Hs 2
by @legendspen
*HASASHEN SOYAYYA💅*
_Imagination of love_
_Story & Written_
_By_
_Amanar-Janafty_
*Sayyid Legendspen*
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
_Page 02_
"Mom Idan na zauna kusa da ita, zuciyata na bugawa da ƙarfi kamar zata fito, idan ta tashi zata fice zanji kamar ina nesa da abinda nake so, idan banje naganta ba banajin daɗi, I don't know what to do Mom."
"Nutsu kaji! Fa'amun komai from the beginning."
Shiru yasa ke yi sai kuma bakinsa dake karkarwa, jawo shi tayi tare da ɗaura kanshi akan cinyarta ta fara shafa masa gashi.
A hankali ya fara sauke ajiyar zuciya, sai da yaɗau kusan minti goma sannan ta fara magana.
~~~~~Usman Yunusa Ahmad
Shine asalin sunansa, haifaffen garin Yobe state Damaturu kamar yadda mahaifinsa yake. Saɓanin mahaifiyarsa dake yar asalin garin kano.
Alhaji Yunusa babban mai kuɗi ne wanda akaf garin Yobe asandashi da kuɗinsa. Babban ɗan kasuwa ne wanda yake kasuwanci har kasashen ƙetare.
A lokacin da yaje Kano gudanar da wani harkar kasuwanci ya haɗu da Zainab wacce yaji ta kwanta masa arai kuma ya yi magana da iyayensa da ƴan-uwansa sukayiwa nata magana akasaka lokacin aurensu.
Bayan anyi auren suka fara gudanar da rayuwar aure mai kyau da tsafta, Yunusa na bata lokacinta a matsayinta na iyalinsa, haka itama tanayi masa biyayya iyakacin yinta, sukan ware lokaci sufita ƙasashen ƙetare.
A wani lokaci da sukaje ƙasar Dubai suka daɗe wajen wata shida, a lokacin ne Zainab tasamu ciki.
Yunusa yayi murna sosai da sosai hakama ƴan-uwansa da kowa da kowa.
Sai da cikin yakai wata bakwai sannan sukabar Dubai, suka tafi Korea inda ananne kuma ta haihu, yaron yaɗakko kammanin mahaifinsa amma yana yanayi da larabawa kodan a ƙasarsu akasami cikinsa, haka kuma gashin kasan ya yi kama dana ƴan korea.
Bayan yaron yayi wata ɗaya suka huce Saudi Arabia alokacin aikin hajji suka gudanar da Hajjinsu, sannan suka dawo gida.
Usman ya taso cikin gata- gata na gaske domin Usman ko zaman sati biyu cikakke bayayi a Nigeria, Nursery School kawai yayi anan amma ko primary school ɗinshi acan south korea yayi, lokacin dasuka tafi tare da Mahaifiyarsa. Wacce bata dawo ba sai da yashiga Junior secondary school.
Sai da Usman ya gama Secondary school kuma yatafi Madina ya had'e haddarshi daganan kuma yakoma Cyprus ya cigaba da karatunshi.
Usman ya dauko sanyin hali dana mu'amala irin naƴan South Korea, idan yana magana kamar mai koya, tafiyarshi dai yanayinta cike da ƙasaita, bashida fushi ko kaɗan amma idan yayi fushi tashin hankaline domin bai iyaba.
Usman yanas on wasa, ya iya wasa da yara sosai sannan kuma yanason yara, ko dan shikaɗai ne wajen iyayensa, sannan yaransa yasa ko da yaushe gidansu yake cike da ƴaƴan-ƴan uwa.
Tun a south korea Usman yasamu sunnan "Senate" sunnan da ya karɓa yakuma ɗorawa kansa, duk da wani wanda yasanshi to da wannan sunan ya sanshi. "Senate"
Anas cousin Brother ɗin shi ne, ɗan wajen ƙanwar Momy wanda Usman take matuƙar ƙauna, yayarda dashi sama da kowa, Usman baya iya doguwar magana da mutane, Daga Momy saikuma Abba domin idan yana tare da Mahaifinsa yakan zama serious cikakken mutum, kowanan sanyin maganar bayayi,saikuma Anas yana magana da Anas sosai da sosai domin gani yake bashida wani ɗan-uwa kamar Anas. Tsiran shekara biyu ne tsakaninsu, shiyasa Usman yake gani kamar Anas ɗin ƙaninshi ne.
Senate yana da abokai guda biyu, Salman da Juraij, sukam sun iya rayuwa dashi a yanda yake, sun haɗu da Juraij a south Korea ne a primary school, shi kuma Salman abokin Juraij ne na gaske, hakan yasa suka zama abokai.
Senate bai taba jin rashin daɗin zama dasu ba, domin suna fahimtarshi akan komai, abokaine na ƙwarai, yana Cyprus mamansu Salman ta rasu, hakan yasa ranar da ya dawo yaje gidansu, anan yafaɗa masa yana school. Kai tsaye Senate yatafi School ɗin.
Shigar shi makarantar ya kira Salman waya, Salman dake lectures yayi text.
"Wait me at the Garden"
Okay kawai ya ce, Sanan ya nufi Garden ɗin. Tun shigowarshi makarantar yaji bugun zuciyarshi ya canja, yaƙaro amma ya alaƙanta hakan da yawan mutanen dake ciki, wani saurayi yagani yana tafiya, da sauri yace masa.
"Assalamu alaikum, Garden please?."
Hannu gayen ya ɗaga masa tare da nuna masa Garden ɗin, godiya yayi masa sannan ya wuce.
Shigarshi Garden ɗin ƙarin bugun zuciyarshi.
" Yasalam."
Yafurta dai-dai lokacin da yashiga Garden ɗin, sakamakon wani irin bugun da zuciyarsa tayi da mugun ƙarfi.
Guri yasamu ya zauna bugun zuciyarna daɗa tsananta, runtse idonsa yayi tare da fara sauke ajiyar zuciya, sautin da ya fara jine yafara rage bugun zuciyar, a hankali sassanyar muryarta ta shiga cikin kunnensa, ƙwaƙwalwarsa ta yi masa record and save ɗinta a lokaci ɗaya.
"Wani yaron zai cewa bazaiban ba, aikuwa na kwanta a ƙasa na ƙwalla ihu ina faɗin, Abba yau nayi kukan rashinka, kafin naƙarasa yayi sauri yatoshemun baki yana faɗin yi haƙuri Yaya nawa zan baki."
Dariya ƙawayenta suka saki sannan Suhaima ta ce. " Gaskiyya baki da kirki, duk ƙoƙarin da mutanen nan suke akanki gun mutuwar mahaifinku amma sai kince kinyi kukan rashinshi."
"Aikin ga ko Abdulwahab ko Yaya Karima, ke har Umma ma idan inason anko sai na kwanta a ƙasa nace nayi kukan rashin uba, last time Umma cewa tayi naita kukan rashin uban, amma nace mata nayi mafarki Abba yace bazaiyafe musu ba, ai Wallahi bayan anko Abdulwahab harda kaini Shopping."
Dariyar suka ƙarayi sanan Amrah ta ce. "Nikam wallahi Yaya Sulaiman yafi ɗanyen kashi ɗoyi, ai ban isaba."
"Ke waya faɗamiki Abdulwahab ɗin Yayanane, ƙaninane fa shiyake bini amma shine mai kuɗin."
Dariya suka sake wanda ko da yaushe idan suka zauna a wannan seat ɗin basu da aiki sai hira kala kala, daganan kuma ajuye gulma.
Kalmar rashin Mahaifi ta Bhatool tashiga cikin zuciyar Senate tasamu waje ta zauna gamgam, wanna hirar tasu itace ta dinga saukarmai da yawan bugum zuciyar harta yi dai-dai, hankalinshi nakan Bhatool da ƙawayenta, hankalin yan mata Yobe State Universtity nakan Senate.
Wayarsa ce tahau ƙara da sauri ya ɗaga yana faɗin:
"Man how far."
"Kana ta ina acikin Garden ɗin?."
"Ina daga wani gefe."
"okay naganka."
Yana Zaune Salman yazo yana faɗin. "Man how far."
Murmushi yayi sanan yace: "Nml Man ya ƙarin haƙurin Momi kuma?."
"Haƙuri sai ma'aiki broo."
"Yasu Haliman kuma."
Murmushi Salman yayi tabbas Senate yanada matuƙar damuwa da kula akan ƴan-uwan abokansa.
"Suna lafiya, kasan ayu engagement ɗinsu dukansu to yanzu kawai ansakko da bikin nasu nan da 3weeks."
"Masha Allah hakan yayi sosai da sosai, Abban yadawo ne?."
Girgizakai Salman yayi batareda yace wani abu.
"Ayyah to yanzu aina ka tsaya."
"Akwai wani gida na Mama shi akayanke za'asiyar harma antayashi 10million, za'ayi hidiman biki ragowar kuma a gyara shi wannan gidan damuke ciki zuwa ko hayane sai asa, nikuma zankoma gidansu juraij."
"Wannam shawarar tayi amma banajin yakanata asiyar da gidan man, sabida gaba zanbada tawa gudumawar insha Allah koda basu isa duka ba za'ayi wani abu."
Senate ya faɗa yana danna wayarshi, Transfer ɗin kuɗi yayiwa Salman ₦10'000'000 kuɗin daka taya gidan sanan yace:
"Wanam gidan abarshi Salman gaba zaiyi muku amfani and insha Allah zanyi magana da Uncle za'anema wane acikin company dinsu kafin ka ƙarasa degree ɗin, sai mubuɗe namun."
Hawaye ne sukafara fitowa daga idanun Salman, gun tasowarsu Senate da Juraij ke ƙoƙari akansu, yanzu haka Juraij ɗin shima yabashi 5million.
"Bani da bakin da zanyi muku godiya kunyimun komai a rayuwa."
"Shut off bro, mene haka dan Allah. Menene amfanin abotar da ba'a taimaki juna ba?."
Shiru Senate yayi domin jiyayi zuciyarshi na tsinkewa kamar yanarasa abinda yafi ƙauna, rufe idonshi yayi yasoma faɗin.
"Inna'illahi wa'inna illahir raji'un."
Da sauri Salman yariƙeshi da faɗin. "Senate lafiya, meyafaru?."
Shiru Senate ɗin yayi kusan minti biyar kuma bugun zuciyarshi yafara dai-daituwa, a hankali yabuɗe idonshi ya kalli Salman sai kuma ya kalli inda ƴan-matannan suke amma babusu.
"Meyafaru?."
Salman yaƙara tambayarshi.
" I don't know wallahi, kawai naji bugun zuciyata yasauya."
"Yasalam yakamata kaga likita."
kai kawai yaɗaga sanan yace:
"Yanzu zakatafi ko kana school ɗin."
"No ina school."
"Okay Sai anjima."
Senate yafaɗa tare da tafiya, bin bayanshi Salman yayi yana faɗin.
"Ka tsaya naraka kamana."
Buɗe baki yayi daniyar yin magana amma yaji zuciyarshi tabuga da wani irin ƙarfi.
"Wallahi bazan shiga class ɗinnan ba, jifa yanda ajin yacika ko attendance bayi zaiba."
Ya jiyo sansanyar muryata na magana, da sauri ya juyar dakai idanunsa suka sauka akan kyakyawar fuskarta, da ɗankaramin bakinta dake magana. Dum yaji Zuciyarshi tabuga da wani mugun ƙarfi sakuma bugin yadaidaita.
Ƙuramata idanu yayi yana kallonta, yanayin yanda take magana ya haifar masa da wata kasala ta mussaman,bai taɓa kallon mace yaji wani yanayi bayan na tsoro sai wanan, wani irin abu yake gani a ciki Idanunta masu kamada taurari.
"Man mekake kallo?."
Da sauri yajuyo ya kalleshi yana faɗin.
"Na'am, muje"
Tafiya sukayi amma baidaina waigen taba, haka yadawo gida yanajinshi empty kamar yabar rabin rayuwarshi kowani babban ɓangare na rayuwarshi a wani waje.
Gaba ɗaya yakasa mantawa da fuskarta ko yanayin maganarta, haka yayini yana faman tunani, babban abinda ya tsoratashi shine yanda yakasa bacci daya rufe idonshi ita yake gani.
Haka washe gari yatashi da tunaninta, yakasayin komai. Haka kawai yaji zuciyarshi na azalzalallashi akan yatafi school ɗinsu, a dai-dai lokacin dayaje jiya kuma wajen da yasamesu jiya, wanan ganin dayayi mata shi yarage masa duk wani yanayi dayakeji a zuciyarsa.
Abu kamar wasa yazama kullum idan yatashi da wannan yanayi yake tashi, jinshi yake empty kamar bai cikaba har sai yaje yaganta, har zuwa yau daya fuskanci ƙawayenta sunfara noticing nasa.
~~~~~
Kallonshi take har yagama bata labari tundaga zuwanshi wajenshi wajen Salman har zuwan dayayi yau dakuma abinda ƙawayenta suka faɗa.
"Tsoranta kake itama?."
Girgiza kai yayi daga kwancen dayake akan cinyarta.
"Is different acikin zuciyata nakejin maganarta, idan nayi nesa da ita inajina empty kamar fankon ashana baby ƴaƴan ashanar aciki."
"Do you believe you're in love?."
"No mom, ta ina zansota bansantaba sai ranar kuma haka akeyinso daga ranar dakaga mutum?."
"Tashi nabaka labari."
Tashi yayi ya zauna yana kallonta, itakuma tafara magana.
"Kasan Dad ɗinka ɗan Yobe state ne ko?."
"Yes Mom."
Yafaɗa tare da daga kai.
"Good! kuma kasani yar kano state ce ko?."
"Yes Mom."
"Bakayi mamaki ta inda muka haɗu ba?, zuwan Dad ɗinka kano nafarko yahaɗu dani,kuma a lokacin yafara sona, kuma yabbayanamun and nayi accepting ɗinshi, to kaima haka ne."
"Mom bangane ba?."
"Senate kafaɗa soyayyar yarinyanan a lokacin farko dakaganta wanan shi ake kira "Love at first sight"."
Shiru yayi alamun yatafi tunani, itakam tana tunani take ɗanta yafaɗa soyayya mai zafi da kuma nauyi, gashi ɗanta tasan yanda take itadai fatanta Allah yasa yarinyar ƴar mutunci ce, wacce zata kula da rayuwar ɗanta.
"Mom mene solution?."
Ta tsinkayi muryarshi, kallonshi tayi sannan tace:
"Kaje kasameta."
"Mom I can't."
"Kaifa namiji ne zaka iya."
Girgiza kai yayi idanunsa suka ciko da ƙwalla kamar zaiyi kuka.
"A haka zakace kanason yarinya, zakaje mata kana hawaye salan ta raina ka...
More chapters on Arewapen. idan kuka yi following zaku dinga samun Update akai akai
Legendspen
***