HAYAT NAZLI

19

by @maryamannour71


Chapter 19 

 

Washe gari sun tashi da tsumayin dawowar Alhaji Auwal Badamasi, tun safe suke ta shirye shiryen tarban zuwansa, da Nazli a ka yi komai, kamar yadda Hajiya Binta ta buƙata da niƙab ta zo ta sunɓula dogon hijabinta da ya sauƙo mata har ƙasa. Tun safe suke cikin kitchen suna girke girke kala kala kama daga abinci zuwa small chops, gidan ko sai tashin ƙamshi girki ya ke kai ka ce gidan biki ne ko suna. 

 

12:00 dai dai na rana suka gama girki, kasancewar Alhaji Badamasi ya sauka yana airport driver ya je ɗauko sa Hajiya Binta ta haura sama domin shiryawar tarban mijinta a ka bar Nazli da tsaftace wuri. Bayan gyara ko ina lungu da saƙo na gidan ta kuna buner ta sa tuarare wuta nan take gidan ya kama ƙamshi ta ko ina. Duba da babu wani aiki da ya rage ya sa Hajiya Binta bata izinin tafiya gida bata da buƙatar ta kuma a yau sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, dan haka ta sallame ta ta bar mata gida tun kafin Alhaji ya zo ya gan ta cikin gidan.   

 

NAZLI. 

 

Koda isar ta gida bata tarar da Ammie a gida ba ta fita kasuwa, a gajiye ta shigo gida duk gaɓoɓin ta na mata ciwo dan ba laifi ta aikatu a gidan Hajiya Binta a yau ba wasa, dan kusan rabi da kwatan aiki duk ita ta yi ita dai Hajiya Binta na ta baki ne ɗauki wannan maida wancan amma duk ita ta yi aikin girkin gami da shara. 

 

A kasalance ta shiga nan baranda ta sulale ta kwanta ta furta. "Washh Allah na gaji." Ta jingina kanta da bangon wajen tare da lumshe idanu cikin sauke ajiyar zucin gajiya, tafi minti 15 a wurin sai dai ta ɗan maida gajiya ta soma dawowa dai dai ta miƙe ta zuba ruwa a bokita ta shiga watsa ruwa, minti ƙalilan wankan ya ɗauki ta fita.  

 

Bata wani sanya kaya mai nauyi ba, vest ce mai siririn hannu ta sa tare da daura zani sai hula da ta tattara tulin gashin ta ta saka. Saboda mugun zafi da ke a garin ya sa bata wani shafa komai ba ta fita ta zauna, bayan ta aje hijab a kusa da ita ta kwanta babu daɗewa kuwa baccin gajiya ya yi awon gaba da ita a nan barandan. 

 

Hayaniyar da ta soma ji a cikin baccin ta ne ya sa ta farkawa, a hankali ta soma buɗe idanuwanta har ta buɗe su tarr kan Ammie da su Sadiq da suka gama shigo mata da kayanta tana raba masu gurlee da ta siyo a kasuwa saboda hakan. Tashiwa ta yi a hankali ta gyara dauren zanin na ta daga zaunen da take ta dubi Ammie ta ce. "Ammie sannu da gajiya har kin dawo kenan ban sani ba." Fuska a sake Ammie ta amsa mata inda ita ke mata ya ban gaji ta amsa da lafiya, tashi ta yi ta nufi randarsu ta ta deɓar ruwa a cufi ami sanyi ta kawo ta miƙa ma Ammie, ba musu ta ƙarba da gode ta sha.  

 

Ammie ta jawo ɗaya daga cikin bakon  

 

 da ta yi siyaya da a ciki ta fidda salat da sauran gurlee da ya rage ta ce. "Ga wannan wanke ki yanka mana mu ci." Ta nuna kular abinci da ke kitchen ta gefe ta ce. "Haɗo da shinkafar can wurhaka na san ba ki ci ba kawo mu watsa a sama mu ci." "To Ammie." Daga haka ta tashi ta shiga kitchen ta dauki wuƙa da kwalanda ta fito ta soma gyara kayan salat ɗin, Ammie ta wurga mata wata ɓakar ledar da faɗin. 

 

"Kya samu na canzawa ke ma." Wata irin kunya ce ta kama Nazli ganin bra da panties ne sabbi da ta siyo mata. "Gwada ki gansu idan sun miki daidai, ni sai da ma na bar wurin matar na soma tunanin ko za su miki dan na ga kema dai tubarkarllah ma sha Allah kina da kaya ba mai iya miki gori." Wata kunya ce ta sake kama Nazli ji ta ke ina ma ƙasa ta tsage ta shiga, wato duk nuƙu nuƙun ta Ammie na lura da ita ta san komai na ta? Da sauri ta miƙe ta shiga ɗaki da gudu tana ɓoye fuskarta cikin kunyar kalaman Ammie wanda hakan ba karamin baiwa manyan hips dinta dake baje cikin zane motsawa ba kamar na wata babbar mace irin hajiyoyin nan da suka gama kwanciya cikin kudi naira ta wadace su suna cikin kwanciyar hankali. 

 

Nazli koda ta shiga ɗaki vest ɗin jikinta ta cire ta soma gwada rigar nonon, kamar kuwa Ammie ta sani sun mata ƙanƙanta amma za ta iya managen su ta na canji da su. Ƙuri ta yi ta zubawa ƙirjinta ido tana ƙare ma halittar kanta kallo, a hankali ta saka hannu saman kirjin na ta tana taɓawa kamar wacce ke son auna girma da nauyinsa, ta ɗan juya gefe ta kalli mazaunanta daga cikin madubi haka ta yi ta juyi tana kallon kanta sai sakin murmushi take tana farin ciki.  

 

Daga wajen da Ammie take ta ɗaga murya ta ce. "Ya dai! Ba su yin bane  ki aje gaba in zan koma na koma da su a canza." A firgice ta dawo hankalin ta cikin sauri ta cire bra ta maida cikin leda ta saka cikin akwatin kayanta kana ta juya ta fita. "A'a Ammie ba sai an maida ba sun yi." "Kin tabbata?" "Ehh Ammie na tabbata." Ta zaɓi yi mata ƙaryar ne dan har yanzu tana bala'in jin kunyar ta ba za ta iya fitowa fili ta fada mata sun mata ƙananu za ta yi managen su a haka har zuwa sanda za'a biya ta albashinta ta shiga kasuwa ta yi siyaya da kanta. Daga nan ba wanda ya kuma faɗin komai cikin su Nazli ta koma ga yanke salat na ta yayin da Ammie kuma ta cigaba da buɗe ledodin ta shigo da su. 

 

======= 

 

Zaune ya ke a ƙasan rumfa kalan ta fulani ta shan iska wacce a ka ƙawata ta da fararen kujerun roba na zaman shan iska, ya ɗaura kafafunsa kan center table ya baje cikin kujera hannunsa riƙe da takardar jarida yana karantawa, yayin da idanunsa sanye suke da farin glass.   

 

Alhaji Auwal Badamsi kenan, dattijon magidanci ne da a ƙimance zai baiwa shekaru arba'in baya, ɓaki ne mai ɗan jiki ga tunbi, ba za'a saka shi cikin jeren masu kyawu ba amma hutu da jin dade ya ɓoye muninsa. Farar jallabiya ce a jikinsa ya maida bayansa ya jingina da kujera. Ya maida dukkan hankalinsa kan karatun jarida da ya ke,  sai dai lokaci zuwa lokaci ya kan ɗaga kai daga inda yake zaune yana kallon harabar gidan. 

 

Sule mai gadi da fitowarsa kenan daga bayi da buta a hannu yana goge bakinsa da aswaki ya ji ƙwanƙwasowar ƙofa, ya a je butar hannunsa ya yi ƙofa cikin ɗaga murya ya ce. "Waye?" Cikin sanyi da zazzaƙar muryarta ta amsa ma sa da. "Ni ce." Da jin muryar ya waye wacece, babu yawon surutu ya buɗe ƙofa tare da bata hanya ta wuce. 

 

Cikin nutsuwa irin na ta Nazli da sallama a bakinta ta saka ƙafa cikin gidan, ko ta kan Sule da ke washe mata haƙora da zabga surutu bata bi ba ta yi shigewar ta ciki dan wannan ba shi ya kawo ta. Abin da ta saka a gaba shi ne aikinta wanda kuma bata hada shi da komai ciki kuwa har da magana da Sule wanda bai saka komai a rayuwarsa sai shiririta da surutai da basu da kan gado.  

 

 Alhaji Badamasi da tun shigowar Nazli a kan idonsa ne ya masa alama da hannu kan ya zo, cikin sauri da gudu gudu ya isa gabansa har ƙasa ya tsuguna ya na mai faɗin. "Alhaji ga ni." Gyara zaman glass din idonta sa ya yi cikin kasa kasa da murya kamar wanda bai son kowa ya ji su ya ce. "Wancan fa?" Daga ina take?" "Ahh Alhaj! Sabuwar mai aikin Hajiya kenan, bata dade da fara aiki ba yarinya sai shegen kyau kamar wacce ta haɗa dangi da aljanu." Ya soma zuba, ganin kalan kallon da Alhaji Badamasi ya basa ne take ya shiga taitayinsa cikin rawar murya ya ce. "A gafarce ni ranka shi dade."  

 

Bai ce da shi  komai ba sai nuni da ya yi masa da ya yatsa da ya bashi wuri, cikin sauri kuwa ya bar wajen yana dafe bakin sa yana godewa Allah da bai saki layi dayawa da har ya sa ya faɗi abin da zai zo yana dana saninsa daga baya, barin ma da ya tuna Hajiya Binta take kuwa jikinsa ya yau ɓari yana fatan ba za ta ji wannan maganar da ya yi da Alhaji. 

 

Nazli kuwa koda ta shiga palo bata tarar da kowa ba, ta so haurawa sama ta same Hajiya Binta da tambayar aikin sa za'a yi amma da ta tuna Alhaji fa na gari ba lallai bane ya kasance tana ita kadai ba ya sa ta fasa ta koma falon ta zauna zaman jiran saukowar ta dan bata lura da Alhaji Badamasi a waje da ta ke shigowa. 

 

Tafi minti 10 a zaune amma shiru bata ji motsin koda yaran ne bare mai gayya mai aiki wato Hajiya Binta, hakan ya sa ta yanke shawarar ta shiga kitchen ta duba idan da wuyar rige wasu ayyuka kafin fitowar madam.