BA SO BANE?

Chapter 8

by @hafsatwaziri1122





BA SO BANE.

Story 

Hafsat Waziri 


Young talent writer's 

•Yota•


Page 8


I Dedicate this book to
 Nanakhadii 💅📕_



Bayan ya rabu da su Adamu, masallaci ya nufa. Anan ya yi dukka sallolin sa. Bayan an idar
kai tsaye gidan Inna ya nufa.

Gidan ƙarami ne sosai mai ɗauke da ɗakuna biyu kacal. Rabin katangar gidan ta riga ta rushe, aka yi dabara aka tare sa da langa-langa. Babu kowa a ƙaramin tsakar gidan, sai hasken farin wata daya haske ko'ina.


Duk mutanen gidan suna cikin ɗaki. 
Saboda yawan sauro, 
A hankali Abdool yake tafiya har ya isa ƙofar ɗakin, inda hayaƙin maganin sauro ke tashi. Bai shiga ba, ya tsaya ya yi sallama cikin sanyin murya.

Wani kyakkyawan dattijo ne mai cike da nutsuwa da kamala yana zaune a kan yar ƙaramar kujera, rediyo a gefensa yana sauraro. Daga gashin kansa har gemunsa fari fat.

Da jin sallamar, ya ɗan leƙo ƙofar. Ganin Abdool-Aziz ne a tsaye nan take fuskarsa ta washe da murmushi, idanuwansa suka cika da farin ciki sosai.

Duk da ya kasance ba shi ne mahaifin Aziz ba, zuciyarsa ta ɗauke shi tamkar ɗansa na jininsa, kamar yadda shima Aziz din ya dauke su. 


Cikin murya mai nuna tsufa ya ce,

"Abdool-Aziz ne? Shigo mana, ɗana."

Ya faɗi hakan cike da zumudi da murna, farin cikin ganinsa na bayyana ƙarara a fuskarsa.

A hankali Abdool-Aziz, wanda ke tsaye a bakin ƙofar, ya zame takalmin ƙafafunsa sannan ya shiga ɗakin. Ya ƙarasa cikin ladabi da girmamawa, ya tsugunna a gaban dattijon yana gaida shi.

Inna kuwa tana kwance kan tabarma. Da jin muryarsa, sai ta tashi zaune tana gyara kallabin kanta da ya ɗan zame.

"Barka da dare, Inna."

Ya faɗa cikin sanyin muryarsa, wadda ta saba da rashin son hayaniya.




Fuskar innah ɗauke da fara'a ta amsa shi tare da sakar masa murmushi. 

Kallon Abdool tayi ta wurga masa tambayar.



"Abdool, yau kai ne a gidan namu?"



sunkuyar da kansa ya yi cikin ladabi, ya ce,

“Eh, Inna. Na same ku lafiya.”


“Ina lafiya ƙalau, Abdool. Kwana biyu ba ka leƙo mu ba, sai aike kawai muke gani. Allah Ya sa lafiya.”



Har lokacin kansa na ƙasa, bai ɗago ba, ya ce,

“Lafiya, Inna.”

“Ina yini, Hamma?”

A hankali ya juya ya kalli yaron da, a ƙiyasin shekaru, zai kai tsakanin sha takwas zuwa sha tara. Yana zaune a ƙasa, ya yin da littattafai ke zube a gabansa da yar filita 
 yana rubutu.

Abdool ya tsura masa idanunsa masu kaifi na wasu daƙiƙu, kamar ba zai amsa ba. Sai kuma ya ce,

“Lafiya lau. Ya makaranta?”


kallonsa ya yi cikin girmamawa ya ce.

“Alhamdulillah, Hamma.”

“Ba wata damuwa ko?”

A hankali yaron ya ɗago ya kalle sa, sannan ya jinjina kai alamar akwai wata buƙata. Sai dai ya san hamman nasa ba wani aikin yi ne da shi ba.

Jiki a sanyaye ya ce,

“Eh, Hamma. Practical books ne guda shida, sai manuals shima guda shida.”

Ya ɗan lumshe idanunsa ƙadan tare da da fadin 

“Ka lissafa duk abin da kake buƙata. Gobe kafin ka tafi makaranta, ka zo ka karɓa.”

Ya ƙarasa maganar tare da ɗauke kansa daga kallon yaron.

Daga nan ya yi musu sallama, ya juya ya fice.





Mammy


****

Fahad ya ɗan haɗiye yawu a hankali. Ganin yadda kowa ya zuba masa ido ne ya sa ya yanke shawarar ya faɗa musu gaskiyar abin da ya faru. Sai dai kuma nan take ya tuna da maganar da Mammy ta yi masa cewa kada ya faɗa musu. Shi kansa ya san cewa rashin faɗan ne ya fi zama alheri.

A hankali ya maida dubansa kan Daddy, wanda ya zuba masa idanu ta cikin farin gilashinsa, yana jiran abin da zai ce.

Ya lumshe idanunsa na ɗan wani lokaci, sannan ya ce,

"Dama d..."

Sai dai bai ƙarasa ba.

Ƙarar wayarsa da ta mamaye falon gaba ɗaya ta katse maganarsa.

Da sauri ya zaro wayar daga aljihunsa, yana sauke numfashi a ɓoye tare da gode wa Allah da Ya kawo masa mafita.

Ya ɗaga kai ya kalli Daddy, sannan ya ce,

"Excuse me, Daddy."

Ba tare da ya jira amsa ba, ya amsa kiran yana ficewa daga falon.

---

Sai da ta ɗauki kusan mintuna ashirin kafin Mammy ta fito daga ɗakinta. Tana sanye da doguwar rigar barci mai launin pink, wadda ta ƙara fito da kyawunta. Dogon gashinta ya zubo a bayanta har kan kafaɗunta, yayin da ƙamshin turaren da ta fesa ya mamaye falon.

A daidai lokacin ne kuma Aunty Aisha, matar Umar, ta shigo tare da ƴaƴanta biyu namiji da mace.


 yaran na hango Mammy, suka kwasa da gudu zuwa gare ta cike da farin ciki.

"Aunty Mammy!... Oyoyo Aunty Mammy!"

Mammy ta saki wani lallausan murmushi da ya ƙara haskaka kyakkyawar fuskarta. Ta ɗan durƙusa tana buɗe hannayenta.

"Come here, my babies."

Nan take suka faɗa jikinta suka rungume ta. Ta sumbaci goshin yarinyar, sannan ta shafa kan yaron tana murmushi.

Cike da murnar ganinta, yaron ya daga kai cikin maganarsa ta yara ya ce,

"We missed you, Aunty Mammy."

"I missed you too."

Ta fada da murmushi mai kyau a fuskanta.


Aunty Aisha ta ƙaraso kusa da ita tana murmushi.

Ta ce,

"Welcome mammy ."

Mammy ta yi mata murmushi kawai, sannan ta ja hannun yaran suka nufi cikin falon.

A daidai wannan lokacin kuwa, masu aikin gidan suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya, suna shimfiɗa nau'o'in abinci a kan babban dining table. Cikin ƴan mintuna kaɗan, teburin ya cika da abinci iri-iri. Kallon teburin kaɗai ya isa ya tabbatar da cewa an shirya liyafa ta musamman domin dawowarta.

Cike da farin ciki, Mammy ta juya tana kallon Daddy.

"Daddy... duk wannan na welcome ɗina ne?"

Daddy ya yi murmushi cike da ƙauna.

"Yes, Princess. An shirya wa sarauniyar England wannan duka ne domin a yi mata kyakkyawar tarba."

Murmushin jin daɗi ta yi, sannan ta yi saurin zagayawa wajen Daddy da nufin rungume shi.

 Sai dai kafin ta isa garesa ta bugi hannunta mai raunin a jikin dining.

"Ashh...!"

Ta furta cikin tsananin jin zafi tare da janye hannunta da sauri tana yar fewa.

Nan take fuskar Daddy ta sauya. Cike da damuwa ya ƙaraso gare ta, ya kamo hannunta cikin tausayi yana dubawa.

"Subhanallah! Me ya faru da hannun?"

Umar da Ammi ma suka matso da sauri.

Umar ya ce,

"Let me see your hand."

Hankalin kowa ya tashi matuƙa ganin yadda hannun ya yi ja ya kuma ɗan kumbura.

Daddy ya ɗaga kansa ya kalli Fahad. Idanunsa cike suke da damuwa kamar yaga hannun na shirin fita daga jikinta ne.


Ganin yadda hankalin su gaba daya ya tashi ne yasa ta, yin murmushi ta shagwaɓe fuska, ta ɗan karya kai ta ce,

"Daddy, na bige ne fa da ƙofa dazu a company. Kuma Yaya ya kira doctor, ya duba ni, ya ba ni magani. Ko ba haka ba?"

Ta ƙarasa maganar tana kallon Fahad da ke tsaye a bayansu.

Da sauri Fahad ya ƙaraso kusa da su kamar wanda ke jiran a basa damar magana dama ya ce''.

"Yes, Daddy. Doctor ya ce ba wani babban abu ba ne. In shā Allah zai warke nan ba da daɗewa ba."

Daddy bai ce komai ba. Ya ci gaba da kallon hannun nata, kamar dai har yanzu zuciyarsa ba ta gamsu da bayanin da aka ba shi ba....