Chapter 5
BA SO BANE.
Story📃 writing
by
Hafsat waziri
Young talent writer's
•Yota•
Page 5
Sosai tashin hankali ya bayyana a fuskar Adamu, wanda a wannan lokacin ba zai misaltuwa ba.
Tun sanda Oga Fahad yace Abdool ya bada haƙuri.
Jikin Adamun ya ɗauki wani irin tsuma, saboda ɗan gajeren zaman da ya yi da Abdool-Aziz ya riga ya karance shi.
Sanin irin kafiya da tsaurin zuciyarsa yasan tabbas kome na iya faruwa,ko da kuwa sama zata haɗe da ƙasa.
Abdool ba zai taɓa bin Umarnin Oga Fahad ba,mussaman akan Yarinyar da ya ke ganin tsana a idanunsa.
Sosai Oga Fahad ya damƙe wuyar rigar Abdool,jijjiga shi yake da iya ƙarfin da Allah ya ba shi.
Sai dai ga mamakin sa ko gezau Abdool bai yi ba,sai ma gyara tsayuwar sa da ya yi.
Adamu da yake tsaye agun duk hankalinsa ya gama tashi, ganin ƙarfin hali irin da abokin sa.
Ba abin da ya ɗaga ma Adamu hankali sai, sanin hali irin na masu kuɗi kar ya masa tozarci mafi muni,a yadda yaga hankalin Ogan nasu ya gushe.
Kafin wani a cikin su ya yi magana, Adamu ya matso gaban Oga Fahad da sauri, ya haɗe hannayensa alamar roƙo. Ya yi kamar zai durƙusa a ƙasa. Muryarsa cike da tashin hankali da rauni, ya ce
"Yallaɓai... don girman Allah ka yi haƙuri! Wallahi Kuskure ne, ba da gangan haka ya faru ba."
Kalaman Adamu suka sake mayar da hall ɗin yin shiru. A hankali, Abdool ya janye idanunsa, waɗanda ke kallon wani gefe, ya fara sauke su a kan Adamu, dake tsaye har yanzu hannayensa a haɗe. Sannan ya mayar da kallon nasa kan oga Fahad dake rike da da wuyar rigarsa. Sai ya sake kallon Adamu da bai fasa magiya da bada hakuri ba. Jin yadda Adamu ke magiya, kamar wanda ake shirin za'a zarewa rai, ya haifar masa da wani mummunan ɓacin rai. Wani tsananin baƙin ciki da ɗaci suka taso daga ƙarƙashin zuciyarsa, suka toshe masa maƙogwaro.
Idanunsa, da tun ɗazu suke a kafe cikin natsuwa da kwarjini, a yanzu suka fara canza launi zuwa wani irin ɓacin rai. Sai dai bai bar hakan ya bayyana a zahiri ba.
Kafin Oga Fahad, da ke kallon Adamu, ya samu damar yin magana, sai ƙarar ringtone daga aljihun wandonsa ta hana hakan.
Da farko ya yi burus da kiran. Yana kokarin aiwatar da abin da ke ransa.
Wani kiran ya sake shigowa.
Cikin wani ɗan guntun tsaki, ya sanya hannunsa ɗaya ya zaro wayar daga aljihunsa, yana sake tamke fuska.
A daidai lokacin da idanunsa suka sauka kan fuskar (screen), sunan DADDY ya bayyana.
Bai tsaya nan ba. Da ya duba gefen notifications ɗinsa, sai ya ga ashe tun ɗazu ake nemansa. Akwai missed calls goma daga Brother Umar, har da huɗu daga Ummi.
Ganin irin wannan jerin kiran daga ahalinsa a lokaci ɗaya, ya tabbatar masa da cewa ba lafiya ba.
Ba tare da ya ɓata lokaci ba, ya saki wuyan rigar Abdool-Aziz da wani irin ƙarfi, har sai da Abdool ya yi baya kaɗan. Ya fita yana ƙoƙarin ɗaukar kiran.
Bayan fitar Oga Fahad, ta saki murmushi kamar wacce ke jiran ya gama ya bata waje, ta juyo tana kallon ma’aikatan da suka yi jugum kamar waɗanda ruwa yawa duka.
Tun kafin ta ce wani abu, ma’aikatan suka haɗi baki, warin faɗin,
“Don Allah, Hajiya, ki yi haƙuri…”
“Ku yi min shiru!” ta faɗa da ƙarfi sosai.
Hakan ya sa wajen ya yi tsit, kamar an yi ruwa an ɗauke.
Ta daure fuska sosai, ta ce,
“Kafin na fara sa ku nadamar ranar da kuka fara aiki a nan, ina son duk ƙazaman da ke cikin wannan kamfani su saurare ni.”
Ta fara nuna su da yatsa ɗaya bayan ɗaya. Lokacin da hannunta ya sauka kan mai shara, wanda yake sunkuyar da kai tamkar tsohon munafiki, sai ta janye hannunta tana sakin wani irin murmushin kasaita.
Ta ci gaba da cewa,
“A yau ya kamata ku gane cewa ba iya bin kyawawan samari, ƴaƴan masu kuɗi, suka sani ba. Ƴaƴan masu kuɗi suke da cikakken iko da damar da za su iya yin komai a kan kowa da komai a wannan duniyar, musamman ma a kan talakawa irinku.”
Abdool ya lumshe manyan idanunsa, sannan ya sake buɗe su a kanta duk a lokaci ɗaya. Fuskarsa ta nuna alamun son yin murmushi, amma sai ya basar, yana shafe gumunsa. Ya gyara tsayuwarsa mai kyau, yaci gaba da kallonta.
Cikin sa'a kuwa, idanunsu suka ci karo da juna. Da sauri ta galla masa harara, sannan ta kau da kai, ta ci gaba da maganarta cikin ɗaga murya, kamar yadda ta fara.
“Abu na farko da zan fara yi shi ne na tabbatar da cewa gaba ɗayanku kun yi dana-sani. Amma kafin nan, yana da kyau ku san ko wace ce ni, kuma menene matsayi na a wannan kamfani.”
Shiru tayi ta ɗan saci kallon sa, kamar saboda shi za ta yi maganar.
Ganin still idonsa na kanta ne yasa taji wani confidence, saurin kawar da kanta ta yi ta cigaba da magana.
“Wannan kamfani, da kuma komai da kowa da ke cikinsa, mallakina ne. S & S Sardines
Nawa ne. Kuma mallakina ne, ni nake da iko akan company ɗin da duk wani abu da yake cikinsa,duk a ƙarƙashin iko na kuke.
Hall ɗin tsit ya yi kamar maƙabarta,ko cikakken motsi basa yi,ba wanda fuskarsa bai nuna tsananin firgici da tashin hankali ba.
Kowa da abin da yake saƙawa a zuciyarsa,wannan rana ta zame musu rana mai cike da barazana akan aikin su.
Kalmar data furta ne ya dawo dasu daga duniyar tunanin da su ka faɗa.
"Bana buƙatar sake ganin kowannen ku a cikin company na and mind you duk inda zaku je ku dage da tsabta,da ƙare maganar ta tana kallonsa.
Tashin hankali wanda ba a sa masa rana kenan. Ma'aikatan gaba ɗaya suka shiga tashin hankali. Mai shara, a gigice, ya ce,
“La haula wa la quwwata illa billah!”
Sai kuma ya fashe da wani irin kuka mai ƙarfi. Cikin kukan ya ce,
“Don Allah, Hajiya, ki yi haƙuri. Ki yi mana rai. Wallahi, wallahi, ba mu sani ba ne. Ba mu san ke ce ba.”
Ta yi banza dashi tana ɗauke kanta. Ta yi ƙoƙarin mayar da kallonta kansa domin ta ga yadda zai yi a lokacin da ya ji ta kore su, sai dai ta kasa samun damar ganinsa, sakamakon ma'aikatan da ke hayaniya sun tare shi.
Gaba ɗaya Hall ɗin ya hargitse da hayaniyar mutane. Ma'aikatan duk suka haɗa baki suna ta roƙonta, amma sai ta burus kamar ma ba da ita suke yi ba.
A ƙarshe ma komawa wajen zamanta ta yi, ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kallonsu.
Shi kam, kallonta kawai yake yi cike da mamakin daya bayyana a fuskansa. A zahirinsa normal yake, kamar babu abin da ke faruwa, amma a cikin ransa ya ke fadin,
"How? Ta yaya ta zama ita ce mai company ɗin? Ta yaya hakan ya faru? Kenan ba..."
Tsawar da ta daka musu ce ta katse masa tunanin. Ya ɗago kai yana kallonta.
“Na ce na kore ku. Ku tattara ku bar mini company ɗina yanzun nan. I mean, now!”
Ta ƙarasa maganar tana dukan teburin da ke gabanta da ƙarfi.
Da sauri wani tsoho ya zube a gwiwowinsa a gabanta, kamar mai shirin yi mata sujada. Cikin kuka sosai ya ce,
“Don Allah Hajiya, ki yi haƙuri. Mun tuba, mun bi Allah, mun bi ki. Wallahi tallahi, da wannan aiki kaɗai na dogara. Ina da mata uku da ƴaƴa goma. Cinsu, maganinsu da duk wani abin rayuwa da wannan aikin na dogara. Idan na rasa wannan aikin, ban san yadda rayuwar yarana za ta kasance ba. Don Allah, saboda darajar Annabi, ki yi haƙuri.”
Ya ƙarasa maganar tare da sake fashewa da kuka kamar ƙaramin yaro.
Ran Aziz, idan dubu ne, gaba ɗaya sai da suka ɓaci a nan inda yake tsaye. Idanuwansa suka sake yin ja, jijiyoyin kansa suka fito sosai. Ya ɗago yana kallonta. Ganin yadda take zaune kamar ba da ita tsohon yake magana ba, da yadda manyan mutane, tsofaffin da suka fi ta shekaru, suke kuka suna ba ta haƙuri amma ta yi shiru, sai hakan ya sake hasala shi matuƙa.
Ya dunƙule hannunsa kamar wanda ke shirin kai naushi.
A zafafe ya ƙarasa wajen da tsohon ke tsugunne kamar almajiri. Ya sa hannunsa ya ɗago mutumin, wanda har yanzu kuka yake yi yana ba ta haƙuri.
Mutumin ya kalli Aziz, sannan ya haɗe hannayensa biyu ya ce,
“Don Allah yaro, ka ba ta haƙuri. Laifin da ka aikata mata ne yasa ta koremu.
Da ƙarfi Aziz ya cije lips ɗinsa, kamar zai huda su. Ya lumshe ido, sannan ya buɗe su a hankali ya sauke su a kanta.
Sai suka haɗa ido. Wani mugun kallo ya yi mata, sannan ya ja hannun tsohon da nufin su bar Hall ɗin.
Ba su fi taku biyu ba, suka ji ta ce,
“And you! Ka tattara ka bar mini company ɗina yanzun nan. Na kore ka!”
Cak ya tsaya, sannan ya juya ya watsa mata kallon tsana. Daga nan ya sa kai zai fita.
Wani mutum da ke tsaye kusa da inda take, wanda kayansa suka bambanta da na sauran ma'aikatan, ya ce,
“Shi ba ma'aikaci ba ne. Dama kawai ya zo ne ya raba mu da aikinmu saboda shi an ƙi a ɗauke shi.”
Ya ƙarasa maganar cikin tsananin jin haushin Abdool a ransa.
“What? Baya aiki a nan?”
Ta faɗa da tsananin mamaki a fuskarta. Sai ta miƙe da sauri har gilashin da ke hannunta ya faɗi. Ta ce,
“No... no... hakan ba zai yiwu ba.”
@all