Chapter 12
BA SO BANE.
Story📃 writing
by
Hafsat waziri
Young talent writer's
•Yota•
Page 12
I Dedicate this book to
Nanakhadii 💅📕
Da sauri ta juyo. Ganin waya a hannunsa yasa ta fahimci abin da yake ƙoƙarin yi.
Cikin É—aga murya ta ce,
"Don't you dare do that, or you'll lose your job."
Ta ƙarasa maganar tare da shigewa cikin motar, ta barsu tsaye a wurin baki a buɗe.
Ya tsaya da wayar a hannunsa, fuskarsa na nuna tsananin tashin hankali.
"Kai kuma, malam, tsayuwar me kake yi a wajen?"
Bai ce komai ba ya gyara Ajmal dake hannun, tare da bin ta gaban su jahpat ya wuce.
Japhat ya bi sa da ido kamar mai son haddace tafiyar sa.
Zagayawa ya yi ya buÉ—e motar, ya saka yaran a ciki, sannan ya shiga ya zauna a mazaunin direba.
Tun da suka fara tafiya bakin Ajmal bai yi shiru ba, sai zuba yake kamar kurna. kuma mafi yawan hirar a kanta ce.
Aunty Mommy kaza... Aunty Mommy kaza...
Har abin da ya faru jiya a dining sai da ya ba shi labari.
Shi dai ya yi shiru, yana jinjina kai.
Jin yaron ya sake É—auko wata hira wacce a ganinta bai kamata direba irinsa ya ji ba.
Yasa ta katse shi cikin wank irin tsawa da ta firgita duk wanda ke cikin motar.
"Kai, dalla yi min shiru! Ko yanzu na fitar da kai ta wannan window!"
Nan take ya shiga rarraɓe idanu kamar zai yi kuka. A tsorace ya ja bakinsa ya yi shiru, domin abu ne da ba a taɓa yi masa ba. Musamman ita, tun da take ba ta taɓa yi musu ihu ba.
Hakan yasa ya ji tsoro sosai, ya lafe cikin kujerar.
Ranta a ɓace ta kalli Abdul, wanda ya ɗauke kansa kamar bai san abin da ke faruwa ba.
Motar ta ɗauki wani irin shiru, tamkar babu masu rai a cikinta. Babu wani sauti da ke tashi sai na injin motar. Ta cikin madubi ta ke ɗan satan kallonsa. Duk lokacin da idanuwansu suka haɗu, sai ta ɓalla masa harara.
Sun yi tafiya mai nisa, amma ta ƙi ta faɗa masa inda za su. Shi kuma ya ƙi ya tambaya, ya ci gaba da tafiya cikin natsuwa. Yadda yake sarrafa steering ɗin motar kamar dama can ya saba, yasa ta ɗan tsira masa ido a kaikaice.
A ranta tana tunanin, ashe a cikin talakawa akwai irin wanda ya fi wasu masu kuÉ—i komai?
Sai ta yamutsa fuska tare da jan siririn tsaki, ta maida hankalinta kan Ajmal da yake har yanzu a tsorace.
Sun yi tafiya mai É—an nisa, sai ta ga ya yi parking a bakin wani makeken supermarket.
Da mugun mamaki ta dago tana kallonsa.
"To, ya aka yi ya san inda za mu? Ko dai maye ne?"
Ta bi sa da kallo har ya zagayo gefen da take, ya buɗe mata ƙofar.
Daga nan ya koma cikin motar, ya zauna tare da rufe ƙofar.
Sai da ta É—auki kusan minti biyar a cikin motar, sannan ta fito.
Cikin da gadara da jin haushin yadda ya shareta ya koma ya zauna ta zagayo side din da yake, da karfi ta shiga yin knocking na gilashin motar kamar zata fasa.
A hankali ya zuge gilashin zaune yake, ya jingina da kujerar motar, idanunsa a lumshe kamar mai barci.
Cikin nuna isa da É—an raini ta ce,
"Yaran da ka bari a waje, wa zai riƙe maka su?"
A hankali ya buÉ—e manyan idanunsa farare tas, waÉ—anda ke cike da barci da rashin son hayaniya. Ya zuba mata ido ba tare da ya motsa ba.
Ta ɗan yatsina fuska kamar wacce ke kallon wani abin ƙyama.
"Ko ni kake so na riƙe maka su ne?"
Nan ma shiru ya yi kamar ba zai amsa ba. Sai can, cikin muryar dake nuna kamar baya jin dadi ya ce,
"A cikin aikina babu rainon yara."
Ya ƙarasa maganar tare da sake jingina bayansa da kujerar motar ya lumshe idanu hankali kwance.
A hasale cikin hargagin da take koya a yanzu ta ce,
"Eh mana! Ka samu mota mai AC, ai dole ka ƙi fitowa."
Ta tura kanta ta cikin windown motar, kamar za ta shige ciki.
"Kai mai tsarona ne. Don haka dole ka fito yanzu. Idan ba haka ba, a bakin aikin waÉ—ancan kazaman..."
Ta ƙarasa maganar tare da bugun jikin motar da ƙarfi.
Ya juya kansa zuwa É—aya gefen, tare da yin murmushi. Wato ta samu abin da zatake masa bazana kenan. Ya sake yin murmushi mai cike da ma'anoni dewa.
Sannan ya ɗago daga kishingiɗar da ya yi. Ya buɗe ƙofar motar ya fito.
Ta ɓalla masa harara tare da miƙa masa jakarta.
Babu musu ya sa hannu ya karɓa.
Wannan ne karo na farko a rayuwarsa da zai riƙe jakar mace. Sai ya rasa yadda zai riƙe ta. Ta ƙasan ido yake bin jama'ar wajen da kallo, yana jin kamar dukansu shi kaɗai suke kallo.
Ba tare da ta bi ta kansa ba, ta yi wucewarta zuwa ciki, yayin da shi da yaran ke biye da ita. Ganin Ajmal ba ya tafiya da sauri ne ya sa ya É—auke shi ya É—ora a kafaÉ—arsa, sannan suka bita zuwa cikin supermarket É—in.
Tafiya take yi cike da izza da takun isa, tamkar supermarket É—in mallakarta ne.
Jama'ar da ke ciki kuwa sai kallonsu suke yi. Duk wanda ya hango su, ganin mata da miji tare da Æ´aÆ´ansu yake musu, saboda yadda sukayi masifar dacewa.
"Wow... very handsome! Wallahi kawata, juyo ki gani."
Wata kyakkyawar budurwa da ke tsaye wajen biyan kuɗi tare da kawarta ta faɗa cikin zumuɗi, tana taɓa hannun kawarta tare da nuna Abdul, wanda shigowarsa kenan.
A hankali kawarta, wacce ke sanye da blue É—in abaya da blue mayafi, ta janye idanunta daga abin da take kallo, sannan ta sauke su a kan kyakkyawar fuskarsa.
Fuskarsa ta ƙurawa ido kamar mai son haddace kamanninsa. Ta ɗauki lokaci sosai tana kallonsa, kamar shi kaɗai ne a wajen.
Ganin yana ƙoƙarin sauke Ajmal daga kafaɗarsa ne ya ankarar da ita. Daga nan ta hangi Afaf da ke riƙe a hannunsa, sannan ta sake kallon Mommy da ke tsaye kusa da shi.
Bakinta ta ɗan taɓe tare da yatsina fuska, kamar wacce ba ta so abin da ta gani ba.
"Eh, ya haÉ—u sosai. But baki ga yana da mata har da yara biyu ba? Kin san dai ni bana harka da irin su, duk kuÉ—i da kyaun su kuwa."
Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta kalli kawarta da ke tsaye.
"Ni kam dai gaskiya ban ga zan iya ƙyale guy ɗin nan ba, Habi. Saboda tun da na gan shi, ya tafi da imanina. Guy ɗin nan ya yi masifar haɗuwa, wallahi! Don haka, ko mata huɗu yake da su, ba zan iya haƙura ba."
Ta ƙarasa maganar tana yarfe hannu kamar wacce ta taɓa wuta.
Cikin takaicin halin maitar kawarta ta ta ce,
"Ke dai Ummul, kin shiga uku da son mazan mutane, wallahi. Wannan ai ya tsufa, me za ki ci a jikin mutum mai mata har da yara biyu? Wannan ai zubar mana mutunci za ki yi."
"Ban gane na shiga uku ba. Wani irin mutunci kuma zan zubar? Ke ai yanzu masu mata sun fi daÉ—in sha'ani. Kuma wallahi, tun da na gan shi, ina so. He must be mine. Ita ma wannan matar ta yi babban kuskure da ta É—auko mijinta ta kawo min shi har inda nake.
Kinga ni, ba wannan ba ma. Ina turarenki nan, ina fatan kin fito da shi. Don ni na bar nawa a gida."
Habi ta sauke ajiyar zuciya cikin takaici, sannan ta ciro wata ƙaramar kwalbar turare daga jakarta ta miƙa mata.
Da sauri Ummul ta karɓa tana shafawa, sannan ta ce,
"Ni, matarsa da yaransa duk ba matsalata ba ne. Baki ji masu iya magana na cewa, duk wanda ya iya allonsa ya wanke ba? Ke dai just wait and see."
"To Allah ya ba ki sa'a, ya saurare ki. Don ni yadda na ga fuskarsa a haÉ—e, kamar wanda aka yi wa zuwan dole, zai yi wahala ya kalle ki ma, bare wani abu ya haÉ—a ku."
Wata ƴar ƙaramar dariya Ummul ta yi.
Tare da yin ƙasa da muryarta,
"Lallai ma kawata, har kin manta wace ce Ummul kenan?"
Ta mayar mata da turaren, sannan ta nufi inda Abdul-Aziz yake tsaye.
Mommy
"Talaka da shi sai shegen girman kain tsiya, ko da me yake taƙama a ƙasar nan?
Mtseew!"
ta faɗa ƙasa-ƙasa, kamar mai tsoron a ji ta,
Sarai ya ji abin da ta faɗa, sai dai ya yi kamar bai ji komai ba. Daga ƙarshe ma, ya zaro wayarsa kirar Tecno daga aljihunsa ya shiga dannawa cikin nutsuwa.
Wata nitsatstsiya tsawa, mai ɗauke da sautin shagwaɓe, ta daka masa saboda takaicin yadda ya share ta.
"Wai kai wani irin mutum ne da ba ka da fahimta ehe? Komai sai an buɗe baki an yi maka bayani? Na juya ina tafiya, sai wani bina kake yi a baya kamar raƙumin da aka kala. Waye kake so ya yi maka siyayya?"
Ta ƙarasa maganar kamar za ta ƙwace wayarsa ta yar.
Sai dai ko gezau bai yi ba, wai an tsikari kakkausa. Sai ma ƙara ba wa wayar hankalinsa da ya yi.
Cikin takunta na izza da yanga ta ƙaraso kusa da inda yake tsaye cikin tsananin fusata, ta ce,
"Malam, da kai nake! Ka tsaya sai kallon Æ´an mata kake yi da ya ke dama abun da ka iya kenan!"
Ta fizge shopping cart ɗin da ke gabanta ta tura masa da ƙarfi, har cart ɗin ya bugi ƙafarsa.
Idanunsa, waÉ—anda suka É—an yi ja, ya lumshe na É—an lokaci, sannan ya buÉ—e su a hankali.