BA SO BANE?

Chapter 10

by @hafsatwaziri1122



BA SO BANE.

Story📃 writing
by

Hafsat waziri

Young talent writer's 

•Yota•


Page 10


I Dedicate this book to
 Nanakhadii 💅📕_


Duk lokacin da ta rufe idanunta, babu abin da take gani sai kyakkyawar fuskarsa da fararen idanunsa masu sheƙi. Suna kallonta kamar yanzu abin yake faruwa.

Da sauri ta buÉ—e idanunta tana sauke numfashi, tamkar wacce ta ga wani abin tsoro. Cike da takaici ta ja dogon tsaki, sannan ta murza goshinta.

"Sai na wulaƙanta rayuwarka irin wulaƙancin da ban taɓa yi wa kowa irinsa ba. Sai na sa ka durƙusa a gabana kana roƙon na tausaya wa rayuwarka. Wannan girman kan naka sai ya zama labari. Wannan alkawarina ne."

Ta ƙarasa maganar tare da kashe fitilar ɗakin.

Washegari...

Misalin ƙarfe shida na safe ta fito cikin shiri tsaf. Doguwar rigar less da ta sanya ta fito da kyawunta matuƙa, yayin da siririn gyalen da ta yafa a kanta ya ƙara mata kyau.

A makeken falonsu, ta tarar da kusan dukkan jama'ar gidan suna zaune a dining suna karin kumallo, ban da Fahad wanda ya riga ya fita.

Yaya Umar, da ke zaune yana danna wayarsa, ya É—ago kai yana kallonta. Murmushi ya bayyana a fuskarsa cikin tsananin so ya ce,

"Wow... the CEO of S&S Sardines! Wannan kwalliyar fa sai kace za ki shiga gasar Sarauniyar Kyau."

Murmushi ta yi, ta ƙarasa wajensa ta yi masa side hug.

Daga nan ta juya tana kallon Daddy.

"Good morning, sweet Daddy."

Daddy ya amsa da fara'a.

"Good morning, Mommyn Daddy. Kin tashi lafiya? Ya gajiyar plait?"

"Alhamdulillah, Daddy."

Ta juya ta kalli Ammi ta gefen ido kamar mara gaskiya. A hankali ta ce,

"Good morning, Ammi."

Ammi, wacce ke zuba abinci a plate É—inta, ta sakar mata murmushi, fuskarta a sake tamkar ba da fushi suka rabu daren jiya ba.

"How are you, dear? Ya gajiyar plait?"

"Alhamdulillah."

Daddy ya ja kulolin abinci yana buÉ—e mata su É—aya bayan É—aya, sannan ya ce cikin kulawa,

"Me za ki ci? Na zuba miki, Mommyna."

girgiza kai ta yi tana É—an yatsine fuska.

"No, Daddy. Zan ci idan na isa company."

Kai ya gyada, sannan ya ajiye cokalin hannunsa ya ce,

"Okay. Za ku tafi tare da Japhat da sauran bodyguards. Su ne za su kai ki, su kuma dawo da ke. Sannan duk inda za ki je, za su kasance tare da ke."

Ya yi maganar yana kallonta cike da kulawa.

Nan take fuskarta ta sauya. Ta shagwaɓe fuska tare da tura baki kamar za ta fashe da kuka.

"Please, Daddy. Ni bana son su riƙa bina. Zan iya kula da kaina."

Daddy ya girgiza kai tare da cewa,

"No. Ba ki san garin sosai ba. That is why."

Shiru ta yi tana kallonsa. Ta ji kamar ta faɗa masa tana da driver, amma ta san idan ta faɗa, allura ne zai tono garma, saboda Daddy zai nemi sanin yadda aka yi ta same shi ita da jiya ta dawo. Idan kuma har ya ji abin da ya faru, ko da by mistake ne. matakin da Daddy zai ɗauka ba ƙarami ba ne. Zai iya tarwatsa duniyar da ya shafe rayuwarsa yana ginawa. Ita kuma ba ta son hakan ya faru domin ta fi son ta ɗauki mataki da kanta.

Wannan ne ya sa ta yarda da bodyguards ɗin, amma da wani ƙudiri na daban a ranta.

Larai ce ta fito tare da Ajmal da Afaf cikin shigar da ke nuna su 'ya'yan wasu ne, saboda sun yi matuƙar kyau.

Da suka hango ta, suka yi kanta da gudu.

"Aunty Mommy!"

Suka faÉ—a cikin farin ciki.

 tsugunnawa ta yi cikin farin cikin ganinsu, ta rungume su gaba É—aya tana murmushi.

Ajmal ya É—ago yana kallonta. Cike da zumudi ya ce,

"Aunty Mommy, supermarket za mu je. Ki siya min katon Teddy irin na Afaf, ko?"

Ya ƙarasa maganar yana nuna yarinyar da ke tsaye shiru tana binsu da ido.

Murmushi kawai Mommy ta yi. Tana matuƙar son yaran, sannan akwai shakuwa sosai a tsakaninsu, domin idan suka je hutu a Ingila, ba ta da abokan hira sai su.

Daddy ya miƙe, suka nufi ƙofar fita tare.

Suna fita compound na gidan, suka tarar da wasu ƙattin bodyguards uku a tsaye tamkar mutum-mutumi. Dukkansu dogaye ne, baƙaƙe, majiya ƙarfi. Sun yi shigar baƙaƙen suit, idanunsu kuma a lulluɓe da baƙaƙen gilashi. Fuskokinsu a tamke, kamar ba su taɓa dariya ba. Kallonsu kaɗai ya isa ya sa zuciyar mutum ta rasa nitsuwarta. Suna tsaye cak tamkar masu tsaron shugaban ƙasa.

Daddy ya tsaya yana binsu da kallo tare da bai wa kansa tabbacin cewa za su yi kaca-kaca da duk wanda ya yi ko da tunanin matsowa kusa da inda take.

Ganin Daddy ya fito ya sa duk suka bar inda suke tsaye suka ƙarasa wajensa.

"Japhat, take good care of her. Don't let her go anywhere without you."

Japhat ya É—an sunkuyar da kansa cikin girmamawa ya ce,

"Yes, Sir."

Ya isa gaban ɗaya daga cikin hadaddun motocin dake parker ya buɗe mata ƙofar.



Juyawa ta yi wajen Daddy, ta ƙarasa gabansa tana murmushi. A hankali ta kamo hannunsa, ta sumbaci bayan hannun cikin shagwaɓe ta ce.

"Bye, Daddy. Have a nice day I will miss you."

Shafa kanta Daddy ya yi cike da kulawa, yana murmushi ya ce.

"You too, Mommyna. Allah Ya tsare min ke."

"Ameen."

Daga nan ta juya ba tare da ta sake kallon Japhat ba, ta shiga motar tare da yaran.

Japhat ya rufe musu ƙofar a hankali, kafin shi da sauran bodyguards ɗin suka shiga motocinsu.

Motoci uku ne suka fita motarta ne a tsakiya sauran biyun kuma na su.



10:38 na safe

 kwance ya ke a kan katifarsa, idanunsa a lumshe tamkar wanda bai da niyyar sake tashi. Fuskarsa cike take da gajiya, kamar wanda bai samu barci a daren jiya ba.

Da sauri Adamu ya shigo É—akin cikin kayan aikinsa masu É—auke da tambarin S&S Sardines. Cikin gaggawa yake daidaita necktie É—insa, kafin ya kalli Abdul-Aziz cike da mamaki.

"Wai har yanzu ba ka shirya ba? Karfe goma da rabi fa ya wuce, ana neman sha É—aya. Sai wani kwanciya kake yi kamar ruwa a kogi.



Sannna ma ina ka kwana jiya? Mun jira ka har dare, ba ka dawo ba. Na kira wayarka yafi sau É—ari a kashe. Mun É—auka ko wani abu ya same ka. 


Yanzu ka dawo, maimakon ka shirya mu tafi, sai ka kwanta."

Shiru ɗakin ya yi. Bayan wasu daƙiƙu, Adamu ya kammala saka tie dinsa ya sake cewa,

"Abdul, daga jiya zuwa yau na kasa gane maka. Duk ka sauya, ba kamar yadda kake ba."

A hankali Abdul-Aziz ya É—ago ya kalle shi.

"Me ka gani?"

Adamu ya sauke ajiyar zuciya.

"Kawai gani na yi kamar kana cikin damuwa ko wani abu makamancin haka. Please, kada ka saka damuwar abin da ya faru jiya a Companyn nan a ranka. In sha Allah komai ya wuce."

Ya kallesa tare da sakar masa murmushi.

Daga nan ya miƙe cikin kasala ya nufi banɗaki domin ya shirya. Bayan ɗan lokaci ya fito, fuskarsa a haɗe kamar wanda aka yi wa dole.


Mammy ce zaune a kan kujerar CEO da ke cikin ofishin, sai jujjuya wayar da ke hannunta take yi, tana cika tana batsewa. A gefenta, Oga Fahad ne zaune, sai faman dannawa yake yi a laptop É—insa. A can gefe kuma, Ajmal da Afaf suna ta wasansu.

Ta duba agogo, ya fi a irga. Tun tana irga seconds har ya zama hours.

Tsaki ta ja a hankali, sannan ta ce, "Tabbas yana buƙatar na koya masa hankali tare da maganin girman kansa."

Ta yi shuru taci gaba da zubawa kofar ofishin ido.

Idanunta na kan kofar ta ji anyi knocking.

Ba tare da ya jira an ba shi izinin shiga ba, ya danne kai ya shigo.

Tun da ya shiga ofishin, a kanta ya fara sauke idanunsa, kamar yadda ita ma idanunta ke kansa.

Sanye yake da wando ruwan ƙasa da farar riga. Duk da kasancewar kayan ba masu tsada ba ne, sun masa matuƙar kyau, sun kuma ƙara fito da kyawun surarsa. Gashin kansa a kwance yake luf, duk da ba wani gyara aka yi masa ba.