BA SO BANE?

Chapter 4

by @hafsatwaziri1122



Adamu ne a zaune kusa da Abdool-Aziz,da sauri ya miƙe tsaye. Tsananin farin cike ne ya ɗauke a fuskarsa,wanda har muryarsa sanda ta bayyana haka.

Juyawa ya yi ya kalli Abdulaziz cikin zumuɗi, 


"kana jin abin da naji kiwa? , kira daga shugaban SS da kansa Gaskiya kai mai sa'a ne"




 ya ƙarasa maganar yana tsalle cike da jin daɗi. Shap ya manta abin da ya faru ɗazu a company. 

Abin da ya fara faɗo masa a rai shi ne,wataƙila addu'an sa ta Allah ya amsa, Abdool ya samu aikin da suka jima suna mafarkin ya samu.

Ga mamakinsa duk irin murna da farin cikin da yake yi,Abdool na kwance a katifa hankalinsa na kan waya,ko kallon Adam baiyi ba balle ya nuna yasan me yake yi.

Wayar hannunsa ya ajiye a gafe, ya gyara kwanciyarsa ba tare da ya kulasa ba.

Farin cikin da ya bayyana a fuskar Adamu a take ya rikiɗa ya koma mamaki,ji ya yi wani baƙin ciki ya daki zuciyarsa a hankali yaja ƙafafunsa da suka masa nauyi ya koma gefe,guri ya nema ya zauna cike da tambayoyi kala kala aransa, sai dai sanin idan zai kwana yana tambayar kansa bai da amsar sune yasa shi kishingiɗa tare da lunshe ido.

Jin yadda zuciyarsa take bugawa kamar zata fito waje ne yasa shi miƙewa, taku ɗaya ya yi ya gansa kusa da Abdool, "yau fa ranar farin cike ne agare mu,amma kayi burus da lamarin sai ma ƙoƙarin gyara kwanciya kake yi" ya ƙare maganan tare da zuba masa idanunsa.


"wai ba ka ji cewa ya yie yana neman ka yanzu ba? Ka tashi mu tafi kafin su canja shawara. Ka san kamfanin nan, ana ta ribibi wajen neman aiki. Idan ka yi wasa, za su maye gurbinka da wani ne."

Aziz, wanda ke kwance har sannan idanunsa rufe kamar mai barci, ya ja ƙaramin tsaki. Da ƙyar ya buɗe baki ya ce,

"Wani kamfani?"

Adamu ya sororo yana kallon rainin hankali a fili ya ji kamar ya kai masa naushi saboda takaici. Sai dai ya daure ya sauke numfashi. Ya ce

"Ohhhhhhh..."

 a hankali, sannan ya sassauta muryarsa. Ya san halin Aziz sarai. Idan ya matsa masa da ƙarfi, zai iya cewa ba zai je ba, kuma da gaske ba zai je ɗin ba.

Cikin murya mai cike da lallashi ya ce,

"Ah haba Aziz. Aiki ne fa za ka samu. Aikin da ka daɗe kana nema. Aikin da mu Inna da Baba muke ta addu'a dare da rana Allah Ya buɗe maka ƙofa. Yanzu da damar ta zo, kai ne za ka ce ba za ka je ba?"

Aziz ya buɗe idanunsa ya kalle shi da wani irin kallon ya ce'' ban son raini kuma ka daina damuna. su nemi wani."

Kalmar ta fito a taƙaice, amma ta sauka a zuciyar Adamu kamar dutse.

Idanunsa suka buɗe saboda mamaki.

" Kana neman abun a wajen mutane ka ce baka son raini?''

Aziz bai amsa ba. Kawai ya sake rufe idanunsa, alamar ya gama magana.

Cikin takaici, Adamu ya miƙe tsaye.




"Wai me ya sa kake haka ne, fisabilillahi? Shi ya sa mutanen unguwar suke maka kallon ɗan girman kai. Wallahi kai babban ɗan girman kai ne! Ka ji wai bakason raini. Allah Ya baka dama, kai kuma ka nuna kamar ba ka buƙatarta."



Aziz ya yi masa banza, ya ci gaba da kwanciyarsa kamar ba da shi Adamu ke magana.

Sai dai duk da hakan, maganar Adamu ta shiga zuciyarsa.

Ɗakin ya yi tsit na ɗan lokaci.

Bayan kusan mintuna uku, Adamu ya gaji da tsayuwa, zuciyarsa na fada masa ya fita harkar Aziz din kawai. Sai kuma da ya tuna a halin da suka fara ganin aziz din. Sai ya yi ya kasa haƙuri. Ya san idan ya ƙyale maganar nan, Aziz ba zai je ba.




"Aziz... kana buƙatar aikin nan fa. Don Allah ka tashi mu je. Ba don ni ba... don Allah."




Ya miƙe ya ɗauko masa rigarsa, sannan ya dawo ya tsaya a kansa.

"Azizzz!"

Ya kira sunansa da ɗan ƙarfi, yana bubbuga gefen katifar da ƙafarsa.

A hankali Aziz ya buɗe jajayen idanunsa, waɗanda suka nuna barci yake ji matuƙa. Ya lumshe su na ɗan lokaci kamar zai sake komawa barci, amma daga ƙarshe ya buɗe su ya zuba wa Adamu ido.

"Ka dame ni fa."

"Eh, na sani. Ni dai ka tashi mu tafi."

Adamu ya faɗa yana miƙa masa rigar da ke hannunsa.


Company****



A can cikin kamfanin kuwa, tun bayan da Fahad ya yi wa Aziz waya, hankalin kowa ya koma kan ƙofar babban Hall ɗin.

Ba wai suna ɗokin zuwansa ba ne don ganin hukuncin da Oga Fahad zai yanke masa. A'a, abin da ya fi ɗaukar hankalinsu shi ne su san wace ce wannan budurwar, kuma meye matsayinta har ta iya juyar da al'amura cikin ɗan ƙanƙanin lokaci haka. Duk dama wasu a wajen sun gama yadda da cewa budurwarsa ne.

Sai Hall ɗin ya yi tsit.

Ƙarar sautin takalmi da suka ji daga bakin ƙofar ne ya sa kowa ya ɗaga kai lokaci guda.

Adamu ne ya fara shigowa.

Da idanunsa suka sauka kan yadda ma'aikatan kamfanin suka taru wuri guda, mamaki ya bayyana ƙarara a fuskarsa.


Dama tun da suka shigo cikin Company ya lura da wani yanayi na rashin kaikomon ma'aikatan. 

Nan take zuciyarsa ta buga da ƙarfi.

Abin da ya faru ɗazu ya dawo masa sabo fil a zuciya.

Cikin tsoro ya ɗaga kansa yana kallon wajen.

"Shin wai me yake faruwa ne a nan?"

Ya tambayi kansa da kansa.

Amma da ya san babu wanda zai ba shi amsa, sai ya yi shiru ya tsaya a gefe.

A daidai wannan lokacin...

Oga Fahad ya ɗaga murya cikin tsawa. Ya ce
"Ina ɗan iskan?"

Bai gama rufe bakinsa ba...

Sai ga Aziz ya shigo kansa tsaye yana sallama cikin ƙaramar murya.

"Assalamu Alaikum."

Nan take idanun dukkan ma'aikatan Hall ɗin suka koma kansa.

Ganin irin da suke masa sai ya tsaya na ɗan lokaci yana kallonsu ta ƙarƙashin ido.

Tun asalinsa ba ya son yawan kallonsa mutane kan yie.

Ganin yadda suka dauke idanunsu a kan ya sa ya haɗe fuska tamkar wanda da bai taɓa yin murmushi ba.

Ko kaɗan babu walwala a fuskarsa.

Sai dai tsananin nutsuwarsa da ƙwarjininsa suka sa Fahad ya kasa aiwatar da abin da ya shirya tun farko.

Da idanunsu suka haɗu...

Sai ya ji kamar wani abu ya sauya a cikin zuciyarsa.

Fushin da yake ji bai ragu ba, amma ya kasa kai masa hari kamar yadda ya yi niyya.

Sai kawai ya dunƙule hannayensa yana huci.

Aziz ya ƙarasa kusa da Adamu ya tsaya. Ya haɗe hannayensa dukka ya rike, yana kallon oga Fahad ya ce,




"Ka kira ni?"




Kafin Fahad ya samu damar ba da amsa...

 muryarta mai cike da izza ta fito daga bayansu.



"He is not the one who called you."




Kowa da ke cikin Hall ɗin ya juya lokaci guda.

Aziz ma ya juya a hankali.

Da idanunsa suka sauka a kanta...

Wani ɗan mamaki ya ratsa shi.

Sai dai bai bari ko kaɗan hakan ta bayyana a fuskarsa ba.

Tana zaune a kan kujerar CEO cikin cikakkiyar isa.

Ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, sannan ta saki wani ɗan murmushi mai cike da raini. Murmushin
da ke nuna a shirye take da duk wani abu da ta shirya.


A hankali ta miƙe tsaye.

Cikin tafiya mai cike da kasaita ta fara takowa zuwa gare shi.

Das... Das... Das...

Sautin takalminta ne kaɗai ke amsa kuwwa a Hall ɗin da ya yi tsit tamkar babu mai rai a cikinsa.

Har ta iso daf da Aziz.

Ta tsaya gab da shi.

Ta saka hannu ta zare gilashin da ke manne a idonta tana kallonsa.

Shi ma bai ja da baya ba.

Ya zura mata ido babu alamun tsoro ko firgici.

Na ɗan lokaci...

Suka tsaya suna kallon juna.

Kowannensu na ƙoƙarin karanta abin da ɗayan yake ɓoyewa a zuciyarsa.

Hall ɗin ya sake yin tsit.

Numfashin ma'aikatan ma kamar ya tsaya.

Bayan kusan mintuna biyu...

Aziz ne ya fara janye idanunsa.

Ya lumshe su na ɗan daƙiƙa, sannan ya sake buɗe su ya mayar da kallonsa gare ta.

Daga ƙarshe ya buɗe baki cikin murya mai sanyi ya ce,



"Gani."




Nan take fuskarta ta sake tsuke wa
Ta watsa masa wani shegen kallo mai cike da raini, sannan idanunta suka fara yawo a jikinsa tun daga sama har ƙasa. Ta tsaya tana kallon farar rigarsa da bakin wandonsa, waɗanda suka fi yi mata kama da na gonje.



Shima haka nan ya tsinci kansa da kare mata kallota ƙarƙashin ido, 
A zuciyarsa ya ce,



"Tana ta kallo na kamar mayya."




Sai dai a zahiri, bai ce uffan ba. Ya kawar da kansa gefe yana jiran jin dalilin da ya sa aka kira shi. Duk da ma dai, ya riga ya fahimci cewa abin da take son yi kawai shi ne ta gwada masa ƙarfin ikonta a gaban kowa.


Oga Fahad ya tako har inda suke tsaye. Ya tsaya gab da Aziz, sannan ya ce cikin murya mai nuna iko,



"Kafin na ɗauki mataki a kan abin da ka aikata, ka ba ta haƙuri."



 Da sauri ya ɗaga ido ya kalle shi, Ya yi kamar zai ciji lips ɗinsa, amma daga bisani ya fasa, ya kawar da kansa gefe yana kallon Adamu da jikinsa keta tsuma. Yadda ya yin ne ta ƙara tunzura Fahad. Cikin matsanancin fushi ya cafke gaban rigarsa da ƙarfi, ya jijjiga shi kaɗan sannan ya ce cikin kakkausar murya,




''Na ce ka ba ta haƙuri... yanzu nan!"✍️✍️