KISHIYA TARA

Chapter 7

by @maryamlitee

*KISHIYA TARA*

MARYAM LITEE

7

Talatu ya duba ya ce sai ya yi shari'a da ita bisa tozarta masa mata da ta yi.
Nan fadan ya kara daukar zafi yana ba zai yarda ba ita ma tana ba za ta  yarda ba, karshe mutanen gidan suka kashe wutar da kyar da jibin goshi ba tare da an je police station ba.
Ita Maman Bose ita aka yanke za ta biya Talatu kudin naman da ta ci wanda da kyar ta yarda dubu biyar don ta ce kullum da ake cinyewa ita ce.
Lokacin da aka tashi fadan gari ya soma haske na wuce na yo alwala na kabbara sallah da na idar na fita inda ake aiki. Talatu ta kira ni na tsaya gefen ta idan ta zuba waina sai ta miko mini in bayar tun ina sa ran za ta zuba mini in ci har na sare, har ta kare tas na hada kayan wanke-wanken na mika su inda ake wankewa, wadda ke yi daban take tana yi kullum tana biyan ta.
Ban samu na raba jiya da yau ba sai da rana da mutumin jiya ya zo ya ba ta kudi ya ce ta ba ni abin da nake so.
Da daddare kuma Abu matar kusa da dakinmu ta miko mata tuwo, shi ne da matar ta tafi ta ce ita kam ba za ta ci tuwo ba, ta yi ma kowa tayi ya ce ya koshi ni sai na amsa na ci.
Mafari ban kwana da yunwa ba.

Da asuba da na yi sallah sai na yi kwanciyata, sanin ko na yi aikin ba abincin za ta ba ni ba, Abu ta yi ta tashi na da za su fita na kara gyara kwanciyata na ce su je kawai.

Na kwanta har karfe tara na safe sannan da fitsari ya cika mini mara dole na tashi riga ce mara nauyi jikina cikin sayayyar da Talatu ta yo mini da ta kawo kuma ta ce ita zan dinga sanyawa ina barci.
Na janyo hulata da ta sabule yayin da nake barci na mayar bisa kaina sai na mike na fita.

Matan gidan sun yi da'ira a karkashin bishiyar mangoro da ke cikin gidan, Talatu ce kadai babu,  cikin su bakwai.
Na hade su na yi musu ina kwana na gifta su sai na ji Maman Sabo ta ce "Oh ikon Allah, duka yaushe yarinyar nan ta zo gidan nan Amma dubi yadda cikin kankanen lokaci ta yi bul-bul ga wani haske da kullum take karawa."
Fasa shigewa bayin na yi na dan rabe a kwanar shiga sai na ji Maman Gambo da duk ta fi su shekaru ta ce "Ni yarinyar kama take mini da mai yaron abin nan duk ta danyace."
Gabana ya doka da saurin gaske sai na dafe kirjina na fada bayin.
Har na gama abin da zan yi gabana bai bar dokawa ba, na fito jiki a sabule na gifta su ina jin suna bi na da kallo, Maman Sabo ita ke ba ni ruwan zafi duk safiya in yi wanka amma maganar da na ji sun yi a kaina ta hana ni in tambaye ta na hakura da wankan na tafi inda Talatu ke zuba waina.
Na samu mai yin wanke-wanke ba ta zo ba ba ta jin dadi sai na zauna na kama yi, abin ba mai sauki ba ne, kana yi ana kawo wasu idan ka wanke kuma a kwashe a je a zuba ma wasu. Wani mutum mai kimanin shekaru arbain ya yi sallama bayan sa wata matashiya na biye da shi doguwa ce fara siririya, fuskarta ta dashe tas da hasken bleaching.
Talatu ta kalle su ta zubar, namijin ya rage tsawo gaban ta ya soma mata kirari "Sikari ba ki yi farin banza ba, mace mai kamar maza kwari ne babu. Kin yi taki kin yi ta mai karamin karfi, baya goya marayu."
Ta galla masa harara "Sai ka fadi abin da ya kawo ka."
Ya gyara tsugunnon yana dan murmushi "Abin da dai aka saba shi za ki yi, ga Laura ta yi tuba za ta dawo kan aikinta ki yi hakuri uwar dakina."
Ta balla ma inda budurwar ke tsaye harara "Ita ba ta da baki ba ta iya bayar da hakurin ba sai kai ne mai bakin magana." Ya juya ya dubi matashiyar da ya kira Laura "Matso Laura ki ba Haj hakuri."
Matashiyar ta matso ta ce "Ki yi hakuri Haj."
Ba ta amsa ba shi ta duba ta ce "Sai dai ban san inda za ta dinga kwana ba don ka ga yarinyar nan ta maye katifarta."
Ta fadi tana nuna ni.
Ya ce "Ba komai, sai su kwanta tare kafin ta tara albashinta sai ta sayi wata."
Ba ta amsa ba sai ta tabe baki, budurwar ta yaye mayafin da ta rufe kanta zuwa wuya kitson attachment din ta ya bayyana sai ta wuce inda ake bayar da abinci. Mutumin ya tashi ya tafi bayan ya sayi waina ya ci, ni kuma ina wanke-wanken ina nazari da alama ma'aikaciyar ta ce, suka samu sabani sai ta tafi, shi kuma wannan mutumin ya kawo ta ya ba da hakuri.
Kafin a tashi suyar na gaji likis, don haka ina samu na karasa wanke-wanken na koma daki na kwanta.
Sai ga Laura ta shigo rike da take away ta zauna gaban katifata ta bude, alale ce kamshinta ya taso ya shige hancina sai na ji yan cikina sun yamutsa zuciyata ta kama tashi! Duk yadda na so daurewa abin gagara ya yi sai na mike tana yi mini tayi na ce na gode na fita dakin.
Wurin da su Abu ke hutawa na nufa na zauna tare da su sai dai kasala na yi ta ji ba abin da nake so irin in kwanta, ina shirin komawa dakin ko ta kammala in kwanta sai ga Talatu ta yafuto ni na isa inda take shinkafa ta ce in zuba akwai mutum a shagon waje in mika masa. Dakin na koma na dauki mayafi na dawo na zuba abincin na tafi kai wa.

Mutumin da ya sai mini abinci ne har sau biyu, na ajiye zan juya ya ce in dan jira shi sai na tsaya tunanin kudin zai ba ni sai na ga yana dauko kallona daga sama har kasa "Ma sha Allah tabarakallah ahsanul khalikin Allah ya yi halitta anan. Kin keru ke din kyakyawar mace ce da aka yi wa baiwar idanuwa farare manya masu daukar hankalin duk wanda ya ci nasarar hada ido da ke ga jiki malam kam....
Tsaki mai karfi na ja na kama hanya sai na ji yana fadin "Zuki kai an yi halitta wurin nan."
Na shiga gidan raina a bace katifata kuma Laura na kwance a kai, duk da yunwar da nake ji sai na kama shirin wanka na daura zane na tube rigar jikina na sanya hijab sai na janyo sabuluna wanda yake daf da karewa zuciyata na ta kasafta mini inda zan samo wani idan ya kare.

Na yo wankana na dawo na samu Laura tana waya, daga yadda take kashe murya da ido na gane da namiji take sai na mayar da hankali na yi kwalliyata ba mai hayaniya ba na zura riga sai ga kiran Talatu, na mike na fita na same ta.
Abinci ta ce in je in zabi wanda nake so, na wuce ina tunanin ladar wanke-wankena ta ba ni sai na ji Abu na fadin "Yarinyar nan ta zo a sa'a, babu abin da Jibrin ba zai mata ba tun daga yanzu ya dauke mata yunwar cikinta."
Kamar kar na zubo jin mutumin nan mai jajayen idanuwa da mayatar kallo bugu da kari ga irin maganganun da ya fada mini yau shi ya kara saya mini abincin, sai dai yunwa da ba ta jin lahaula ta sa na wuce na zubo na dawo na zauna gindin bishiya ina ci ina sauraron Talatu da ke ta la'antar auren miji irin Saminu tun daga ranar da suka yi fada kan tana aikena raba abinci da ya yi wanka ya bar gidan bai kara dawowa ba sai dai dan halak aka ce ya ki ambato shi din ne ya shigo gidan yana sabe da malum-malum jikinsa riga da wando ne na shadda wadda duk da squeezing din da ta yi bai hana bayyana ita din mai tsada ce.
Matan gidan da masu mata aiki suka yi ta yi masa barka da dawowa ni ma na bi sawun su wurin yi masa barka da zuwa Talatu sai harara take balla masa kamar idonta zai fado.
Ya dan tsaya yana dan murmushi "Kanwata ce ta yi kyau haka Talatu lallai kin rike amanar da aka damka miki."
Ta mike tsaye "Wace amana wallahi kudi za ka kawo mu je dakin."
Ta bi shi suka shiga dakin, wanda ko minti biyar ba a wuce ba na ji muryarta tana kwalla mini kira.
Na tashi na nufi dakin yadda na same su sai na dan ji kunya Saminu duk ya rikice ita kuma tana bakin kofa, ina isowa ta koma ciki ta zauna bisa kujera shi kuma da na samu a tsaye sai ya zauna bakin gado. "Ai inda ka je akwai irin shi na tabbata ba ka da kewa ta don me zan ba kaina wahala in...
Ya dago da fuskarsa daga cikin tafukan hannayensa"Don Allah a bar maganar nan Talatu a gaban yarinya kuma za ki yi wannan maganar?
Ta gatsina baki "Ai kam Badi'a ba yarinya ba ce daga ta san auren nan ta zauna da miji."
Ya ce "Na ji a bar shi haka. Yaya Badi'a ba wata matsala ko?
Kafin na yi magana ta karbe "Kai ka ga alamar matsala a jikinta? Kudade kawai na abinci za ka sauke."
Ya ce "Ban dawo da kudi ba ki ci gaba da ba ta zan hada duka na biya.
Ta nuna shi "Ka gani ko na ce kadangarun bariki ke cin kudinka ka ce a'a am...
Ya yi saurin mikewa yana dakatar da ita "Tun da ba za ki gane ba daidai ba ne abin da kike yi bari na bar miki dakin, kin kira yarinya kina zantuka masu nauyi a gaban ta ."
Daga haka komai bai jira ba ya fice ta bi bayan sa da kallon takaici "Hakan ma ya fi ka tafin, don ban ci nanin ba nanin ba ta ci na, ko ruwan sha ba ka shigo mini da shi ba sai in zauna ka yi ta sassaka ta, wadanda kake ba kudinka ka je su ba ka, sai dai ku guji ranar bacin rana."
Ta ja kwafa "Ranar duk da na kama ka da kowace shegiya kai har ita sai dai mu hadu a lahira."
Ta juyo gare ni "Kina dai ganin irin yayan naki kin san ba ki da Yaya, don haka tun wuri ki koyi wayon karbar kuɗi wurin duk wanda ya shiga komar ki."
Na daga mata kai na tashi na fita da na koma daki Laura tana bisa katifa sai na zauna a kasa har yamma ina dakin, wankan da ta fesa ta zuba turare kamshin ya hautsina mani ciki dole na fita.

Da daddare ina zaune cikin matan gidan ana hira Saminu ya aiko kira na na tashi na shiga dakin.
Ya fesa wanka ya sheka kwalliya shaddar jikinsa sai maski take ga turare yana ta zabga kamshi, Saminu ya fi kama da wani babban kusan gwamnati ba direba ba ko yaron me kudi ya iya tashin wanka ga jikin ya goge da ado.
Ya dube ni da murmushi yayin da nake zama a kasa shi kuma yana daura agogo a tsintsiyar hannunsa"Ya ya Badi'a gidan dai ba matsala ko?
Wani takaici ya taso ya kulle ni kamar in ce mishi sai dai ta yunwa, sai kuma na yi tunanin tayar da husuma tsakanin sa da matarsa daga ya ce ta dinga ba ni zai biya.
Na girgiza kai "Babu komai."
"To ki yi hakuri ki yi zaman ki anan ina nan ina yi ma Alh magana a kanki har mu samu ya juyo gare ki."
Wani takaicin ya kama ni sai aka kira wayarsa ya koma bakin gado yana amsa wayar ya nuna mini da hannu in jira shi.
Na gyara zama na bude kunnena ina sauraron shi.
Gaisuwar da yake yi cikin girmamawa ta sa na zargi Alh ne sai kuma da ya ce "Mutuniyar ka ta gyagije Alh zan so ka gan ta kamar ba ita ba."
"Alh ya ja tsaki "Ko a can yarinyar ta yi mini, matsalar da aka samu Hajiya ce, fargaba ce kurum ta sa na kasa sakewa da ita har na bari ka tafi da ita. Kuma sai na fahimci matar nan maraba kawai take nema da yarinyar nan ya sa  ce sai na kwanta da ita bukata ta za ta biya, yanzu kana gani tun da muka dawo na aiwatar da hayakin nan ko ta ina kasuwa budewa take yanzu haka dazu da yamma an kira ni dillancin wannan Estate din da aka hana ni watannin baya."
Saminu ya yi shewa cike da jin dadi ya taya ogan nashi murna ya tambaye shi gobe da yaushe zai fito Alh ya ce sai la'asar sakaliya suka yi sallama bayan ya tuna ma Alhaji kudaden abincina da yake ba shi duk sati ya ce ba damuwa da safe zai sanya.