasala Ma'u ta ce "Jamila wai ba ki da hankali ne? Ke ba ki san mutuwa ba ne? Kina tunanin Yaya zai iya saurarar wata mace ne a yanzu? Ni kar ki sake yi mini wannan maganar. Duk abina na san abin da ya dace". Daga haka ta yi gaba abin ta, ta bar Jamila nan sake da baki tana bin ta da kallo.


Amanarcool
***