KISHIYA TARA

Chapter 3

by @maryamlitee

*KISHIYA TARA*

RUBUTUN
MARYAM LITEE

3



Na dubi kofar dakina duhun dare ne ba kuma agogo ko da na waya ne da zan san awanni nawa ya rage gari ya waye na yi ido hudu da Amine na shaida mata bakina ya bude.
Na koma bakin gado na zauna barcin ya gudu daga idona gabadaya haka na kai safiya, bayan na gabatar da sallah na ci gaba da zaman daki har sai da na ji dakan Amine na fita da sauri har ina tuntube.

Yadda take jifa ta da murmushi tun kafin na karaso ni ma murmushin nake mata "Barka da safiya Amine."
Ta dafe baki sai ta ce "Bakinki ya bude? Kai Allah na gode maka."
Ta yi saurin takowa gabana ta tsaya sai ta rage tsawo don ita din doguwa ce ta fi ni tsayi "Ki kula kar wanda ya san bakinki ya bude ya tsaya ni da ke."
Na gyada mata kai, muka yi ta magana kasa-kasa duk ta murnar budewar bakina ta tambaye ni mene ne sunana na ce "Badi'atu." Garin mu fa? Na girgiza kai kafin na ce "Ba zan iya tunawa ba."
Ta gyada kai "Da sannu za ki tuna."
Na dauko tsintsiya na fara share gidan, har na kammala ita kuma ta kammala dakanta, ta wanke gero.
Kamar kullum madarar shanu na sha a matsayin abun karya kumallo na yi wanka Amine ta kintsa muka fita da Shanu.

Sai da muka kai wurin kiwon na ciro kullin maganin nan da Babanta ya ba ni na nuna mata tare da bayanin yadda ya ce in yi amfani da shi, ta yi dan shiru kafin ta karbi garin "Zan je na samu Baban shi zai sanya a rubuta maki ayar."
Na ce "Na gode sosai Amine."
Ta yi murmushi daidai da bullowar Kado ya koro dabbobi, na ga ta yi saurin boye
maganin.
Ya karbi kiwon muka koma gida ta shirya ta fita kai nono da kwai ga masu saye.

A ranar kuma ta samu nasarar zuwa wurin Babanta ta sanya a yi mini rubutun wanda ta ce kwana biyu ya ba ta ya ce ta tura ni.

Ranar da za mu je fakon Inna muka yi ta yi wadda ta kafa ta tsare, har sai da wata kawarta ta zo suka fita tare wadda ita ma muna hada ido da ita tsigar jikina ta yi ta zuba.

Ni kadai na tafi na bar Amine a gida, na hadu da Baban mun zauna a inda muka zauna zuwa na na farko ya yi ta yi mini tambayoyi game da rayuwata ta baya na kasa fada masa komai.
Murmushi ya yi ta yi yana girgiza kai sai na yi masa bayanin halittun da ke zuwa mini da daddare har da mafarkan da nake da su.
Sai da ya gyara zama sai ya fara ba ni labari "Mayu sukan canza halitta suffa irin yadda aljani ke rikida zuwa wata halitta, dabba ko tsuntsu, ko wata halitta daban, ya kan tashi sama.
Akwai hanyoyin da ake gane maye.
Da sauri na daga kai na dube shi na ce "Ya za a yi a gane maye?
Ya yi murmushi "Akwai kwalli, kwallin idan aka shafa shi ba maye ba har aljani ana gani za ka ga kansu yana hayaki. Amma fa wannan sihirin boye ne.
Na hadiyi yawu sai na ce "To Baba mene ne maita da manufar ta?
Ya ciro goro daga aljihunsa ya gutsura ya tauna sannan ya fuskance ni

Asalinta daga wanzamai take, ko in ce mayu suna wanzanci taimako suke badawa saboda suna ganin duk cutar da ke cikin jikin ɗan'adam komai cikinsa suna gani shi ne asalin yin maita. Daga nan ne bature ya fara tunanin ya zai yi ya maida abun na cigaba da zamani ya yi scanning machine, mayu sune likitocin da kafun su gurbace su zama haɗari ga al'umma dalilin rikiɗewar su zuwa cuta shi ne da bakaken aljannu suke wannan aikin, shi kuma duk abin da ba Allah ciki kuskure da haɗari ya fi yawa, kuma Mayu ba su baiwar fassara rayuwar mutum ta jiya ko yau balle gobe ma'anar anan shi ne sanin gaibu akan rayuwar mutane kamar yanda masu aiki da aljannu ko ramli ko hisabi ke yi saboda shi iska yana tsari da dokoki iya abin da kake so shi zai ma, amma a cikin su ana samun wasu musamman manyan cikin su suna sanin mai zai faru gaba idan shaharar takai shahara kenan wannan shi ne manufar maita.
Na yi murmushi na ce "Na gode maka Baba. Amma mene ne asalin ta?
Bai amsa mini ba sai da ya tashi ya gaisa da wasu mutane biyu da suka zo wucewa kan keke, sai da suka tafi ya dawo sai ya ci gaba
Asalinta kuma ƙirƙirarta ake yi ya danganta da yadda kowa yasan iliminta aihinin kowane mutane da hanyar da suke bi domin gina ta da kafa ta har ta girma a cigaba da aiki da ita MAITA NA KAMA DA DODO wata nau'in maita ya yi kamanceceniya da dodo yayin da ake yin ta sai an yi nisa suke bambanta ta yanayin wasu abubuwan :-ita maita ana rokon jinnu su bada ta kai tsaye wasu kuma jinnun ke ba su ilimin yadda za su haɗa ta har su cimma gaci. Daga bisani maita ta koma wani ɓangare na mugunta da zalunci tunda dama ba farin iska ba ne, ko raufani baƙi ne tutturna, wasu mutanen sun maida ta abun so da abun nema dan su zalunci jama'a da yan'uwansu misali irin su rindawa dan jefe wani makiyinsu haka manoma suma sun tsunduma ciki domin tara arziki da dukiya, haka yan dambe sun afka domin samun nasarar abokin fadan su suna ganin komai na mutun inda za su daka ya fadi ko ya mutu kuma idan akwai wani shiri na asiri wato sa'a za su karya shi su samu nasara. Sannan yan fashi na da,  suna amfani da wani asirin maita wanda suke rikiɗewa su canza halitta zuwa wata dabba mai ban tsoro su razana mutum su kwace dukiyarsa.
Na yi fakare ina sauraron Baba na bude baki don jefo masa wasu tambayoyin ya miko mini wata jarka karama ya ce "Je ki gida yarinya sai kuma wani lokaci."
Ba don raina ya so ba don ina da abibuwa da yawa da nake son sani daga gare shi don yanzu na gano mayu ne ke zuwa saman rufin dakina, su kuma ne nake fada da su cikin dare har su ji mini ciwo kuma zuwa na dajin nan yana da alaka da su.
Jiki ba karsashi na mike na kama hanyar gida wadda a hanya ta nake ta haduwa da jama'a daidai daidai.

Na isa gida na samu Amine a ranar kuma muka aza tukunyar maganin mayu. Kwana uku kamar yadda ya ce  na fara amfani da maganin nan ta hanyar sha da shafe jiki.
Na ga ikon Allah sam-sam Inna ta kaurace ma zama inuwa daya da ni har Amine ta fada mini Inna ta yi ma Kado maganar yaushe zai sanya ni a hanya na koma inda na fito shi kuma ya ce ba zan tafi ba sai na fara magana.
Kan dole Inna ta bar ni bisa sharadin sai na fara magana, ni kuma ganin yadda take shakka ta da guduna sai na yi amfani da damar sai da tana zaune tana shan iskar hantsi na fito na bi ta gaban ta na bar gidan.

Gidan su Amine na nufa, sai dai yau ko da wasa ban hadu da Babanta ba a hanya, hakan ya sa na bi kwatancen da ta yi mini har zuwa gidansu.
Gida ne babba na fulani mai manya-manyan garken shanu, aka tarbe ni da hura da nono na sha ruwa wata dattijuwa ta sanya wata yar yarinya ta raka ni wurin Buffalo, sai da muka shiga wani daki na ga Baban Amine.
Ya tarbe ni da maraba na gaishe shi da girmamawa ya yi mini albashir din na kusa barin jejin nan, sai dai in yi hattara kwarai ko da aka yi maganin Inna,  muguntar su tana da yawa ba za ta hakura ba za ta yi shiri yadda za ta salwantar da ni don zuwa na nan din ma shirin ta ne wanda aka sanya ta a irin mutanen da take yi wa aiki.
Na yi jugum ina tunanin wane ne zai sanya a dauko ni a kawo ni nan?
Ganin na shiga damuwa mai yawa ya fara lallashi na ta hanyar fada mini zantuka da za su sa in saki raina, ko ganin ina son sanin abin da ya shafi mayu da maita sai ya gyara zama ya ce  "Zan yi miki karatu akan sirrin tushen mayu da wuraren da suke tsafin su. Manufar su da rabe-raben su.
  
Kin ga wannan karatun tonon silili ne da wani mahaluƙi bai taɓa yin sa ba sanin sa ma sai kaɗan daga cikin mutane sai dai in mutum maye ne, ko wanda yake ɗan baiwa da kuma mujjitahidi da ƙwanƙwanton ilimi gangaran kenan.
       Asalin maita ana yin ta ne da manufofin tsawon lokaci yaushe ta fara kuma za ta qare babu takaimaiman lokacin da ta fara haka kuma ba za ta rushe  a duniya ba har karshen zamani amma qur'ani ya ba mu hujja da makama wadda za mu iya ɗan samu ɗiso na haske ilimi daga lokacin da ta bayyana cewar Allah subhanahu wata'ala ya yi ( wa'inyakadu lazina kafaru layazliƙunaka bi absarihim lamma sami'uz zikira wayaƙuluna innahu lamajanun. )ayar ta sauka ne akan mayu wanda idan suka ƙurama mutum ido suka ƙullace shi a zuci kafun kwana 3 zai mutu shine suka yi wa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam Allah ya kiyaye shi ya kuma tona masu asiri ta hanyar saukar da wannan ayar hakan na nuna cewa tun nan akwai su, don haka sun girmi duk wani tsafi da hatsabibanci a duniya irin su occultism, illuminaty, freemason, secret society,mafia, demon's, ETC maita akwai ta a ko'ina a duniya sai dai kowane ɓangare da yanda suke yin ta, ma'ana hada ta da ƙirƙirarta maita sannan tana canza salo sannan suna da kungiyoyi term meye tushen ta da manufofin ta?  Mene ne dalilin da tsarin ta ya juya zuwa yau ma'ana a da da kuma yanzu meye sharadin ta duka zan yi miki bayani nan gaba kaɗan. Bari na ba ki wani dafa'i kafin ki tafi gida na kambun baka da dangogin sa ki samu garin ganyan magarya+garin kaikaikoma kanmashekiya+garin ƙanƙamarka ta bi ka -li'ilafi 1k a sha zazzafa ne.
Daga gama wannan bayanin sai ya juya fuskarsa na yi masa godiya ya ce "Tashi ki je gida yarinya."
Na mike ina kara yi masa bnkwana na fita na yi sallama da mutanen gidan na kama hanya.

Isa ta gidan abin da idanuwana suka gani ya daga hankalina, kayan dakina kaf har karan gadon da nake kwanciya an yo waje da shi.
Ba abin da ya fi tayar da hankalina irin tukunyar maganina da aka yasar gefe daya har ta fashe, abin mamaki kuma Amine ba ta matso inda nake ba sai Innar tana zare idanuwa.
Na  wuce na fara tattara kayan ina mayar wa ciki cike da fargabar idan suka kore ni ina zan nufa?
Ko hanyar da zan bi ta fitar da ni dajin nan ba ni da masaniya.
Na gama gyara kayan nan na hau karan gadona na buga tagumi kwakwalwata na son sanin nan din ina ne yana karkashin wane yanki?
Alwala kadai ke tayar da ni in yi sallah sai in dawo in zauna abinci ranar ban samu ba don Amine ba ta leko ba.

Shigowar duhun dare yunwa ta ci ni har ta cinye na gaza barci, idan na kwanta kan karan gadona na yi juyi sai in tashi in zuba wa kofa ido.
Motsin da na ji ana kawar da karan da aka yi don rufe kofa ya sa gabana cewa ras ganin inuwa ta mutum tana haramar shigowa dakin.