ALIYU HAYDAR

Chapter 29

by @nieemartullah

Da safe mom ta kai wa dad kayan breakfast ɗin shi, sannan ta aika Munarh  ta kai wa nata mijin ita ma da ke ɗakin baki shima nashi kayan breakfast ɗin.

Su kuma matan gidan suka haɗu a kan dining gaba ɗayan su suna breakfast.

Bayan sun gama Ummi ta ce " toh mu kam idan Allah ya kaimu anjima zamu koma KD, tunda duk munji sauƙi alhamdulillah."

Mom da ke cin abinci a cikin plate ɗinta ta ɗago ta ce " na ɗauka ai zaku bari zuwa ayi biki sai ku koma?"

Murmushi Ummi ta yi ta ce " ai saboda wurin aiki kinga  excuse ɗin sati ɗaya suka ɗauka gashi har sati ɗayan ya yi."

" Kinga ai ya kamata a koma ɗin."

" Amma kuma ina ganin sai a bar ita Maimunatu a nan saboda shirye shirye ni da Abdul sai mu koma."


Ba don mom ta ji daɗi ba ta amsa mata da " toh amma dai ai zaku dawo lokacin bikin ko." Ta tambaya.

Murmushi Ummi ta yi ta ce " zamu dawo in shaa Allah."

Jinjina kai mom ta yi ta ce " toh Allah ya nuna mana."

Hajiya mama da Ummi suka ce " ameen."

Wuraren ƙarfe sha ɗaya na safe bayan Jiddarh ta kawo breakfast Zannur ya ci, ya ce ma mamy " zai je gida ya yi wanka ya dawo."

Ta ce to shikenan sai ya dawo.

Gida ya wuce ya yi wanka yana fitowa ya shirya cikin ƙananun kaya, wayarsa da ya bari a ɗakin HAYDAR ya shiga ya ɗauka sannan ya fito ya koma cikin mota ya zauna.

Wayar da ya ɗakko ya buɗe ya shiga cikin call logs ɗin shi.

Missed calls da yawa ya tarar ga na mamy sai kuma wanda ya ba shi mamaki kiran Sadeeq da ya gani.
He hesitate for a second sai kuma ya danna kira ya kira shi back.

Ringing ya yi har sai da ya kusa katsewa kiran sannan aka ɗaga.

" Assalamu Alaika." Zannur ya faɗa bayan Sadeeq ya ɗaga kiran.

Daga ɗaya ɓangaren Sadeeq da ya fito daga wanka ya ɗaga ya ce " Wa'alaikassalam Warahmatullah."

Shiru Zannur ya yi sai kuma ya ce " i'm sorry doctor sai yanzu nake ganin miss call ɗinka."

Sadeeq da ke sauraron shi ya ce " ba damuwa engineer na san ai kana busy ne shiyasa."

" Yanzu zan fito  idan ba damuwa ina so mu haɗu a BluCabana akwai maganar da nake so muyi."

Zannur da ke sauraren shi ya ce " toh shikenan bari na fito dama nima akwai maganar da nake so za muyi."

Bayan sun kashe wayar Zannur ya kunna motar da yake ciki ya hau kan titi ya yi hanyar zuwa BluCabana.

Ya riga Sadeeq kasancewar dama shi ya fito already.

Sai da ya zauna na wasu ʼyan mintuna sannan sai ga Sadeeq ya zo.

Bayan sun gaisa Sadeeq ya ce " ina ta neman layin ka baya shiga, sai daga baya kuma na ga ya shiga."

Zannur ya ce " maybe network ne nima na fita na bar wayar a gida shiyasa."

Jinjina kai Sadeeq ya yi ya ce " dama ina son zan yi aure ne in the next two weeks so ina son za'a ƙara yi man fenti da kuma ɗan abinda ba za'a rasa ba."

Jinjina kai shima Zannur ya yi ya ce " ba damuwa zan tura wanda zasu yi aikin and zan zo nima na ɗan yi supervising ɗin su."

" Tohm shikenan,and sai maganar da ka ce za muyi."

Kallonshi Zannur ya yi sannan ya ce............................

Da yamma gaba ɗayan su suka fito zasu yi wa su Ummi da yaya Abdul rakiya zasu koma kaduna.

Back seat Ummi da yaya Abdul suka shiga driver ya zauna a driver seat.

Bayan sun zauna Ummi ta ce " mun gode sosai da karamci, Allah ya saka maku da alkhairi."

Mom ta ce " haba ai an zama ɗaya."

Murmushi ta yi sai kuma ta kalli Jay ta ce " toh amarya sai mun dawo biki kenan." Ta faɗa tana murmushi.

Rufe fuska Jay ta yi tana dariya ta ce " kai Ummi har kin sa na ji kunya."

A haka suka yi sallama ana ta raha.

Bayan motar su ta tashi su kuma suka koma cikin gida.

A parlour suka yada zango gaba ɗayan su, mom ta ce " Jay daddynki ya ce na tambaye ki programs ɗin da zakiyi?"

" Mom ni fa ba zan yi wani program da yawa ba walimah ce kaɗai zan yi."

" Amma Sadeeq ya ce zasu shirya dinner ta ɓangaren su."

" Toh shikenan zan faɗa mashi, dama na ji ya yi maganar kama hall ne da kuma decoration."

Munarh da take ta jinsu bata ce komai ba ta ce " amma ke dai yar baƙin ciki ce wallahi."

" Haka kike nufin za'a yi bikin daga walimah sai dinner?"

" Ba'a yi events a nawa bikin ba, naki ma kice ba za'a yi ba?"

Dariya Jay ta yi ta ce " ki ji man yarinya, wa ya hanaki yi a naki bikin."

" Ni bana son bidi'a ne da Sadeeq zai yadda ma ko dinner ɗin ma ba za'a yi ba."

Tun kafin ta rufe bakinta Munarh ta ce " wallahi kuma kin yi kaɗan, sai dai in an yi kar ki zo."

Mom da hajiya mama dake ta sauraronsu suka fara yi musu dariya.

Jay da ke murmushi ta ce " kiji man yarinya biki na ne ko naki?"

" Bikinki ne amma ai ba haka nan zamu zuba maki ido kina yin abinda kike so ba." Munarh ta bata amsa.

Dariya ta yi ta ce " yawwa kin ji ke da kanki me bakin ki ya ce, biki na ne don haka dole a bi abinda nake so ehe."

Haka suka yi ta gardama a tsakaninsu har suka gaji suka yi shiru.

Nafeesarh ce ke haɗawa aunty kayanta a travelling bag ɗin da zata yi tafiya da shi.

Bayan ta zuge zip ɗin ta aje ta a gefe ta ce " aunty kinga wannan lace ɗin ɗazu muka zaɓe shi ni da su aunty Zulaikha a matsayin ankon dinner ɗin yaya, ya yi kyau?"

Karɓar wayar ta yi ta duba, sai kuma ta ce " ya yi kyau sosai amma ina fatan kun nunawa Sa'adarh saboda ita ma ta kai ɗinki da wuri? kun san telolin nan ba alƙawari garesu ba.

" Wallahi aunty na kasa faɗa ma Sa'adarh yaya zai yi aure."

" Duk da na san dole zata ji ko a wani wurin amma ni dai ba zan iya faɗa mata ba."

" Bari na je na samu Hannah da aunty Zulaikha idan wani a cikin su zai iya faɗa mata, ni dai ba zan iya ba."

Shiru aunty ta yi bata ce komai ba saboda babu wanda bai san Sa'adarh na son Saddeq ba, amma ya suka iya tunda shi baya sonta dole su yi haƙuri Allah ya bata wanda ya fi shi alkhairi.

Nafeesarh ta ce " bari na je part ɗin mama na dawo."

Bata jira me aunty zata ce ba ta fita.

Da taje part ɗin mama babu kowa a parlour sai ta wuce ɗakinsu.

A kwance ta same su suna ta duba irin ɗinkin da zasu yi.

Hannah na ganinta ta ce " yawwa dama yanzu nake shirin kiranki na ce ki zo mu zaɓi ɗinkin da zamuyi."

Zama ta yi a gefen gadon ta ce " ni yanzu duk ba ma ta ɗinki nake yi ba."

" Yanzu na nunawa aunty ankon dinner ɗin nan ta ce wai ya kamata a ce mun nunawa Sa'adarh da wuri saboda ta kai ɗinki."

" Amma ni gaskiya ba zan iya tunkarar Sa'adarh da wannan lace ɗin na ce mata ga ankon yaya ba."

" Wallahi tunda aka saka bikin kunyarta nake ji, shiyasa dama na zo idan aunty Zulaikha ke zaki turo mata ko kuma Hannah."

Kafin ta gama faɗin sunanta Hannah ta ce " count me out wallahi nima ba zan iya turawa Sa'adarh ankon yaya ba."

" Ai sai taga ma cin mutunci ne, mun san fa tana son yaya kuma yanzu za'a yi bikin shi saboda ni ce sarkin marasa kunya sai na kama tura mata anko, ni dai ba zan iya ba sai dai ko idan aunty Zulaikha zata iya."

Zulaikha ta ce " nima dai ba zan iya ba gaskiya, amma kuma ina da wata idea, naga su aunty suma sun fitar da nasu ankon, why not idan aunty zata turawa yakumbo Maryam na su na manya sai ta tura mata da namu, a ce mata wannan na ʼyan mata ne."

Nafeesarh ta ce " you are a life saver aunty Zulaikha shiyasa nake ƙaunarki."

Hannah ta ce " tunda mun gama da issue ɗin Sa'adarh sai kuma mu dawo kan ɗinkin da zamuyi."

Nafeesarh ta ce " amma aunty Zulaikha brocade ɗin wani colour zamu saka mu."

" Da na ce mu saka red amma da naga wani green and white sai naga yafi wancan red ɗin yin kyau shi zamu saka yanzu, ɗinki kuma mun gama magana da wanda zai ɗinka mu yake jira mu kai masa.

Cardiac monitor ɗin da aka jona ma HAYDAR ne ya fara ƙara Beep........beep........beep........ mamy da ke zaune tare da Jiddarh ta miƙe da sauri tana ƙarasawa inda yake ta ce " Jiddarh maza je ki kira doctor."