KISHIYA TARA

Chapter 4

by @maryamlitee

*KISHIYA TARA*

4

MARYAM LITEE

A'uzu bi kalimatil lahi tammat min sharri ma khalaka.
Ita na kamo na fara karantawa kafin na ga hasken tocila ya haske ni,
abin mamaki Kado ne.
Ajiyar zuciya ta kwace mini na daga masa hannu ya miko mini koko na karba hura ce duk kuma da mashahuriyar yunwar da ta ci ta cinye hanjina ban nuna zalama ba na hakura ban fara sha ba ya zuba mini ido kafin ya ce "Tun da ba a samu kin dawo cikin nutsuwar ki ba kin gane su wane ne danginki da garinku to na yanke aurenki!
Na fada ma Inna dazu."
Saurin duban shi na yi kokon hannuna na neman subucewa don tsabar razanar da na yi jin zancen shi, sai na fara girgiza kai.
Ya yi dan murmushi "Ki bude bakinki ki yi mini magana Badi'a ko?
Na bude baki ina mishi wani kallo da madaukakin mamaki "Ki yi mini magana don na san bakinki ya bude kuma sunan ki Badi'a."
Na shiga girgiza kai"Ba zan aure ka ba daga zuwa na ba ku san daga ina na fito ba ni ma haka."
Ya yi murmushi sai ya juya, sai da ya fita ya kashe tocilarsa mai tsananin haske.

Tunanin lamarin da Kado ya zo mini da shi ya hana ni kwanciya na dai sha hurar saboda cikina da ya kasa barin kiran ciroma, hannu na daga ina rokon Allah ya kawo mini mafita ya dawo mini da tunanina ya ba ni ikon barin wurin nan.

Da gari ya waye ma ko da na fita Amine ba ta kula ni ba na matsa ina yi mata magana ta share ni, sai da ta bar gidan na dauko hura na zuba nono na sha da rana kuma na soya kwai na ci.

Fita sha'ani na da Amine ta yi ya fi komai taba ni fiye da zancen da Kado ya zo da shi ko kuma alaka ta da Inna da take me tsami, har hawaye sai da na zubar karshe na hakura na rungumi sabuwar rayuwa ni kadai.

Ina zuwa na tsinto kwai don na ci ma cikina hurar Amine sai ba ta nan nake daukowa in sha, idan Kado ya je kasuwar kauye tsaraba ta ta musamman ce amma ba na ci. Ina da burin son komawa wurin Baban Amine na shaida masa maganin da na fara sha ya zube.

Ranar wata laraba na yi nufin komawa amma sai na fara biyawa na samo kwai.
Garin ya yi lub-lub ciyayi sun yi kore shar saboda ruwan da aka kwana yi jiya da dare yanayin ya yi mini dadi.
Ba sanannen ciki na ji muryar Kado a kaina na waiwayo cike da tsoro muka hada ido na hade rai sosai na ce "Me ya sa ka biyo ni?
Ya yi murmushi"Na biyo ki ne don mu sa ranar aurenmu."
Na dube shi baki bude sai na kama kugu "Daga gani na ba ka san daga ina na fito ba ina da aure ko ba ni da shi kawai sai ka aure ni ina ka ga ana yin haka?
Gidanku ne daga kun gaji da ni zan tafi."
Ya hade hannayensa yana ba ni hakuri ba mu gaji da ke ba hasali ma ni kaunar ki nake kuma aurenki zan yi mu zauna tare."
Na buga masa harara "Haka kawai saboda wani son zuciya naka ka hada ni da Amine."
Ya yi murmushi "Idan na aure ki za ta bar komai ku zauna lafiya."
Na motsa baki da niyyar jan tsaki sai kuma na fasa, ya matso da niyyar magana muka ji muryar Amine.
Cikin fada sosai take magana da harshen su ni dai na yi fakare kamar yadda Kado ma ya zuba mata ido.
Na duka da niyyar ci gaba da abin da nake na tsinkayi muryarsa shi ma yana mayar mata da martani, na mike na dubi Amine sai da na dafa kafadar ta na ce "Ki yi hakuri Amine ba zan auri mijinki ba kin ji?
Na taka na wuce su na yi tafiya ta.
Duk da hantsi ya soma dagawa hanyar gidansu Amine na mike.

A gida na samu Buffalo kamar yadda iyalansa ke kiran sa aka yi mini iso dakinsa bayan na gaishe shi hawaye na yi ta zubar wa ina tsugune gaban shi.
Ya ce "Ki bar kuka ya ta ki fada mini damuwar ki."
Na share hawaye da bayan hannuna wasu suka sake zubowa Har yanzu ina zaune ban san ko ni wace ce ba, ban san yaushe tunanina zai dawo na koma garinmu ba.
Na kuma san a duk inda ahalina suke a yanzu na san suna cike da damuwa kan bata na."
Ya gyara zama ya balli goronsa ya tauna sannan ya ce "Ki kara hakuri diyata in sha Allahu tunanin ki zai dawo, za kuma ki bar wurin nan.
Na goge fuska da duka hannayena sannan na yi masa bayanin fashewar tukunyar kasa ta ta magani kwana uku kacal da soma sha.
Ya jinjina girman hasarar fashewar sannan ya ce "Ki yi hakuri. Idan na hada wasu kayan zan ba ki maye sai dai ya gudu ya bar ki."
Na furta na gode cikin sanyin murya.
Ya yi mini murmushi "Yau ba ki son jin labarin mutanen ki?
Cike da rashin fahimta na ce "Su wa ye mutanena?
Da sauran murmushin saman fuskarsa ya ce "Mayu mana."
Ba shiri murmushi ya subuce mini na rufe bakina da bayan hannu sai na gyada kai "Ina so sosai."
"Yawwa ranar nan mun yi magana kan maita da manufar ta, to yau za mu yi kan rarrabuwar maita.
Maita ta kasu kaso da yawa: ta farko akwai maitar  kudi. Sai maitar bada magani. Maitar kimiyya da fasaha. Maitar daukaka yin suna kenan.
Sannan ana yin maitar tsawon rai
Sannan akwai maita ta kankara wadda idan ka sha za ka dinga ganin abubuwan da ke kasa irin su zinare da azurfa shi ya sa ake kudi da ita nau'in maita ta karshe ita ce maita ta ƙullatar zuci, ita wannan maitar idan mutum ya ga abu ya rike shi a zuciyarsa da mugun nufi to  zai samu abun ko na alkhairi sai ya faru ita shanta ake yi.      Amma akwai wa'yanda hakan ke faruwa da su ba tare da sun sha wani abu ba wani min indillahi ne wanda hakan ke faruwa dalilin faruwar hakan shi ne suna da abu biyu na farko ƙarfin ruhun raufaniyyatu wanda ke da girma da ƙarfin wajen captured abubuwa masu ma'ana irin su ne idan suka yi hasashen da lissafi be zama kuskure, na biyu suna tare da kudurar Ubangiji a koda yaushe akwai wani zabi da Allah ya yi musu akan hakan, wannan baiwa ce irin wadda ake yi wa annabawa da zaɓaɓɓun bayi ------ sai dai kamar yadda ake gudunar da nashi aikin da tsari shi ma shedan na can bayan fage yana nasa.  shiyasa wasu al'amarin nasu ba daga Allah ba ne na bakaken aljannu ne suke ingiza su shi ne sai a samu wani wannan bak'ar aniyar ce ta aure kuma ya biye mata yana ta cutar da mutane saboda bakaken iska ne tare da shi ɗamfare da yaso yin wannan cutar a zuci kawai zai ƙaddara shikenan. Wannan kenan.
    dalilin yasa wasu ke samun wannan abun shi ne wasu suna amfani da wasu dafa'i ɓaki mai ƙarfin gaske wanda ake cewa  rangwangwan a jikinsu sai suna shan sa to zuciyar mutum na canzawa da sauri wanda in ya yi furuci take tabbata ko idan an taɓa su ransu ya sosu ake  samun matsala  haka nan yan dambe dake shàye shàyen magungunan guba don su daki mutum ya fadi wannan gubar dake shiga cikin jikin su na masu wannan aikin.
  Yana mini bayanin ina ta gyada kai ya ce "Bari na fada miki sirrin jinnul ashik ko don watarana wato namijin dare, a samu kan bushiya da kowar wake a dake su sai a zuba cikin gorar duma (ko normal buta/Cattle) a zuba ruwa ana kama ruwa da daddare tsawon kwana 14, mujarrabun ne wannan.
Bai tsaya nan ba ya ba ni na bushewar gaba wanda ya ce matukar shi ne matsalar diya mace ta zo karshe ya sallame ni na tashi na kama hanya.

Inna tana da baki wanda na lura manyan mutane ne, don haka tsakar gidan ba kowa, irin wannan lokacin kuma na san Amine ba ta gidan sai kawai na shige daki.
Zuwa azahar zafi ya ishe ni na fito da niyyar watsa ruwa sai na yi alwala na yi wankan na fito daga ni sai zane iya kirji muka hada ido biyu da Inna da ke zaune kasan bishiya gabana ya ce ras! Na shige daki ba tare da na yi alwala ba a wannan dare kuma sai da na yi mafarki da matar da ke zuwa mini sai dai ba ta ci galaba a kaina ba a damben da muka yi.
Da gari ya waye wasu baki ne suka halarci gidan yan'uwan mahaifin Kado ne sun zo shaida ma Inna auren da Kado zai yi wanda suka tashi baran-baran Inna ta ce ba zai auri yarinya bakuwa ba ni kenan, su kuma sun ce tunda yana so gobe za su daura aure.

Sun tafi wayewar gari sakon mutuwar babban su ta riske mu inda dangin su suka yo gangami sai sun kona Inna don ita suka dora ma alhakin mutuwar tashin hankali aka yi sosai da kyar Baban Amine ya zo ya raba rigimar don suna ganin girman sa, amma fa sun sha alwashin daura auren da an share zaman makoki ko da za ta karar da su duka.

Ranar kwana uku da mutuwar ina daki kwance na ji shigowar baki ban motsa ba don sanin abin bai shafe ni ba amma sai ga Amine tana wani cin magani ta ce in zo in ji Inna.
Na zuba mata ido ina mamakin canzawar ta kamar ba Amine ba, har ta juya ta fice sai na koma tunanin ita kuma Inna neman me take mini?
Na yunkura na tashi sai na bar dakin.

Ban ji dokawar gaba ba da na tunkari dakin illa iyaka dai addu'a na yi ta janyowa ta A'uzu bi kalimatil lahi tammat min sharri ma khalaka.
Na daga labulan dakin na cusa kai manyan mutane ne su biyu daya ya sha wankan farar shadda yar ciki da wando da malum-malum, ga hularsa da ke ta zuba sheki.
Na biyun blue shadda ce riga da wando da hula na tsuguna daga bakin kofa ban yi magana ba su duka ukun suka dube ni sai Inna ta ce "Tashi ki tafi."
Na mike na juya jikina na ba ni suna bi na da kallo.

Inna ta dube su "To ka gan ta. Idan ka yarda zan sa a daura maka aure da ita ku tafi da ita sirrin daukakar ka zai fito daga jikinta, a duk sadda ka kwanta da ita jinnu za su tsotsi jininta har zuwa ranar da zai kare za ta bakunci lahira kai kuma arzikinka zai ci uban na da, duk wanda ka ga filinsa ko gidansa ka ce kana so sai ya sayar maka, haka ma duk wanda ya ga naka yana so  sai ya saya."
Alhajin mai manyan kaya ya share zufa sannan ya dubi na kusa da shi kafin ya dubi Inna "Ko za mu iya fita mu yi shawara?
Ta daga kai tana masu wani kallo da idanuwanta da suka kada suka yi ja.

"Saminu mu je waje mu yi magana." Ya ce ma mai blue shadda"Ok Alh." Ya fadi yana yunkurawa suka fice.

Bayan dakuna suka tsaya Alh ya dubi Saminu da kyau "Ina ganin ba zan yi aikin nan ba Saminu."
Bakin Saminun har yana hardewa ya ce "Saboda me Alh? Ka san yadda aka ba mu labarin matar nan idan muka zo bukata ta biya kuma za ka fadi ka fasa Alh?
"Zunubin ne yana da girma Saminu. Bayan haka ina zan kai yarinyar nan Haj ba ta sani ba?
Batun Haj mai sauki ne wuyar ta ka amince da aikin biyan bukata ya fi dogon buri Alh."
Ya girgiza kai "Kisan rai fa Saminu."
"Sai ka yi ta tuba kana sadaka Alh."
"Alhajin ya cire hular kansa ya shafa sumarsa sannan ya mayar da hular yayin da Saminu ke ta kara tunasar da shi yadda harkarsa ta dillancin gidaje ta fara kasa bai gushe ba sai da Alhajin ya amince, suka dunguma suka koma ciki.
Inna tana zaune a inda suka bar ta Saminu ya ambata sun amince amma Alh ya tambayi to ita wannan yarinyar wace ce da har za a bayar da ita?
Ta ce kar su wani damu da son sanin wace ce abin bukata kawai bukata ta biya ta mike don kawo musu magani ta fita dakin, ina zaune gindin bishiya ganin masu gidan ba su nan muka hada ido da inna ta galla mini harara ta wuce jikin danga inda take soke magungunanta.

A daki kuma Alh ya dubi Saminu "Yanzu ya kake gani zan hada shimfida da wannan yar kauyen gefe daya ya zan yi da Haj?
Ya yi murmushi "Wannan duk mai sauki ne.