BA SO BANE?

Chapter 7

by @hafsatwaziri1122

BA SO BANE.

Story📃 writing
by

Hafsat waziri

Young talent writer's 

•Yota•


Page of 7



Ya yi ƙaramin murmushi, kafin ya jawo ta jikinsa a hankali. Da sauri ta riƙesa tare da runtse idanunta tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi.

Ya ɗan sunkuyar da kansa, ya kai bakinsa kusa da kunnenta, cikin sassanyar murya ya raɗa mata,

“Ta yaya zan bar wacce nake karewa ta faɗi?”

Ta dago da sauri ta kallesa, kalaman nasa suka ƙara tunzura ta. Cikin jin haushi ta sa dukkan ƙarfinta ta tura shi baya. Da ƙyar ya ɗan ja da baya kaɗan, 

Ta harare shi da idanunta dake cike da tsoro har yanzu. Shi kuma sai ya haɗe fuska, tamkar ba shi ne ya faɗi maganar ba. Idanunsa ma suka koma cike da natsuwa, abin da ya ƙara bata mata rai.

Gaba ɗaya ma'aikatan da ke wurin suka sauke ajiyar zuciya. Wasu suka yi murmushi a ɓoye, wasu kuma suka yi hamdala. Sun yi zaton yau fa za a ga tashin hankali tsakaninsu.

Oga Fahad ya gyara tsayuwarsa, ya kalli ma'aikatan sannan ya ce,

''duk ku watsa.''

Huba ne ya fara fita. Da ya isa ƙofar fita sai ya tsaya yana jiran su Jim kaɗan sai ga Adam shi ma ya fito. 

Ba da daɗewa ba wurin ya fara yin shiru. Kusan duk ma'aikatan sun watse, 

Oga Fahad ya ɗaga kai ya kalle ta. Ganin har yanzu tana tsaye ba tare da alamar tafiya ba, ya yi murmushi ya ce,

“Last go, Mommy?”

Ya faɗa yana ɗaukar laptop ɗinsa daga kan tebur.

A hankali ta ɗaga idanunta ta kalli Aziz da ke tsaye bakin ƙofar fita. 

Wani shegen murmushi ya bayyana a fuskarta. Ta kalli oga Fahad cikin shagwaɓa, sannan ta ce,

“No... zan zo da sabon driver.”

Oga Fahad ya ajiye abin da ke hannunsa.

“No, Mommy. Kinsan fa, tun da kika sauko ƙasar nan ba gida kika fara zuwa ba, nan kika fara zuwa. Daddy yana ta kirana tun ɗazu. Har Brother ma ya kira. Duk hankalinsu ya tashi. Ki bari yau gobe sai ya je har gida ya ɗauko ki. Ko?”

Ya faɗi hakan cikin kulawa da lallashin ta kamar karamar yarinya. Sai da tayi narai narai da idanunta ka

Ta juya ta nufi wajen da Aziz ke tsaye shi da su Adam cikin takun nan nata na isa. Da ta iso gabansa sai ta tsaya, ta dago , tana kallonsa kai tsaye cikin idanu. Muryarta cike da umarni da nuna iko ta ce


“Be prepared tomorrow. You start work at 4:00 a.m. sharp... and don't you dare be even a minute late.

Tana gama maganarta ta taka masa ƙaramin ɗan yatsa da duk ƙarfinta. Sannan ta wucesa fuuuu tana tafiya kamar sarauniya

“Ashh...”

Ya furta a hankali, yana ɗaga ƙafarsa da sauri. Ya cije leɓensa yana Binta da kallo 

 
Can ƙasan zuciyarsa kuwa wani murmushi ya kwanta.

“Lallai...” ya faɗa a ransa.

“Kin zaɓi mutumin da za ki yi wasa da shi. Ki ci gaba da wannan isar. Ranar da zan karya wannan girman kan naki, ke da kanki za ki nemi sassauci.”


Jibirin driver ya yi musu sannu da zuwa cikin ladabi. Ya karɓi jakar hannun Oga Fahad, ya buɗe musu ƙofar motar, sannan ya ajiye jakar a gaba.

Bayan sun shiga, ya zagaya ya zauna a kujerar direba, ya kunna motar cikin natsuwa, sannan ya ja ta a hankali suka fice daga harabar company ɗin.

Dukkan su suka bi motar da kallo har ta ɓace wa ganinsa.

Sannan ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, ya shafa yatsarsa da har yanzu yake ma












Safiyya Sa'ad Umar Lekki, wadda kusan kowa ya fi sani da suna Mammy, kyakkyawar budurwa ce mai shekaru ashirin da biyu. Ita ce kaɗai ƴa mace a gidansu. An sanya mata laƙabin Mammy ne saboda sunan kakarta da ta ci. Mahaifinta ya saba kiranta da wannan suna tun tana ƙarama, har ya zama sunan da kowa ke santa da shi.

Mahaifinta, Alhaji Sa'ad Umar Lekki, fitaccen ɗan kasuwa ne mai tarin dukiya. Babu wani fanni na kasuwanci da bai shiga ba, domin yana da manyan kamfanoni masu zaman kansu, baya ga kasancewarsa har da harkar siyasa yana yi.

A ranar da Safiyya ta cika shekaru ashirin da biyu, mahaifinta ya mallaka mata wani katafaren kamfanin sarrafa kifi a matsayin kyautar zagayowar ranar haihuwarta, duk da cewa a lokacin ba a Najeriya take zaune ba.

Safiyya ƴar gata ce ta gaske, shalele kuma ƴar shagwaɓa, bata taɓa neman abu ta rasa ba tun da take. Gata da kulawar da take samu daga mahaifinta da ƴan'uwanta sun sa ta taso cikin rayuwar jin daɗi da wadatuwa. Duk da irin tarbiyyar addini da ilimin boko da ta samu, tana da wani irin girman kai. Ba ta son talauci, kuma ba ta son talakawa ko kaɗan. A ganinta, kuɗi da matsayi su ne ke ƙayyade darajar mutum. Saboda haka ba kasafai take bai wa talakawa wata kima ba. Hulɗarta da su ta tsaya ne kawai a matsayin ma'aikata ko masu yi mata hidima.

Sai dai, duk da taurin kanta da son mulki da nuna isa da take yi, zuciyarta tana da sauƙin sarrafuwa. Duk wanda ya fahimci raunin zuciyarta, kuma ya san hanyar da zai bi wajen lallashinta, zai iya rinjayar tunaninta cikin sauƙi. Ko da yake a zahiri tana nuna kamar babu wanda ya isa ya sauya ra'ayinta.

Allah Ya azurta Safiyya da ilimin boko mai inganci, tare da ilimin addini da kyakkyawar tarbiyya. Tana da natsuwa, ba ta cika son hayaniya ko yawan surutu ba. Sai dai yawan gata da aka yi mata tun tana ƙarama ne ya jawo ta kasance mai wasu ɗabi'u na nuna isa da raina wasu.

Safiyya ba ta da wata alaƙa da maza, domin sam ba ta yarda da soyayya ba. A ganinta, yawancin soyayya yaudara ce da ɓata lokaci. Ko mutum yana da kuɗi, matsayi ko kyakkyawar fuska,






🥹



Mammy


Safiyya Sa'ad Umar Lekki, wadda kusan kowa ya fi sani da suna Mammy, kyakkyawar budurwa ce ƴar shekaru ashirin da biyu a duniya. Ita ce kaɗai mace a gidansu. An sanya mata laƙabin Mammy ne saboda sunan kakarta da ta ci. Wannan dalilin ya sa mahaifinta ke kiranta da Mammy. Tun tana ƙarama, sunan ya zauna.

Mahaifinta, Alhaji Sa'ad Umar Lekki, fitaccen ɗan kasuwa ne wanda babu wani kasuwancin da ba ya yi. Yana da wasu manyan kamfanoni masu zaman kansu, kuma yana taɓa harkar siyasa. A ranar da Safiyya ta cika shekaru ashirin da biyu ne mahaifinta ya mallaka mata kamfanin sarrafa kifi, duk da cewa ba a ƙasar take rayuwarta ba.

Safiyya ƴar gata ce ta gaske, wanda gatan ta yasa bata taɓa neman abu ta rasa ba, shalele kuma ƴar shagwaɓa. tana da wani irin girman kai. Ba ta son talauci, kuma ba ta son talaka ko kaɗan. A ganinta, kuɗi da matsayi su ne ke ƙayyade darajar mutum. Saboda haka, ba kasafai take bai wa talakawa wata kima ba. Ba ta hulɗa da su ko kaɗan. Iyakar hulɗarta da su ita ce su yi mata aiki.

Sai dai, duk da taurin kanta da son mulki da take nunawa, zuciyarta tana da sauƙin sarrafuwa. Duk wanda ya fahimci raunin zuciyarta da hanyar da zai bi wajen lallashinta, yana iya rinjayar tunaninta cikin sauƙi, ko da kuwa a zahiri tana nuna kamar babu wanda ya isa ya juya ra'ayinta. Ta samu ingantaccen ilimin boko, da ta addini. Tana da natsuwa. Ba ta cika son hayaniya ba. Kawai dai gatan da ya yi mata yawa ne ya sa take wasu abubuwa.

Safiyya ba ta da wata alaƙa da maza, domin sam ba ta yarda da soyayya ba. A ganinta, yawancin soyayya yaudara ce da ɓata lokaci. Ko da mutum yana da kuɗi, matsayi ko kyakkyawar fuska, bai isa ya sa ta sauya ra'ayinta ba. Ta kuduri aniyar cewa ba za ta bari soyayya ta rinjayi rayuwarta ba, duk da cewa zuciyarta tana da sauƙin sarrafuwa idan mutum ya san hanyar da zai bi wajen shigarta.

(Wannan ita ce Safiyya Sa'ad Umar Lekki, a taƙaice.)





Har suka isa dankareren gidansu Fahad na lallab'ata saboda sai ɓata rai takeyi wai saboda mesa wannan driver din zai dauko ta. Suna Shiga daga cikin tashiga bin gidan da kallo 


Jibril ya yi parking cikin nutsuwa, sannan ya fito da sauri ya zagaya ya buɗe mata ƙofa cikin girmamawa. Ta fito tana ɗan turo baki, sannan ta juya ta kalli Fahad da wani salon shagwaɓa irin na wanda gata yama yawa.

"Don't tell Daddy anything"

Fahad ya ɗan kalleta kamar mai tunani sai kuma ya ce,

"Okay."

Daga nan suka nufi cikin katafaren falon gidan.

Idanunta suka sauka kan mahaifinta. Kafin ma ta yi magana, mutumin ya miƙe tsaye cikin matsanancin farin ciki, fuskarsa ta washe da murmushin da ya bayyana irin ƙaunar da yake yi wa ƴarsa.

"Mammyna"


 da gudu kamar ƙaramar yarinya. Ta zo ta faɗa jikinsa ta rungume shi gam, ta ce

"I miss you, Daddy."

Ya rungume ta shima yana shafa bayanta cikin kulawa sosai ya ce''.

"I miss you too, Mammyna"

Ya ɗan janye ta kaɗan yana kallonta daga sama har ƙasa, tamkar wanda yake son tabbatar da cewa babu abin da ya same ta.

"But me ya sa kika zo ke kaɗai? Me ya sa ba ki sanar da mu kina zuwa ba? Ina Hamzan? Ya ya bari kika yi wannan doguwar tafiya ke kaɗai?"

Ta sake mannewa a ƙirjinsa tana shagwaɓe fuska.

"Daddy, ni na hana shi fa ya gaya maka. I wanted to surprise you."

Ya girgiza kai yana murmushi, amma damuwa bayyane ƙarara a idanunsa ya ce

"Ko da haka ne, Mammy, kin san yadda ƙasar nan ta lalace da rashin tsaro. Bai kamata ki yi irin wannan tafiyar ke kaɗai ba."

Kafin ta ba shi amsa, Hajiya Zainab kyakkyawar mace ta taso daga kujerar da take zaune. Duk wanda ya kalleta tare da mammy zai fahimci cewa babu shakka uwa da ƴa ce. Saboda yadda suke tsananin kama idanuwansu masu haske, siffar hanci, murmushi da ma yanayin tafiyarsu duk tamkar an tsaga kara. Sai dai shekaru ne kaɗai suka bambanta su.

Tana ganin Ammi, ta saki Daddy da sauri ta ruga zuwa gare ta.

"Ammina!"

Ta faɗa jikinta ta rungume ta gam, cikin farin ciki Ammi ta sumbaci goshinta da kumatunta cike da tsantsar so da ƙauna.

" Na yi kewarki sosai Ammina."



Ammi ta dagota tana kallon ta ta ce''

"Ya aka yi kika taso daga England ke kaɗai? 

Mammy ta ɗaga kai tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, sannan ta yi wata irin shagwaɓa kamar zata yi kuka ta ce'' 

I wanted to see you 

“Allah ya tsare mini ke, 



“Amin,” ta faɗa cikin murmushi.
sai ta tsaya ta rungume yayanta Umar, wanda ke tsaye a gefen Ammi. Umar ya sauke ajiyar zuciya, ya shafa kanta a hankali yana cewa,



“Kin ba mu tsoro sosai, Mammy.”

Ta ɗaga kai tana murmushi kaɗan, amma ba ta ce komai ba.

Daddy ya dubeta da idanu cike da kulawa, sannan ya ce,

“Ki je ki watsa ruwa.”

Ta gyada kai cikin shugaba ta ce.

“To Daddy.”

 Ta matsa kusa da shi, ta ɗan rungume shi sannan ta sumbaci bayan hannunsa. Daga nan ta juya ta nufi matattakalar da za ta kai ta ɗakinta na sama. Kowa da ke falon ya bita da kallo har sai da ta ɓace daga ganinsu.



Fahad kuwa ya ƙarasa ya zauna a luntsumemiyar kujerar falon. Yana cire agogon hannunsa a hankali, ya lura yadda daga Daddy har Ammi da Umar duk suke zaune cikin damuwa. Sai ya ɗan yi murmushi yana ƙoƙarin kwantar musu da hankali.

“Daddy, ga ta nan fa, lafiya ƙalau. Babu abin da ya same ta.”

Kafin Daddy ya ce wani abu, Umar ya katseshi cikin fushi.

“Me ya sa ba ka kira ka sanar da mu tana Company ba? Ka san yadda hankalinmu gaba ɗaya ya tashi? Mun yi ta kiran wayarka amma ba ka ɗauka ba.”

Daddy ya jinjina kai, alamar shi ma wannan tambayar yake son ji.

Fahad ya ɗan gyara zamansa kafin ya ce,

“Daddy, ni ma haka nan na ganta a Company. Ban ma san ita kaɗai ta zo ba. Kuma ban samu damar yin magana da ita sosai ba saboda abin da ya faru ɗazu a Company...”

Nan take ya yi shiru, yana ƙoƙarin haɗiye sauran maganar. Don ya kau da zancen, sai ya ɗaga murya ya kira mai aikinsu.

“Ladi...”

Ammi, wadda tun farko take zaune cikin natsuwa ba tare da ta ce uffan ba, ta ɗaga idanunta ta kalli Fahad sosai, sannan ta ce,

“Fahad... menene ya faru a can ɗin?” 


Sai duk suka juyo suna kallon sa...