Chapter 2
by @maryamlitee
*KISHIYA TARA*
*RUBUTUN
MARYAM LITEE*
2
Fitowar Innar ta sa ni mikewa Amine na yi mini murmushi ta ce "Ina za ki ba ki kada miyar ba?
Daki na nuna mata na wuce da sauri tun da na shiga kuma ban sake fitowa ba sai da na ga gari ya yi duhu shaidar an yi sallar magrib na fito na tsuguna a kofar daki na yi alwala na koma ciki na gabatar da sallah.
Na idar na jingina da bango Amine ta shigo dauke da kwanoni ta ajiye mini a gabana ina murmushi da nuna alamar yi mata sannu, sai da ta fita na bude kwanonin na tuwo ne da miya, miyar kukar da ta kada ta yi dadi kwarai na ci tuwon sosai na yi hamdala don cikina ya cika abin da ya zame mini tarnaki ya hana ni barci raunin da na samu a cikina ya yi ta yi mini radadi.
Sai da na samu ya lafa na shiga barci wanda ban dauki lokaci mai tsawo ba dire-diren halittu irin na jiya suka cika kunnena, ban aune ba wani dogon maciji ya fado tsakiyar dakin ya fasa kai take kuma dakin ya koma haske tarwai iska mai tsanani ta fara kadawa.
Macijin ya fara nufo ni yayin da na fara addu'a sai ya koma mace wadda ba na iya shaida fuskarta, rikici sosai muka fara ni da ita kafin na yi nasarar kai ta kasa sai ta tunkude ni ta yi wata irin girgiza ta koma maciji ta fita dakin.
Da na farka duk da addu'o'in da nake yi jikina wani irin ciwo yake mini na shiga cikin matsananciyar kidima babu abin da nake so irin in bar gidan nan, sai dai ta yaya zan bar shi ni da ban iya magana? Ban kuma iya tuna komai a kaina? Ban kuma san nan din a ina nake ba.
Na share hawaye cike da tsoro na fita kofar daki na yi alwala na dawo na yi sallah.
Sai da gari ya waye na gane kafadata ta bugu tana mini ciwo, ban kuma fita ba sai da Amine ta shigo ta yi mini magana.
A gindin bishiyar darbejiya da ke tsakiyar gidan idanuwana suka shiga cikin na Inna, ga mamakina goshinta ya kumbura suntum, Amine ta ja ni zuwa madafi ba jimawa Kado ya fito ya nufi inda Inna take kumburin goshinta ya tambaye ta wanda ta rufe shi da fada ya mike yana ba ta hakuri
A yau Kado gari zai fita cin kasuwa don haka Amine tsintar kwayaye kawai za ta, sai da ya yi ma dabbobi ciyawa ya shirya ya fita idanun Inna kamar za su fado kan harara da ya shigo da ciyawar.
Muka tafi tsintar kwayaye Amine na ta ba ni labarin halayen Inna, auren ta da Kado danginta kaf ba su so saboda bakin halin Inna ita ta nace sai Kado duk bakin halin Inna kuma ta rasa yadda za ta yi da ita kasantuwar mahaifin Aminen wani shahararre a yankin nan nasu da ya san duk wani lakani na miyagu.
Rashin iya magana ta ya sa ban tambayi Amine to ita Innar muguwa ce?
Sai dai tambayar ta yi ta kai kawo a zuciyata.
Mun tsinto kwai muka kamo hanya Amine na yi mini alkawarin za ta kai ni wurin Babanta ya yi mini magani "Ba dai kina magana ba kafin zuwan ki nan?
Ta jeho mini tambayar, na daga mata kai da sauri don tabbatar mata da tabbas ina magana.
Gabatowar mu gidan wasu jibga-jibgan motoci masu numfashi muka hango a kofar gidan, Amine ta matso daidai kunnena ta rada mini ""Wurin Inna a ka zo kin san tana bayar da magani, amma mugunta ta fi yawa cikin maganin nata. Ana zuwa daga garuruwa masu nisa karbar magani."
Na gyada kai tunanuka masu yawa na rufe ni kan Innar.
Babu kowa a tsakar gidan sai kwalleliyar rana in ka dauke karkashin bishiyar darbejiyar nan, ruwa na fara watsowa na shiga daki ina waiwayen kofar dakin Inna da takalman maza kafa biyu ke ajiye kuma masu asalin tsada.
Kwanciya na yi saman gadon karan har sai da Amine ta shigo ta ce ta yanka mini zabo in zo in dafa na fita ba takalman nan a kofar Inna kuma ita ma Innar ba alamar motsin ta Amine ta tabbatar mini ba ta gidan, sai na saki jikina na sarrafa naman zabon nan na ci ban sha furar da Amine ta dama mini ba.
Da yamma Kado ya riga Inna shigowa, tsaraba kala-kala ya dawo da ita dangin kosai buredi sugar sabulu omo ni kam har da zannuwa ya sawo mini kala uku duk da atamfofin masu saukin kudi ne dinkin ma kuma irin na Amine ne na yi murna kwarai sai nuni nake masa da hannu, daga karshe na mike da zannuwan ban yarda na amshi kosai da buredin da Amine ta ba ni ba na dai karbi Omo da sabulu na wuce dakin.
Da na sanya daya daga cikin dunkunan sai kallon kaina nake, a raina ina rokon Allah ya kawo sanadin da zan bar wurin nan ya dawo mini da tunanina da na manta.
Daren yau na yi barci salin alin ba tare da mugayen mafarkai ba, ko in ce zuwan mugaye a mafarkin nawa.
Da safe muna gindin bishiya Amine ta rage murya tana shaida mini yau idan mun fita za ta raka ni wurin Babanta na cika da murna sai dai ina dagowa Inna na gani bayan mu tana aika mana mugun kallo, ni na fara mikewa cikin tsananin tsoron ta na nufi daki.
Ban san ya suka kwashe da Amine ba sai da na ji ta zo cikin sanda tana kiran sunana ta bayan dakuna muka fita gidan muka kama hanya, wata doguwar shararra muka mike bayan mun bar gidajen kauyen mun iso marabar hanya muka dauki wata hanya da ta yi kudu Amine na dariya ta ce mun ji kamshin gida na taya ta murnar sai dai me jikin wata bishiya da muka iso Inna muka tarar a tsaye cikin bakar atamfar da na taba ganin ta da ita harara take balla mana kamar idanuwanta za su fado kasa ta nuna hanyar gida tana tambayar Amine inda za mu.
Kame-kame Amine ta hau yi karshe ta ce mu koma gida, tilas muka juya ni da Amine ban san wanda ya fi jin takaici ba, don ni dai kam har yan hawaye suka sulalo mini na kai hannu na share.
Amine na ta ba ni hakuri da karfafa mini gwiwa ko ba yau ba za mu je, har muka koma gida wunin ranar kuma sam na ki in fito har Kado ya dawo daga kasuwa ya kawo mini brush da maclean da na yi masa sako, bakina kawai na fito na wanke sai na koma ciki.
A wannan dare tsoro aka yi ta ba ni da halittu iri-iri tilas na hakura da barcin na tashi na zauna a'lamarin da ya janyo ina yin sallar asuba na mayar da kaina na kwantar na shiga barci har sai da hantsi ya take Amine ta shigo tana tashi na a hankali in tashi mu je samo kwai, ina son cin kwan don haka na yunkura don na kula Amine na yi mini kirki kan komai ba kuma abin da take hana ni amma kwanta ba ta hada shi da komai ba, shi kam tattara abin ta take ba ta ba ni.
Har muka je muka dawo labarin Inna take ba ni, muka dawo yau ma Inna tana da baki, na soya kwai na da na samo na ci don Amine ta ce ba ta son karni, ina son ce mata nama ma haka ta ce ba ta son karni karshe da na gyara ta lashe, to kwan ma rashin albasa ya sa ba su iya ci ni kuma na sanya.
Rashin iya furta magana ya sa na kyale ta na cinye kwaina na sha ruwa.
Kwana uku aka kara da fitar mu don zuwa gidan su Amine muka fita da niyyar samo ciyawa don Kado sammakon fita ya yi Amine ta sanya ni a hanya ta ce in yi ta sauri ta kwatanta mini yadda zan gane Babanta a hanya ta ta zuwa gidansu.
Ina cike da fargaba kirjina na dokawa na dauki hanya, na zo inda muka yi kacibis da Inna na ga wani farin siririn dattijo mai farin gashin kai da gemu zan gifta shi ya ce "Yarinya."
Na waiwayo da tsoro, "Ina za ki tafi? Na nuna mashi bakina sai na girgiza kai, ya yi murmushi sai ya yafito ni na isa inda yake na durkusa"Daga ina kika fito?" Ya tambaye ni na kara nuna bakina sai ya yi murmushi"Sannu yarinya kin hadu da sharrin miyagun mayu ko? sun baro ki daga mahaifarki gidanki da ma iyalinki sun kawo ki nan don cimma munanan manufar su a kanki. To in sha Allahu ta Allah ba ta su ba idan ba su yi hankali ba asiri zai tonu za a yi walkiya kowa ya gan su."
Ya yi wani irin murmushi yayin da ya tura hannunsa a aljihu ya zaro wani kullin magani "Kin ga wannan? Duk wanda mayu suka damka har suka turo masa bakin iska ya hana shi sukuni, wannan wata gajeruwar fa'ida ce sai dan karen zafi da karfi. Duk iskancin maye da tsiyatakun sa da tarkacen da ya haddasa miki, sai ya kwashe kayansa ya yi nasa wurin. Dama sun fi raina ku mata saboda rauni da sakaci da rashin juriya wurin magani.
Ko ma me ya sanya miki a jiki sai komai ya tarwatse sai kin buwaye su, in sha Allahu. Kin ga wannan maganin saiwar alliki, idan so samu ne ta kusurwa hudu, gabas yamma kudu arewa, ko'ina a deba, ko a sawo a kasuwa sai dai debowar ya fi sirrin ya fi aiki da tasiri.
Sai sauyar sanya, kasar shuri, kasar gidan turwa, sai kasar magamar hanya, sai barkono guda tara, tazargade, gero gwangwani hudu yanzu za ki samu ki samu garwashin wuta guda tara bayan kin hada ki zuba cikin babbar tukunyar kasa dama kin sa an rubuta maki ayar*Wa'in yakadu* har zuwa karshen ayar sau dubu a wanke a zuba cikin tukunyar a rufe sai ya kwana uku a bude ana sha ana shafe jiki har tsawon kwana 21 ko 41 Allah ya ba da sa'a da nasara."
Na zuba mishi ido jin ya kai karshe na kuma karbi kullin maganin sai ya gane me nake nufi ya yi mini murmushi da na gane dabiar sa ce ya ce "Tashi ki je gida diyata in sha Allahu bakinki zai bude ba da jimawa ba."
Na jinjina masa hannu alamar godiya sai na mike na kama hanyar komawa gida.
Yau ma akwai mashina a kofar gidan da na san na masu zuwa neman taimako ne wurin Inna, na wuce na shiga daki sai kuma na kasa zama a karo na farko na fito zuwa dakin Amine.
Ba bakin da zan yi mata sallama sai na daga labulai ganin ta tare da Kado ya haddasa mini jin kunya tare da saurin komawa baya na tafi dakina, sai dai ina zura kafata a dakin ita ma tana sanya ta ta.
Ta kama hannuna tana murmushi muka zauna bakin gadona na nuna mata kullin maganin da aka ba ni ta tambaye ni Babana ya ba ki?
Kai na daga mata "Na fada mishi za ki zo jiya da na saci jiki na je gida, ban san me ya sa Inna ta hana shi ya bar ni in tafi gidanmu ba tun da kika zo."
Na juya hannuna tun da ba halin amsa mata ta tashi za ta tafi tana fadin "Tun da kika ga Babana in sha Allahu za ki samu waraka."
Ta fita na bi bayan ta da kallo.
Ba ni da baki ballantana in yi ma Amine bayanin yadda zan yi amfani da maganin da aka ba ni sai na ajiye shi har zuwa lokacin da bakina zai bude.
Sai dai a daren ranar na kwanta soma barcina na ji an shake ni cikin barci a barcin kuma na yi ta karanto hasbunallahu waniimal wakil lahaula wala kuwwata illa billah.
Shakar ba ta yi sauki ba sai da na fara karanta ayatul kursiyu da na dire na dora Amanar rasulu, a hankali na fara samun saukin shakar, ban gushe Ina ta ayatul kursiyun ba da amanar rasulu har na farka daga barcin abin mamaki kuma da farin ciki sai na tsinci harshena yana ambaton wadannan addu'o'in, ina ankara bakina ya bude na mike tsaye ina zare ido