62
by @halimahz
Don Allah don Annabi ku yi haƙuri da ni...abin da zan iya ce muku kenan.
With confusion Baffa ke kallon Turaki. Da ace a wannan lokacin wani likita zai zo ya gaya masa cewa wani ɓangare na ƙwaƙwalwar yaron ya samu matsala, da hakan ya fi masa sauƙin gaskatawa fiye da ya gaskata maganar da ta fito daga bakin Ɗansa Muhammad.
Saboda abu ɗaya ya sani...
Idan har a cikin ƴaƴansa akwai ɗan da zai rantse da Allah ba zai taɓa janyo masa abin kunya ba, to Muhammad ne.
Babu yadda za ai Muhammad ya ɗaura wa kansa aure ba tare da waliyyan da addini ya halatta sun tsaya masa ba. Muhammad ba ya cikin yaran da zai janyo wa iyayensa abun kunya da Allah ya wadai, babu ta yadda Muhammad zai iya zuwa ya je ya ɗaurawa kansa aure ba da sanin manyansa ba, bai san ta yadda ƙwaƙwalwarsa zata karɓi hakan ba a lokacin da Ɗan nasa zai maimaita masa ido cikin ido.
Wani irin zafi Baffa ya ji ya taso daga ƙasan zuciyarsa ya bazu zuwa gaba ɗaya ƙirjinsa. Ba zafin fushi ba ne kaɗai... Zafin takaici ne. Zafin cin amanar yarda, da tarbiyyar da bai taɓa tsammanin zata ruguje daga wajen ɗan da ya fi so ya fi yarda da shi ba.
Hankali kwance yake zaune a ɗakinsa yana kallon ball, Samha ta shigo a gigice har ta kasa haɗa magana yadda ya kamata.
"Baffa... zo... don Allah zo... Mum da Maama..."
Iyakar abin da yarinyar ta iya furtawa kenan. Yanayin fuskarta kaɗai ya isa ya tabbatar masa cewa ba ƙaramin al'amari ne ya ke faruwa ba.
Tashi ya yi tsaye tsam, bai tsaya yi mata tambayoyi ba. Da wannan hargitsin ya biyo bayanta da sauri. Har suka iso bakin ƙofar ɗakin Turaki. Lokacin da ya saka hannu ya murɗa handle ɗin ƙofar...
A dai-dai wannan lokacin ne kunnuwansa suka cafke kalaman Turaki.
"Maama... she is my wife... na bayar da sadakinta five months da suka wuce... na damƙa sadakinta a hannun mahaifinta."
Kalaman suka tsaya cak a kunnuwansa. Kamar an buga masa guduma a tsakiyar kai haka yaji kunnuwansa sun toshe dummm. Ya tsaya a bakin ƙofar ba tare da ya iya motsawa ba.
Idonsa ya sauka kan Turaki. Sai kan Fullo da sai hankalinka ya kai kanta kafin ka gane tana wajen. Ya sake dawo da kallon kan Turaki.
Kamar dai yana jiran wani ya ce masa duk abin da ya ji mafarki yake yi, ko kuma bai ji da kyau ba. Ya ɗan lumshe idanunsa a hankali, yana son tattara nutsuwarsa da yake jin tana neman gushewa.
Karɓar wannan maganar kaɗai ya fi ƙarfin zuciyarsa. Ta ina zai fara? Yana jin kamar bai sani ba, kamar a karon farko yana jin ba zai iya amsa sunansa na Alƙali ba.
A rayuwarsa ta Alƙalanci, ya saba warware rikice-rikicen abubuwan da suka shafi mutane. Ya saba sauraron ƙorafi da shaidu. Ya saba tantance gaskiya da ƙarya.
Amma a yau... Ji yake kamar idan ya ce zai tsaya sauraron ɗansa, zai rasa ta inda zai fara. Don yana jin kamar ba shi ne Alƙali Dikko ba. Kamar duk ilimin da shekaru suka tara masa yau ba za su masa aiki ba.
A gefe guda kuma...
Maama ta kasa ɗauke idanunta daga kan Turaki. Ko ƙiftawa ba ta yi. Ta rasa ta wanne ɓangare za ta fara tunani. Sam zuciyarta ta kasa karɓar abin da kunnuwanta suka ji. Tambaya ɗaya ce kawai ke ta kai komo cikin kanta.
A ina ta yi kuskure? A wane mataki ne ta gaza wajen tarbiyyar Turaki har ya iya zuwa ya yi wa kansa aure ba tare da kowa nasa ba tamkar dai wani haihuwar gaba da fatiha.
Me ya sa bata gano wannan ɓular da zata haifar musu da fitina ba tuntuni ta tosheta ba, sai a yanzu da take jin kamar kanta ya yi nauyin da ba zai iya ƙara ɗaukar komai da aiwatarwa ba.
Mum ta jefar da kwalbar hannunta, ta watsawa Bello wani mugun kallo wanda ya kafeta da idanu tun ɗazu, a tsorace yake da ita, kar ɓacin rai yasa ta ce zata zartar da hukunci da kwalbar hannunta akan Turaki.
Da sauri Bello ya sunkuyar da kansa, Wannan kaɗai ya isa ya tabbatar masa cewa kafin a fahimci Turaki za a kai ruwa rana.
Baffa ya sauke wata irin ajiyar zuciya mai nauyi. Ajiyar da ta fito daga can ƙasan zuciyarsa.
Har sai da kowa ya ji sautin fitarta. Sai kuma ya ɗaga kansa.
Muryarsa ta fito a sanyaye. Irin sanyin da ya fi kowacce irin tsawa firgitarwa.
"Ku same ni a parlo."
Kalmomi uku kacal. Ba ƙari. Ba ragi. Ya juya ya fita. Bai ƙara waiwayowa ba. Sai ƙamshin turarensa da nutsuwarsa da suka saba sanyaya zuciyoyi ne suka bar ɗakin da mutanen cikin ɗakin a fargaba. Yayin da shi kuma ya tafi ya bar musu wani irin nauyin da ya mamaye zuƙatansu.
Turaki ya ji gabansa ya faɗi. Wannan muryar ta Baffa... Ya santa sosai ma.
Idan ransa ya kai ƙololuwar ɓaci baya hayaniya. Sai dai ya yi shiru. Kuma wannan shiru nasa ne ya fi komai razana Turaki. Idan ran Baffa ya ɓaci gwara ya yi magana akan ya yi shiru, mutum yafi samun natsuwa.
Bello ya shafa kansa a hankali yana furzar da iska mai nauyi.
A zuciyarsa ya ce,"Yau kam mun shiga uku..."
Mum ta wuce ta gefen Turaki fuuu kamar zata tashi sama. Kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci cewa tana tsaye ne da ƙarfin hali kawai. Idan aka ƙara mata kalma ɗaya... Ko dai ta suma. Ko kuma ta aikata abin da daga baya ita da kanta zata yi danasani.
Turaki ya bi bayanta da ido. Sai ya dawo ya kalli Maama. Ya buɗe baki zai yi magana. Da sauri ta ɗaga masa hannu.
"Dakata."
Ta haɗiye wani irin ƙullutun baƙin ciki da ɓacin rai kafin ta ci gaba.
"Kar ɗan ƙwaya ya sake ya ce zai min bayanin da kaina ba zai ɗauke shi ba."
Hajiya Madina uwa ce mai matuƙar rauni akan ƴaƴanta, wata iriyar soyayya ce ubangiji ya dasa tsakaninta da ƴaƴanta da duk girman laifinsu kaɗan take ganinsa. Bata iya son abun da ya higa zuciyarta ba. Ba ta iya tsayar da hawayenta akan lamarin Yaranta, wala na farin ciki ko akasinsa. Ko a yanzu da ranta ke matuƙar ɓace, kokawa take wajen hana hawayenta zubowa.
Ta juya zata fita, har ta kai bakin ƙofa... Sai kuma ta tsaya. A hankali ta waigo. Idanuwanta suka sauka kan Turaki. Ta dube shi na wasu sakanni. Ba ta san taƙamaiman abin da take ji ba.
Ciwo ne? Takaici ne? Ko kuma rashin yarda da abin da ya faru?
Ita kanta ta kasa tantancewa. Sai da ƙyar ta buɗe baki, muryarta ta fito a raunane, raunin da ya fi kuka ciwo.
"Ka zalunce ni..."
Ta yi shiru na ɗan lokaci tana haɗiye tsananin ɓacin ranta. Sannan ta ci gaba. "Ka ɗauki haƙƙina, ka tarwatsa min wani farin ciki da alfahari da na daɗe ina rayuwa da shi a zuciyata."
Ta ɗora hannunta a ƙirji.
"Duk duniya kai ne mutum na farko da zai iya ba da shaida cewa ba haka na shirya wa aurenka ba."
Ta girgiza kai cikin takaici.
"Shikenan ka rusa min wannan tanadin da na jima ina yi akan aurenka Muhammad? Na jima ina mafarkin ranar da zan zauna mu tsara aurenka tare, amma ka ɗauke min wannan damar baki ɗaya. Shin ka daina ɗaukana a matsayin Uwa kenan da har ka kasa zuwa ka faɗa min abin da kake so, matsayina ya sauka tun da ba zaka iya yin shawara da ni ba akan rayuwarka?"
Sai ta yi murmushin ciwo. Turaki ya motsa zai yi magana. Da sauri ta girgiza masa kai alamar kar ya ce komai. Ba ta shirya saurarensa ba. Ta ci gaba da magana, muryarta na ƙara karyewa da ɓacin rai. Ta lumshe idanunta.
"Ka bar ni kawai in ji da ciwon da ka haddasa min a zuciyata, Allah zai duba ni."
Ta yi wani gajeran murmushi na takaici. Sannan ta sake kallonsa, irin kallon uwa da aka karya wa zuciya.
"Ashe ka jima da mayar da ni shashashar Uwa. Duk irin ƙoƙarina akan tarbiyanka, duk irin addu'ar da na ke yi akanku. Me yasa zaka aikata hakan? Me ya sa ka kasa yin shawara da ni? Mutane nawa ka ke tunanin za su yi min dariya?"
Turaki ya sake sunkuyar da kansa. A wannan karon kam, sai ya ji wannan tambayar ta fi duk marin da Mum ta wanke shi da shi zafi. Ta fi zagin da Mum ta yi masa karya zuciya.
Domin ba shi da amsar da zai bai wa Maama. Ko yana da ita, to bai san ta yaya zai iya furtawa ba. Idan yana jin Hajiya Ramla a matsayin Rayuwarsa, to ita Hajiya Madina duniyarsa ce.
Kaman saukar aradu haka ya ji saukar maganar Maama.
"A wannan karon ba ni da wasu kalaman kare ka a gaban mahaifinka."
Ta yi shiru na ɗan lokaci. Kamar tana haɗiye ciwon da ya tsaya mata a maƙoshi. Sannan ta sake cewa,"Ba ni da su Muhammad."
Ta ɗan juya zata fita, amma sai ta sake waigowa. Ƙarara yana hangen tarin tausayinsa da son tsaya masa a cikin ƙwayar idonta, amma kuma a zahiri tana nuna masa babu hakan, hakan daga gareta ba zai yiwu ba.
"Kar in ji ka saka ni cikin lamarinka."
Ta nuna shi da yatsa.
"Yadda ka dama kayanka kai kaɗai, to ka shanye kai kaɗai."
Ta faɗi hakan ba tare da ta sake kallonsa ba ta juya ta fita.
Da rufewar ƙofar sai ɗakin ya sake nutsewa cikin wani irin shiru. Shirun da yake ɗauke da nauyin zuƙatan da suke cikin ɗakin.
Daga shi sai Fullo sai Bello suka rage a ɗakin.
Turaki ya miƙe a hankali. Ji yake kamar kansa zai rabe gida biyu.
Kafafuwansa sun masa nauyin da ya ke jin tamkar ba zai iya takawa ba. Bello ya dawo ya jingina da jikin ƙofar.
Ya daɗe yana kallon abokinsa. A yau karon farko yake ganin Turaki kamar ba abokinsa mai tarin confidence ba. Ya rasa duk wata nutsuwar da aka san shi da ita. Cikin tausayi Bello ya ce,"Ka zo mu je..."
Ya sauke numfashi.
"Tun wutar tana da sanyin sanyinta... before ta balbala ta ƙona mu baki ɗaya."
Turaki ya kallesa ya ɗauke ido, ya mayar da kallonsa kan Fullo da har yanzu take a wajen duƙe, kamar ma kowa ya manta da ita, kukanta take ta yi.
Cikin sanyin jiki ya taka zuwa gabanta. Tafiya yake kamar ba zai kai ba har ya isa gabanta.
Ya durƙusa, a hankali ya kama hannunta. Yana jin yadda yake rawa a tafin hannunsa.
Ya ɗagota tsaye. Cikin murya mai cike da nadama ya ce,"Please... stop this crying."
Ya haɗiye wani abu da ya tokare masa a maƙoshi.
"It hurts me a lot."
Ya rumtse ido gam.
"From today... ba zan ƙara saka ki hawaye ba."
Ya kalleta kai tsaye.
"I promise."
Yana son ya jawota jikinsa ya ɗora kanta a ƙirjinsa. Amma da sauri ta ja baya ta hana shi.
Ta ɗago kanta. Idanuwanta sun kumbura saboda kuka. Ta zuba masa idanu tana kallonsa ƙwayar idanunta na jujjuyawa a cikin nasa.
Cikin rawar murya ta ce,"Me ka ce musu?"
Sai kuma ta kalli bakin ƙofar sannan ta sake kallonsa.
"Kamar fa ka saka Maama da Mum kuka."
Hawaye suka sake cika mata ido. Like duk a ruɗe take neman fita hayyacinta take. Ta shiga girgiza masa kai.
"Kuma fa ina ta faɗa maka bana so... Bana jin daɗin abin da kake yi min...Amma kai ba ka ji. Ka ƙi ka daina. Na sha faɗa maka za a iya zuwa a ganmu amma ka ƙi dainawa."
Yadda take maganar ka san hankalinta ya kusa barin jikinta.
Ba ta fahimci komai daga abubuwan da suka faru a ɗakin ba. Tsoro ne fal a tattare da ita. Tsoron abin da zai biyo baya. Tsoron hukuncin da take ganin babu makawa zai sauka a kanta.
Tun daga lokacin da Mum ta shigo ɗakin Turaki ya saketa daga jikinsa... Babu abin da take gani sai fuskar Ummi. Fuskar nan tata idan ta yi fushi. Fuskar da take sa ta kasa ko numfashi yadda ya kamata idan ta yi laifi.
Turaki ya kai hannu ya murza karan hancinsa. Yana jin kowacce ƙwalla da take zubarwa kamar ana sauke narkakken ƙarfe ne a cikin zuciyarsa.
Ciwon da yake ji dalilin hawayenta ya fi ƙarfin kalmomin baki. Ya miƙa hannu zai ɗago haɓarta da sauri ta doke hannun.
Sabon kuka ya ƙwace mata. Ta shiga dukan ƙirjinsa da ƙananun hannayenta. Dukan ba ƙarfi, amma kowannensu yana sauka ne kai tsaye a zuciyarsa.
Tana kuka ta ce,"Ba za ka wanke ni ba? Ba za ka faɗa musu ni ba ni da laifi ba?..."
Ta ƙara bugun ƙirjinsa.
"A jikinka suka ganni fa! Me ka faɗawa Mum da Maama?"
Turaki ya ja dogon numfashi ya sauke shi a hankali. Ya daɗe yana kallonta. Kafin ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, tukunna ya sake buɗe su, cikin murya mai nauyi ya ce,"Ce musu na yi..."
Ya yi ɗan shiru idonsa na kallon nata.
"Ke Matata ce."
Akwai wata shekara da aka yi mamakon ruwan sama. A daren wata Juma'a. An tafka wata irin tsawa. Tsawar da tun daga ranar ba ta ƙara jin wata ta razana ta kamar ita ba. Har yanzu idan ta tuna da ita sai jikinta ya ɗauki ɓari.
To irin wannan razanar ce a yanzu ta ji kalaman Turaki sun haddasa mata.
"Ce musu na yi ke Matata ce."
Cak gangar jikinta ta ƙame. Idanuwanta suka ƙafe a kansa babu ko ƙifce. Kamar dai kunnuwanta ne suka ji mata ba daidai ba. Kamar ba shi ne ya faɗi maganar ba. Ta daɗe tana kallonsa cike da ruɗani, cike da tsoro, cike da rashin fahimta.
A hankali kallon nata ya sauya. Ya koma irin kallon da ake yi wa mutumin da aka tabbatar hankalinsa ya gushe. Kamar tana son ta gano ta ina haukar ta fara. Turaki ya fahimci abin da ke zuciyarta. Ya sake matsowa kusa da ita kaɗan.
Murya ƙasa-ƙasa ya ce,"Da gaske nake..."
Ya saka ƙwayar idonsa cikin nata.
"Ke ɗin Matata ce."
Ya haɗiye yawu.
"Na aure ki ba jimawa da yawa."
Ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ci gaba.
"Da ban aure ki ba duk abin da nake yi miki ba zan taɓa yi miki shi ba Fulani..."
Muryarsa ta ƙara laushi.
"Ai ni ma na san halal da haram. Sai da na tabbatar da sadakina a kanki tukunna nake miki duk irin abin da ba kya so."
Ya ɗan murmusa murmushi mai ciwo. Kamar yana son ya sa ta yarda da shi ɗin.
"Na aure ki..."
Ya sake maimaitawa.
"Na aure ki ne fa ta hanyar da ta da ce."
Fullo ta ci gaba da binsa da kallo. Har yanzu ƙwaƙwalwarta ta ƙi karɓar abin da yake faɗa.
A ƙarshe cikin rashin fahimta ta ce,"Shi auren film ne dama?"
Turaki ya kalli cikin ƙwayar idonta da kyau, da nutsuwa ya ce,"Ba film ba ne... Namu ne dai ya zama kamar a film."
Yana faɗin haka ya ɗan matsa gareta. Da sauri ta fizge jikinta ta tankaɗe shi baya. Sabon kuka ya ƙwace mata.
"Leave me alone!"
Ta girgiza kai tana hawaye.
"Allah i hate you...Ji matsalar da ka jefa ni... Alhalin ni babu wanda ya taɓa riƙe ko hannuna ma."
Muryarta ta karye.
"Shikenan yanzu zaka ja Ummina ta yanka ni."
Turaki ya lumshe ido. Ya ji kalamanta suna huda zuciyarsa ɗaya bayan ɗaya. Cikin matsananciyar damuwa ya ce,"Mu je."
Ta girgiza masa kai ta ƙi motsawa. Ransa a ɓace ya ɗaga murya kaɗan.
"Na ce mu je ko."
Ba don ta so ba... Sai don tsoron yadda muryarsa ta sauya. Jikinta ya fara karkarwa. Ya kama hannunta, a hankali suka fita a ɗakin.
Tafiyar da suke yi ba ta mutanen da ke cikin kwanciyar hankali ba ce.
Kowannensu yana tafiya ne da wani irin nauyi da ya danne zuciyarsa. Turaki ji yake kamar kansa babu komai a cikinsa.
Kamar an kwashe duk wani tunani daga cikinsa. Bai san ma ta ina zai fara ba.
Bello yana binsu a baya. Ya shafi goshinsa cikin damuwa.
Ya kalli Fullo ya ce cikin sigar lallashi,"Ki ɗaga ƙafa don Allah. Kinga a cikin matsala fa muke... Tun ɗazu Baffa ya ce mu same shi amma mun ɓata lokaci."
Turaki ya ɗaga ido ya kalli Bello, kamar yana so ya ce ya ba shi mafita tun kafin su isa.
Bello ya ce da shi,"Kai ta faɗin Innalillahi ni kuma zan riƙa yin Hasbunallahu wa ni'imal wakeel."
Ya san addu'a kaɗai ce ta rage musu. Sai da ya yi addu'o'i a ransa kafin ya sami ƙarfin halin saka ƙafarsa cikin parlon.
Ƙafafun Fullo suka fara shiga sannan na Turaki, idon Maama ya sauka akan hannunsa da ke riƙe da nata gam. Wanda da alama forcing nata ya yi ta ƙasa ƙwacewa, lallai Mai babban suna ya riƙa da yawa.
Turaki bai da ƙwarin gwiwar kallon fuskar kowa ba. Bai kuma yi yunƙurin nufar inda iyayensa mata suke zaune ba. Sai dai har a lokacin hannunsa na cikin na matarsa, a ransa yake jin ba zai iya sakin hannun nata ba ko mai za a yi kuwa. Shine kariyarta, shine mafakarta yanzu, idan ya saketa tsoro zai ci gaba da wanzuwa a tare da ita.
Ya zagaya da su ta bayan kujerun. Sannan ya fito ta ɗaya ɓangaren, har suka iso tsakiyar parlon. Fullo ta sake ƙoƙarin ƙwace hannunta a karo na ƙarshe amma ya sake riƙeta da ƙarfi.
Sai da ya zauna sannan ita ma ta zauna a gefensa. Komai yana faruwa ne ƙarƙashin idanun Baffa. Idanun da suke cike da mamaki da takaici, da kuma tambayar da babu wanda ya san amsarta.
Sai bayan sun zauna ne Turaki ya saki hannunta. Fullo kuwa kamar wadda aka saki daga tarko ta yi saurin matsawa gefe.
Ta ƙara tazara tsakaninsu gwargwadon yadda kujerar ta ba ta dama.
Baffa ya ajiye wayar da ke hannunsa a hankali saman center table. Yatsunsa suka haɗe wuri guda. Ya jingina bayansa da kujerar, ƙafarsa ɗaya na girgiza a hankali.
Shiru ya yi, shirun da ya fi duk wata magana da zai yi firgitarwa.
Ya kasa ɗauke ƙwayar idanunsa daga kan Turaki tun shigowarsa parlon. Kallonsa yake yi, ba kallon Uba ga ɗansa ba, kallon Alƙalin da yake ƙoƙarin tabbatar da ko wanda ake tuhuma yana cikin hayyacinsa kafin a yanke masa hukunci.
Ya daɗe yana kallonsa, har sai da ya tabbatar idanun Turaki ba su yi ja ba, numfashinsa da yake fitowa a gab da shi ba ya wari, sannan yanayinsa ba na wanda ya sha wata ƙwaya ta bugar da shi ba ne.
Tukunna ya ce da murya mai matuƙar girgiza allon ƙirjin mai laifi.
"Maimaita abin da ka faɗa ɗazu."
Turaki ya yi saurin ɗagowa. Lokaci guda ya ji Maƙoshinsa ya bushe tamkar yawu ko ruwa ba su taɓa ratsawa ta bakinsa ba.
Da matuƙar wuya ya haɗo kalamai a bakinsa haƙorinsa na datsewa kamar wanda aka tsoma cikin ƙanƙara ya ce,"Baffa...".
Ganin yana neman yi masa dogon jawabi, Baffa ya katse shi da wata razananniyar murya, muryar da Turaki ya ji tamkar takobi akasa a fatar jikinsa aka keta.
"Ce na yi ka maimaita abin da ka faɗa, ba dogon turanci na ce ka min ba".
Ya faɗa idanuwansa suna ƙara kaifi na tsoratarwa ga Turaki.
Turaki ya ji shi kamar ansa hannu ana matse zuciyarsa. Ya haɗiye yawun da babu shi. A hankali ya sunkuyar da kansa. Muryarsa ta fito da ƙyar.
"Na aure ta..."
Sai ya ɗan dakata. Kamar kalmar ta ƙi fitowa duka.
"Tun watanni biyar da suka wuce na aureta."
Parlon ya sake yin wani shiru. Shirun da ya fi na farko nauyi. Baffa bai ce uffan ba. Shaida yake nema! Shaidar da zata tabbatar masa da abin da yaron yake faɗa! Wataƙila yana son kare kansa ne daga tuhuma kamar yadda mahaifiyarsa ta faɗa masa a yanayin da ta samesu, shi ya sa yake ganin faɗa musu cewa ya aureta shine zai kare shi daga hukuncin da ya dace da shi.
Wallahi babu ruwansa, zai manta da cewar Turaki ɗansa ne ya maka shi a kotu bisa laifin haikewa yarinya. Ai ba zarginsa suke ba, mahaifiyarsa ta kama shi da kanta.
Amma sai ya ji wani abu ya ratsa ta cikin kunnensa ya yi shawagi a cikin kansa tukunna ya taɓa zuciyarsa.
Zuciyar tasa ce ke faɗa masa gwara ace auren nata ya yi, sama da tunanin da ba ya ƙaunar yake gimla masa, yafi tsoron hakan, idan ya tabbata neman haikewa yarinya ya yi, to lokacin da za a gurfanar da Ɗan nasa a kotu, shi kam ya daɗe da barin duniyar, domin tabbas zuciyarsa bugawa zata yi farat ɗaya, don ba zai iya ɗaukar wannan tashin hankalin ba.
Da sauri ya girgiza kai don tunanin hakan ya bar kansa. Kawai ya juyar da kansa ya kalli Bello. Ko da ace Bello zai kare abokinsa, to ya sani ba zai ɓoye gaskiyar komai ba, ya riga ya yiwa yaron farin sanin da zai iya cewa ko nasa mahaifin bai san shi kamar yadda ya san shi ba.
Kuma wannan kallon da Baffa ya yi masa ya isa ya sa Bello jin kamar ana datse masa ƙafafu.
Da sauri ya gyara zamansa yana gyaɗa kai ya ce,"Eh! Ehh Baffa... da gaske ne ya aure ta."
Baffa ya ci gaba da kallonsa. Ba tare da ya canja yanayin fuskarsa ba. Ya ce,"Kai ka zama waliyyin?"
Gaba ɗaya jinin Bello ya ƙafe. Da sauri ya girgiza kai. "A'a Baffa. Ban ma san ya yi auren ba sai daga baya... Wallahi ban san yadda auren..."
"SHUT UP!"
Tsawar da Baffa ya daka masa, Sai da Bello ya ji kunnuwansa sun yi wata ƙara kafin su toshe dumm. Zai iya rantsewa ji ya yi Parlon yana girgiza su.
Hatta Fullo da tun ɗazu take kuka, Sai da ta firgita ta ɗago kai ba shiri. Tana kallon Baffa tsaye a gabansu fuskarsa tamkar ta zaki.
A karon farko tun faruwar al'amarin. Fushinsa ya bayyana sosai. Ya nuna Bello da yatsa.
"Stupid boy! Wa ya tambaye ka tarihin rayuwarka? Wa ya ce ka wanke kanka?"
Ya haɗe hannayensa ta baya.
"Wa yake marainin wayonka a nan?"
Ya daki ƙirjinsa da hannu.
"Ni? Bello kana ganin ban san ku ba ne gaba ɗaya?"
Ya yi shiru yana jin ɓacin ransa na sake ninkuwa. Tabbas Muhammad ya raina shi, ya mayar da shi uban banza, ko dukan mutuwa ya yi masa, ai bai goge abun kunya da ala wadai ɗin da ya ja musu ba.
Yana kallonsu duk su biyun ya ce,"Marasa mutunci..."
Tukunna ya nuna Turaki da yatsa. "Marar tarbiyya..."
Numfashinsa ya yi nauyi.
"Ɗan iska mara hankali da tunani, mutumin banza, mutumin wofi, shashasha gantalalle..."
Ya faɗa yana kai ƙafa zai hamɓare Turakin. Kuma kalaman nasa suka sa Hajiya Madina saurin ɗago kai. Da damuwa ƙwarai ta ce,"A'a! Ka tausasa kalamanka."
Ko kallonta bai yi ba. Sai ya ɗaga mata murya ya yi da cewar,"Rufe min baki Madina!"
Parlon ya bayar da wani irin tsit mai motsa zuƙata dalilin yadda ya ɗagawa Maama murya. Kafin ya juyo da kallonsa gareta ya nuna ta da yatsa.
"Idan ina magana da yarana kar ki sake saka min baki. Idan kuwa ba haka ba, zan ci mutuncinki a wurin nan wallahi."
Kalaman suka sauka akan kowa kamar saukar tsawa a cikin daji a duhun dare. Kalamai ne na kashedi da gargaɗi ya yi mata ta sigar da bai kamata ya yi ba a gaban yaransu.
Hajiya Madina ta yi yunƙurin sake magana. Amma Hajiya Ramla ta taɓa hannunta a hankali alamar ki yi shiru.
Ba don ta so ba ta haɗiye maganar. Ta sunkuyar da kanta. Wani irin ciwo ya tokare mata a zuciya. Fata take yi, fatan ina ma akwai ikon da zai hana kunnuwanta jin sauran kalaman da za su fito daga bakin mijinta.
Ta san Dikko fiye da kowa. Ba mutum ne mai yawan fushi ba. Amma idan ya yi fushinsa kan rinjayi harshensa. Sai ya riƙa furta kalaman da daga baya idan ya huce, shi kansa kan yi nadamarsu.
Hajiya Madina ta kasa jurewa dai, ta ƙwammaci komai zai faru sai dai ya faru, amma ba zata bari ya ci gaba da faɗar tsauraran kalamai akan ɗanta ba. Saboda haka ta ɗago kanta a hankali.
Murya ƙasa ta ce,"Ka yi haƙuri ba zan iya yin shiru ba, kalaman da za su sake fitowa daga bakinka tabbas na san za su fi haka tsauri, ya zama dole na dakatar da kai."
Ta yi shiru sannan ta ɗaga ƙwayar ido ta ɗan kalle shi, kallo ɗayan da ta yi masa ta hasko yadda ya ke kokawa da kansa wajen danne kansa ga cin zarafin da zuciyarsa ke hassala shi akan ya yi mata.
"Ka daina kiransa da ɗan iska, ka daina ce masa gantalalle don Allah."
Ta yi magana cikin ladabi. Ba don tana kare abin da Turaki ya aikata ba.
"Gyarawa kake so ayi. Kar kuma sanadin gyaran ya sake jawo wani ɓacin... Ka manta ne? Kaifin kalaman iyaye akan ƴaƴansu yana da nauyi. Wasu kalaman..."
Ta ɗan dakata.
"Suna tasiri akan Ɗa, kuma suna binsa har ƙarshen rayuwarsa."
Baffa ya ɗaga hannu da sauri wajen dakatar da ita.
"Madina! Na ce idan kika sake min magana zan ci zarafinki. Da Ƴaƴana na ke magana ba ke ba."
Ya nuna Turaki.
"Ba Ɗan iskan ba ne shi? Tun da har ya kai matsayin da ya ke ganin iyayensa ba bakin komai ba. Tun da har ya isa ya yi ma kansa aure ba tare da sanin iyayensa ba, ba tare da waliyyin da addini ya halatta ba. Ya zaɓi ya nunawa duniya shi ɗin ba haihuwar sunnah ba ne, ya zaɓi ya janyo mana abin kunya da mutuncina da komai a gari... To me ya rage tsakaninsa da ƴan iskan gari waɗanda aka haifa aka watsar a titi?"
Hajiya Madina ta lumshe ido zuciyarta na zafi. Ba ta sake magana ba. Saboda ta san a wasu lokutan idan zuciya ta cika da fushi, ba kunne take da shi ba, ba ta ji bata gani sai dai bayan ta huce.
"Baffa ka yi haƙur...."
Bello ya yi ƙarfin halin faɗin hakan, kuma bai ida rufe bakinsa ba Baffa yasa ƙafa ya hamɓare shi gefe. Turaki ya dube shi da sauri, ba zai yi magana ba, komai za ayi ba zai yi magana ba, amma dai ba zai bari Baffa ya sake kaiwa Bello duka ba, zai kare amininsa nasa, shi ya yi laifin, duk abin da ya aikata shi kaɗai ya yi, Bello bai sani ba, saboda haka shi ɗaya za a hukunta.
"Ni za ku mayar mutumin banza, da mutuncina a idon jama'a za ku watsar min da shi, martabata za ku wulaƙanta min? Kuma har kuna da zarafin da zaku tsaya a gabana kuna maimaita min irin rashin mutuncin da ku ka aikata saboda ba ku da kunya ba ku da ɗa'a?."
Yawun bakinsa kamar zai koma kumfa. "In yi auren sunnah na samar da kai ta hanyar sunnah, shine zaka je ka nunawa duniya ba ka da uba. Baka isa ka ja min zagi ba a duniyar nan, baka isa ba wallahi ka yi kaɗan, kuma a yau na yi danasanin raɗa maka suna mai daraja, domin baka yi deserving sunan ba, na ji takaici da ba zan iya ambatar sunanka kai tsaye ba na zazzageka."
Numfashinsa ya fara nauyi. Jijiyoyin wuyansa suka fito.
Ko a kotu, ba a taɓa kawo case ɗin da yake jin ya taɓa shiga cikin irin wannan yanayin ɓacin rai da tashin hankalin ba. Ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, kafin ya sake buɗe su.
Ya sauke kallonsa kan Turaki. Wannan karon... Ba kamar yana kallon ɗansa ba. Kamar yana kallon mutumin da bai taɓa sani ba ne.
Ya ce a hankali,"Muhammad..."
Sunan ya fito da wani irin nauyi.
"Ka raina ni. Ka wulaƙanta ni, ka raina matsayin da Allah ya ba ni akanka."
Ya nuna Hajiya Ramla da Hajiya Madina.
"Ka raina iyayenka. Wallahi... Da wani ya zo ya gaya min ka aikata wannan abun kunyar da zan ƙaryata. Ashe ni ne ban san waye ɗana ba, ashe ban san bala'i na haifawa kaina ba."
Turaki ya ji kalaman suna shiga zuciyarsa, sun mata mugun matsa kamar za a cizgota. Ya rumtse ido sosai.
Ya kasa numfashi yadda ya kamata. Baffa ya ci gaba.
"Kafin ka faɗa min shaidun bogi da suka tsaya maka na yi shari'a da su. Tun da na san shi uban yarinyar ba mahaukaci ba ne irinka da zai ɗauki ƴarsa ya baka babu magabatanka. To ina ba ka Umarni. Ba roƙonka na ke ba. Ba shawara ba ce. Umarni ne na kai tsaye."
Ya ja dogon numfashi ya sauke.
"A matsayina na Uban da ya kawo ka duniya... Yadda ka nuna min banda wata daraja a wajenka, Yadda ka je ka yi gaban kanka a matsayinka na ɗan iskan da ya isar ma kansa. Har ka ƙulla wannan abin da kake kira aure, to haka yanzu..."
Ya buga center table da tafin hannunsa har gilashin saman tebur ya amsa da ƙara.
"ZA KA WARWARE SHI!"
Kowa ya razana banda Hajiya Ramla da abin ya yi mata daɗi. Bello da sauri ya runtse ido. Hajiya Madina ta dafe kai. Baffa ya nuna Fullo.
"Wannan ka ke kira ka aura, ita kake kira Matarka, to saketa Muhammad."
Kalmar ta fito a sarari. Ba tare da wata cizgiya a muryar ba. Amma ta sauka kamar saukar aradu.
"Ni ubanka ba zan taɓa yarda da wannan auren iskar ba. Ba a gidana ba. Ba a cikin zuri'ata ba.... Ka saketa yanzu ko kuma na zareka a cikin Ƴaƴana, don sai dai ka nemi wani uban amma ba ni ba."
Kalmar "Ka saketa."
Ita ce kawai ta riƙa yawo cikin kunnen Turaki. Ya daina jin komai. Hatta bugun zuciyarsa ba ya ji. A yadda yake ji kamar furucin na Baffa ya daskarar masa da jinin jikinsa. Sannan yana jin kamar duniya ta tsaya ne akan waɗannan kalmomi guda biyun.
A hankali ya ɗaga kansa ya dubi Baffa. A karo na farko. Ya ga ba fushin Uba yake gani ba. Hukunci yake gani. Hukuncin da babu sassauci a cikinsa.
Sai ya waigo gefensa yana kallon Fullo da jikinta ke mugun karkarwa.
Gabansa ya faɗi. A wannan lokacin Turaki ya ji kamar an tsamo zuciyarsa ne daga ƙirjinsa. Numfashi ya tsaya masa na wasu daƙiƙu. Tabbas ya taɓa jin tsoro. Ya taɓa shiga tashin hankali. Ya taɓa fuskantar haɗari.
Amma... Zai rantse da Allah bai taɓa jin wata magana ta girgiza ginshiƙin rayuwarsa ba kamar yadda waɗannan kalmomi suka yi.
Kuma sai a yanzu ya fahimci cewa. Ba wai Baffa yana fushi da shi ba ne kawai. A'a! Ya zo ne da batun rusa dukkan rayuwarsa.
Zaɓi biyu ne ya ba shi. Ko ya saki matar da ya ke da guarantee ɗin ita ce cukon numfashinsa, ko kuma ya rasa amsa sunan Ɗan Alƙali Dikko.
Ya runtse idanunsa. Sai ya ji zaɓuɓɓuka biyun duk suna kama da mutuwa a gare shi.
Na farkon ba zai iya ba. Ko da za a ɗora wuƙa a wuyansa. Ko da za a karɓe masa duk abin da ya mallaka. Ba zai iya furta kalmar saki ga Fulani ba. Ba zai iya ba.
Na biyun kuma... Ya ji kamar wani ya ciro zuciyarsa yana gasata irin gashin tsire. A hankali ya waigo. Idonsa ya sauka kan Hajiya Madina.
Idon Mum ba a kansa yake ba, amma ita Maama na ta ƙwayar idon akansa take, yana iya ganin ruwan da ke shimfiɗe cikin ƙwayar idon nata da ke ɗauke da fargaba gami da tausayiwa a gare shi.
Kallonta yake yi, kallon neman taimakonta. Agajinta yake nema.
Kamar ƙaramin yaron da gobara ta kewaye shi. Idanunsa kaɗai suke magana a gareta.
"Maama... Don Allah... Kada ki bari... Ki ce wani abu... Ki ceci rayuwata..."
Hajiya Madina da ta ga irin roƙon da ke cikin idanunsa. Zuciyarta ta karye. Da sauri ta kauda kanta ta kasa ci gaba da kallonsa.
Saboda ta san idan ta ci gaba da kallonsa, za ta karaya ne.
Turaki ya ji ƙafafuwansa sun yi sanyi kamar wanda aka yanke masa hukuncin kisa.
Hope ɗinsa ɗaya! Maama ce! Ita ɗaya yake da ita a wannan dambarwar. Kuma a yanzu ta nuna ba zata goyi bayansa ba. Ya zai yi?
Sai a yanzun ne yake jin zai iya buɗe baki ya yi magana da Baffan. Zai ce wani abun, zai ajiye taurin kansa a gefe.
Ya haɗiye wani dunƙulallan abu da ya tsaya masa a wuya.
Da ƙyar ya sami damar ɗaga kansa ya kalli Baffa kai tsaye.
Muryarsa ba irin muryar Turakin da kowa ya sani ba ce. Murya ce ta mutumin da zuciyarsa take gab da tarwatsewa.
"Na san na ɓata maka rai..."
Ya haɗiye yawu.
"Na san na yi ba daidai ba... Ka yi min duk hukuncin da ka ga ya dace..."
Sai muryarsa ta karye. Da ƙyar ya iya ƙarasa maganar.
"Amma don Allah. Don girman Allah Baffa..."
Ya ji numfashinsa ya tsananta rawa.
"Ka janye umarnin da ka ba ni..."
Ya lumshe ido. Da ace daga shi sai Fulani ne kuka zai saka mata.
Ya ci gaba. "Ba zan iya ba. Ba zan iya sakinta ba Baffa..."
Ya haɗiye sauran kalamansa, sakamakon marin da Baffa ya kai masa, wanda sai da kansa ya karkace gefe guda. Wani irin ƙara ya ji cikin kunnuwansa.
Na wasu daƙiƙu ya rasa ji. Ya rasa gani. Ya rasa sanin inda yake. Sai zafin da fuskar ke ji kamar an ɗora mata garwashi.
Kafin ya dawo hayyacinsa... Kamar cicciɓar Hajiya Madina aka yi haka ta miƙe da azama akan kujera. Ta yo kan Baffa da sauri tana shiga tsakaninsu don dakatar da mugun bugun da take ganin ya na shirin yi masa.
"A'a don Allah. Ni ka duke ni, amma shi ka ƙyale shi, don Allah Baffa."
Baffa ya zura mata ido.
"Madina ki kauce min a gabana ko na haɗa da ke."
Hajiya Madina ba ta matsa ba. Ba zata iya matsawa ba, idan ta ƙyale shi dukan mutuwa zai yi masa, bai ƙi ya dinga tamole da shi ba har compound, babu ruwansa da wani girmansa tun da dai shi ya haife shi, yana yawan faɗa musu ba zai yarda da iskancin yaro ba, saboda haka su dinga kiyayewa suna ƙara sanin shi ubansu ne.
Ta ci gaba da girgiza kai, muryarta ta fito a rauna ne.
"Kuskure ɗaya ne kuma a karo na farko... Ranka ya daɗe ka samu nutsuwa ka fahimce shi don Allah."
Ta nuna Turaki.
"Yana maka biyayya. Ya kare mutuncinsa. Ya kare maka naka. Ya kare martabar zuriyarka. Baffa idan da ya so ya tozarta mu..."
Sai ta yi shiru.
"Ba aurenta zai yi ba. Lalata zai yi da ita."
Kalmar ta sauka da nauyi a zuciyar kowa.
"Wallahi zai ɓoye ne ya keta mata haddi. Ya dawo gida kamar babu abin da ya faru. Anan kuma wa zai ba ka shaida? Wa zai gaya maka? Ba zaka san komai ba, wataƙila har sai ranar da za a kawo maka jariri..."
Muryarta ta karye.
"Ace ga jikanka."
Ta girgiza kai.
"Yanzun ma ba ɓoye maka ya yi ba Baffa, dama zai sanar maka, tsoro ne kawai ya hana shi, tsoron ta yadda za ku karɓi abun..."
Rai a ɓace Baffa ya dakatar da ita daga surutan da ko ɗaya ba su shige shi ba, balle su yi tasiri a ransa.
Murya a ɗage ya ce,"Yanzun ma ƙarya yake yi, ban yarda aurenta ya yi ba, ban yarda da shi ba Madina. Idan ba haike mata ya je yi ba to ya fara sakinta..."
Ya ƙara ɗaga murya.
"Sannan Wataƙila..."
Ya jaddada kalmar.
"Wataƙila in iya gamsuwa da cewar ya aureta ɗin."
Turaki ya miƙa hannu a hankali ya kama hannun Maama ya damƙe tamau. Wani irin riƙo ne na mutumin da yake neman ceto daga nutsewa a cikin ruwan teku, amma ya san babu wanda zai iya ceto shi.
A wannan lokacin, ji yake kamar rayuwarsa gaba ɗaya ta rataya ne akan waɗannan igiyoyi ukun da Baffa yake so ya datse.
A cikin zuciyarsa ya ke jin wata murya na ci gaba da maimaita masa,"Igiyoyi uku ne... idan aka yanke guda ɗaya, za ka iya rayuwa da sauran biyun har ƙarshen numfashi."
Amma zuciyarsa ta ƙi yarda. Domin igiyar da aka umurce shi ya datse. Ita ce igiyar da take riƙe da numfashin rayuwarsa.
He had no other choice, except to obey his father. Wannan shi ne abin da hankalinsa yake gaya masa.
Amma fa zuciyarsa ta ƙi karɓar wannan hukuncin. A hankali ya ɗago idanunsa. Suka sauka kan Fullo. Ya ji maƙoshinsa ya bushe. Ya buɗe baki sai ya kasa furta ko harafi ɗaya.
Kamar wani abu mai nauyi ne ya tsaya masa tsakanin zuciya da maƙoshi.
Ta yaya zai haɗa kalaman saki ya furta su ga macen da ya rantse zai zama mafakarta? Ta yaya zai saketa bayan ya yi alƙawarin zame mata uwa uba?
Ta yaya zai ce mata ya saketa alhalin ita ce kaɗai abin da yake jin ya na da ita a duniya bayan iyayensa?
Numfashinsa ya fita ba a daidai ba. Ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci. Bai san ta inda zai fara haɗa kalmomin da zai furta mata ba. Domin wasu kalaman ba wahalar faɗa ne da su ba. Wahalar rayuwa da sakamakon faɗar su ne illa.
"Baffa zan saketa, saki nawa zan yi? Sannan furtawa zan yi ko kuma rubutawa zan yi? Ka bani umarnin yadda zan yi Baffa."
Hannun Hajiya Madina ya sauka akan gashinsa. Kuma ɗumin tafin hannun nata ya ratsa cikin kansa ya shiga jikinsa. Sai ya ke jin kamar ta gama warware duka matsalar, kamar ta kawo ƙarshen komai ne.
Hajiya Madina ta ce,"Ka sa ya kira duk waɗanda suka tsaya masa a auren. Sannan ka nemi mahaifin yarinyar da waliyyinta. A zauna da su gaba ɗaya. A gabanka, kuma a gabansu, zai warware abin da yaje ya ƙulla ba tare da sani ko izinin Manyansa ba. Saki uku zaka saka shi ya yi mata a gabansu. Ta hakan ne zaka mayar da mutuncin da ya je ya zubar maka a wurinsu."
Hajiya Ramla ta dinƙa kallon Hajiya Madina. Ta kasa ganewa furucin da ta yi, shin goyon bayan sakin take yi, ko kuwa tarkonta take shiryawa cikin hikima.
Halima.hz
***