20
Chapter 20.
Tana tsaka da aiki sai ga Hajiya Binta ta ci gayu da kwallaiya kai ka ce uwar biki za ta, sai wani ɗaga hanci ta ke tana cika tana basarwa, ba tare da ta amsa gaisuwar da Nazli ke mata ba ta soma buɗe tukana tana tambayar abin da a ka dafa.
"Uban me kike yi da tun ɗazu ba ki a za komai ba?" Ta yi maganar cikin jefan ta da wani kallo me cike da zafi da kuma kishin da take ji a game da ita, dan ita fa Allah ya ji ya gani dan ba ta da wata hanyar ce da koda wasa ba za ta bar yarinya kamar Nazli tana mata aiki ba. Tana matuƙar kishin mijinta bata son ko wace mace ta raɓe shi idan ba muharramarsa ba shi ya sa take matuƙar taka tsantsan da saka masa ido a komai da ya ke. Kowai dai bata da yadda za ta yi ne amma ta tsani ta rufi ido ta kalli yarinyar, ga shi kullum kamar wacce a ke ƙarawa kyau kullum sake ganin kyawun yarinyar take. Ko ita da take mace kyawun yarinyar na matuƙar ruɗan ta bare kuma namiji, banda kyawun fuska da fata tana da diri me daukan hankalin yan maza.
Nazli da dama tun shigowarta ta shaƙa barin ma ƙin amsa gaisuwarta da bata yi ba kamar tai mata banza ta manna mata na kurama amma sai ta danne zuciyarta, da ta tuna ita ɗin gaba take da ita kuma daɗin daɗawa a ƙarƙashin ta take ya zama dole ta mutuntata tare da bata girmanta.
Ta ƙaƙulo annurin dole ta yafawa fuskarta kana cikin sanyi da ɗacin zuciya ta ce. "Afuwan Hajiya umarnin ki na ke jira kar na yi gaban kai na ba tare da sanin ki ba, amma kiyi haƙuri idan na yi ba daidai ba." "Mtchwww." Ta ja siririn tsaki ta raɓa ta shiga store yayin da Nazli ta girza kai kawai ta maida hankalin ta ga mopping da take, Fari ce ta shigo kitchen da sleeping dress a jikinta yayin da hannunta riƙe da waya tana dannawa sai murmushi take sake da gani duk abin da take a wayar na matuƙar yi mata daɗi. Ba tare da ta ɗago ko kallon wanda ke kitchen ta dauƙe bowl ta haɗa conflasks ta ɗauki cokali ta fita abin ta.
=======
UNKNOWN PLACE.
Tsaye take a bakin window ta baiwa ɗakin baya, hannunta nannaɗe a bayan ta yayin da take sauraron rahoton da a ka kawo mata. "Wannan su ne hotunan ta da inda take zuwa, a binciken da muka yi mun gano gidan da takewa aiki." Faɗin wani daga cikin ƙattin maza uku da ke tsaye sun harɗe hannaye fuskar nan a ɗaure tamau kai da gani ka san no nonsense ne su, sai dai daga yanayen dressing ɗinsu da kuma yanaye kaɗai zai bayyanar maka da cewa babu rahama ko tsoron Allah a zuƙatan su.
Ɗayan da ke tsaye a ta hannun damarsa ne ya fito da hotuna kusa goma sha ya baza su kan table tare da faɗin. "Wannan ce ita, ba su da kowa daga ita sai mahaifiyyar ta suke rayuwa sai aikin da ta samu a ƴan satuttuka da suka wuce, a binciken da muka yi mun gano ba su da wasu shaƙiƙai na kusa su kaɗai ke rayuwa a wata anguwa ta masu karamin ƙarfi." A hankali kamar bata so ta juyo cikin izza da ƙasaita ta samo taku cikin ɗakin ɗai–ɗai har ta tsaya gaban waɗan nan zaratan ƙattin da har yanzu suke tsaye ba su motsa daga inda suke ba ta, duk umarnin ta suke jira su aiwata ko ma me a wuce wurin.
Hannu ta saka ta ɗaga hoto ɗaya da ke bayyana Nazli tsaye a bakin titi za ta shiga napep, sai na gaba wanda kuma da Ammie a ka ɗauke su ba tare da sanin su ba da gani anguwa za su.
Wani irin makirin murmushi da baida ɗikon rahama ta saki kana ta ce. "Good! Aikin ku na kyau." Ta ƙara zubawa wani hoton Nazli idanu, take annurin fuskarta ya ɗauke cikin tafarfasar zuciya take kalli hoton ta soma magana kamar wanda a ka cewa tana jinta. "Kin shiga gonar da ba ta ki ba, kin ɓata min shiri da na daɗe na ke dako da tsumayin tahowarsa amma rana tsaka daga sama kika faɗo kin ɓata min aiki da cikan buri." Sai kuma ta yi shiru ta koma kan kujera ta harɗe ƙafafu ta ɗaura ɗaya kan ɗaya, har yanzun hoton Nazli na hannunta kamar wadda ke son gano kuskure ko nakasu a hoton haka take kallonsa. A hankali ta furta. "Now tell me wani irin hukunci kike son na yi miki?" Dole ki san kin taɓa wanda bai kamata ba, kin ratsa gonar da ba taki ba, yadda kika saka ni ƙunci da takaici dole ki ƙarbi tukwicin ki." Ta faɗa hakan cikin sakin wani mugun murmushin da ke ɗauke da ma'anoni da dama. Ta ɗago ta kalle su ba ki dayan ta ce. "I want her died."
=======
Tafe take cikin hankali da nutsuwa kamar ta ta, a yadda take ɗaga ƙafa ɗai–ɗai take tafiya kai ka ce tana cikin filin fashion show ne ba kan titi ba. Sai dai ga wanda bai san ta ba sai ya ce iyayi ne zalla amma ga wanda ya santa ya san haka tafiyarta take ko ya ya ta ke ko me ta yi sai ka ɗaga kai ka kalleta. Nazlin Ammie kenan, yau ta yi latti tun da ta bar gida jikinta ke bata kamar da wanda ke bibiyarta a baya, sai dai da ta juya sai ta ga wayam babu alamun kowa amma ita ta sani tana jin idanu a kanta.
Dalilin da ya sanya ta ɗaga ƙafa kenan cikin sauri take tafiya yayin da take jero addu'oi a jajjere tana fatan ba wani abun ne ke bibiyarta ba kuma, ta ƙanƙame jakar hannunta gam jira kawai ta ke ta ji tass ta arce a nakare. Sai da isa gidan Alhaji Badamsi ta shiga kafin ta samu nutsuwa ta soma sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta yi gudun tsere saboda tsoro.
Tana zuwa ta kama aiki, komai da ta san na ta ne sai da ta aiwatar kan ta bar gidan. A hanya ta tsaya a gefen titi dan tsaida mai napep ba zato ko tsammani sai ga wata mota jeep baƙa mai tinted ta yo kanta da mugun gudun tsiya, kan ta farga ta yo kanta da kyar ta sha ta yi saurin ja da baya wanda hakan ya haddasa mata faɗuwa cikin kwata cunɓul,take kuwa ta soma wutsil–wutsil da neman taimako.
Da sauri kuwa jama'an wurin suka yo kanta a ka samu a ka fidda ita daga cikin kwatan sai dai fa babu kyan gani dan gabaki ɗaya jikin ta ya ɓace da ruwan datti hatta fuskarta ta sha ruwa ba kaɗan ba. Da taimakon bayin Allah nan a ka samu a ka nemo mata ruwa ta wanke fuskarta suka samar mata waje ta zauna sai sauke ajiyar zuciya take suna mata sannu tare da tambayar ko ta ji ciwo? Amma Nazli ba baki sai ɗaga masu kai take dan gabaki ɗaya bata gama dawo hayyacinta ba, duk a tsorace take sai wulla idanuwa take jikinta na faman kyerma, ba wani ciwon na a zo a gani ba ta ji ɗan gaucewa ce a ƙafa.
Haka suka dinga Allah wadai da wasu mutane ga shi nan dai mai motar ya kusa kaɗe ta da motarsa a gaban idon su idan ba Allah ne ya kare ba amma ɗan tahaliƙi nan ko tsayawa bai ba bare ya san a wani hali yar mutane ke ciki ba ya yi tafiyarsa abun sa ba tare da ko waiwayowa ba.
Haƙuri suka dinga bata a ka samu wani ya tsaida mata adaidaita sahu ya biya har gida a ka kaita, Ammie kuwa ba ƙaramin tashi hankalin ta ya yi ba ganin Nazli a haka nan ta soma tambayar abin da ke faruwa. "Ammie ba fa wani abun a tada hankali ba, akasi a ka samu garin tsalleke kwata na faɗi kuma ban wani ji ciwo ba." Ta ɓoye mata haƙiƙanin gaskiya dan ta san da zarar ammie ta ji abin da ya faru to hankalin ta ƙara tashi zai yi ita kuma ba za ta so hakan ba, ita kanta har yanzu a tsorace take zuciyarta bata dena bugu ba barin ma idan ta tuna da wanda ke bibiyarta duk da bata tabbatar ba amma jikinta na bata duk motsin ta da akwai idanun wasu a kanta.
Ammie zuciyarta ɗaya ba tare da tantama ba ta yarda da abin da Nazli ta faɗa dan ta san ba za ta yi mata ƙarya ba, kujera ta ja ta zaunar da ita kana da kanta ta haɗa mata ruwa cikin bokita ta kai mata har bandaki kana ta ta ce da ita ta je ta yi wanka ta fidda kayan jikin nan ta. Nazli na cikin wanka ta kawo mata zani da hijabi ta rataya mata kan ƙofa kana ta koma ciki.
=======
Wasa wasa a kwana a tashi ba wuya Nazli har tai wata biyu da fara aiki, zuwa lokacin har ta saba da abubuwan da ta ke gani a gidan ta fahimci halayen kowa a cikin su shi ya sa take bi da so a yadda suke. Ta saki jiki sosai tana aiki bil hakki da gaskiya komai da zuciya ɗaya take yinsa, kamar yadda aikin na ta ya buƙata da safe take zuwa ta yi abin da ya kawo ta koma da yamma. Ganin kyan aikin na ta ya sa Hajiya Binta ta haɗa mata da shara da gogen gida tare da ƙara mata kuɗin albashin ta, sai ya zamana da ta zo ta girki shara wanke wanke komai na wuyarta.
Tana jin daɗin aikin na ta sai dai abin da ba za'a rasa ba, kuma har yanzu ba a dena bibiyarta ba dukkan motsin ta a hannunsu ya ke, haka zalika ba su dena kai mata hari ba Allah ne kaɗai ke kare ta tun abun yana bata tsoro har ta zo ta fauwalawa Allah lamarinta dan ta san shi ne mai karewa.
Tsakanin ta da Hajiya Binta kuwa kadaran kadaham ne tana dukkan me yuwa dan ta gujewa abin da zai saɓa ma sharuɗan da ta gindaya mata, duk inda ta ga Alhaji Badamasi to bata ko raɓar wurin bare zuwa. Tsaknain ta da Fari (Farida) kuwa sam basa ga maciji, ita Fari ta ɗaurawa kanta ƙarya izza ƙasƙantar da na ƙasa da ita ba komai bane a wurin ta, barin ma Nazli da ba ƙaramin kishi take da ita ba ganin irin kyawun da Allah ya hure mata ta tsani ta rufe ido ta ga Nazli ji take ina ma za ta samu ta caka mata wuƙa ta zana mata fuska yadda ba wanda zai ji sha'awar ta bare mararin ganinta, ita ga ta nan kullum ta ƙare cikin jigilar zuwa salons da beauty parlour amma ko kaɗan bata kama koɗa yatsan ta a kyau ba.
Yarinya yar talakawa a cewarta ta fita kyau ta tsani ta ga wani ya fita da abu a rayuwa, shi ya sa kullum bata rabo da wani aiki ko neman rigima da Nazli amma ita bata biye mata dan ba girmanta bane, yadda ta tsani Nazli haka ta yi poisoning Abla a kanta haka suke haɗuwa suna tsula tsaiyarsu amma Nazli bata biye masu abin da ya kawo ta shi take yi ta yi tafiyarta.
Idan da abun da rayuwa ta koya mata a yanzu to shi ne haƙuri juriya da kwantar da kai, she's been through alot to care about what people will do or say about her. A kasin Fari da Abla, Araf sai ya kasance mai saukin hali babu ruwansa tho da farko ba ya jituwa da ita amma daga baya sai ya saki jiki har hira ya kan mata wani bin idan tana aiki ma yana tayata, haka nan zai ɗauki litattafan sa ya zo tana taya sa homework idan a ka basu a makaranta......