Chapter 1
by @maryamlitee
*KISHIYA TARA*
*RUBUTUN*
*MARYAM LITEE*
Wani irin daji ne mai manyan bishiyoyi iya ganin idonka tare da kukan tsuntsaye, ba tare da la'akari da cikin jikina ba nake gudu duk inda na taka kafata kuma sai dai ka ji cas karar da take bayarwa kenan gumi gabadaya ya lullube ni na kara daga kafa yayin da na hango karshen dajin wani fili ne fetal na isa gare shi ban fasa gudu ba wani irin zafin rana na ji a tafunan kafafuna duk da babu ranar ban fasa ba na cigaba da gudu har na fara hangen wasu gidajen Fulani na karasa cike da sa rai wata mata da ta fara shiga shekarun girma na gani jikin wata bukka ta zubo mini ido.
Baka ce gajeriya, na kusa daf da ita na yanke jiki na fadi daidai da farkawa ta daga barcin da nake wannan mafarki, duk na yamutsa shimfidar gadona gumi ya rufe ni na tashi zaune ina dafe da kaina kafin na mike tsaye ba abin da nake so sai na bar gidan na nufi inda na gani a mafarki jikina daga ni sai bakar doguwar riga da bakar hula sanye a kaina.
Ban tsaya neman takalmi ba na fita ba da wanda na hadu har na fice sashena na isa harabar gidan masu hidimar gidan da ke kai da kawo ba wanda ya gwada ya gan ni har na bude kofar masu fita a kafa get man da abokansa biyu masu taya shi hira ba su dube ni ba.
Da fita ta gabas na nausa sai da na yi tafiya mai tsananin gaske na riski dajin da na gani a mafarki abin da ya faru a mafarkin shi ya kasance banbanci wannan ba gudu nake ba, har na tarar da bakar mata a bakin bukka faduwa ta ban san me ya faru ba na farka ne na gan ni karkashin bishiya an yi mini shimfida wani kakkarfan matashi fari tas dogo da ba zai gaza shekaru talatin ba durkushe gabana da wata yar matashiya da na yi tunanin matarsa ce.
"Ta tashi Amine. Samo ruwa a ba ta."
Ya ba ta umarni, ta tashi da saurin gaske ta tafi.
Ta dawo da koko ta mika masa ya dube ni "Tashi baiwar Allah."
Na yunkura sai na ji jikina ko'ina na ciwo, sai da na daidaita zamana ya miko mini kokon na karba farin ruwa ne tas na sha sai ya ce na shafa ma fuskata.
Na yi kamar yadda ya ce sai ya fara tambaya ta sunana da garin da na fito na bude baki da niyyar magana na kasa, na kama makoshina amma magana ta gagara wai wankin kuturu da sabulu.
Ya dubi matar ta dube shi "To raka ta dakin Inna."
Ta yi saurin zaro ido sai ta dubi cikin jikina sai ta yi masa magana da fulatanci ya amsa mata da Hausa sai ta tashi ta tafi.
Mun zauna shiru na wani dan lokaci ta dawo ya ce ta taimaka mini na tashi na mike da taimakonta muka taka zuwa wani daki da ke bayan bukkokin su ta daga farin labulen dakin mai shara-sharan da ake hangen waje muka shiga da alamar dakin na ajiye shirgi ne duk da ta yi kaye-kaye da sauran kaya sai gadon kara wanda aka yi wa shimfida ta ce na zauna na yi yadda ta ce ta zauna kusa da ni tana murmushi "Bakinki zai bude za mu yi miki magani babu abin da zai same ki. Da ganin ki na ji ina son ki ba zan bari komai ya same ki ba musamman da na ga kina da ciki."
Ta shafa cikinta "Ina son na gan ni da yara sai dai masu gidan sun hana.
Na daga mata kai "Ki kwanta ki huta, zan je na kawo miki hura."
Na kara daga kai ta tashi ta fita na kwanta hannuna saman cikina ina son tunano wani abu game da ni karan kaina amma abun ya faskara har sai da na ji kaina ya fara sarawa na hakura na lumshe ido.
Ta dawo dauke da hura cike da koko fari tas wadda ke alamta nonon da ke ciki ya rinjayi hurar, ta ajiye gabana tana murmushi "In sanya miki sugar?"
Na daga kai ta yi yar dariya "Dama ku mutanen birni akwai son sikari."
Ta ba ni na zuba sai da na fara sha ta fara yi mini hira ina kallon ta na murmushi in yi murmushi har na kammala ta karbi kokon ta fita.
Na dade zaune a dakin duk da harshena ba ya magana istigfari nake kirgawa da yatsun hannuna har Amine ta dawo ta kama hannuna wai surukarta ta dawo in zo mu tafi.
Na bi ta muka fita.
Gajeriyar matar nan na gani a gindin bishiya kanta da lullubin mayafi ta zuba mini ido har sai da na ji kafafuna suna rawa Amine ta kamo ni na zauna sai na gwada mata zan yi sallah ta dauko buta ta ba ni na mike ta nuna mini kewaya, na zagaya na zo na yi alwala Innar dai ba ta yi mini magana ba illa kallon kurulla da ke haddasa mini rawar kafa.
Na yi sallah a dakin, Amine ta kawo mini mayafi duk da na ji yana karnin nono rashin yadda zan yi na yafa shi na yi sallar.
Na dade zaune ina rokon Allah ya yaye mini abin da ya same ni wanda na kasa sanin mene ne.
Da duhu ya rufa Amine ta kunna mini fitila da na yi sallah ta zo ta fita da ni don na ci tuwon dare, tuwon dawa ne da ya tuku ya yi laushi a miyar aka samu matsalar wadda aka yi daga daddawa sai maggi gishiri da kuka, sam na kasa ci dole na tsame hannuna har Amine ta kula da ni.
"Ba za ki iya cin miyarmu ba ko? Na yi shiru ta ce "Dare ya yi da an gasa miki kaza."
Nan ma shirun na kuma yi ta tashi ba ta samu sukuni ba sai da ta dama mini fura na sha sai na tafi daki don na washi zama kusa da Inna wadda ke ta aikin yin igiya.
Na kwanta sukar da karan gadon ke yi mini ita ta hana ni barci, hakan ya sa har dare ya fara nisa idona biyu saman soron gidan na fara jin koke-koke na dabbobi kala-kala, tsoro ya yi mini kawanya na rufe idanuwana ruf ina janyo addu'a duk wadda ta zo bakina.
Iska ta fara kadawa bakin duhun da ya mamaye dakin ya gushe zuwa haske tamkar wata dan daren goma.
Cikin matsanancin tsoron da ya yi mini rubdugu wani barci ya sace ni da ya haddasa mini tsunduma cikin mafarki, iskar tana ta kadawa a cikin dakin wata mata ta bayyana wadda na kasa ganin fuskarta ta yo kaina tana kawo hannunta kan cikina na kai mata kyakyawan dukan da ya sanya ta juyawa ba shiri ta fice daidai da farkawa ta, dakin kuma ya koma daidai ba iska ba hasken nan na shiga addu'o'i kafin barci ya dauke ni.
Na farka da asuba na yunkura in tashi na ji gefen cikina na zafi na tashi ina jin radadi har na fita rike da butar da Amine ta kawo mini jiya ta ce na dinga amfani da ita.
Da na yi sallah addu'o'i sosai na yi ma kaina na matsalar da nake ciki muhimmi rashin iya magana ta da kasa tuna komai game da ni.
Sai da gari ya yi haske Amine ta shigo ko ta manta ban iya magana ta yi ta fadin afuwon ku dai kafin ta daga farin labulen mai yala-yala ta shigo tana mini murmushi na daga mata hannu ta dan zauna sai take yi mini bayani za ta je ta yi surfe da za ta yi hura na daga mata hannu ta fita.
Ba jimawa na tashi na bi bayan ta ita kadai ce a filin tsakar gidan tana surfe ban san yadda ake yin shi ba sai na zauna ina kallon ta har ta kammala sai da ta wanke geron ta tsane shi ta tafi tatsar nono cikin Shanu, kokon farko da ta cika da madara mai zafi sai ta miko mini, na karba na gwada kafa kai sai na ji zan iya sha, na sha sai da na ji cikina ya cika na mika mata kokon ina daga mata hannu alamar godiya a gare ta.
Ta cigaba da aikinta tana yi mini bayani wadannan shanun babanta ya hado ta da su da za a yi aurenta, su take samun kudi da su idan ta tatsi nono ta gyara akwai masu zuwa rugar suna sari, sannan tana shiga daji tsintar kwayayen zabi suma tana sayarwa mijinta kuma da mahaifiyarsa dabbobi gare su dangin tumaki da awaki sai kaji ita ke da shanu.
Na jinjina kai.
Ta kammala ayyukanta ta yanka tuwon dare ta sanya a tukunya don yin dumame ni kuma na taimake ta da sharar gida sai sannan mijinta mai suna Kado ya fito na daga masa hannu ya yi mini murmushi
Shanu ya fara kwancewa zai kai su kiwo nan Inna ta fito ta fara fada cikin harshen fulatanci da na fahimci hana shi fita da Shanun ta yi ya mayar ya daure su, ya kora awaki da tumaki.
Na koma daki saboda radadin da cikina ke yi mini, sai da na zauna na bude cikin shaidar hannu ce kwance a gefen cikin ta fito rado-rado abin mamaki kuma cikin nawa da ya fito sosai yau ya koma ya shafe na dafa inda ke ciwon cike da tsoron shatin hannun da ke wurin na yi addu'a.
Na dade zaune kafin Amine ta shigo, ta zauna gefena sannan ta ce "Zan kai shanu wurin kiwo."
Na mike tsaye na nuna mata hanya shaidar ina son bin ta.
Murmushi ta yi ta ce mu je, muka fita ina bin ta a baya.
Ba kowa a tsakar gidan har ta kwance shanun nata guda uku ta kora su muka bar gidan.
Sai kallon dajin nake ina ganin gidajen Fulani da zuwa na ban kula da su ba, ciyawar da ke kwance lub a ko'ina ita ta fi komai kayatar da ni.
Mun isa inda ta saki dabbobin don su yi kiwo ta ja ni zuwa gindin wata bishiya muka zauna tana ba ni labarai har mijinta Kado ya bullo cikin bishiyoyi magana suka yi da yaren su ta mike tana fada mini za mu tsinci kwayaye sai mu koma gidan maigidan zai yi mata kiwon.
Na taya ta muka tsinci kwayaye muna zubawa a cikin kwarya sai da ta kusa cika ta ce mu tafi gida.
Ba mu samu kowa a gidan ba sai randunan ruwa da aka ciccika ta yi murmushi tana jinjina ma mijinta Kado.
Nan da nan ta shiga shiri anan kuma ta bar ni ta tafi kai ma masu sari kwai da nono.
Na yi barci da na tashi na yi sallar Azahar yunwa ta kawo mini ziyara, na bude cikina ina shafa wurin da na yi rauni tare da kara mamakin nokewar cikina da ya fito da sosai.
Karfe uku Amine ta dawo ta iso gabana ta durkusa a gwiwoyinta tana ba ni hakuri ta tafi ta bar ni da yunwa na kada mata hannuna alamar babu komai, ta gabatar mini da tuwo da miya na girgiza kai ta yi jugum tana tambayar me zan ci, da kyar na ganar da ita ina son yin miya da kaina ta fita da sauri sai ga shi ta dawo da kaza a yanke ita ta gyara ta ni kuma na kama aikin miya tana fada mini karni ke hana su cin nama da kwai murmushi kawai na yi mata na karbi kayan kamshi na zuba wa miyar ga daddawa ta kalwa da suke da ita da albasa tasa miyar na tafasowa kamshi ya gauraye gidan.
Yamma likis Kado ya fara shigowa da shanu kafin mahaifiyarsa Inna ta shigo cikin bakar atamfa take riga da zane da lullubin zanen atamfar, gabana ya fara harbawa ganin ta ta wuce daki ba tare da ta amsa sannu da zuwan da Amine ke yi mata ba