24
by @sadisakhna
______👑 *JODA* 👑_____
Na
*Sadi-sakhna*
Ƴar mutan Jama'are
THE TRIO OF TALES
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)
@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp
LITTAFI NA 1
👑*Warƙa ta (24)*👑
Gini ne mai tsayi kuma na alfarma,ya ƙawatu sosai banda kamshin miski da kuma mutane sanye da Silki kala kala babu abinda mutum yake gani, wajene mai tsari da kuma nuna Izza,hatta bayi sanye suke a cikin kayansu na bayi a tsaftace kuma cikin shiri. Babu wani hayaniya a cikin fadar, sai magana sama sama kowa yana nasa harka.
Dogayen filu da suka rike babban ginin su kansu sunsha fenti mai kyau sai walwali yakeyi anyi masa ado na zinare.
Fadar Daular masar kenan,fada wacce ta samu daruruwan shekaru tana damawa a cikin sha'anin mulki.
Wata baiwa ce tafito daga cikin ainihin babbar fadar ta nufi wani sashe a gefen hagun. Shima ya ƙawatu sosai,amma zanene filawoyi a yafi yawa a bangaren,harma da furannin kala kala wanda aka kawosu daga kasashen ƙetare an shukasu ta ko ina suna bada kala da ƙamshi yanda ya dace.
Taron bayi take wucewa rukuni rukuni,wani suna ɗinka ado a jikin mayafai,wani na aikin goge ƙasan wajen wanda yayi ƙyal dashi har ɗaukar ido yakeyi. Sannan wasu na zaune suna ƙada abun sauti suna hira cikin raha. Wasu kuma na aikin saka turare a kowanne ƙusurwa dake sashen. Duk inda ta wuce ɗaga musu hannu take suna gaisawa har ta isa bakin wata katafariyar turaka,da bakin ƙofar ma abin kallone yanda ya ƙawatu da ado mai ɗaukar ido. Turawa tayi amma kafin ta shiga sai sukayi kicibis da wata mata zanye da kayan bayi amma kore,kanta ɗauke da hula irinta al'adar masar,farace ta fara shiga Shekarun manyantaka, suna kama da wacce tashigo da gudun kaman zata tashi sama. Suna haɗa ido da babbar matar ta tayi saurin sunne kai alamar batayi daidai ba.
"Lafiya Layla daga ina kike haka,meyasa ne koyaushe ina miki faɗa akan nutsuwa amma bakyaji ne uhm"
Shuru tayi tana goshi cikin yarinta,takai shekara sha biyar amma kaman ƴar shekara goma yanayinta.
"Kiyi haƙuri ummi,abin farinciki na jiyo shiyasa nake ta sauri na faɗawa Gimbiya Hillah"
"Uhmm toshikenan,amma kinsan idan kika shiga mata a haka bazaku shirya,domin yanda ta tsani Ƙazanta haka nan ta tsani rawar kai da rashin nutsuwa kinsan da haka"
"Ehh nasani ummi dama zan nutsu idan nashiga......"
"Wayene a bakin ƙofar Ummi Layla naga kin tsaya kuna magana?"
Wata siririyar murya mai cikeda nutsuwa ta faɗa daga ciki.
"Uhmm Layla ce zata shigo shine nake tare ta akan tabari ki gama gyaran jikin tukunna"
"Ohh ina tashigane tun safe ban ganta ba,ki barta ta shigo kawai abinda nakeyi bazai hanani yin magana ba ai"
Jin abinda ta faɗa yasa Ummi layla matsawa tabawa ƴar tata hanya tashiga turakar Gimbiya Hillah. Ƴa ɗaya tilo Mace ga Sarkin Masar ɗin Abduljalal dakuma Amaryarsa Jalilah. Matarsa ta farko kuma Sarauniya Aziza ita ƴaƴanta dukka maza ne ciki harda Mai jiran gado Abdurrahman. Hakan yasa kowa ya ɗauki son duniya ya ɗorawa Hillah,kuma ta taso gata kyakyawa kuma mai nutsuwa da son gayu. Saidai batason kazanta da ƙarƙanci hakanne yasa ko bayinta take sake musu abun rayuwa yanda zasu gyara kansu,bayin ta sun garuwa da aiki kam amma kuma basa ƙorafi kasancewar tana sakemusu abubuwan rayuwa. Ko waje zataje sai an tsaftace mata keken doki,Su kansu dawakanta kullum sai anyi musu wanka ballantana kuma masuyiwa dawakan wanka. A nata bangaren ita kanta ko yaushe tana cikin kulada kanta,wanka ne,gyaran fatane turara jikine da turare,gyaran gashine na farcene da sauransu. Kowa ya ganta sai ya tabbatar da cewar ita ɗin wanke ka tabace. Tun cika shekararta goma sha biyar Sarakuna biyu suka turo neman hannunta na aure ga ƴaƴansu,amma suna zuwa tace wai kazamaine bazata iya zama dasu ba,ɗayan kam daya kama hannunta kwana tayi tana zuwa banɗaki yin amai kamar wata mai laulayin ciki.
Duk abinda takeyi babu wanda yataba nuna mata ba daidai takeyi ba,kasancewarta ƴar so kuma abarso. Kowa abinda takeso shi yakeyi da hakan ta tashi,idan ka bata mata rai to tamkar ka batawa Daular masar raine.
"Ranki ya daɗe yanzunnan naji ana labarin wai takarda ta iso daga Daular mali cewar yarima Hammarou yana biɗar hannunki da kansa na zama gimbiyarsa kuma sarauniyar gobe wanda za'a yi nanda Wata shida masu zuwa"
Tashi tayi ta sauri tacire Kurjin dayake kan idonta da kuma lemon tsamin da aka mammanna mata a fuska wanda aka tsomashi yakwana a cikin zuma da kurkum.
Ciccirewa abubuwan tayi ɗaya bayan ɗaya,aka kawo mata ruwan ɗumi mai ɗauke da turaren fuska ta wanke fuskarta,ta goge da wani farin tawul. Har sannan bata kalli layla bayan tashi kawai da tayi zaune tana cire abinda yake jikinta. Tashi tayi daga wajen taje ta zauna akan wata kujera. Masara mai ɗumi wacce tasha zuma aka kawo mata,saida tayi kurba uku kafin tayuwa layla alama da hannu ta ƙariso inda take. Idan da sabo tasaba inhar ta isar mata da saƙo tana wani abun to bazata kulata ba har sai tagama abinda yakamata tayi tukunna,yanzun ma tayi mamaki da bata gama yin adadin lokacin da takeyi ba amma ta cire saboda jin abinda layla ta faɗa,wanda hakan ya nuna kenan tana son labarin datazo mata dashi sosai.
"Shin labarin da kika faɗamin da gaske kike layla,Hammar ne da kansa ya yake son na kasance a gefensa"
"Tabbas ranki ya daɗe hakane,na tabbata zuwa dare mai martaba zai nemeki da zancen,ni dama nasan dole kina ransa shaƙuwar da kukayi kuna yara bazata taba gogewa a ransa ba,kaman yanda kike tunashi na tabbata shi yana tunaki fiyeda haka,domin ke ɗin ta Fasihmman ce da samunki gareshi wata babbar kyautace a gareshi"
Wani murmushin ƙasaita Gimbiya Hillah tayi,Allah ne kaɗai yasan iya farincikin da take ciki sanadiyyar jin amsar gayyata na sayayya daga wajen abin sonnata wanda sonsa yake ta dawainiya da ita tsawon shekara da shekaru.
Bayan anyi sallar isha kaman yanda layla tafaɗa mahaifinta yayi ƙiranta turakarsa,bayan sunyi hira ta tsakanin uba da ɗa ya mika mata takardar gayyatar neman kasancewar ta a bikin xaben sarauniyar gobe da za'a. Baiso ace ƴarsa sai tashiga gasa kafin a ɗauketa a sarauniya ba,a ganinsa hakan tamkar rage darajarta ne,amma kuma dayaji cewar iya dama mata huɗu ne zasu yi gasar,kuma wacce taci iya matsayin Babbar cikinsu za'a bata,kuma sashenta zai zama shine babba kuma sashenta Yarima hammar zai fara shiga,har sai yayi tsawon sati gudu kafin ya shiga na sauran,amma dukkansu zasu kasance matansa ne. Daga nan kuma wacce tafara haihuwa Fasihmman ɗa na miji zata samu matsayin uwar magajin gobe. Amma duk da haka ba itace zata zama sarauniya ba,wacce taci gasa itace da matsayin sarauniya, wacce zata yi mulkin cikin gidan sarauta,komai na iko daya shafi cikin gida da kuma matsalolo na mata zai kasance yana hannunta ne ,wannan dalilinne yasa ake gasa domin a sabi wacce tafi kowa basira. To idan aka samu nasarar itace ta fara haihuwa kuma to dukka matsayin zai kasance nata ne.
A al'adar Daular mali ɗan sarki na farko da aka haifa a kowanne karni za'a saka gasane na matan da aka zaba daga gidaje masu daraja,idan sukayi duk wacce tayi nasara to itace wacce zai aura. Saboda a tsarinsu Sarki yana raba wasu ayyukan da sarauniyarsa,tana da wani matsayi da take takawa a cikin sha'anin mulki,shiyasa akeson zabar wacce takeda juriya,kaifin basira da kuma hangen nesa..
Idan mata goma aka zaba to zai auri huɗun farko sauran shida zasu kasance kwarƙwarori amma a hankali a hankali rayuwa tana sauyawa har yazamo iya huɗu kawai ake ɗauka,kwarkwara ko baiwa idan yaso daga baya da kansa sai ya ƙara. Kasancewar jinin sarautar mali an sansu da ƙarfin mazantaka yasa Ake aurawa kowanne mai shirin zama sarki mata huɗu,kuma dabarar hakan shine a buɗa dama na samun magaji a cikin matan da ya aura.
Wannan matsayi da sarauniya ke samu yasa Sarkin masar zai bar ƴar sa taje a matsayin mai shiga gasar,kuma akwai zumunta tsakanin kasancewar Mahaifiyar keita Hammar ƙanwarsa ce,kuma itace sarauniya a lokacinta kafin ta rasu,duk da ma ta auri Sarki mansa ne a lokacin yana ƙanin Mai jiran gado,a yaƙin da akayi yana shekara ɗaya da hawan mulkin Keita mansa ya rasa ransa. A lokacin matan da aka aura masa suna kan rikici da ƙullace ƙullace,babu wacce tasamu ciki sai labarin mutuwar sa kawai sukaji,ciki harda Denti Shuwarah itace mai jiran gadon sarauniya,sai ta auri Mahaifin su Hammar. Amma ba a maida mata matsayin Sarauniya ba sai aka bawa Denti maleeka matarsa. Wanda a lokacin ko wata biyu batayi ba da haihuwar Hammar. Sauran matan kuma suka koma ƙasarsu,dan cewa sukayi bazasu sake zama da denti Shuwarah ba,domin su kaɗai suka san abinda tayi musu.
Lokaci guda aka tada biki aka auro masa sauran mata biyun,sukazo aka fara fafatawa.
To wannan juyewar da rishe yayi da mujiya wa denti Shuwarah ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,tana matsayin sarauniya ta koma baya matsayin matar sarki kawai, ga danasani ya cikata,da ta haihu da Sarki mai rasuwa da shikenan danta ne akan mulki ko anƙi anso. Amma a yanzu ma ganin ta haihu na mijin yasa taji tsugunne bai ƙare mata ba akwai sauran rina a kaba.
*** *** ***
Bayan wata uku
Cikin rawar jiki Ungozaman ta fito daga cikin turakar hannunta wanke da jini tamkar ta yanka saniya,a razane Sunkia madina take ƙare mata kallo,tun kafin tace wani abu matar tafara magana.
"Ranki ya daɗe ki gafarceni amma abun yafi ƙarfina,yau kwana uku kenan duk wata dabara danasan zanyi amfani da ita nayi amma ko kan ɗa banajin alamarsa ballanatana ace haihuwa tazo kusa. Har yakai yanzu tafara fita hayyacinta,sannan ga jini daya tsinke yau yana ta zuba babu yanda bamuyi ba amma yaƙi ya daina zuba,inda ma ta haihu ne to da sauƙi amma shuru"
Cikeda damuwa take faɗawa sunkia madina halinda ake ciki,wanda ko bata zayyana mata ba itama tana gani da idonta. Watan su uku kenan da dawowa daga Wajen magani inda suka kaita cikin Jami'a tun lokacin dasuka dawo ta samu lafiya sosai,domin Sunkia madina tana ƙoƙari wajen ganin ta kiyaye duk abinda Joda ta faɗamusu,lokacin da sukaje sunso yin koda satine amma Asmah tafara rigima da taga tasamu sauƙi kan ita baiwa bazata dunga dubata ba,haka dole suka dawo gida. Anan sashenta ta ajiyeta tana kulada ita,Fasihmman data kula ummul aba'isin faruwar ciwonnata mijintane Yerima kabeer,wanda yanzu ko ɗuriyarsa basa gani sosai a sashen,dan ko tambayar jikin Matar tasa ma ya daina zuwa yi. Labari yazo mata kan cewar sun ɗinke da Zaleekah,batasan waye yakaiwa Asmah labarin ba shikenan dataji jiki ya yatashi haihuwa ma tace gatanan amma mai dauke da gagarumar matsala,dama kuma cikin yakamata ace ta haifeshi tun watan jiya,amma saida ya haura ya shiga na goma. To yanzunma gashinan da alama yaron bayason fitowa duniyar.
Kaiwa da kawowa takeyi a turakarta ta,kaman an tsikareta tace.
"Ungozuma nace to ko wajen maganin can zamu koma wanda muka je watannin baya,naga yarinyar tanada baiwar magani sosai,wataƙila sai kiga idan tasaka hannu an dace"
"Ehh to bazan ja da shawararki ba Ranki ya dade,to amma a halinda gimbiya Asmah take ciki banajin zata iya yin tafiya mai nisa har zuwa cikin jami'ar Al'azhar. Saidai idan ita mai maganin za'a ƙira taxo."
"Uhmm zanso hakan to amma kin manta dokar Wajenne basa barin Bayinsu Fasihmman ma mai ilimi kaman ita tafito daga cikin jami'ar"
"Dokarsu batakai dokarki ba ranki ya daɗe,kefah uwace ga wannan nahiya,akwai wanda zayyi biris da ƙiranki ya shugaba"
Shuru tayi tana nazari kafin daga baya tace.
"Hakane akan dokarsu baza'a bari Matar Yeriman ƙasa ta rasa ranta ba,gashi mahaifiyarta tana hanya gobe,da wanne ido zamu kalleta muce mata mun gaza ceto ƴar ta?"
"To kin gani inaga a aika tazo kawai ranki ya daɗe,wataƙila saikiga Allah yayi ikonsa idan tazo,amma idan ba haka Rayuwar gimbiya tana cikin wani hali".
Daga haka sunkia madina ta tafi neman mafita,itakuma ta koma wajen Gimbiya Asmah wacce take kwance tana fidda numfashi ɗaɗɗaya,nishin ma yanzu ta daina. Bayinta suna gefe wannan tana goge mata jiki wata kuma tana gyara mata jinin dayake fita daga jikinta. Yanayin dai abun tausayi.
Sultan kuwa gaba ɗaya kularsa ta koma hannun Aminatou dan yanzu baya yarda da kowa sai ita,yana samun kula sosai da gareta,ganin idan zata tafi sashen bayi yana kukan sai ya bita yasa dole ta tattaro kayanta ta dawo bangaren sunkia madinan,inda bayinta masu yi mata hidima suke. Kasancewarta mace mai sauƙin kai kuma batada ganda yasa kowa kejin daɗin zama da ita,ita kanta Gimbiya Asmah yanzu babu wadda hankalinta yake kwanciya da ita ga ɗannata kaman Aminatoun,domin ta kula babu alamar mugunta ko kaɗan da take nunawa gameda ɗannata,kular da take bashi ko ita da sunkia madina albarkar. Ita kanta Aminatou tana jin tausayin halinda Asmah take ciki,duk da itama batada kirki amma kuma rashin mutuncin da Yerima kabeer ɗin yakeyi mata yayi yawa. Fasihnman dasu akan idonsu yake sheƙe ayarsa ko a jikinsa,ita kamma suna tsaka da baɗalarsu da Zaleekah sai ƙirata takaimusu abun motsa baki,haka zata runtse idonta ta ajiye tabar wajen. A ranta tana Allah wadai da wata ɗabi'a ta ƴaƴan sarauta dai. Matsayin da Allah yabasu gani suke kamar babu hisabi akansu,kowa yasani shima yasani cewar yanzu Zaleekah ba baiwar sa bace,duk abinda sukeyi a matsayin zina yakeyi amma ko a jikinsa haka yake aikatawa. Kuma babu wanda zai ɗaga yatsa yace masa abinda yake ba daidai bane. Saboda shi ɗan so ne shi ɗan sarautane kuma mai jiran zama sarkin gobe a hakan.
Sadi-sakhna ce ✍🏼
Comment
Like
Share
Follow