Chapter 5
by @maryamlitee
*KISHIYA TARA*
RUBUTUN.
MARYAM LITEE
5
Gyaran muryar Inna ya sa Saminu ya saurara da shawarar da ya fara ba Alh.
Ta shigo ta koma mazaunin ta ta mika maganin gare su Saminu ya yi saurin mika hannu ya karba.
"Hayaki zai yi a tsakiyar dare kuma tsirara."
Sannan ta miko wata yar roba "Wannan kuma mai ne da za ka shafa a gabanka yayin haduwa da yarinyar."
Saminu ya kara mika hannu ya karba a karo na biyu.
Suka tambayi ladar aiki ta fadi Alh ya karkace ya fito da su ya zuba a gaban ta, suna shirin mikewa ta ce ya za su tafi ba a daura auren ba?
Alh ya ce sai sun sake dawowa don yanzu za su tafi su tatrauna yadda za su yi da yarinyar.
Ta girgiza kai tana tabe baki "Yana cikin sharadin aikin za a daura aure a yau ku tafi da ita."
Saminu ya yi saurin amsawa da sun amince yayin da zuciyar Alh ke rawa.
Inna ta zaro salularta cikin bujenta na ciki ta kira wata lamba da ta ambaci mamallakinta da Wakili ba jimawa mutane biyu suka iso sai da aka gaisa suka nemi sadakin Badi'a Alh da yake jin kamar an sammace shi ya zaro kudaden ya ajiye, Inna ta fita take suka fara siga ta daurin aure.
Bayan kammalawa daya ya fita ya kira Inna ta shigo su Alh suka fita don jiran fitowar Badi'a.
Uku Inna ta kasa kudin sadakin ta ba su Wakili kaso daya suka mike suka bar gidan, sannan ita ma ta mike ta fito.
Amine da ke ta kai kawo don sanin hakikanin abin da ke faruwa a dakin Inna, ta dube ta bayan fitowar ta ganin dakin da Inna ta nufa ya kara daure kanta.
Ina zaune jingine da bango sai Inna na gani tsaye a kofar daki "Ga sadakinki Badi'a, yanzu aka daura aurenki, za kuma ki bi mijinki yanzu ku bar garin nan."
Na dube ta fuskata na bayyana mamaki mai yawa "Amma wane irin aure kika yi mini ni da na zo gidanku ba tare da na tuna daga inda na fito ba maimakon ki yi kokari wurin taimakona na koma ga ahalina, sai kuma ki kara dagula a'lamarina."
Na nemi hawaye a wannan kadami amma na rasa, ido na kafe ta da shi ta kara daure fuskarta wadda koyaushe dama a turbune take kamar kunun kanwa, kuma ko alama ba digon mamaki na jin yau na yi magana.
"Ba shawara na zo mu yi ba hukunci na yanke kuma iyakar maganar kenan, minti goma ki kammala kintsawa suna waje suna jiran ki."
Ta juya ta bar dakin.
Ban samu damar ko bin ta da kallo ba, tunani na zurfafa wanda na kasa samun mafita.
Zumbur na mike na fice ni ma na iske Amine a dakinta.
Kafadarta na dafa sai yanzu kuma hawaye suka goce mini"Kin ji abin da Inna ta yi mini Amine? Ta aura ma masu karbar magani wurin ta ni?
Da sauri ta dube ni alamun razana karara kan fuskarta amma sai ta maze ta ja tsaki tana tabe baki ta cire hannuna a kafadarta ta fita dakin.
Na bi ta da kallo sai na mika duka hannayena na goge fuskata kamar kafata ba za ta dauke ni ba na bar dakin na koma nawa.
Da shiga ta kayana na soma hadawa wadanda ba su wuce kala uku ba wadanda Kado ya saya mini kala biyu ta ukun ce a jikina, sai ainahin doguwar rigar da na zo da ita a jikina.
"Daga inda ka jefo ni masu gidan ba su bukata ta, na bar su ya Allah.
Ka zame mini bango abin jingina a duk inda za ka kai ni."
Na fadi ina daga hannyena zuwa sama.
Kafin na share sabbin hawayen da suka sulalo mini.
Na dauki kayan da na kudundune a dankwalin atamfata na fita dakin ban yi zuciya ba inda Amine take na nufa na tsaya a bayan ta "Zan tafi Amine sai watarana. Na gode kwarai da karamcin ki a gare ni. Idan kin je gida ki fada ma Buffalo na tafi ina godiya kwarai bisa dimbin alherinsa."
Daga haka na sa kai na yi gaba ban ko waiwayi Inna da ke tsaye a kofar dakinta ba ta kafe ni da ido.
A kofar gidan na ja tunga mai blue shadda ya baro jikin motar ya taho wuri na "Zo mu wuce."
Ya fadi yana nuna mini inda motar take da hannunsa.
Na bi bayan sa ya bude mini bayan motar na shiga, ya zagaya zai shiga mazaunin direba Kado wanda tun safe ya bar gidan ya iso gaban shi da sauri sai da ya gaisa da shi sannan ya ce "Don Allah yarinyar da ke cikin motar nan ina za ku da ita?
Wani kallo ya yi masa sannan ya ce "Ka shiga gidan nan za ka samu amsa daga nan muka samu iznin tafiya da ita."
Kado ya dubi gidan ya juyo ya dubi motar sai ya ce "Don Allah ina zuwa."
Ya nufi cikin gidan da matukar sauri.
Sai dai shigar shi ke da wuya mutumin ya fado cikin motar ya tashe ta Alh mai manyan kaya na gefensa muka fara tafiya ina kallon kauyen tare da tunanin ababen da suka faru da ni a rayuwata a cikinsa.
Tafiya ce kamar ta neman uwa muka ci kafin mu kai ga titi.
Alh na dafe da habarsa Saminu ya rage murya ya dubi baya kafin ya dawo ga Alh, "Lafiya Alh kamar kana cikin damuwa?
Ya gyada kai shi ma cikin rage muryar ya ce "Ban san yadda zan fuskanci Haj da yarinyar nan ba ba ma zai yiwu ba, sai dai ina ganin in kai ta gidan gonata da ke Kuje kawai zuwa lokacin da za mu gama."
Saminu ya gyada kai"Hakan ya yi sosai." Daga haka suka yi shiru Saminu na aikin tukinsa Alh kuma ya fara amsa waya.
Sai dare muka shiga babban garin da ban iya shaida ko ina ne.
Wani tafkeken gidan gona mai gadi ya wangale kofa muka shiga sai dai ni da mai tuka motar kadai muka fita ya ce in biyo shi a baya
Inda ainahin ginin gidan yake muka shiga wuri ne babba sai dai ba a sanya komai ba na more rayuwa illa katifa a wani bedroom ya ba ni iznin zama hasken da ke a ko'ina bai hana ni jin tsoro ba yana juyawa ya tafi ya bar ni ji na yi tamkar in bi shi don yadda tsoro ya mamaye ni.
Na zauna na takure wuri guda yan cikina na kadawa har dai na ga ba sarki sai Allah sai na mike na bude wata kofa, kamar yadda na yi zato toilet ne, alwala na dauro na dawo dakin barcin na yi sallah addu'a sosai na yi Ubangiji ya kawo mini mafita.
Kasa hawa katifar na yi don tsoron kwanciyar nake a irin wannan wuri ni kadai, sai dai da yake barci barawo ne ban san sanda ya sace ni ba sai dai na ja jiki na haye katifar na ci gaba da barcina mafarkai na shiga yi wanda ya fi tsaya mini matar nan ta zo yau zaune take dirshan tana kuka kafin ta fara magana da daga sauti cikin kuma fushi.
"Kin samu nasarar barin gidana ba tare da na cika buri na da ya sa na baro ki da gidanki ba, na kira ki zuwa zauren tudu ne don na lashe dan da ke cikinki bayan kishiyoyinki sun kira ni suna son na yi musu aiki a kanki.
Na yi asara na yi asara na yi asara! Sai dai ba zan taba bari ki dawo cikin nutsuwar ki ba har ki tuna ke wace ce! Dariya ce ta biyo baya wadda ban gushe ba ina jin ta har na farka na tashi zaune da sauri ina zare ido.
Karshen katifar na koma na jingina jikin bango, wani iri nake ji cikin kaina tamkar ana buga mini gudumar da ke toshe ko'ina cikin kaina.
Na jima dafe da kaina kafin addu'a ta zo bakina, yin addu'ar shi ya sa ni samun sassauci na ji kaina ya yi garau, sai na gyara zama don ba na jin zan iya komawa barci a wannan dare.
Ban ji kiran sallah ba don haka zama na ci gaba da yi har sai da haske ya fara lekowa ta labulai, na mike na dauro alwala na yi sallah, anan inda na yi sallar na yi ta zama tsawon lokaci har na gaji don na soma gyangydi amma ban son barci ya kama ni, wanka na shiga na yi ko in ce watsa ruwa daga ba sabulu na fito na canza kaya maimakon in zauna sai na bude kofa na fito ina kara nazarin wurin har na bude babbar kofar falon na fita.
A yau har ya fi mini girma gidan gonar sabanin jiya da muka shigo, na dan tsaya jim sai kuma na taka ina tafiya ina kara kallon wurin har na kai get.
Ban yi mamakin ganin Mai gadi ba wani tsoho da ya tuna mini da Buffalo don jiya na gan shi sabanin shi da ya nemi diriricewa da ya gan ni.
"Daga ina yarinya?
Ya tambaye ni yana gyara wata doguwar sanda da ke hannunsa.
Na gyada kai sai na gaishe shi ganin bai gamsu ba sai na kara masa da bayanin jiya aka kawo ni cikin dare.
"To to to." Ya fadi sai ya koma wurin zaman sa ya dauki radiyonsa da ya baro ya kanga a kunne, ni ma ganin haka na hau wani dutse da ke kusa da shi na zauna ina kallon shuke-shuken wurin.
Ban jima ba ya mike ya nausa cikin shuke-shuken sai ga shi ya dawo da mangoro gwaiba da lemo har da ayaba ya ajiye gabana na yi masa godiya sosai sai na fara cin ayabar don dama na fi son ta kuma cikina yana ta kiran Ciroma, sai da na ci har ta ishe ni na tashi na wanko mangoro a wani famfo da ke wurin, ban sha ba, cikin girmamawa na yi ma dattijon sallama na koma ciki.
Ban dade da zama ba na ji ana buga kofa sai da na kalli ko'ina a dakin sannan na mike na kama hanya na fita.
Ina bude kofar babban falon Mai blue shadda da Alhajin nan ya kira da Saminu na gani, yau cikin wando da riga yake na brown din yadi kansa ba hula.
"Sannu da zuwa."
Na ce ina duban shi, ya kare mini kallo sannan ya ce "Yawwa. Ga sako daga Alh."
Sai ya fara bude ledar hannunsa ya ciro sabulai na wanka manya guda uku, sai na wanki guda hudu, sai Omo, sai turare sai abun goge baki, takalmi silifas ne karshe.
Ya mayar da su a ledar yana mini bayanin in dinga wanka sau biyu a rana ina shafa turaren ina wanke bakina kafin Alh ya zo.
Na gyada masa kai sai ya bude wata ledar ita kuma set ne na kayan gyaran gashi, nan ma ya ce in gyara gashina na yi ta kallon sa yadda ya dage yana kwatanta mini yadda zan yi.
Ledar karshe abinci ne a take away.
Ya juya yana mini gargadin in kula na koma ciki bayan na rufe kofar.
Toilet din na shiga na yi wanka da sabulu mai kamshi na wanke bakina na bi yadda ya ce kuma na wanke gashina wanda tun zuwa na zauren tudu bai samu wanki ba, na yi ta kallon kaina a madubin da ke bayin kafin na fito na sanya doguwar rigata sai na zauna cin abinci, duk yadda na so rage ma Baba Mai gadi abincin nan hakan faskara ya yi don dadin da abincin ya yi mini.
Illa dai da na cinye sai na dauki sabulu daya na wanka na wanki daya na sa a leda na fita na ba shi, hakika dadin da ya ji ba ya misaltuwa wanda ya sa ya shiga a'lamarina tun daga ranar idan ya ga ban fito ba zai zo ya kwankwasa in bude na bi shi bakin get ya gutsura mini abin da ya ci in sha yayan itace haka na rayu har tsawon sati guda Saminu ko Alh wani bai kara dawowa ba har matar Baba mai gadi ta dawo dama ya ce mini ganin gida ta je.
Ita ma dattijuwar ta karbe ni kamar yadda mijinta ya karbe ni, idan ta yi girki tana zuwa ta miko mini sai dai ba na karba in shige fita nake na je wurin su na ci har na samu sati biyu da yammacin ranar Alh ya zo tare da Saminu, ban san tare suke ba don shi kadai ya shigo bayan ya buga na zo na bude sai yau na kare masa kallo kamar yadda ya hade hannayensa yana murza su yana kare mini kallo ni da dakin.
Hakika asalin dogo ne baya da jiki sosai haka ma ba ya da duhun fata, a yau da yake sanye da jallabiya fara sai ta fi bayyana tsawon sa.