ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

24

by @gureenjoh

Kusan awanni uku da zama cikin conference hall ɗin an fara program ɗin ne da basu abin kari wanda serve ur self ne ya dibi abin da zai iya ci ya ci ya sha coffee, kan aka soma abin da ya tara su gabadaya vibration na Wayanshi ne ke daukar hankalinsa ganin ba za'a daina kira ba ne ya sa ya fitar ya fara dubawa sai ya yi mamaki.


Abbiey bai taɓa yi masa ƙira sama da ɗaya ba ga jerin calls nashi uku, ga na Ammiey ma har uku Maamah biyar Abba biyar Ammar duk ya fi su yawa goma sha wani abu sai hankalinshi ya tashi tunaninshi kawai wani abu ya faru a gida ne, Excuse ya nema kawai ya bar ɗakin taron sai da ya samu wuri marar hayaniya kan ya shiga ƙiran Abbiey.


Yana ɗaga wa bai ko samu daman sallama ba Abbiey yace 

"Irshad! Menene hadinka da yarinyarnan 'yar daba wacce dabancinta yayi shura a garin Kano? Da gaske kazamtaccen soyayya kuke? Ana cewa ba'a shaidar ɗan yau Irshad tarin saninka za ka take?"


Ya shiga wani yanayi ba yanayin komai ba sai jin ɓacin rai tsantsa akan harshen mahaifinsa wannan fushi sanadiyarsa ya zama tamkar an ɗiga masa dalma ne ko wuta a cikin ransa.


"Abbiey ka yi haƙuri ka zauna idan a tsaye kake"


"Image ɗinka da ya fi na gidan nan shura a duniya Irshad kana shirin tarnishing ɗin shi"


"Abbiey har yanzu ban fahimci menene laifin ba? Babu abin da ya haɗa ni da wata 'yar Daba Abbiey...schedules dina ma babu lokacin kaina bare wanchan lokacin, Abbiey kar wani zargi ko kokonton zan saɓawa Ubangijina ya ɗarsu a ranku. Har abada mu'amala da wata macen bana fatan ya zama kaddarata bare wannan 'yar daba, mashayiya da kuke magana"


Hankalin Abbiey ya ɗan fara kwanciya don a yanzu muryarsa ya ɗan yi sanyi

"Ka hau online ka ga abin da ke faruwa"


Yana sauke wayan kan ya hau ɗin Ammiey ta kira shi dole yayi Picking itama dai ranta a bace take mishi faɗa irin wanda gabadaya rayuwarsa bai taɓa ji ta mishi ba, sai ya sake shiga wata damuwar.


Idanu ya runtse yana sauraronta har ta ƙarashe 

da 

"Irshad Idan ma akwai wani abu tsakaninku ko tsaftataccen soyayya ce na haramta shi har abada, har gaba da Abada wannan yarinyar da take kallon tsabar idanuna take kwalfar kayan maye ba zan taɓa iya haɗa jini da ita ba gwara ma ka sani"


Ko da ta katse ƙiran bai cire daga kunnensa ba na seconds masu yawa kan ya saukar ya ja a hankali ya kunna data, Karon farko gabanshi ke faduwa na abin da zai tarar da ya bata ran iyayensa, Facebook ya shiga don magana ya fi yaduwa cikinta kamar wutar kara scrolling uku ya yi sai ya runtse idanu ya sake bude wa akan caption da aka yi.


Hoton Diva ce a sadda take shiga dakinshi ɗauko akwatinta shi kuma ya ɗan karkata yana kallon bayan ta tsaye a jikin kofar.


"Wai ka bi maganan Malam amma kar ka bi halinsa"

Shine caption ɗin, wani abu mai daci ya haɗiye ya sake scrolling ƙasa nan ya ci karo da hotuna huɗu, suna zaune a Airport, suna zaune cikin jirgi tana shiga motar da yake ciki sannan tana shiga dakinshi.


"Wato Malam ba zai iya tafiya shi kaɗai ba dole da mai debe masa kewa"

Comment section ya shiga ya Subhanallah!


Da sauri ya fita yana mamakin mutanen arewa, wani irin yanayi yake ji da ba zai iya fasaltawa ba, idanunsa har yaji yaji suke masa amma ya dake ya shiga ambaton Allah, idanunsa na haska masa wani comment da ke rantsuwar dama Ai da walakin rashin aurensa babu namijin da zai haura talatin bai nemi mace ba muddin bashi da aure.


Ya jima kwarai yana kokawa da zuciyarsa cikin ambaton Allah da kuma neman agajinsa a hankali sai natsuwa ya fara saukar masa, scandal me muni ne wannan a kansa zina! Sai yayi saurin a'uziyya bai motsa ba har lokacin daga inda yake tsaye. Call na Ammar ya yi picking amma bai ce komai ba kawai yayi shiru.


"Shehi!"

Bai amsa ba don ko ya amsa muryarsa ba lallai ya fita da kyau ba.


"Are you okay?"


"Uhmm zan koma program we talk later!"

Yana kai nan ya katse wayan dama da kyar maganar ya fita, juyawa yayi ya koma cikin hall din bayan ya saka wayar flight mood don ya san kira kam zai sha shi idan ya bari buɗe.


Har karfe wurin biyar suka tashi na ranan iyakaci sallah ke fitar da su daga ɗakin taron sai lunch da aka tsaya aka yi, bayan sun tashi bai jira komai ba ya wuce hotel yana shiga reception idanunsa basu faɗa kan kowa ba sai ita, idanu ya ɗan zuba mata yana jin zafin abin da aka fitar a kanshi game da ita, idan zai neme mata ma sai ya nemi ta titi? Dressing ɗinta duka takaici yake ba shi tamkar ba musulma ba, yadda kullum idan zai ganta da gashi waje hakan ya fi komai baƙanta masa a matsayinsa na wanda ya san addini amma karshe ita aka haɗa da shi.


Ɗauke idanunsa yayi ganin ta waigo waya a kunnen ta tana kallon mashigar a daidai ya wuce ya shiga elevatorn ɓangaren da yake, kai tsaya kaya ya kwaɓe ya faɗa toilet ya sakarwa kansa ruwa masu sanyi.


****


Bayan ta gama exercise ɗinta na safe wanka tayi ta kwanta bacci, ko da ta tashi sha biyu ta gota Wayanta dake bedside ta ɗaga ta duba ganin almost 50 missed calls sai ta shiga mamaki kiran Shaly tayi da duk calls ɗinta ya fi yawa.


"Diva ki duba online ki ga abin da ke faruwa! Me ya haɗa ki da Sheikh Irshad Al-Noor?"


"Me haɗina da shi kuwa? Babu!"


"Diva na sanki da riko da rashin yafiya har yanzu kina bibiyarsa ne? Don shi kika tafi Abuja?"

Tsaki ta ja ta katse ƙiran da a fili ne da Idanun Divan kaɗai ba za su bar Shaly ƙarasa zancen ba.


Media ta shiga ita kanta tayi mamaki dukda ita din ko a jikinta sai ma a fili ta furta

"Na ja maka shiga bakin duniya"


Dira ta yi bata bi kiran kowa ba ta shiga wanka bayan ta fito ta shiga cikin wani oxblood long sleeve t-shirt da ya amsheta ta saka blue cotton palazzo trouser da abin wuya tsiriri ta feshe jikinta da turaruka tare da gyara gashinta ta ɗora facing cap ta fice.


A wani fancy restaurant ta ci abinci bayan ta gama ta miƙe tana biyan kudi ta fito ta dawo hotel dinsu da ƙafa ta taho saboda rage lokaci don har ta gaji ma da zaman Abujan dukda a chan Kanon ma ba wai hira ko surutu take ba anyhow amma ko yaya akwai motsin su Skipo.


Fahimta tayi kaman ana bin bayanta abin ya bata mamaki, me hakan ke nufi? Har ta shiga hotel ɗinta ta tsaya reception tana kallon kofar bata ga an shigo ba, Wayanta ta fitar ta kira Jagaban zuwa yanzu sam bata yarda da shi ba.


Yana ɗaga wa ta fara tuhumarsa akan abubuwan da ke faruwa ya nuna mata ta kula Sossai shima kuma daga Kano zai yi abin da ya dace babu abin da zai faru, she's not convinced sam tana cikin wayan ne ta ɗaga ta kalli kofar Shigowar sai ta ga gilmawansa fuskarsa na nuna wani yanayi marar daaɗi karo na farko ta ji bata ji daaɗi ba akan abin da ya faru amma ta danne ta ɗauke kanta ta cigaba da waya.


Ita don an ƙirata 'yar iska ko ƴar daba duk ba komai ba ne amma shi da ya riƙe kamalarsa bai kamata a ja shi a taɓo haka ba, mutane suna da daukar dala ba gammo, suna kwashe zunuban mutum ba tare da sun sani ba, irin wannan har depression zai iya jefa mutum ba tare da sun yi  la'akari da hakan ba kowa na tofa abin da ya mishi masu rantsuwa na yi masu jin daaɗi na yi. 


Barin wurin tayi itama ta nufi ɗakinta fuskarshi na dawo mata da yadda ya shigo.


*****


Tana zaune tana juya shawarar da kawarta ta bata na muddin tana so ta mallaki Shehi da gaske sai ta nemi taimako, ko da ta tambayi wani irin taimako? Abin da ta faɗa mata ya barta speechless, wani zuciyar na nuna mata ba komai ba ne muddin za ta mallaki sheikh wani zuciyar kuma na kwaɓarta da tuna mata irin gidan da ta fito.


Numfashi mai nauyi ta sauƙe kan ta janyo Wayanta ta shiga media, wani irin bugawa zuciyarta yayi ta zubawa Irshad da Diva idanu hankalinta na tashi, da gudu ta dira tayi wurin Mamanta tana kwala kiran suna ta


"Mama! Mama!!"

"Menene wai Na'ima?"


"Kalli ki ga... Wannan shahararriyar 'yar dabar Sheikh zai lalacewa? Anya ba asiri a lamarinta?"


Maman ta karɓi wayan tana dubawa ita kanta zuciyarta ya buga, maganganu babu irin wanda ba'a yi ba kowa neman followers yake da post ɗin, har post na baya inda suke tsaye a titi bayan ya mareta sai da aka dawo da shi dama tun lokacin ake zargin alaƙarsu gashi yanzu ya tabbata (a cewar 'yan media).


"Babu batun Asiri Na'ima kuma ni ban yarda zai nemeta ba dukda namiji ko ya yake namiji ne amma da ayar tambaya kan alaƙarsu"


Baya ta koma ta zube a kan kujera tana dafe kai tuni hawaye ya shiga wanke mata fuska don yadda take ji kuka ne kawai za tayi ta ji sanyi.


****


Ma'u na kwance kan cinyar jiddah Idanunta a rufe jiddah na shafa kanta cikin damuwa da kulawa, a haka ma basu bar Ma'un ba jiya sai da wani ya taɓa ta sun kwana kuka daga ita har Ma'un da bata hayyacinta, addu'a kawai jiddah ke yi tana rokon Allah ya kawo musu mafita ko daga ina ne ta san yana ji kuma zai amsa mata.


Shadow ne ya shigo

"ke tashi!"


Babu musu ta ɗaga jiddah ta kwantar kan pillow

"Kina da aiki yanzu"


Wucewa tayi ta karɓi kayan uniform din ta saka kan ta nufi waje ta shiga mota duk a wani kalar yanayi na sanyin jiki haka kawai take ji a ranta kaman wani abu ne zai faru dukda bata san menene ba.


Awanninta biyu da fita ta dawo, inda ta bar Ma'u ta je sai dai bata nan kuma ta san idan ba ɗaga ta aka yi ba ba za ta tashi ba, dakuna ta fara dubawa tana tambayar duk wanda ta ci karo da shi

"Ina Ma'u? Kun ga Ma'u?"


Tun tana yi da rawar murya har ta fara kuka mai sauti kaman za ta zauce duk inda ta shiga bata ganta ba wurin su shadow ta dawo tana rokonsu su fito mata da Ma'u amma ko ci kanki babu wanda yace mata kuka ta fashe da shi mai tsuma zuciya tana yi tana ihun su fito mata da Ma'u amma kaman duwatsu haka suka zuba mata idanu suna kallo ta faɗi a wurin tana kuka.


*****


Duk yadda ya so yayi bacci a daren kasa wa yayi, yayi nafilfili mai yawa yayi karatun alqur'ani, Miƙewa yayi yaje jikin windown hotel din ya buɗe sai dai iskar bai mishi ba, a hankali ya fita sanye da baƙaƙen Pjamas dogon wando da V neck silk shirt dinshi, elevetor ya shiga ya danna sama gabadaya har ya haye da shi don hotel ɗin mai open rooftop ne.


Yana ƙarasa hawa wani iska mai ni'ima ya shiga kaɗashi, duhu ne Sossai dukda a kan titunan Abuja har lokacin akwai zirga zirgan motoci, a hankali ya ƙarasa jikin ginin wurin yana sanya hannaye a aljihu.


Warin kayan maye ya shiga ji yana sarƙe mishi iskar da yake shaƙa mai ni'ima a hankali ya waiga sai idanunsa suka faɗa kanta tsaye sanye da wasu coffee brown Pjamas abu take sha don yana iya ganin hayaƙin a iska.... Yanzu wannan ce ake alaƙantashi da ita? A hankali haushinta da tsantsar takaici ke mamaye mishi zuciya har zuwa harshe, itama juyowa tayi don ta ganshi tun yana shigowa ganin sun haɗa idanu ya sa ta kawar da nata tana tsintar kanta da kashe abin da take sha ɗin ta cigaba da tsayuwa a wurin, nufarta yayi yana takun kaman ba zai je ba idanunsa har lokacin basu bar kanta ba.