KISHIYA TARA

Chapter 6

by @maryamlitee

*KISHIYA TARA*

MARYAM LITEE

6

Wayarsa ya zaro a aljihun jallabiyarsa ya yi kira, fada ya shiga yi don me ya zo ya same ni a yanayin da ya gan ni? Ina kayan da ya ce ya saya mini?
Ban ji me Saminun ya ce ba, ya dai sauke wayar ya mayar da ita aljihu, ya ci gaba da murza hannayensa har Saminun ya turo kofa ya shigo.
Wani fadan ya rufe shi da shi shi kuma ya yi ta kame-kame karshe ya ce "Ina gani Alhaji abin da za a yi a dauke ta wurin nan ta koma gidana, wurin Talatu, ita za ta koya mata yadda za ta gyara kanta." Alhajin ya yi dan shiru kafin ya ce "Haka ne. Sai dai inda matsalar take kar Talatu ta fada ma Haj halin da ake ciki."
Saminu ya yi saurin girgiza kai "Ko daya ko alama Alh. Zan sanar da ita yarinyar yayar mahaifiyata ce mijinta ne ya rasu shi ne na taho da ita.
Alh ya yi wani abu da fuskarsa mai kama da murmushi"Ka zo da dabara Saminu hakan ya yi, yanzu ka sauke ni a gida sai ka dawo ka tafi da ita."
Ya fara takawa ya bar dakin kafin Saminu ya bishi kasa-kasa yana fadin "Idan ban da abin Alhaji, ruwan kashe gobara ba sai mai kyau ba ya gaggauta abin nan a samu biyan bukata ya tsaya wani iyayi."

Tun daga get Alh ya ce ya tsaya ya sauka ya yi saurin sauka shi ma ya bude masa kofa ganin Alh zai wuce ya ce "Uhmm Alh."
Alhajin ya waiwayo "Uhumm ina jin ka."
Ya shafa kai "Dama Alhaji kudaden da za a yi mata sayayyar da za ta yi fes ka gan ta kamar yadda kake so."
Alhajin ya dan tsuke fuska "Wadancan kudaden da na bayar fa?
Ya shafa kai bai yi magana ba, Alhajin ya wuce "Idan na shiga ciki zan sanya maka wasu."
Ya shiga godiya sai da Alhajin ya shige ya koma motar ya bar wurin.

****""""

Da tafiyar su fitowa na yi na zauna tare da matar Baba mai gadi da nake kira matar Baba muna hira a kofar dakinta wanda labari take ba ni kan garin su da shekarun su a Abuja. Don sai da ta dawo na gane garin da na samu kaina a karo na biyu bayan barowa ta zauren tudu Abuja ce.

Muna zaune horn ya cika kunnuwanmu Baba ya fito daga cikin bishiyoyi da sauri ya je ya wangale get.
Na yi mamakin ganin motar Alh ce ta dawo muka bi motar da kallo har ta samu wuri ta yi parking Saminu ya fito, matar Baba ta bi shi da gaisuwa sai ya kira ni.
Na mike na isa inda yake "Ki shiga ki hado kayanki mu tafi."
Abin da ya fara ce mini kenan da isa ta. Na hadiyi yawu sannan na wuce zuwa ciki.

Ban sha wahalar hada kayana kala uku ba na ware sabulan da ya kawo mini da nufin kyautar da su ga matar Baba na fito ina yi ma wurin kallon karshe.

Tuni Saminu ya koma mota na tsaya na yi ma tsofaffin biyu sallama matar Baba har tana share ido wai zan tafi na ba su sabulan da man na tafi wurin motar inda suka biyo ni har na shiga ya ja motar muka fita gidan.

********

Bude idanuwana na yi na kalli gari sosai har muka fita cikin garin Abuja muka shiga Suleja. A Kaduna road gidan nashi yake, wani babban gida mai  rumfar cin abinci a gaban shi, ya tsaya.
Shi ya riga fita, sai da na fita na bi shi a baya shaguna ne a gaban gidan wanda su ma duk baki ake karba masu zuwa cin abinci, muka shiga gidan wanda kofa ce, ta sada mu da filin tsakar gidan mai matukar girma, a can karshen gidan ainahin ginin gidan yake wanda yake dakuna  falle dai daya, hatta matarsa Talatu daki daya ne da ita.
Yana ta gaisawa da matan gidan suna yi mishi sannu da zuwa muka wuce zuwa dakinta, dakin yana da girma babu laifi wanda ya mallaki gado da mirror da wardrobe sai kujera doguwa guda daya, Talatun na zaune a kasa tana lissafin kudi wanda muna daga labulai ta yi saurin sanya su matse matsi ta boye abin ta.
Ta bi mu da kallo har ya zauna saman kujerar ni kuma na zauna a kasa.
"Ba sannu da zuwa Talatu?"
Ya fadi yana zare hular kansa, ta tabe baki "Na gan ka da rana tsaka kuma har da mace biye da kai."
Ya yi murmushi "Kanwata ce Talatu."
Ta kara kyabe baki "Ban taba jin ka ambaci kana da kanwa ba Saminu."
Ya yi yar dariya "Maganar ce ba ta zo ba Hajjaju, Badi'a kenan kanwata ce da Ummarmu ta haifa bayan ta bar gidan Babana a can wani kauye, can ta girma har aka aurar da ita, to yanzu auren ne ya mutu mahaifin nata ma ya mutu kin san kuma Ummata ta dade da rasuwa dole rikon ta sai ni Talatu shi ne kanen Ummanmu Baba Jatau ya turo mini ita ni da ke sai mu rike ta."
Wani kallo take masa idanuwanta tsaye tun da ya fara maganar.
"Lallai ma Saminu! Ta nuna  ƙirjinta"Ni ce mai rike maka kanwarka? Bayan kai din ma ba ka rike kanka ba?
Ya yi yar dariya "Duk abincin da na ci na san kin rubuta yau zan biya ita ma duk abin da ta ci biya zan dinga yi, za ki kula mini da ita kafin ta gyagije ta san gari aiki zan samo mata ma ta tafi."
Ta mike ta haye gadonta "Da dai ya fiye maka."
Gane ba za ta saurare shi ba ya karkace ya zaro bundle na dubu daya ya ajiye a kasa ta yi saurin bin kudaden da kallo ya kara mayar da hannun ya ciro wasu daurin har biyu sai ta sauko daga gadon ta cabe kudaden.
Ya yi wani munafukin murmushi sai ya bugi kusa da shi ya ce "To zauna mu yi magana."
Ba musu ta zauna gefen shi ya ce "Yawwa idan kika ware kudaden da kike bi na na abincin da na ci sati biyu ne ko uku sauran za ki saya ma Badi'atu kaya na kwalliya da suturu kamar yadda na ce ki kula da ita ta dawo yar birni abincinta ma zan dinga biya kina lissafi."
Ta kamo hannuna tana jujjuyawa a hannunta "Wannan ma ai kamar ba tashin kauye ba fatarta lafiya lau babu wata damuwa, cikin lokaci kadan za ka gan ta ta yi yadda kake so ai ba kauyanci a tare da ita wuyar ta ta cire wannan atamfar ta mutanen mu na can."
Ya kara yin dariya yana shafa keya "To ba ki gaishe ta ba Badi'atu, ita ce matata Talatu."
Na dan dukar da kaina sai na gaishe ta ta amsa tana ci gaba da kallona ya ce "Kin ga muna kama ko?
Ta kyabe baki "Ni ban ga kama ba ta fi ka kyau nesa ma ba kusa ba."
Ya mike yana dariya "Ni bari in je in yi sallah."
Ta ce "Ni ma tashi zan yi in samu masu aikina."
Ta fita ta bar ni ni kadai ina ta karanta Wasikar jaki wucewar lokaci wata mata ta shigo dauke da tray abinci ta ajiye gabana sai da ta fita na bude na samu jallop ne na shinkafa da cinyar kaza sai lemo.
Na ci abincin na sha lemon sannan na fita da nufin yin sallah, matan gidan duk sun dora girki a kofar dakunan su ita kuma Talatu tana nata aikin da masu taya ta abincin sayarwa, na tambaye ta ta sa aka ba ni buta na kewaya makewayin da ya ba ni tsoro ganin yawan jama'ar gidan a ce a wadannan bayuka kwaya uku kacal za su yi amfani.
Na kewaya na fito na daura alwala sai na koma dakin Talatu na yi sallah, ita ta aiko in fito in sha iska na fita na zauna ina ta kallon hada-hadar mutanen gidan.

A satina na farko lafiya lau ina samun kulawar Talatu, ta je kasuwa ta yi mini sayayya ta kayan sanyawa sai dai ba masu tsada ba kamar yadda mijinta ya ce,  ta saya mini kayan kwalliya tana ba ni abinci ni kuma ina taya masu aikinta aikin abinci, a dakinsu ma nake zaune wanda ta kama masu haya bayar da abinci ne dai Saminu ya hana ranar da ya dawo ya same ni ina mika abinci, fada suka yi sosai har tsakar gida mutanen gidan na ba su hakuri, abin sai ya shafe ni ta daure mini fuska da gari ya waye ba ta ba ni abin karyawa ba ta ce kudaden da ya bayar sun kare.
Sai wata Abu da muke kwana tare ta kwance zanenta ta fito da kudi ta mika mini ta ce "Ungo bashi na ba ki da kin samu ki biya ni idan ba rashin mutunci ba ta ina ake barin mutum da yunwa?
Na karba na yi mata godiya na fita dakin,  tsakar gidan ya rikice ana fada kan daya ta ce mijin matar kusa da dakinta yana leka ta idan tana bandaki kuma yana kallon ta idan za ta wuce.
Na wuce su na samu Talatu inda take bayar da waina yi mata suyar ake ita kuma tana bayar wa, don ta ce cutar ta suke.
Na tsaya daga kusa da ita na ce "A ba ni waina." Ta dubi kudin a yatsine kafin ta miko hannu ta karba ta zuba mini na koma gefe guda, na cinye don guda uku ce ta dari uku, sai na mike matar kusa da dakinta ke sayar da pure water na karbi guda daya naira hamsin na sha sai na koma daki.

Da rana ban samu komai na ci ba gudun tijarar Talatu ta sa ko fita ban yi ba inda ake sayar da abincin amma sai ta aiko aka kira ni, abincin ta sani bayarwa na mika ma wanda ta aike ni suna magana da wasu maza da na dawo na koma gefe daya na tsuguna ta dube ni a lalace "Abinci dai wallahi ba zan bayar ba har sai ranar da ya ba ni wasu kudin na abincin naki, Don ba zan ta datsa ma kare ciyawa ba."
Daya daga cikin mazan ya yi dariya "To Haj ni a ba ni ita mana ai sai na ci gaba da biyan kudaden."
Ita ma ta yi dariyar jin dadi ta mika masa hannunta "Ba ka da matsala Alhajin Allah idan na ji dumus."
Ya karkace ya zaro kudi ya ba ta take kuma ta tambaye ni abin da zan ci cikin nau'in abincin da take da su.
Na ce shinkafa da kayan ciki. Ta yi mini wani kallo kafin ta ce in wuce wurin mai bayarwa ta zuba mini, da haka na koma daki na bar su.

Karfe sha daya na dare masu aikin nata duk sun kammala sun nabba'a a makwancin su sai hira suke kamar ba wuni suka yi zirga-zirga ba, Abu ta shigo karshe tana ce ma Ta sallah "Na gama hada miyar na janye wutar yar wadda ta rage ta ishi miyar ta yi ta dahuwa zuwa asuba sai dai mu sauke."
Kafin Ta sallah ta yi magana ta juyo gare ni "Badi'atu Haj na kira."
Na yaye mayafin da na lullube jikina don sanyi da ya fara kunno kai sai na zura silifas dina da yake gaban shimfidata na mike na bar dakin.

Da sallama na yaye labulen dakin, tana zaune a kasa tana lissafin kudi.
Ta yi mini fara'a "Ashe ba ki yi barci ba Badi'atu?
Na daga mata kaina "Barka da dare Haj."
Ta amsa sai ta matso ta dafa kafadata"Shawara zan ba ki Badi'a, kin ga wannan dan'uwan naki da ya hana ki shiga harkar sayar da abincina ba iya ciyar da ke zai yi ba, daga ba zama yake da rana ba ki shiga a yi da ke, ta hanyar masu sayen abinci in sha Allahu ba za ki zauna da yunwa ba.
Ni da na gane kula maza take so ta sanya ni gefe guda kuma ina tuna auren da inna ta daura mini na hadiyi yawu na ce "Zan iya yi miki aiki in shiga cikin masu yi miki aiki sai ki dinga ba ni abinci."
Ta dan bata rai "Ai kin fi karfin tsayawa daga abinci kawai, kina bukatar kayan kwalliya masu kyau yadda kike ma sha Allah din nan kina gyara kanki maza za ki ga sun yi miki caa ki wanke su yadda kike so."
Dan mu rabu lafiya na ce mata to ta sallame ni na koma daki.

Kafin kiran assalatu gida ya kacame da hayaniya wadda ta sa dole muka fito, daya daga cikin matan gidan ce Talatu ta kama tsamo-tsamo tana tsamar mata naman miya.
Don ta ce ta dade tana zargin ana satar mata naman idan sun hada miyar sun bar ta a waje cikin dare, shi ne yau ta ki barci karfe hudu ta ji bude kofa sai ta leko ganin Maman Bose ce sai ta saurara ganin ta nufi inda tukunyar miya take ta bude a hankali ta ce don bala'i ma hannu ta zura namana duk yanka daya dari biyar shi ta dinga yi ma cin bi-biyu.
Ta kawo ashar ta maka ta ce yau police za su raba ta da Maman Bose.
Mijin Maman Bose ya ratso taron matan inda aka zagaye matarsa daga shi sai gajeren wando da farar singlet ga shi kato mai katon tumbi