BA SO BANE?

Chapter 6

by @hafsatwaziri1122




BA SO BANE.

Story📃 writing
by

Hafsat waziri

Young talent writer's 

•Yota•


Page 6


Ta yi shiru. A ranta ta ce,

"Idan ba a nan yake aiki ba, hukuncin me na masa? Kenan ban wulakanta shi ba? ya ci banza kuma?"

Ita a ganinta, idan har ta kore shi daga aiki, shi ne ta yi masa wulakanci mafi muni, saboda ta san raba talaka da wajen samun abincinsa shi ne abin da ya fi zama masa tashin hankali a duniya.

Yanzu ya za ta yi kenan? Ina alwashinta fa? Alwashin da ta ci na cewa sai ta wulakanta shi, Hakan ba zai taɓa faruwa ba, sam.

Da sauri ta É—ago kanta tare da faÉ—in,

"Wait!"

da ƙarfi.

Jin abin da ta ce ya sa Hall É—in ya yi tsit. Masu kuka ma duk suka yi shiru. Tsayawa ya yi cak ba tare da ya juyo ba. Cikin É—aga murya ta ce,

"Na É—auke ka aiki daga yau."

Gaba ɗaya ma'aikatan Hall ɗin suka tsinci maganarta kamar a mafarki. Sai komai ya tsaya cak. Kowa ya tsaya da mamakinsa a ransa, saboda sun san ba abu ba ne mai yiwuwa. To idan ba ita ba, ai shi ya san ƙudurinta a kansa. Saboda shi ne wanda bai san ciwon kansa ba, sai kawai ya karɓa? Ai hakan ma ba zai taɓa faruwa ba.

Oga Fahad, da tun ɗazu ya shigo ya zauna yana kallo, sai yanzu ya taso ya zo inda take tsaye. Cikin magana ƙasa-ƙasa ya ce,

"Why are you doing this, Mammy? Is he the one you're going to hire? Ki tuna, he is the person who caused you that injury."

Ya nuna ciwon da ke hannunta.

Ta É—ago kai tana kallonsa. At that moment, tears filled her eyes. Looking at him, ta ce,

"All I want is to get revenge for what he did to me. I want to humiliate him even more than he humiliated me in front of everyone."

Shiru ya yi, ya juya ya koma mazauninsa tare da haɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya. Ya zuba musu ido kawai, saboda ya san halin kafiyarta. Duk abin da za a yi, sai dai a yi, domin ba za ta taɓa fasa abin da ta ƙudura ba.

Still yana nan tsaye a wajen, bai juyo ba. Ta sake maimaita abin da ta faÉ—a da farko. Sai a sannan ya juyo ya mata kallo.

"Amma dai baki da hankali ko?"

Sai ya ɗan taɓe bakinsa kamar mai shirin haɗiyar yawu. Ya kawar da idanunsa daga kanta, ya juya yana bin ma'aikatan da ke cikin Hall ɗin da kallo.

Idanunsa suka sauka a kan Habu, da ke tsaye kusa da Adamu. Duk ƙauɗin Habu da rashin nuna abin da ya dame shi, sai ya ga ya yi sanyi yau. Ya daɗe yana kallonsu kafin ya dawo da kallonsa kanta.

Ya sake hannun tsohon mai share-share, ya mayar da hannunsa cikin aljihunsa.

A hankali ya fara takowa zuwa inda take tsaye cike da ƙasaita da izza, kamar ba talaka mai neman abin da zai ci ba.

A hankali, kamar baya son taka ƙasa, sai da ya zo gabanta kafin ya tsaya tare da sake tura hannayensa duka biyu cikin aljihunsa.

Yana kallon kyakkyawar fuskarta da yanayinta irin na mutanen da ba sa son hayaniya.

Shi ma cikin izzar da ta fi tata, ya yatsina fuska kamar mai kallon kashi ya ce,

"Me ya sa kike so ki É—auke ni aiki, bayan kuma yanzu kike kore ni?"

Harararsa ta yi sama da ƙasa, ta yatsina fuska kafin ta ce,

"Yes! So nake na É—auke ka, kuma daga baya na kore ka, just like a dog!"

Shiru ya yi. Ya zugi iska cikin kirjinsa, sannan ya fesar a hankali. Bai ce komai ba. Ya juya yana sake bin ma'aikatan da ke cikin Hall É—in da kallo. Sai ya sake juyowa yana kallonta from head to toe, kafin nan ya ce...



''Ok na amince but kafin nan, ina da sharaci.''

Ya karasa maganar yana kawar da idanunsa daga kanta.



"What?" ta faÉ—a da wani mugun sauri, kamar wacce ta ji ana yanke shawarar kashe ta.

Ya juya ya kallonta na wasu 'yan daƙiƙu. Kafin ya shafe gashin gemunsa, ba tare da wata alamar tsoro ko shakka ba, ya sake maimaita mata abin da ya faɗa.

Cikin tsananin ɓacin rai ta ce,

"Kai har ka isa? Who are you? Waye kai da har kake tunanin ka isa ka ba ni sharaÉ—i? Who do you think you are?

Ko ka manta cewa ni ce ke da iko a kan gaba É—aya talakawan da ke wajen nan? Ciki kuwa har da kai. Sannan ko magana babu mai damar yi idan har ba ni na ce a yi ba.

Ka kama kanka ka sauke duk wani girman kai da talauci ya É—ora maka. Ka san inda kake, kuma ka san a gaban wa kake. I am the owner of this company."

Ta yi maganar tare da nuna kanta da yatsa.

"And look at the size of this company, sannan ka faÉ—a mini, how can a poor person like you ya isa ya ba ni conditions? Are you even in a position to do that?"

Ta ƙarasa maganar cike da isa da kuma izza.

Shiru ya sake mamaye wajen, kamar babu wani abu mai rai a cikin hall É—in. Duk mutanen da ke wajen, shi suke kallo.

Sai dai shi, ko a jikinsa ba za ka iya gane wani hali yake ciki ba. Fuskarsa babu alamar damuwa. Yana kallonta har ta gama maganarta.

Daga nan ya juya zai fita daga hall É—in.

Sai ya ji muryar Yallabai Fahad yana cewa,

"Wait!"

Amma ya ƙi tsayawa. Ya ci gaba da tafiyarsa, kamar ba da shi ake magana ba.

Ganin ya kusa fita daga hall É—in ne, yasa ta yi saurin cewa,

"Okay... mene ne sharaÉ—in?"

Ya yi kamar bai ji ta ba, har ya kusa bakin ƙofa kafin ya tsaya. Ba tare da ya juyo ba, ya ce,

"Idan har ana son na yi aiki a wannan company, to lallai ne, kuma dole sai tare da ma'aikatan da aka kora. I mean, a dawo da su."

Yallabai Fahad ya yi suman tsaye saboda yadda ya ji Aziz na zuba sharaÉ—i kamar shi ne mai company.

Adam, wanda ke kallonsa cike da mamakin ƙarfin hali da tsabar taurin idon Aziz, ya girgiza kai kawai a ransa, yana addu'ar Allah Ya sa dai su yarda, saboda su kansu ba su san inda za su sa ransu ba idan suka rasa wannan wajen.

Har yanzu Aziz bai juyo ba. Alamar amsarsu kawai yake jira.

Jikin Habu kuwa duk ya yi sanyi, kamar ba shi da lafiya. Da ƙyar ya iya takowa zuwa wajen da Aziz ke tsaye. Cike da tsoro ya ce,

"Aziz, me kake yi haka ne? Mutane ne da companynsu. Ka yi shiru, kar ka yi magana. Ka ga kamata ya yi mu bi su a hankali, mu ba su haƙuri, har Allah Ya sa su haƙura. Don Allah, kar ka sake cewa komai, ka ji?"

Ya ƙarasa maganar, damuwa na sake bayyana sosai a fuskarsa.


Kallonsa Aziz ya yi, ya gyaÉ—a masa kai alamar "to", kamar da gaske.

Ita kuwa, cike da isa da gatsali, ta ce,

"Yes, na yarda zan mayar da su. But ni ma ina da sharaɗi, kuma dole ne ka bi shi ba tare da wata ƙorafi ba."

Sai a sannan ya juyo yana kallonta, tare da takawa kusa da ita. Yana bin kyakkyawar fuskarta da ido, ya É—aga kafaÉ—arsa alamar I don't care, ya ce,

"Okay."

Wani harara ta watsa masa, kafin ta ce,

"Amincewar da ka yi cewa za ka yi aiki a ƙarƙashina shi ne kuskure mafi muni da za ka taɓa yi a rayuwarka."

Tana kaiwa nan, ta ɗan yi shiru tana kallonsa daga sama har ƙasa. Sannan, cike da kasaita ta ce,


"Hope ka iya driving? Anyway, idan ba ka iya ba, zan sa a koya maka. Allah Ya sa dai kwakwalwarka tana functioning, ba sai an yi ta nanata abu É—aya ba."

Tun da take magana bai É—auke idanunsa a kanta ba. Ya yi shiru yana kallon yadda lips É—inta ke ta motsawa.

Murmushi ta sake, sannan ta ci gaba da cewa,

"Sai aiki na biyu. Za ka zama bodyguard ɗina. Wanda ko kallon banza mutum ya yi mini, za ka ɗauki mataki. Da fatan kana riƙe abin da nake faɗa maka?"

"Sai aikinka na uku. Za ka zama mataimakin shugaba, wato ni. A kowane lokaci kuma za ka kasance tare da ni. Za ka riƙa mini jaka, ka buɗe mini ƙofa, ka share mini takalmi. Da fatan kana fahimtata?"

Ta sake hurga masa tambayar, wanda ya sa ya É—aga kai da sauri, kamar wanda bai san a kan me take magana ba.

Gaba É—aya hall É—in ya yi tsit, kamar babu mai rai a ciki. Shi ma shiru ya yi yana kallonta.

Ganin gaba É—aya attention É—insa yana kanta ne, ya sa ta sakar masa murmushi, don nuna masa cewa abin da take son isarwa ya fara isa. A wulakance ta ce,

"Okay, na san me kake tunani. Don't worry about salary. Zan biya ka yadda zai ishe ka ka shawo kan wannan tarin matsalolin naka. I hope dai kana da account number?"

Yana tsaye yana kallonta har ta gama. Ganin alamar ba za ta sake cewa komai ba ne ya sa ya fara takawa ta gabanta zai wuce.

Da sauri ta sa masa ƙafarta da niyyar ya faɗi. Kamar ya san hakan zai faru, saboda yana ankare da ita, ya yi saurin tsallake ƙafarta, tare da buge tata ƙafar a lokaci guda.

Tsinin takalminta da santsin tiles ɗin wajen suka ja ta. Ta zame luuu... za ta faɗi. Har ta kusa kaiwa ƙasa sai ya yi saurin riƙo hannunta, ba tare da ta kai ƙasa ba.

Sake riƙe hannunsa ta yi gam-gam, tare da damƙe idanunta, domin ta gama believing a ranta cewa ta faɗi ƙasa.

Wani É—an iskar murmushi ya yi mata, tare da lasar lips É—insa. Ya É—aga mata gira É—aya.

Zazzaro idanu ta shiga yi. Tsoro da firgici suka bayyana ƙarara a kan fuskarta, saboda ta san tabbas sake ta zai yi.

A take idanunta suka cika da hawaye. Nan take ya nemi ganin wannan izza da isa, amma ya rasa su a tattare da ita.

A yanzu babu abin da yake gani face wata ƙaramar yarinya da ke neman taimako.

Oga Fahad ne ya miƙe a zafafe. Cikin murya mai ƙarfi ya ce,

"Kai! Kai! Kada ka kuskura... Don't! Kada ka kuskura ka sake ta! Ka jawo ta yanzu nan! Ka jawo ta, na ce!"

Ya ƙarasa maganar cikin wata irin tsawa.

Har yanzu Aziz na riƙe da hannunta. Ya juya yana kallon Oga Fahad ba tare da ya ce komai ba.

Daga bisani ya É—auke kansa, ya mayar da kallonsa kanta.

Cikin tsananin tsoro, Adamu ya ce,

"Aziz... Aziz... Don Allah, Aziz, kada ka sake ta. Please, ka jawo ta. Don Allah!"

Ya ƙarasa maganar cikin muryar roƙo mai rauni.