HASASHEN SOYAYYA

HS 1

by @legendspen

*HASASHEN SOYAYYA*
_Imagination of love_

Free Book. 


       _Story & Written By_
_Amanar-Janafty_
*SAYYID LEGENDSPEN*
                          

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*


_Page 01_







Labarin rayuwar Bhatool Senate,Soyayya mai ɗauke da salon burgewa, rayuwar aure mai cike da hargitsi da ruɗani.



Matashiyar buduruwa ce wacce aƙalla zata kai shekara 22 zaune a backseat na motar ƙirar GLK, tana sanye cikin atamfa Super holland mai adon ja da touch din green, fara ce kyakkyawa tagani tafaɗa, tana da tsayi amma ba doguwa can ba, dara-daran idanunta masu matukar kyau, haka ƙananan pink lips dinta masu ɗaukar hankali, green veil ta yafa sai kuma ƙaramar handbag da takalmi golden cloud, wuyanta yasha manya sarƙoƙin gold haka yatsunta.

Yau ne fitar ta farko tun bikinta da aka yi, watanni uku da ya wuce, wannan shine karon ta na farko zuwa makaranta tun bayan bikin na ta. 

Tunda driver yayi parking motar tasu wacce a wajen rubuta lamba aka rubuta *Senate* gaba ɗaya hankalin yan matan yayo kan motar, driver ne ya fito daga wajen da yake tare da buɗe mota ƙofar inda take zaune, hill sheo ɗinta ne ya fara fitowa kafin kuma ita ta fito, ai tuni wajen ya ruɗe da faɗin. "Fatima senate! Fatima senate!!."







  ~ Asalin labari ~

Fatima Ahmad Ishaq shine asalin sunanta, haifaffiyar garin Yobe state cikin unguwar Nyan'ya, Mahaifinta Malam Ahmad dan kasuwane mai rufin asiri yayi aure tare da matarsa Habiba da yara guda uku.

Karima itace babba, sai kuma Fatima da ƙaninta Abdulwahab wanda tsiran shekara ɗaya ne tsakaninsu,hakan yasa suka zama abokan tsama na gaske.

Cikin yaran Malam Ahmad Allah ya jarabceshi da son Fatima, tun baya iya bayyanawa har ya fara, Habiba tayi duk ƙoƙarinta wajen kar ya bayyana hakan domin zai'iya kawo saɓani cikin yaran nasu.

Sunanta Fatima amma ana kiranta da Bhatool, Bhatool ta taso yarinya mai rawar kai, gayu da kuma iyayi, ko magana Bhatool take abun tsayawa a kallane, bare kuma tafiya da yanayin rayuwarta.

Wanan rawar kai ta Bhatool taja mata rashin so daga ɓangaren mahaifinta, waƴanda dama basa wani ƙaunar mahaifiyarta tun farko, saɓanin Karima wacce take shiru-shiru bata da wata damuwa, tana da haƙuri.

Haka shima Abdulwahab, bashi da wata damuwa, idan kaga damuwarshi ko hayaniyarshi to da Bhatool ne, domin shi a yanayin rayuwarshi ma bashi da hayaniya, shiru yafi yawan maganarshi, Bhatool ce kaɗai kansashi magana harda faɗa da hayaniya.

Karima nada shekara sha takwas, Bhatool sha shida, Abdulwahab kuma nada sha biyar. Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa sakamakon hawan jini daya dameshi.

Lokacin da rashin lafiya taci ƙarfinshi, yahaɗa amininshi Alhaji Aminu da Abdulwahab man yanuna masa harkokin kasuwanci, domin yasan yana mutuwa ƴaƴansa da matarsa sun rasa gata, yasan halin ƴan-uwanshi ciki da bai, haka bayan ya haɗa Abdulwahab da Alhaji Aminu yanemi Alhaji Aminu daya raba dukiyarsa gida uku, ya ajiye gida biyu zuwa sanda ƴan uwansa zasuyi rabon gadonsu na son zuciya, sai yaɗora Abdulwahab akai yasan zaikula da kanshi da ƴan-uwanshi.

Haka kuma acikin gida bashida magana sai dai.

"Habiba ki kulamun da yarana, ki tsaya kai da ƙafa su samu ilimi da rayuwa mai kyau."

A cikin ƴaƴansa kuma bashi da magana sai.

"Ku haɗe kanku, kuzama tsintsiya ɗaya maɗauri ɗaya, kuso junanku, ga kuma amanar ƴar-uwarku nan Bhatool ku kula da ita, takasance mai rauni, Abdul Allah ne gatanku, kaine gatansu, kazama gatanta,kar kabari ko sau ɗaya tayi kukan rashin mahaifi."

Sai yajuyo ga Karima itama ya fara.

"Karima kizama babba, komai ki ɗauka Bhatool ƙanwarki ce mai kuma rauni, ki zama yayata ƙwarai a gareta, karki bari ko sau daya tayi kukan rashi na."

Da irin waƴanan kalaman yake kwana yake tashi, kowa yasa ba dasu a cikin gidannan, ranar da zaiyi magana ta ƙarshe dasu ya tarasu baki ɗaya, ya fara magana.

"Karima, Kamar yadda nasha faɗamiki ke ce babba,Allah ne gatanku kece na ƙannenki, Allah zai buɗamiki, domin ki kula da ƙannenki, ga Bhatool nan ako yaushe ina faɗamiki, dan Allah dan Annabi karki bari koda sau ɗaya tayi kukan rashin mahaifi."

"Fatima! Karima yayarki ce, Abdulwahab ƙaninki ne, inaso ki haɗa kiyimusu biyayya kai ɗaya shida yayarki, ki maidashi yayanki, Bhatool koda sau ɗaya karki bijire musu, nasan bazasu taɓa barinki kiyi kukan rashi na ba."

"Abdulwahab! Kaine ƙarami amma Allah ya baka girman, kazama uba a garesu, kazama bango a garesu, kubi umarnin mahaifiyarku sau da ƙafa, Abdul ko sau ɗaya karka bar ko ɗaya tayi kukan rashi na."

"Karima banida abinda zance miki, kiyi tarbiya a wajen yaranmu, amma ako yaushe ina faɗamiki amanar Bhatool."

Shuru sukayi baki ɗaya, sun saba jin irin wannan maganar awajenshi, amma na yau sai yayi musu daban, harta Bhatool dake jindaɗi idan yayi irin wanan maganar amma yau sai abun yazo mata wani kala.

A daren ranar Alhamis wayewar garin juma'a Allah yayi mai rasuwa, wacce ta kiɗima iyalanshi haka kuma ƴan-uwanshi sukazo sukayi ta ihu, bayan kwana uku sukace sunaso araba gado.

Malaminsu na bogi suka ɗakko yazo yayi rabon ha'inci da son zuciya, ya kwashe rabi da kwata na dukiyar yabasu, ƙarshe dai gidan da suke ciki suka tsira dashi.

Bayan ƴan-watanni da rasuwarshi Alhaji Aminu, ya buɗewa Abdulwahab babban shago a kasuwa, bayan yayi mai tsallake-tsallake a makaranta ya tsira da takardar gama secondary.

Abdulwahab ya fara kasuwanci, kuma Allah ya dafa mai aciki, Karima da fatima sun cigaba da makaranta, suna rayuwa cike da nutsuwa abubbuwa daya ba sufi ƙarfinsu ba.

Ana wannan matakin ne kuma ƴan-uwan mahaifinsu waƴanda basu sake bibiyarsu ba, tun mutuwar mahaifinsu suka zo da buƙatar sunason aurar da Karima da Bhatool, a lokacin Karima nada shekara sha-tara zuwa Ashirin ita kuma Bhatool tana da sha bakwai.

A lokacin akwai wani mutumi da suka haɗu da Karima lokacin tana aji na farko a makarantar kwaleji ta, Shehu Sule collage of Health science shiyasa da sukazo da maganar, Maman tace musu Karima nada wanda takeso amma Bhatool ba yanzu zatayi mata sure ba, domin ko secondary school bata gama ba, sanan shekarunta basu kaina wacce zata yi zaman aure ba, ga kuma halinta na rawar kai ba kowanni namiji bane zai zauna da ita.

Wanan kalami na Mama ya tayar da tashin hankali babba ba ƙarami ba, a cikin ahalinsu domin su akwai wanda ma sukesu subawa yaran a cikin ƴaƴansu dasuka lalace, sanan kuma sunsami labarin yanda kasuwancin Abdulwahab ke haɓaka a kasuwa, amma Mama ta d'age ta tsaya sosai domin tasan aure shine cikon rayuwar ƴa mace, to baza taso akai su inda aure zai wahalal dasu ba, bata taɓa magana akan hukuncin da suka yanke akan yarantaba sai yanzu.

Badan ransu yaso ba, Bashir ya gabatar da kansa a matsayin wanda yake son Karima, aka saka lokacin aurensu wata shida.

Su da suka zaƙe akan sai an aurar da yaran baka ƙarajin bakinsu ba, sun koma gefe sai Mama suka bari da ƴan-uwanta, daman kuma Maman mai tanadace.

A haka bikin Karima yazo da mijinta Bashir wanda yake ma'aikacin NNPC, a lokacin wannan bikin ne Bhatool taja magana mai tsayi cikin ƴan-uwanta domin abunda tayi, tayi ɗinkuna irin waƴanda ake gani a jikin ƴan film da kuma mutanen da akewa kallon ƴan-iska su *Zuge darling*, *Show me your back* da sauran ɗinkuna, hakama eyelashes (gashin ido) a wanan lokacin a iya idanun ƴan film ake ganinshi sai kuma waƴanda ba musulmai ba, ga kuma karin gashi na brazil mai-jar kala.

Wannan abu ya jawa Bhatool magana sosai da sosai, wasu nacewa tazama ƴar iska, wasu na cewa zata zama,haka akayi biki aka tashi kowa da magana a bakinsa.

Haka rayuwarsu Bhatool taita tafiya, tana samun duk wata kulawa a wajen ƴan-uwanta baki ɗaya, barima yanzu da Karima ta yi aure kuma mijinta irin mazajen nan da'ake kira *mijin marainiya ne*, domin duk wata buƙatar data ƴan gidansu ya ɗauke mata, ya tsaya mata akan karatunta harta kammala, yanzu haka yana ciku cikun buɗemata clinic ne.

Haka shima Abdulwahab yazama babban ɗan-kasuwa mai nasibi, gashi yaro amma da manyan ƴan-kasuwa yake mu'amala, ya koma karatu part-time a yanzu haka akwai shagona guda biyu bayan na farko da akabuɗe musu.

A ɓangaren Bhatool ma, yanzu ta girma kyawunta ya ƙara fitowa, gayu da iyayi sunƙaro amma yanzu sun haɗu da ilimi da wayewa, komai nata classy ne.

A yanzu tana first year a jami'ar Yobe State University (YSU), tana karanta Entrepreneurship. A yanzu haka suna first semester ne sababbun ɗalibai, ƙawayenta guda uku ne waƴanda suma gani sukayi halinsu yazo ɗaya kuma tana burgesu yasa suka nemi ƙwance da ita, domin Bhatool akwai farin jini.











~~~~~Unguwar Red Bricks 

Makeken gida ne iya ganinka, ya gaji da haɗuwa tundaga girman shi, yanayin tsaruwar shi da kuma adon shi.

Gida ne irin flat house amma mai girma sosai da sosai, part ɗaya ne mai girma da kuma tsaruwa.

A cikin gidan wani ƙaramin part wanda a ƙalla shima yayi girman wani gidan, kyawawan samari ne guda biyu, ɗaya fari ɗayan kuma baƙi.

Farin baya kama da mutanen Nigeria gaba ɗaya, yafi kama da mutanen ƙasashen larabawa,amma yanayin sumar shi yana akwance kuma ya zubo har zuwa wajen giransa kamar na ƴan Korea.

Lips dinsa pink ne sosai da sosai kamar baitaɓa kai wani abu bakinsa ba, girarsa a cike take da gashi kuma baƙi ne huluk, ɗayan kuma baƙine, kuma mai kyau amma kuma baikai ko rabin kyan farin ba, baƙin ne yake ta magana amma farin ya yi shiru.

"Senate magana nake fa."

Shiru yaƙarayi amma idanunsa nakanshi, ko ƙiftawa bayayi.

"Idan bazakayi magana ba I will leave.."

Girgiza masa kai yayi alamun "A'ah"

"To talk."

A hankali yafara magana yana buɗe karamin bakin kamar mai koyan magana.

"Bud-die."

Wata iriyar murya mai mugun sanyi da sanyaya zuciya.

"Basan ta'ina zanfara ba."

"Fara ta ko'ina, Senate."

"Idan naganta zuciyata canja bugu take, tanayi da ƙarfi kaman zata fito, and I'm scared." Yaƙara faɗa cikin sassanyar muryarsa, kallon shi ya yi sannan ya ce:

"Wace?."

"Idan bangantaba bana jindaɗi, zanjini empty, Idan nayi nesa da ita zanji kamar I'm leaving what I love the most."

"Senate who is she?."

Girgiza kai Senate ɗin ya yi sannan ya ce: "Actually I don't even know her name."

"A ina kake ganinta?."

"School."

"Which school?."

" ( YSU)."

"What take you to Yobe state university, Senate?."

Girgiza kai yafarayi kamar ƙaramin yaron dayayi laifi aka kamashi, sannan ya ce. " Naje wajen wani secondary school mate ɗinane da mamansu ta mutu, time ɗin ina Cyprus, shine naje yimai gaisuwa ya ce muhaɗu school ɗinsu."

"Kafaɗawa Momy?."

"Nope naso faɗamata amma nakasa Anas, shiyasa nakiraka inajin tsoro."

Murmushi Anas yayi domin yasan tabbas dagaske Senate ɗin najin tsoro, domin haka allah yayi sanyi kamar ƙaramin yaro, magana ahankali sanan babu abinda take tsoro kamar mata, amma fa yanada zafi sosai idan yatashi ɗaukan zafin, he is cool but difficult to handle.

"You know you have to tell her ko?, dan bazan yi advising naka ba daga baya kaje kace nina hanaka faɗamata."

"I will okay, but please Anas what do you thinks is this?."

Dariya Anas ɗin yayi sanan ya ce. "Might be you fall in love."

"Love." Senate ya faɗa aɗan tsorace.

"Yes."

Anas ya faɗa tare da ficewa, kwantawa yayi kan gadonsa tare da rufen idonsa, amma itaɗin yagani ɗazu cikin ƙawayenta suna hira tana ta dariya amma cike da yanga da kuma gayu, bude idon yayi sannan kuma ya sake rufeshi.










~~~~~~ Yobe State University (YSU)


Bhatool da team ɗin ƙawayenta zaune wajen da suka saba zama suna hira, ɗaya cikin ƙawayen nasu mai suna Jannah ce ta ce:


"So yanzu ankon yakama 78thousand kenan, Kuma payment ɗin cikin satinan za'ay."

Daga kai sukayi sannan ɗaya maisuna Amrah ta ce. "Nan da 2weeks bikin, amma gaskiyya Suhaima baki kyauta mana ba, aiko engagement ɗin kyafaɗamana muzama cikin shiri, yanzu ina zamuje mu samu dubu ɗari da motsi."

Dariya wacce aka kira da Suhaima tayi sanan ta ce. "Time ɗin da muka shigo school ɗinan ai anyi engagement ɗin, kuma nasan ku big girls ne sannan kuna da rich-boyfriend's they can afford anything for you."

Sai a lokacin Bhatool ta bud'e baki ta yi magan. "Amma Suhaima kinci kai, kina tunanin samarinmu kemana wannan sutturar, to ni wallahi Yaya Karima da Abdulwahab ne, kuma nakaisu bango banji zasuyimun naki."


"Nima dai nakai Anty bango, banjin zatayi mun."Amrah ta faɗa tanakai hannunta kan cinyar Bhatool tana taɓota da alamun gulma.

"What?."Bhatool ta faɗa tana dukan hannun Amrah.

"Have you girls notice this guy." Amrah ta faɗa tana nuna musu Senate da baki wanda ke zaune ɗan nesa dasu yana danna wayarsa, amma hankalinsa nakansu kuma zuciyarshi na bugawa da saurin data saba.

"Yes." Jannah ta faɗa sannan taƙara cewa. "Kusan 3weeks kenan."

"Nikam bantaɓa kula dashi ba." Cewar Bhatool cikin ranta, domin da gaske bata taɓa kula dashi ba.

"Gaskiyya yadaɗe yana bibiyarmu, namayi tunanin ɗaya cikinmu yakeso." Suhaima ta faɗa, tana kallonsu shiru Bhatool tayi na ƴan-mintina saikuma ta ce.

"Ku barshi Allah yasa gobe yazo."

Daganam suka tashi sukabar wajen, shi kuma yayi shiru na cankuma ya ce. " I have to tell my Mother."

Daga haka ya tashi ya nufi motarsa ya wuce gida, su Bhatool kam wata lectures ɗinsuka shiga, sannan su a tsarinsu koda sungama lectures basa tafiya gida sai shida, kullum fitar takwas komawar shida.








~~~~~Red bricks

A makeken main falo ɗinta ya sameta, wanda yasha ado da tsadaddun royal chairs, datijuwar mata wacce kuɗi da ilimi suka ɓoye shekarantu, domin a kallon farko zaka iya cewa batafi shekara 30 ba wanda a zahiri takai shekara 45, farace itama mai kamanni da larabawa, tana sanye cikin wani ɗan ubansu lace maroon clour.

Shigowa yayi ba tare da yace da ita ko ƙala ba, zama ya yi nan kujera tare da haɗe hannayensa biyu ya zuba tagumi.

Matsowa ta yi kusa dashi tare da sa hannu ta cire mai tagumin da ya yi.

"My prince, what is going on?."

Kallonta yayi idanunshi cike da ƙwalla, a hankali ya buɗe baki ya ce. "Mom! I'm scared."

"What happen, and what are you scarring for?."

"Mom the girl."

"Which girl?."

"Mom Idan na zauna kusa da ita, zuciyata na bugawa da ƙarfi kamar zata fito, idanta tashi zata fice zanji kamar ina nesa da abinda nakeso, idan banje naganta ba banajin daɗi, I don't know what to do Mom."

"Nutsu kaji! Faɗamun komai from the beginning."

More chapter on Arewapen
ku yi following Arewapen, domin samun notification da zarar mun ɗaura, Free book ne

Legendspen
***