Chapter 9
BA SO BANE.
Story📃 writing
by
Hafsat waziri
Young talent writer's
•Yota•
Page 9
I Dedicate this book to
Nanakhadii 💅📕_
Daddy da kansa ya ja mata kujera ta zauna. A hankali ta riƙa buɗe murfin kowane kwano ɗaya bayan ɗaya tana dubawa. Duk wanda ya yi mata, sai ta tsakura da cokali.
Cikin rashin sa'a, ta kai hannunta kan wani kwano wanda kusan shi ne na ƙarshe. Ta buɗe shi, da sauri ta tura kwanon baya tana toshe hancinta da hannayenta biyu. Ta fara kakarin amai.
Fahad, da ke zaune kusa da ita, ya ga abin da ya faru. Ya leka cikin kular, ganin ferfesun kifi ne a ciki ya sa ya rufe murfin da sauri tare da matsar da ita daga gabanta.
A hanzarce Daddy ya leƙa kular shima dan ganin abin da ya ke ciki. Nan da nan yanayin fuskarsa ta sanja. cikin ɗaga murya ya shiga kiran masu aikin gidan ba ƙaƙƙautawa.
Masu aikin, su uku suka fito da sauri daga kicin suna amsawa. Cikin rawar murya suka ƙaraso, duk da sun san ɗaya murya ba halin Alhaji ba ne. Idan aka ga yana ɗaga murya haka, to kowa ya san an taɓo masa yar Gold ne.
Da suka iso, ya nuna kwanon da yatsa cikin fushi.
"Da izinin waye a ka dafa kifi?"
Jikin mai aikin ya kama rawa. Ta sunkuyar da kanta ƙasa cike da tsoron kada itama a kore ta don tun ɗazu Larai ke bata labarin akan mammy an sha korar masu aiki da dama a lokacin da take ƙasar. Sai dai Larai din bata fada mata cewa batason kifi ba.
Cikin rawar murya ta ce,
"A yi haƙuri, Alhaji. Na ga yaran suna son sa sosai, shi ya sa na..."
Daddy ya katseta ta hanyar daga mata hannu.
"Ɗaga shi daga nan! Kada wani ya sake girka kifi a gidan nan daga yau. Duk wanda yake buƙatar ci, ya fita waje ya ci."
Cikin tsoro, mai aikin ta kwashe kular, hannunta na rawa.
Daddy ya maida dubansa gare ta yana shafa bayanta a hankali.
"It's okay, sweetheart?."
Ta gyada masa kai alamar eh, sannan ta É—auki cokali suka ci gaba da cin abinci.
shiru wajen ya yi na wasu ƴan dakiku, kowa ya maida hankalinsa kan abin da yake ci. Ba ka jin sautin komai sai ƙarar cokula da faranti.
Mammy ta katse shirun da cewa,
"Daddy, I want to start going to the company tomorrow."
"What?"
Daddy ya faÉ—a cikin É—an sarkewar murya. Amma kafin ya sake magana, Ammi ta riga shi da cewa,
"Mammy, what are you going to do at the company?"
"Work."
Ta faÉ—a tana kai haÉ—aÉ—É—iyar fried rice bakinta.
Ga mamakinta, sai ta ga duk sun tsaya da cin abincin, suka yi shiru suna kallonta.
ɗago kai tayi, a shagwaɓe ta ce,
"Daddy, did I say something wrong?"
Kafin Daddy ya yi magana, Ammi ta sake riga shi.
"No, Mammy. You're not going anywhere."
"What? Why, Daddy?"
Ta yi maganar tana kallon Daddy, kamar shi ne ya hana ta.
Da ta ga shi ma ya yi shiru bai ce komai ba, hakan ya tabbatar mata Ammi ta faÉ—i gaskiya kenan ba za ta je ba.
Nan take abin da ya faru a Company ya fara dawo mata. Tabbas rashin komawarta Company dai-dai yake da saba alƙawarin da ta ɗaukarwa kanta.
Cikin tashin hankali ta juya ta kalli Fahad da ke zaune kusa da ita, kamar tana neman ya taimake ta.
Amma ganin ya kawar da kansa daga gare ta, nan take hawaye suka cika idanunta. Ta ajiye cokalin hannunta, ta kama hannun Daddy tana girgizawa.
Cikin rawar murya ta ce,
"Please, Daddy."
Shiru Daddy ya yi. Duk da har cikin ransa yana jin ba dadi akan yadda take ta roƙonsa. Sai dai ya san gaskiyar Ammi ne zamanta a gidan shi ne mafi alheri.
"Please, Daddy..."
Ta sake faÉ—a a karo na ba adadi, tana kallonsa da idanunta dake cike da hawayen shagwaba. Ta san idan Daddy ne, ba zata dauki lokaci tana rokonsan ba zai amince ko da baya so.
Daddy ya lumshe idanunsa tare da janye hannunsa dake cikin nata a hankali. Nan take duk wani abin da ke motsi a jikinta suka tsaya cak. Idan ba ganinta ne ya yaudare ta ba, Daddy ya zare hannunsa daga riƙon da ta yi masa. Abun da bai taba faruwa ba tsawon rayuwarta.
Da sauri ta miƙe da niyyar barin wajen tana kokarin danne kukanta.
Ganin haka yasa Daddy ya miƙa hannu ya riƙo nata, yana kallon yadda hawaye ke gangarowa a fuskarta kamar an buɗe famfo.
"Mammy, yi haƙuri ki zauna."
Ya faÉ—a yana kallonta.
Ba tare da musu ba ta zama, tana kuka ƙasa-ƙasa irin na shagwaɓaɓɓun yara. Ganin yadda take kuka ne ya tayar wa Daddy da hankali. Ya sauke nauyyen zuciyar zuciya.
"Cool down, my Mommy. Idan zuwa Company ne, ki sa a ranki cewa za ki je."
Jin abin da Daddy ya faÉ—a ya sa Ammi ta É—ago ta kalle shi. Za ta yi magana, sai ya É—aga mata hannu alamar kada ta ce komai.
Hakan ya sa ta miƙe a hankali ta bar musu dining ɗin cikin ɓacin rai.
Shi kuwa Daddy, ko a jikinsa. Ya É—an bi ta da kallo kadan, sannan ya juya ya ci gaba da lallashin Mammy tare da tabbatar mata cewa idan maganar Company ce, babu abin da zai hana ta zuwa.
Ta kwantar da kanta a kafaɗarsa, shi kuma ya daura hannunsa a bayanta yana shafawa. Ajiyar zuciya ta riƙa saukowa kamar wacce ta kwana tana kuka.
Sun É—an daÉ—e a haka kafin ta É—ago kaÉ—an tana kallonsa ta ce,
"Thank you, Daddy."
Murmushi ya sarkar mata tare da miƙewa ya bi bayan Ammi.
Daddy na barin falon, su Umar suka zagayeta. suna sake lallashinta.
Aunty Aisha, wacce take tamkar ƴar babbar aminiyar Mammy tun na yaranta, ta ɗan ja tsaki ta tabe baki. Tana jin haushin irin kulawar da mutanen uku nan ke yi wa Mammy wanda ita a ganinta hakan ya yi yawa. Duk wani dan adam yasa ba komai ake nema a samu ba. Amma ban da mammy bata san wannan ba, saboda duk lokacin da ta nuna tana son abu to tabbas sai ta samesa. Shi ya sa ma ba ta cika shiri da Mammy ba. Ba wai don tana da mugun halin ƙi ba, a'a, sangarta da gatanta ne kawai suke yi mata yawa.
"Sorry, Aunty Mammy."
Ajmal, wanda ya zo kusa da ita, ya faÉ—a cikin rawar murya, shi ma kamar zai fashe da kuka.
Ta É—an yi dariya, kamar ba ita ce ta gama kuka ba yanzu. Tana kallonsa ta ce,
"Don't cry, my boy."
Ya gyaÉ—a kai alamar ya ji.
"Grandpa ya ce za ki je Company. Ki je da ni."
Ta gyaÉ—a masa kai tare da murmushi, sannan ta yi hanyar É—akinta.
---
"Bansan mesa ka ke biyewa yarinyar nan ba. Ban san kesa ka biye mata bayan ka san yadda komai ke tafiya a ƙasar nan ba. Me ya sa yau kawai ba za ka hana ta abin da take so ba? Fisabilillahi, me zai kai ta Company?"
Ammi, wacce ke tsaye, ta faɗa cikin murya mai cike da baƙin rai.
wayoyinsa ya ajiye a kan tebur ya ce,
"Na ga Companyn nata ne."
"Idan Companynta ce, ai ga yayanta yana kula da shi ba. Me za ta je ta yi? Mene ne amfanin ta riƙa fita daga gida da sunan zuwa Company? Me take nema? Ni sam ban san mene ne ya dawo da ita ƙasar nan ba ma."
ta ƙarasa maganar a hasale.
"Kinga, Zainab. Da Allah a bar maganar nan. Tun da ta nuna tana son zuwa, shi ke nan, ta je. Allah Ya kiyaye Ya tsare."
Ya ƙarasa maganar tare da wuce ta ta gefenta.
---
Mammy ta gama shirinta na kwanciya barci gaba É—aya. Ta hau kan makeken gadonta mai kyau da tsada da niyyar yin barci.
Sai dai ko kaɗan barcin ya ƙi zuwa. Ba wani dalili ne ya hana ta ba, sai hannunta da ke mata mugun raɗaɗi tun dazu da ta buge shi da jikin dining. Daurewa kawai take yi.
Tashi ta yi zaune, ta kunna fitilar É—akin, sannan ta kalli hannunta da har yanzu ya ke nan a kumbura. Lumshe idanunta ta yi tare da É—aga kanta sama...